Shugaba Xi Ya Yaba Da Ci Gaban Kasar Sin Duk Da Kalubalen Da Aka Fuskanta A Shekarar Dragon
Published: 27th, January 2025 GMT
A yau Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar ta samu ci gaba mai inganci wajen zurfafa raya zamanantarwarta a cikin “yanayoyi masu sarkakiya da kalubale” a tsakanin watanni 12 da suka gabata.
Ya furta hakan ne yayin gudanar da wata kasaitacciyar liyafar maraba da sabuwar shekara ta kasar Sin.
Shugaba Xi wanda har ila yau shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (CPC) kuma shugaban kwamitin tsakiya na sojojin kasar ya kara da cewa, “a cikin shekarar dabbar Dragon, mun nuna kuzari da ruhi mai karfi na iya aiwatarwa. Mun jure wa guguwa mai karfi kuma muka ga bakan gizo.”
Shugaba Xi a wajen liyafar, wadda kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin da majalisar gudanarwar kasar suka shirya don bikin shekarar maciji da za ta fara ranar 29 ga Janairu, ya ce, yayin da aka fuskanci yanayi mai sarkakiya da kalubale, kasar Sin ta mayar da martani cikin natsuwa tare da aiwatar da cikakkun matakai daban-daban, ta kuma yi nasarar shawo kan matsalolin, kana ta kara dagewa da kuma nuna azama. (Abdulrazaq Yahuza Jere).
এছাড়াও পড়ুন:
Yanayin Rudani Na Tsawon Kwanaki 100 Kashedi Ne Ga Amurka
A ganin gwamnatin Amurka, manufar ramuwar haraji za ta taimaka wajen farfado da masana’antu a kasar da kara samar da guraben aikin yi, amma yadda ta daidaita matsalolin tattalin arzikinta ba ta hanyar da ta dace ba, da kuma gazawa wajen bin ka’idojin tattalin arziki, ya haifar da damuwa a zukatan al’umma da kuma tsoro a kasuwanni, lamarin da ya sa Amurka ta kara shiga mawuyacin hali.
Cikin kwanaki 100 da suka shude, wasu kasashen duniya sun ki mika wuya ga cin zalin Amurka ta fuskar manufar ramuwar haraji. Misali, kasar Sin ta fara mayar da martani, a kokarin kiyaye halastattun hakkokinta da tsarin tattalin arziki da cinikayya da ma na adalci a duniya. Kana kuma kungiyar tarayyar Turai EU ta zartas da matakan mayar da martani kan Amurka a zagaye na farko. Firaministan kasar Japan Ishiba Shigeru kuma ya bayyana a fili cewa, bai shirya mika wuya don cimma yarjejeniya kan harajin kwastam cikin hanzari ba.
Yanayin rudani da Amurka ke ciki cikin kwanaki 100 da suka gabata ya ilmantar da jama’a cewa, babu wanda zai yi danniya bisa ganin dama. Kuma babu wanda zai hana dunkulewar tattalin arzikin duniya. Hadin gwiwa mai kunshe da kowa da samun moriyar juna da nasara ga ko wane bangare, ita ce hanyar da ta dace. (Tasallah Yuan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp