Hukumar NOA Ta Bukaci Al’umma Su Kara Hakuri Da Kaunar Juna
Published: 2nd, March 2025 GMT
Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa NOA, ta yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi amfani da wannan lokaci na watan Ramadan wajen tunanin abubuwan da za su amfani kasa baki daya.
Kodinetan hukumar na jihar Jigawa Mallam Ahmed Tijjani Ibrahim
ya yi wannan kiran a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Dutse, babban birnin jihar.
Malam Ahmed Tijjani ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi addu’ar zaman lafiya, da tsaro da ci gaban jihar da kasa baki daya.
Ya bayyana watan Ramadan a matsayin wata mai alfarma da ake son musulmi su kara kusanta ga Allah SWT, ta hanyar tsarkake zukatansu.
Don haka Tijjani ya umarce su da su zama ’yan uwan juna, su kasance masu hakuri da kamun kai, da tausaya wa marasa galihu a cikin al’umma.
Ya kara da cewa, NOA za ta bi sahun gwamnatin jihar domin sanya ido da kuma lura da al’amuran da ke gudana a watan Ramadan na wannan shekara domin tabbatar da ganin komi ya tafi yadda ake bukata.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Ramadan
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’ar Jihar Gombe za ta fara sabbin darussa 6 a fannin noma
Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) ta amince da fara karɓar dalibai a sabbin darussa guda shida a fannin noma a Jami’ar Jihar Gombe (GSU) a shekarar karatun 2025/2026.
Za a gudanar da shirye-shiryen ne a sabuwar Tsangayar Noma da aka kafa a garin Malam Sidi da ke Karamar Hukumar Kwami.
A ranar Litinin bayan taron majalisar gudanarwar jihar, Kwamishinan Noma da Kiwo, Barnabas Malle, ya bayyana cewa an amince da fara aikin sabuwar tsangayar aikin nomar ce ranar 21 ga Watan Mayu, 2025.
Sabbin darussan da aka amince da su sun haɗa da digir a bangaren Noma, Digiri a bangaren Gandun Daji da Dabbobin Jeji, Digiri a Kimiyyar Noma da Digiri a Kimiyyar Kasa, sai Digiri a fannin Tattalin Arzikin Noma.
Wani mutum ya mutu yayin raba faɗar ma’aurata ’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a sabon hari a AlkaleriBarnabas Malle ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ware filin gona mai girman hektar 365 a Garin Tafida da ke Karamar Hukumar Yamaltu Deba, domin bincike da aikin gwaji na ɗalibai.
Ya kara da cewa ana kokarin samun ƙarin fili a Garin Kurugu da ke Karamar Hukumar Kwami, don fadada ayyukan kwalejin a nan gaba.
Kwamishinan Ilimi Mai zurfi, Shettima Gadam, ya kuma tabbatar da cewa NUC ta ba da cikakken izini ga jami’ar don fara daukar daliban ne a wadannan darussa daga shekarar karatun 2025/2026.