Red Crescent ta Falasdinu ta nemi a yi bincike kan kisan da Isra’ila ta yi wa ma’aikatan agaji
Published: 6th, April 2025 GMT
Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa kan kisan da Isra’ila ta yi wa ma’aikatan agaji a zirin Gaza, bayan da wasu sabbin hujjojin bidiyo suka nuna yadda sojojin Isra’ila suke harbin motocin daukar marasa lafiya.
Bidiyon da ya ci karo da wani nau’in lamarin da sojojin Isra’ila suka yi cewa “an gano wasu motoci marasa da yawa suna tunkarar sojojin Isra’ila ba tare da fitillu ko alamun motocin ambullance na gaggawa ba”.
Shugaban kungiyar agajin ta Falasdinu Younes al-Khatib, ya bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa kan kashe-kashen, yana mai jaddada cewa ba za a iya amincewa da binciken da sojojin Isra’ila ke jagoranta ba.
“Ba mu amince da duk wani binciken da sojojin suka yi ba, kuma wannan ne ya sa muka fito fili a kan cewa muna bukatar bincike mai zaman kansa kan lamarin,” in ji al-Khatib a wani taron manema labarai a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke New York, yayin da yake magana kan harin da ya kashe likitoci da ma’aikatan jin kai 15 a Gaza.
Ya yi Allah wadai da karuwar hare-haren da ake kai wa ma’aikatan jin kai da wuraren aikinsu, yana mai jaddada cewa ana kai hari kan tambarin kungiyar agaji ta Red Crescent, wanda ya kamata a kiyaye a karkashin dokokin kasa da kasa.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: sojojin Isra ila
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu zai gana da Trump kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya
Fadar Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa nan da wasu kwanaki Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gana da takwaransa na Amurka, Donald Trump, domin tattaunawa kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya.
Mai ba wa Shugaba Tinubu shawara na musamman kan yaɗa manufofi, Daniel Bwala, ne ya tabbatar da hakan a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.
Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin SudanA cewar Daniel Bwala, shugabannin biyu — Tinubu da Trump — sun yi tarayya da juna kan fahimta ta haɗin kai wajen yaƙi da ta’addanci da duk wata barazana ga bil’adama.
“A bayan nan Shugaba Trump ya taimaka wajen ba da izinin sayar wa Nijeriya makamai, kuma Shugaba Tinubu ya yi amfani da damar yadda ya kamata wajen yaƙi da ta’addanci, kuma muna da sakamakon da za mu iya nunawa,” in ji Bwala.
Ya ƙara da cewa duk wani saɓanin fahimta kan ko ‘yan ta’adda a Nijeriya na kai hari ne ga Kiristoci kaɗai ko kuma mabiyan addinai daban-daban, “za a tattauna kuma a warware su” a yayin ganawar shugabannin biyu, wadda za ta gudana “ko dai a Fadar Shugaban Kasa ta Abuja, ko a Fadar White House da ke Washington.”
Sanarwar ta zo ne bayan barazanar Shugaba Trump ta kai farmaki a Nijeriya, inda ya umarci Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta Pentagon da ta fara tsara yadda za a kai hari kan ƙasar, saboda abin da ya kira “kisan gillar da ake yi wa Kiristoci” a Nijeriya.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a Truth Social, Trump ya ce Amurka “a shirye take ta turo sojojinta da manyan makamai zuwa Nijeriya don kare Kiristoci,” yana mai cewa idan gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci, Amurka za ta dakatar da dukkan tallafin da take bai wa Nijeriya, kuma “mai yiwuwa ta shiga ƙasar don kawar da ‘yan ta’adda masu zafin kishin Musulunci.”
Barazanar Trump ta jawo cece-kuce bayan ya yi iƙirarin cewa an kashe Kiristoci aƙalla 3,100 a Nijeriya, ba tare da ya bayyana takamaiman inda ya samo waɗannan alƙaluman ba.
Sai dai a martanin da ya mayar, Shugaba Bola Tinubu ya jaddada cewa Nijeriya tana nan daram a matsayin ƙasa mai kiyaye dimokuraɗiyya, wadda kundin tsarin mulkinta ke tabbatar da ‘yancin yin addini da haƙuri tsakanin mabambantan addinai.
“Tun daga shekarar 2023, gwamnatinmu tana gudanar da tattaunawa sosai da shugabannin addinai na Kiristanci da Musulunci, tare da ci gaba da magance matsalolin tsaro da ke shafar jama’a daga addinai da yankuna daban-daban,” in ji Tinubu.