Kasashen Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa sun bayyana matukar damuwarsu kan yadda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta sake dawo da yakin kisan kare dangi a zirin Gaza da kuma hare-haren da Amurka ke kaiwa kasar Yemen.

A wata tattaunawa ta wayar tarho a wannan Juma’a, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da takwaransa na UAE  Abdullah bin Zayed Al Nahyan, sun tattauna batutuwan da suka shafi yankin, musamman ma ayyukan wuce gona da iri na Isra’ila a Gaza da kuma hare-haren Amurka a Yemen.

Araghchi ya yi kakkausar suka kan kisan gillar da gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta yi wa daruruwan Falasdinawa  da ba su ji ba ba su gani ba tun daga ranar Talata, yana mai jaddada cewa yin hakan saba yarjejeniyar tsagaita bude wuta ne da aka rattaba hannu a kansa.

Ya kuma yi Allah wadai da hare-haren da sojojin Amurka ke ci gaba da kai wa kasar Yemen, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mata da kananan yara da dama, tare da lalata muhimman ababen more rayuwa na yankin, da kuma jefa mutane cikin kangin talauci da yunwa.

Araghchi ya kara da cewa, laifuffukan da gwamnatin yahudawan sahyoniya ke aikatawa a Gaza da kuma harin da Amurka ta kai kan kasar Yaman na bukatar daukar matakin gaggawa da hadin gwiwa daga kasashen yankin da kum akasashen musulmi, domin dakatar da wannan ta’addanci da ke  ci gaba da kawo rashin tsaro a duk fadin yankin gabas ta tsakiya.

A nasa bangaren, Ministan kasar UAE Abdullah bin Zayed ya bayyana matukar damuwarsa kan tabarbarewar al’amura a yankin, yana mai bayyana lamarin a matsayin abin damuwa matuka.

Ya jaddada bukatar ci gaba da tuntubar juna tsakanin kasashen yankin domin hana ci gaba da tabarbarewar zaman lafiya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa sojojin Isra’ila sun zafafa kai hare-hare ta sama da kuma ta kasa a zirin Gaza tun daga ranar Talata, inda suke  kai hari kan wuraren zaman jama’a da hakan ya hada da wuraren da aka tsugunnar da dubban mutane da suka rasa muhallansu da kuma gidaje, gami da asibitoci, tare da hana duk wasu ayyuka na jin kai ko ceton jama’a ko kai daukin gaggawa.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

An kashe Falasdinawa kusan 30 a wani sabon kisan kiyashin Isra’ila a Gaza

Bayanai daga Falasdinu na cewa akalla Falasdinawa 35 dane  suka hada da kananan yara aka kashe a wanisabon kisan kiyashi na Isra’ila a zirin Gaza.

A cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza, wadannan hare-haren sun yi sanadin mutuwar mutane 35 tare da jikkata 109 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata.

Adadin wadanda sukayi shahada sakamakon yakin kisan kare dangi da Isra’ila ke yi a yankin da aka yi wa kawanya ya zarce 52,400.

Adadin wadanda suka jikkata kuma ya kai kusan 118,014 tun daga watan Oktoban 2023.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta yi gargadin barkewar ayyukan jin kai a Gaza.

Hukumar samar da abinci ta duniya (WFP) ta fitar da wani kakkausan gargadi game da matsalar jin kai da ke kara tabarbarewa a Gaza a dai dai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-haren bama-bamai da kuma killace fararen hula da ke fama da yunwa.

Tun cikin watan Maris ne Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya haramta kai kayan agaji zuwa Gaza, a wani mataki da ya ce na da nufin tursasa Hamas ta amince da tsawaita matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Isra’ila.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Araghchi : Za’ayi Tattaunawar Iran da Amurka ta gaba a Rome bayan taron E3
  • An kashe Falasdinawa kusan 30 a wani sabon kisan kiyashin Isra’ila a Gaza
  • Katafaren Jirgin Daukar Jiragen Yaki Na Kasar Amurka Harry Truman Zai Fice Daga Tekun Maliya
  •  Falasdinawa 40 Sun Yi Shahada A Cikin Sa’oi 24 A Gaza
  • An kashe mafarauta 10 a Adamawa
  • Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kutsa Cikin Quneitra Na Kasar Siriya Tare Da Kafa Shingen Bincike
  • Abubuwan Da Na Gani A Yankin ‘Hero Bay’ Da Ke Cikin Kasar China
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Ci Gaba Da Killace Gaza Da Kashe Mutane, Laifi Ne Da Ba A Taba Yin Irinsa Ba
  • Jiragen Yakin Amurka Sun Kashe Mutane Da Dama A lardin Sa’ada Na Kasar Yemen
  • Uganda Ta Sanar Da Kawo Karshen Ebola Da Ta Barke A Kasar