Rasha za ta bude ofishin jakadanci a Nijar nan ba da jimawa ba
Published: 6th, April 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Nijar ya sanar da cewa nan ba da jimawa ba za a Rasha za ta aika tawagar diflomasiyya a Nijar.
Nijar ta tabbatar da aniyar ta na karbar bakuncin ofishin jakadancin Rasha a karon farko cikin sama da shekaru talatin, in ji ministan harkokin wajen kasar ta yammacin Afirka, Bakari Yaou Sangare a ranar Alhamis.
Bayanin ya fito ne yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa a birnin Moscow bayan tattaunawa tsakanin ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov da takwarorinsa na kasashen Nijar, Mali, da Burkina Faso.
M. Sangare ya bayyana cewa, a halin yanzu Nijar na neman wurin da ya dace domin gina ofishin jakadanci na tawagar diflomasiyyar Rasha a kasar, ya kara da cewa Yamai na fatan nan ba da jimawa ba Moscow za ta nada jakada.
‘’Mun rufe ofishin jakadancinmu a Rasha a cikin 1990s, amma daga baya mun gane cewa wannan kuskure ne,” in ji shi.
Lavrov ya tabbatar da cewa kasashen biyu suna kan hanyar dawo da wakilcin diflomasiyya. “A nan gaba kadan, tare da taimakon ku, za mu kammala dukkan ayyukan don dawo da ofishin jakadancinmu.
Kuma tabbas za mu yi hakan a cikin shekarar nan ta 2025,” in ji ministan harkokin wajen Rasha.
A farkon wannan shekara, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta tabbatar da cewa, Moscow na da niyyar bude sabbin ofisoshin jakadanci a kasashen Afirka da dama da suka hada da Nijar, Saliyo, da Sudan ta Kudu.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: harkokin wajen
এছাড়াও পড়ুন:
Wakilin Gidan Talabijin Na Al-Alam Ya Bayyana Yadda Shi Da Iyalansa Suka Rayu Kwanaki Biyu Babu Abinci A Gaza
Mummunar yunwa a Gaza.. Wakilin gidan talabijin na Al-Alam ya bayyana cewa: Shi da iyalansa kwana biyu ba su ci abinci ba
Wakilin gidan talabijin na Al-Alam na kasar Iran ya ruwaito cewa: An samu barkewar yunwa mai tsanani a Gaza, inda ya tabbatar da cewa ya kwashe kwanaki biyu bai ci komai ba.
Basil Khairudden wakilin gidan talabijin na Al-Alam a Gaza, ya ce: “A ranar Juma’a, shi da iyalinsa da daukacin al’ummar Gaza ba su iya samun ko da biredi guda da za su ci ba, sakamakon yunwa da ake fama da ita a Gaza.”
Ya tabbatar da cewa a Gaza akwai mutanen da ba su ci abinci ko da sau daya a tsawon kwanaki uku. A ranar Juma’a mutanen Gaza sun yi ta yawo a kasuwanni, tituna, da unguwanni ba tare da samun kilo guda na gari ba.