2025-06-16@00:28:29 GMT
إجمالي نتائج البحث: 740
«Abubakar Tafawa Balewa ATBU»:
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Juma’a, ta haramta wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio tattaunawa da manema labarai yayin da ’yar majalisar ta shigar da ƙara a gaban kotu. Mai shari’a Binta Nyako ce ta yanke hukuncin a ranar Juma’a bayan ƙorafin da lauyan da ke...
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinu ta sanar da cewa adadin wadanda su ka yi shahada a cikin sa’o’I 24 da su ka wuce, sun kai 86, yayin da wadanda su ka jikkata kuwa sun kai 287. Asibitocin yankin na Gaza sun karbi wannan adadin na shahidai da kuma wadanda su ka jikkata, suna karbar magani....
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan a zantawarsa tan wayar tarho da yerima mai jiran gadon sarautar kasar Saudiya sannan Firai ministan kasar Muhammad bin Salman ya taya shi murnin salla karama ya kuma yiawa dukkan kasashen musulmi fatan alkhairi. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana cewa, JMI bata neman yaki...
Jakadan kasar Iran a cibiyoyin MDD a kasashen Turai ko Geneva Ali Gahraini ya yi tir da amincewar da hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD ta yi da zargin kasar ta take hakkin bil’adama a taronta na baya-bayan nan abirnin Geveva. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Baraini yana cewa, hukuncin da...
Kasashen duniya na ci gaba da mayar da martini tare da shan alwashin ramuwar gayya game da harajin da shugaban Amurka Donald Trump ya lafta musu kankan kayayyakin da ake shigowa da su kasar. Gwamnatoci da kamfanoni da dama sun sanar da matakan gaggawa na samar da matakan dakile matakin da Amurkan ta dauka kansu....
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Akwai cututtuka da dama da ke yaɗuwa, kuma mafi yawan mutane da ke ɗauke da su, ba su san suna da su ba. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce zaman lafiya, samun abinci da wadata, da rashin damuwa a ƙwaƙwalwa na daga cikin abubuwan da ke tabbatar da lafiyar...
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da nadin Dr. Mohammed Hassan a matsayin Darakta Janar na farko na Hukumar Fasahar Sadarwa da inganta Tattalin Arzikin ta fasahar zamani ta Jihar Jigawa. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar a Dutse. Kafin nadin...
Kungiyar malaman musulmi ta duniya ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana cewa laifuffukan gwamnatin sahyoniyawa a Gaza sun ketare dukkanin iyakokin kasa da kasa, tare da yin kira da a kawo karshen kashe-kashen mata da kananan yara da makamai masu guba, da yunwa, kishirwa, da cututtuka. A cewar jaridar Arabi 21, kungiyar malaman...
Aljeriya ta kira taron gaggawa na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya domin tattauna halin da Falasdinu ke ciki. Bayan karuwar laifuffukan da yahudawan sahyoniyawa da suke aikatawa a kisan gillar da suke yiwa Palastinawa a yankin zirin Gaza da kuma ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri da sojojin yahudawan sahyoniya suka...
Masu ababen hawa da dama sun maƙale a gadar Namne da ta rufta daura da hanyar Jalingo zuwa Wukari a Ƙaramar hukumar Gassol ta Jihar Taraba sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a da aka yi ranar Laraba. Ruwan sama ya kawar da gadar da aka gina ta wucin gadi a hanyar da aka...
Gwamna Umar Namadi ya amince da naɗin Dr. Jummai Ali Kazaure a matsayin sabuwar shugabar Kwalejin Ilimi, Shari’a da Nazarin Addinin Musulunci (JSCILS) da ke Ringim. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar. A cewarsa, kafin wannan naɗi, Dr. Jummai ta kasance malama a...
“A yau ne Gwamna Dauda Lawal ya fara rangaɗin wuraren haƙar ma’adanai da masana’antu, inda ya fara ziyarar aiki a wani kamfani mai zaman kansa na Comet Star Industry da ke Ƙaramar Hukumar Anka. “Ma’aikatar, mallakin Prince James Uduji OON, tana sarrafa kusan tan 1,000 a kullum. Tana da cikakkun kayan aiki da sabbin...
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa sojojin kasar na karbe iko da wasu yankunan zirin Gaza, a wani mataki na kara matsin lamba kan kungiyar Hamas domin tilasta ta sakin mutanen da ta ke garkuwa da su. “Muna karbe zirin Gaza tare da kara matsin lamba mataki-mataki domin tilasta su mayar da mutanen da...
Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya nanata shirin Tehran na shiga tattaunawar da Amurka kan shirinta na nukiliya na zaman lafiya, yana mai gargadin cewa barazanar soji daga Amurka na dagula halin da ake ciki a yanzu. “Jamhuriyar Musulunci, kamar yadda ta kasance a baya, a shirye take don yin shawarwari na hakika,” in...
Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, ya bayyana a yau Talata cewa, al’ummar Sinawa da ’yan kasar Rasha sun ba da gudummawa gaya wajen samun nasarar yakin duniya na biyu. A wata hira da ya yi da rukunin gidajen rediyo da talabijin mallakin kasar Rasha wato Russia Today a yau a birnin Moscow, Wang...
Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, a ranar Talata ya yaba wa Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano bisa bayar da fifiko akan ilimi, kiwon lafiya, noma, da tsaro a jihar. Sarki Sanusi II ya bayyana jin dadinsa ne a lokacin da ya kai gaisuwar Sallah ga gwamnan Kano, kamar yadda aka saba gudanarwa...
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi baƙuncin Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, a fadar gwamnatin jihar. Sarkin dai ya kai wa gwamnan ziyarar ce kamar yadda aka saba a Hawan Nassarawa da ake gudanarwa bisa al’ada duk shekara. Gangamin da zan yi a mazaɓata babu fashi — Natasha Muna kiran Natasha ta...
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi baƙuncin Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, a fadar gwamnatin jihar. Sarkin dai ya kai wa gwamnan ziyarar ce kamar yadda aka saba a Hawan Nassarawa da ake gudanarwa bisa al’ada duk shekara. Sai dai a sakamakon haramcin gudanar da haye-hayen sallah da rundunar ’yan sandan jihar...
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma, Dakta Abdul’aziz Yari, ya yi kira ga ‘yan siyasa da masu hannu da shuni da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu na alheri fiye da watan Ramadan. Da yake zantawa da manema labarai a mahaifarsa Talatan Mafara, a wani bangare na...
Game da aka yi wa mafarauta 16 a Udune Efandion, karamar hukumar Uromi ta jihar Edo, gwamna Monday Okpebholo ya yi kakkausar suka ga wannan aika-aika na rashin hankali, yana mai bayyana hakan a matsayin “wani abu da kuma muguwar dabi’a. Okpebholo, tare da Gwamna Abdullahi Yusuf na Jihar Kano, sun yi addu’a...
Jami’ar Bayero Kano (BUK) ta kaddamar da wani tsari na yanar gizo wanda zai baiwa dalibai damar shiga da duba sakamakon kammala karatunsu ta hanyar lambobi. Wannan sabon yunkuri shine karo na farko da cibiyar ta samar da sakamako ta hanyar irin wannan dandali. An sanar da shirin ne a cikin wata takarda...
Masarautar Zazzau ta sanar da soke Hawa Bariki a wannan sallar ta bana — daya daga cikin haye-hayen shagulgulan Sallah na al’ada da masarautar ke gudanarwa a washegarin idin karamar Sallah. A bisa al’adar Hawan Bariki, Sarkin Zazzau ya kan kai wa Gwamna gaisuwar sallah tare da duk hakimansa yayin da mazauna za su yi...

Iran Ta Ce Tattaunawa Da Amurka Tare Da Mai Shiga Tsakani Na Gaba, Ya Danganci Matakan Da Ta Dauka Kan Iran
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa gwamnatin JMI ta yi watsi da tattaunawa kai tsaye dangane da shirinta na makamashin Nukliya, sannan ya kara da cewa amma tattaunawa tare da masu shiga tsakani a bude take. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana cewa tuni, mun bawa gwamnatin Amurka...
Asbitin ‘Mount Sinai’ (Dotsen Sinaa’ a kasar Amurka ta salami wata likita daga aiki, bayan da aika da wani rubutu da hoto a shafukan yanar gizo tana, wanda Asbitin tana cewa ai Musanta hare-haren ranar 7th ga watan Octoba ne’. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta bayyana cewa Dr Leila Abbasi,diyar shekara 46...
Hukumar Ƴansandan Jihar Kano ta kama wani matashi mai shekaru 20, Usman Sagiru, bisa zargin kashe wani ɗan Bijilanti a tawagar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II bayan Sallar Eid. Iftila’in ya faru ne da ƙarfe 12:40 na rana a Lahadi, lokacin da ayarin Sarkin Kano ke watsewa daga filin Sallar Idin. A cewar kakakin Ƴansanda...
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa, Iran ba ta shiga tattaunawa da Amurka kai tsaye ba, yana mai mayar da martini kan wasikar da shugaban Amurka ya aike mata, amma kuma ya bayyana cewa hakan zai bude kofa ga tattaunawar kai tsaye. Da yake magana a wani taron majalisar ministocin a ranar Lahadi, Pezeshkian...
Shugaban majalisar mulkin kasar Sudan kuma kwamandan Sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan ya tabbatar da cewa, farin cikin samun nasara a Sudan ba zai cika ba har sai an kawar da tungar karshe ta mayakan RSF a kasar, yana mai jaddada cewa kasar ba za ta ja da baya ba har sai an murkushe wadannan...
Ya ce: “Ya ‘yan uwa Musulmi na Jihar Zamfara da ma sauran wurare, ina miƙa saƙon barka da Sallah tare da taya mu murnar kammala azumin shekarar Hijira ta 1446, wannan wata mai alfarma ta kasance lokaci na sadaukarwa ga Allah (SWT). “Yayin da muke gudanar da bukukuwan Ƙaramar Sallah, ina kira ga kowannenmu...
Bugu da kari, tawagar za ta gana da shugabannin al’ummar Hausawa na jihar domin tattauna lamarin tare da bayar da shawarwarin da suka dace. Sanarwar ta bukaci ‘yan jihar da su kwantar da hankalinsu tare da kaucewa duk wani abu da zai iya haifar da tarzoma, tare da tabbatar wa jama’a cewa, ana daukar...
Kungiyar Hamasa a gaza ta bada sanarwan cewa ta amince da shawarar da kasashen da suke shiga tskaninta da HKI kan cewa ta amince da kafa gwamnatin hadin kan Falasdinawa, amma ba zata taba mika makamanta ga wani ba ko waye shi. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban Kungiyar Khalil Al-Hayya...
A kasar Jordan gwamnatin kasar ta bada sanarwan cewa a gobe Litinin ce za’a gudanar da bukukuwan sallah karama bayan azumun watan Ramadan na kwanaki 30. Muftin kasar ta Jordan Ahmed Hasanat a lokacinda yake bada sanarwan a jiya Asabar yace, ranar Litinin 31 ga watan Maris, ita ce ranar Sallah daya ga watan shawwal...
Shahararren masanin tarihin nan na Jihar Kano, Ibrahim Ado Kurawa, ya bayyana cewa soke hawan Sallah da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya yi tamkar wani wasan kwaikwayo ne. A makon jiya ne dai Sarki Aminu Ado ya sanar da janye hawan Sallar da ya ce zai jagoranta kan abin da ya kira...
Wadanda suka rasa ‘yan uwa ko suka jikkata sakamakon fashewar tankar mai da ta afku a Majia, Jihar Jigawa, a bara, za su karɓi Naira miliyan huɗu kowanne domin rage radadin halin da suka tsinci kansu a ciki. Gwamna Umar Namadi ne ya bayyana haka a lokacin da aka fara rabon kuɗin tallafin ga waɗanda...
Kungiyar JIBWIS a Karamar Hukumar Giwa ta bukaci al’ummar Yakawada da su ci gaba da rungumar koyarwar Al-Qur’ani a rayuwarsu ta yau da kullum. Mataimakin Shugaban kungiyar, Malam Ibrahim Mustafa Shatiman Giwa, ya yi wannan kira ne yayin bikin rufe Tafsirin Ramadan na bana da aka gudanar a Masallacin JIBWIS da ke Yakawada. Malam...
Wani babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khaminae shawara kan harkokin tsaro ya bayyana cewa hare-haren ‘WaaduSsadik na III’ don maida martani kan HKI saboda hare-haren da ta kaiwa Iran a shekarar da ta gabata suna kan hanya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Manjo Janar...

Wani Jami’in Leken Asirin HKI Ya Bukaci Kasashen Afirka Su Taimaka Su Karmi Falasdinawan Da Za;a Kora Daga Gaza
Gwamnatin HKI ta bukaci hukumar hukumar ayyukan leken asiri na kasar MOSAD ta nemi kasashe musamman a nahiyar Afirka wadanda zasu amince su karbi Falasdinawan da za’a kora daga Gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyoyin HKI na cewa Firai ministan kasar Benyamin Natanyahu yana neman wata kasa ko kasashen nesa...
Wannan hanya, na matukar taimakawa sosai wajen sarrafa sinadarin insulin a jikin mutum. 2-Maganin Hawan Jini (Hypertension) Ganyen mangwaro na rage matsin jini, sannan kuma yana karfafa jijiyoyin jini. Saboda haka, a nan sai a nemi sabbin ganyen mangwaro, a tafasa su sosai a tace, sannan a sha rabin kofi da safe da kuma...
Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta haramta gudanar da bukukuwan hawan sallah da aka saba yi na al’ada a faɗin Jihar Kano. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori ya fitar a wani taron manema labarai da ya gudana a hedikwatar rundunar da ke Bompai a wannan Juma’ar....
“Jami’an ‘yansanda da ke ofishin ‘yansanda, Mayo Belwa, sun isa wurin, inda nan take suka garzaya da wanda abin ya shafa zuwa asibitin Cottage, Mayo-Belwa, domin kokarin ceton ransa, amma abin takaici, an tabbatar da mutuwarsa a lokacin da ya ke karvar magani.” Kakakin rundunar ‘yansandan ya ce, ya yi saurin shiga tsakanin wanda ake...

Iran Ta Bada Amsa Ga Wasikar Shugaban Kasar Amurka Ta Gayyatar Kasar Zuwa Tattaunawa Kan Shirinta Na Makamashin Nukliya
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin kasar ta Mayarwa Shugaban kasar Amurka Donal Trump amsar wasikarsa ga kasar danagne da shirinta na makashain Nulkiya ta hanyar kasar Omman. Aragchi ya bayyana haka a jiya Alhamis a lokacinda yake hira da kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran. Ya kuma kara...

Kasar Sin Na Adawa Da Kara Yawan Kamfanoninta Cikin Jerin Wadanda Amurka Ta Takaita Fitar Da Kayayyakinsu
Mai magana da yawun ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya bayyana cewa, kasar tana matukar adawa da yunkurin Amurka na kara yawan dozin-dozin na kamfanoninta a cikin jerin kamfanonin da aka takaita fitar da kayayyakinsu zuwa kasashen waje. Jami’in, wanda ya bayyana haka a ranar Larabar nan, ya ce, matakin na Amurka ba komai ba...
Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya sanar da soke bukukuwan Sallah na bana, saboda bukatar tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar. A wata sanarwa da aka fitar, Sarkin ya bayyana takaicinsa kan matakin amma ya jaddada cewa, tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi shi ne babban abin da ya sa a...
Jiniyar gargadi ta kada a cikin sassa masu yawa na Falasdinu dake karkashin mamaya bayan harbo makami mai linzami da mutanen Yemen su ka yi. Kafafen watsa labarun HKI sun ce, jiniyar gargadin ta kada a cikin garuruwa 255 a HKI daga cikin har da birnin Kudus. Jaridar “Yediot Ahronot” ta buga labarin dake cewa,...
A Isra’ila dubban masu zanga-zanga ne suka taru a Tel Aviv domin nuna adawa da mulkin firaministan kasar Benjamin Netanyahu. Masu zanga zangar sun kuma bukaci a tsagaita bude wuta da kuma sako fursunonin da ake tsare da su a Gaza. Sun rike alluna masu dauke da hotunan wadanda ake tsare da su a Gaza...

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin da Talata a matsayin hutun sallaGwamnati Ta Ayyana 31 Ga Maris Da 1 Ga Afrilu A Matsayin Ranakun Hutu Don Bukin Eid-el-Fitr Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin, 31 ga Maris, da Talata, 1 ga Afrilu, a matsayin ranakun hu
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 31 ga watan Maris, da Talata, 1 ga watan Afrilu, a matsayin ranakun hutun ƙaramar salla. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da sakataren ma’aikatar, Magdalene Ajani, ya fitar a ranar Laraba. Ahmad Lawan ya raba tallafin N27m da buhun shinkafa 300...
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya bayar da gudummawar Naira miliyan 27 da buhunan shinkafa 300 ga mutanen da gobara ta shafa a ƙananan hukumomi uku da ke mazaɓarsa a Jihar Yobe. Ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Machina, Nguru, da Yusufari. An kama mutum 3 kan zargin sata da...

Sojojin Sudan Sun Kwace Wuri Na Karshe Da Yake A Hannun “Rundunar Kai Daukin Gaggawa” A Cikin Birnin Khartum
Rundunar sojan Sudan ta sanar da shimfida ikonta akan filin saukar jiragen sama na Khartum wanda shi ne tunga ta karshe da ta saura a hannun rundunar kai daukin gaggawa. Kwamandan rundunar sojan Sudan da take fada a birnin na Khartum Lafatnar kasar Abdurrahman al-Bilawi ne ya sanar da cewa, an shimfida iko a cikn...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhummanci a makon da ya gabata, dangane da siyasa tattalin arziki zamantake tsaro da sauran, sannan mu yi masu karin bayani daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su....
Kwamitin tallafawa marayu da masu karamin karfi na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Ikamatis Sunnah dake karamar hukumar Babura ta jihar Jigawa ya tallafawa gidajen marayu da masu karamin karfi da kayan abinci na kusan naira miliyan 9. Shugaban kungiyar Sheikh Hassan Sabo Musa ya bayyana hakan yayin rabon kayan da aka gudanar a...
Bayan gazawar tattaunawar da hukumar ta IAEA ta yi da Tehran, babban daraktan hukumar Rafael Grossi ya jaddada muhimmancin komawa kan teburin shawarwari nan gaba don tabbatar da cewa Iran ba ta mallaki makamin nukiliya ba. Hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ta ce tattaunawar da ta yi da wani babban jami’in...