An tsawaita yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da Lebanon na tsawon kimanin makonni uku bayan da gwamnatin kasar ta ki janye dakarunta kamar yadda aka kulla da farko.

An bayyana cewa yarjejeniyar tsakanin kasashen biyu za ta ci gaba da aiki har zuwa ranar 18 ga Fabrairu, 2025.

Shi ma firaministan kasar Labanon Najib Mikati ya tabbatar da tsawaita wa’adin, yana mai kara da cewa Lebanon za ta mutunta hakan.

Bisa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka sanar tsakanin Isra’ila da Hizbullah a watan Nuwamba, a jiya ne ya kamata sojojin Isra’ila su fice daga kudancin Lebanon.

“Gwamnatin Lebanon ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta har zuwa ranar 18 ga Fabrairu, 2025,” in ji Mikati a cikin wata sanarwa, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.

Duk da haka a ranar Lahadi sojojin Isra’ila sun bude wuta kan al’ummar Lebanon da ke kokarin komawa gidajensu a kudancin kasar, inda suka kashe fararen hula akalla 22 tare da jikkata wasu fiye da 120 na daban.

‘Yan kasar ta Lebanon, sun sha alwashin komawa kauyuka da garuruwansu, duk da barazanar da Isra’ila ke yi.

A karshen mako ne, sojojin Isra’ila suka gargadi al’ummar Lebanon da kada su koma garuruwansu na kudancin kasar.

Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hizbullah a ranar 27 ga watan Nuwamban 2024, bayan ta tafka asara mai yawa a fagen daga da kuma kasa cimma burinta duk da kashe mutane sama da 4,000 a Lebanon.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: yarjejeniyar tsagaita

এছাড়াও পড়ুন:

Hana shigar da abinci da Isra’ila ta yi zuwa Gaza ‘laifi ne na yaki’: MDD

Jami’in kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce matakin da Isra’ila ta dauka na hana agajin abinci ga Falasdinawa da ke fama da yunwa a yankin Zirin Gaza da aka yi wa kawanya ya zama laifin yaki.

“Muna ganin abinci dake jibge a kan iyakoki kuma ba a ba da izinin shigar da shi ba a lokacin da jama’a a gefen iyakar ke fama da yunwa, a yayin da muke jin ministocin Isra’ila suna cewa sun ayin hakan ne don matsa lamba kan al’ummar Gaza,” in ji Mataimakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Tom Fletcher a wata hira a ranar Jumma’a.

Irin wannan na a matsayin laifin yaki ne,” in ji shi.

Baya ga hakan ma a cikin ‘yan kwanakin nan, sojojin Isra’ila sun kashe masu neman agaji da dama a lokacin da suke kokarin isa wurin rarraba kayan agaji a yammacin Rafah a karkashin tsarin Amurka da Isra’ila.

Tuni dai hukumomin agaji na kasa da kasa suka yi gargadin cewa shirin da Isra’ila ke yi na sarrafa rabon kayan agaji a zirin Gaza, ciki har da shawarar da Amurka ke marawa baya, zai kara wahalhalu a yankin Falasdinawa.

A baya-bayan nan ne dai shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ya yi Allah-wadai da sabon salon agajin da Amurka ke marawa baya a Gaza, yana mai cewa “wani cin zarafi” da ke faruwa a can.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kungiyar Hamas Ta Bukaci Masu Shiga Tsakani Amurkawa Su Gamsar da Ita Za’a Dakatar Da Yaki A Gaza
  • Hukumar Shiga Tsakani Za Ta Samar Da Sabbin Damammakin Sulhunta Rikici
  • Jami’ar Jos Ta Samu Lambobin Zinare 14 A Gasar NUSSA, Yayin Da FUT Daura Ta Lashe Kofin Kwallon Kafa
  • Hana shigar da abinci da Isra’ila ta yi zuwa Gaza ‘laifi ne na yaki’: MDD
  • Kudin Shigar Masana’antar Manhajojin Sin Ya Karu Da 10.8% A Watanni Hudu Na Farkon Bana
  • An Yi Bikin Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Kafa Hukumar Shiga Tsakani Ta Kasa Da Kasa A Hong Kong Na Kasar Sin
  • Han Zheng Ya Halarci Bikin Bude Tattaunawa Ta Hudu Kan Musaya Da Koyi Da Juna A Tsakanin Al’ummomi Ta Fannin Wayewar Kansu
  • Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Aiwatar Da Kisan Kiyashi Kan Falasdinawa A Yankin Zirin Gaza
  • Duniyarmu A Yau: Wasikar Lawyoyi 800 Ga Firay Ministan Kasar Burtaniya Kan Gaza
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Kulla Yarjejeniyar Hadin Gwiwa Kasar Indiya Don Habbaka Kiwon Dabbobi