A Gobe Litinin Za A Yi Atisayen Sojan Ruwa Na Hadin Gwiwa Tsakanin Kasashen Iran, Rasha Da China
Published: 9th, March 2025 GMT
Kamfanin dillancin labarun “ Irna” ya nakalto cewa; Jiragen ruwa na soja da kuma dakarun kare juyin musuluni na Iran za su shiga cikin atisayen na hadin gwiwa da kasashen Rasha da kuma China.
Bugu da kari da akwai wasu kasashen da za su turo sojojin masu sa ido, da su ne; jamhuriyar Azerbaijan, Afirka Ta Kudu, Oman, Khazakistan da Pakistan.
Wannan atisayen dai za a yi ne a sansani na uku na sojan ruwan Iran wanda yake a arewacin tekun Indiya.
Manufar wannan atisayen dai shi ne bunkasa yadda kasashen za su rika aiki tare a tsakanin kasashen sojojin ruwan Iran, Rasha da kuma China.
Wannan dai ba shi ne karon farko da sojojin ruwan kasashen Iran Rasha da kuma China su ka yi atisayen soja na hadin gwiwa ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Da Myanmar Da Thailand Za Su Fatattaki Zambar Da Ake Yi Ta Hanyoyin Sadarwar Waya
Labarin da dan jarida ya samu daga ma’aikatar tsaron jama’a ta kasar Sin a yau Lahadi ya nuna cewa, a kwanan baya kasashen Sin da Myanmar da Thailand sun gudanar da taron ministoci karo na biyu don yaki da laifukan zambar da ake aikatawa ta hanyar sadarwar waya.
A gun taron, sassan da abin ya shafa na kasashen uku sun cimma matsaya kan zurfafa hadin gwiwar tabbatar da doka da oda, kuma za su ci gaba da yin hadin gwiwa wajen dakile laifukan zamba ta hanyar sadarwar waya a Myawaddy da sauran wurare, da kawar da harkokin zamba ta hanyar sadarwar waya gaba daya, da kame dukkan ma’aikatan da ke da alaka da laifin zamba, kana za su yi tsayin daka wajen yaki da dukkan laifuffukan da ke da alaka da zamba.
Bugu da kari, an fahimci cewa, tun daga farkon bana, sassan da abin ya shafa na kasashen Sin da Myanmar da Thailand sun yi hadin gwiwa wajen kaddamar da yaki da ayyukan zamba ta hanyoyin sadarwa a yankin Myawaddy, tare da kamewa da mayar da mutanen Sin sama da 5400 da ke da alaka da zamba zuwa Sin. Ana iya cewa, sun riga sun samu sakamako a bayyane. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp