Tun ranar 4 ga watan nan da muke ciki, Amurka ta fake da batun maganin Fentanyl, da nufin kakabawa Sin karin harajin kwastam na kashi 10% kan kayayyakin kirar kasar Sin da za ta shigar da su kasar Amurka. Game da wannan mummunan mataki mai sabawa ka’idar cinikin duniya da karya lagon tsarin kasuwanci tsakanin kasashen biyu, ba shakka Sin na matukar adawa da shi, kuma ba za ta zura ido ta rungume hannu tana ta kallo kawai ba.

A wannan ranar kuwa, Sin ta mayar da martani, inda da farko ta kai kara a gaban kunigyar cinikin duniya ta WTO kan matakin da Amurka ke dauka, daga baya ta kara kakabawa Amurka harajin kwastam kan wasu kayayyakin da za a shigo da su kasarta, har ma ta shigar da wasu kamfanoni masu ruwa da tsaki cikin jerin sunaye wadanda ba su da aminci a kasar Sin. Jerin matakan da Sin take dauka na mayar da martani sun bayyana niyyar Sin ta kare halastaciyyar moriyarta da kiyaye tsarin cinikin duniya tsakanin mabambantan bangarori, abin da ya zama wajibi kuma ya dace da halin da ake ciki.

To, saboda ganin Amurka tana son nacewa kan batun maganin Fentanyl, ya zama wajibi mu san gaskiya game da batun. Jiya Talata 4 ga watan nan da muke ciki, gwamnatin Sin ta gabatar da takardar bayani kan matakan kayyade maganin Fentanyl ta Sin, inda Sin ta yi bayani kan dimbin ayyuka da take gudanarwa da amfani da fasaha da dabarun da take da shi na kayyade amfani da wannan magani a kasar. Muna iya fahimta daga takardar cewa, Sin daya ce daga cikin kasashen duniya mafi tsauraran manufofi na dakile miyagun kwayoyi da nuna iyakacin kokarin kawar da wannan mummunan aiki tun daga tushe a kasar. A shekarun nan baya, Sin ta amince da matakan da Amurka ke dauka kan batun Fentanyl bisa tunanin jin kai, amma sabanin da fahimtar da Sin take nuna mata, Amurka tana fakewa da wannan batu da nufin matsa mata lamba a bangaren harajin kwastam.

Amurka ba za ta magance matsalar Fentanyl dake dabaibaye kasar ba, sai ta yi shawarwari da bangaren Sin, don daidaita abubuwan dake tsakaninsu. Sin za ta bude kofarta don rungumar shawarwari tsakaninsu, amma idan Amurka tana nufin cimma wata boyayyiyar manufarta ta hanyar yakin harajin kwastam, to Sin za ta mayar da tsattsauran martani ba tare da bata lokaci ba. (Amina Xu)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: harajin kwastam

এছাড়াও পড়ুন:

An Bude Sabon Babin Huldar Sin Da Koriya Ta Kudu

 

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya November 1, 2025 Daga Birnin Sin An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya November 1, 2025 Daga Birnin Sin Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar November 1, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Bude Sabon Babin Huldar Sin Da Koriya Ta Kudu
  • Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka
  • Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza
  • MDD Tana Sa Ido Akan Kashe-kashen Da Ake Yi A Zaben Kasar Tanzania
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini
  • ‘An Kashe Masu Zanga-zanga Akalla 500 a Tanzania’
  • Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan
  • Kofin kofi mafi tsada a duniya ya shiga kasuwa a kan Naira miliyan 1.5m
  • Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda
  • Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa