2025-08-01@08:07:03 GMT
إجمالي نتائج البحث: 924

«Abubakar Tafawa Balewa ATBU»:

    A bisa jagorancin Alhaji Mustapha Junaid, iyalan mamacin, da suka haɗa da matan sa da ‘ya’ya da jikokin sa, sun tarbi tawagar, kuma sun yi masu godiya. Minista Badaru ya miƙa saƙon ta’aziyya daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana cewa, “Rasuwar Baba Aminu ta taɓa Shugaba Tinubu matuƙa. Yana addu’ar Allah ya yi masa...
    Kasar Sin ta kawo karshen aikin bayar da agajin gaggawa mafi girma a gundumar Rongjiang da ke lardin Guizhou, a yankin kudu maso yammacin kasar da misalin karfe 10 na safiyar ranar Lahadi, yayin da aka kammala ruwan saman da aka tafka kamar da bakin kwarya kamar yadda mahukuntan yankin suka bayyana. Lardin Guizhou da...
    Ya ce a tare da shi a cikin tawagar, akwai Ministan shari’a, Antoni-janar na tarayya, Yarima Lateef Fagbemi, SAN; Ministan yaɗa labarai, Alhaji Mohammed Idris, da ƙaramin Minista a ma’aikatar gidaje, Hon. Yusuf Abdullahi Ata. Tawagar ta kuma haɗa da wasu manyan Malamai, waɗanda suka ƙunshi, Dr Bashir Aliyu Umar, Sheikh Aminu Ibrahim...
    Tawagar Sarki Muhammadu Sanui II da  Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da Gwamnan Jigawa Umar Namadi sun sauka a Madina domin halartar jana’izar Alhaji Aminu Dantata.
      Da yake jawabi jim kadan kafin tashinsa a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, Gwamna Yusuf ya bayyana marigayi Dantata a matsayin uba ga mutane da yawa, wanda karamcinsa da sadaukarwarsa ya wuce iyaka.   Gwamnan ya jaddada cewa, zuwan tawagar a Madina shaida ce ta matukar mutuntawa da jama’a da gwamnatin jihar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wannan ne ma dalilin da yasa wasu ke ganin hadakar za ta iya yin karfi kwarai da gaske, kasancewar ta samu wakilci a sassa daban-daban na wannan kasa. Dalili kuwa shi ne, ‘yansiyasa ne da a baya suka samu damar rike manya-mnyan mukamai, sannan kuma har zuwa yanzu yana da tasiri a fagen siyasar kasar...
    Masu bincike sun gano cewa sojojin HKI sun kashe Falasdinawa akalla 100,000 tun bayan fara yakin tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekara 2023. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kan cewa farfesa Michael Spagat da kuma Khalil Shikaki  Bafalasdine masanin masanin fasahar siyasa a Jami’ar London na kasar Burtania...
    Wasu daga cikin jami’an sojojin HKI sun yi furuci da cewa, an ba su umarni ne da su rika bude wuta akan Fararen hula Falasdinawa da suke zuwa cibiyoyin karbar kayan agaji, suna jaddada cewa, wadanda su ka kashe din ba su yin wata barazna a gare su. Jaridar “Haarezt” ta ‘yan sahayoniya ta buga...
    Tashar talabijin din Aljazira ta bayar da rahoton da yake cewa; Rashin abinci mai gina jiki da karewar madarar jarirai a yankin Gaza, ya sa jarirai biyu sun yi shahada. Majiyar asibitin Nasar ta a  birnin Khan –Yunus dake kudancin Gaza, ta ambaci cewa jariran biyu sun rasa ransu ne saboda rashin abinci mai gina...
    Hukumar samar da bunkasa da hadin gwiwar kasa da kasa ta kasar Sin ta gabatar da taron manema labarai a yau Juma’a, inda aka yi karin haske game da yadda Sin take baiwa kasashen Afirka tallafi da samun bunkasa tare da su cikin hadin gwiwa. An ce, ya zuwa yanzu, Sin tana taimakawa kasashen Afirka...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ban da haka kuma, wani babban dalilin da ya sa kasar Sin ke kokarin tallafa wa sauran kasashe a fannin aikin likitanci, shi ne akidarta ta “kafa al’ummar duniya mai kyakkyawar makoma ta bai-daya”. A cikin gidan kasar, an yi nasarar kawar da talauci, da kokarin neman wadatar da dukkan al’ummun kasar, lamarin da ya...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Benuwe, sun kama mutum biyar da ake zargi da hannu a kisan wasu matasa biyu ’yan asalin Jihar Kano. Waɗanda aka kashe sun haɗa da Jamilu Ahmad da Barhama Suleiman, kuma an kai musu hari ne cikin daren ranar Litinin a unguwar Agan, kusa da ƙofar shiga Makurdi. Gwamnatin Neja ta...
    Dan wasan mai shekaru 40 ya zura kwallaye 93 sannan ya taimaka wajen zura 19 a wasanni 105 da ya buga a dukkanin wasannin da ya buga a kungiyar ta Saudiyya, amma har yanzu bai samu nasarar lashe kofi a gasar ba, a kakar wasan da aka kammala kwanan nan, Al Nassr ta kare a...
    Tun da farko, Gwamna Aliyu ya ce, gwamnatinsa ta bullo da shirin ne domin ta saukaka farashi da kashi 20 ta hanyar saukar da farashin kayan abinci kasa warwas. Gwamnan ya ce, an tsara shrin ne domin saukakawa ma’aikatan jiha, na kananan hukumomi da masu karbar fansho ta hanyar samar da nau’ukan kayan abinci...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce wakilan ƙasarsa za su gana da na Iran domin ci gaba da tattaunawa kan makaman nukiliyarta a mako mai zuwa. “Za mu tattauna da Iran a mako mai zuwa, ƙila mu ƙulla yarjejeniya ko kuma akasin haka, ba na ce ba,” in ji shi yayin jawabinsa a taron ƙasashe...
    Sanarwar ta ƙara da cewa, aikin Sahara ba wai kawai aikin jaridar bogi ba ne; ya samo asali ne zuwa da suna ‘Gonzo’, wanda ke da alaƙa da ƙarairayi wajen bayar da rahoto.   Sanarwar ta ci gaba da cewa: “An ja hankalinmu kan labaran ƙarya da Sahara Reporters ke yaɗawa, shafin da ya shahara...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya bayyana matukar damuwar da Sin ke da ita dangane yanayin da yankin Gabas ta Tsakiya ke ciki, tare da bayyana fatan ganin an tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da Iran nan bada jimawa ba. Guo Jiakun ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai na yau...
    Mataimakin shugaban majalisar dattijai, Jibrin Barau, ne ya sanar da kudirin bayan amincewa da rahoton kwamitin majalisar dattawa kan samar da kayayyaki.   Adeola ya ce, karin wa’adin ya zama dole domin baiwa gwamnatin tarayya damar kammala wasu manyan ayyuka da suka samu jinkiri sakamakon karancin kudaden shiga. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
    Iyalan mafarauta 16 ’yan Jihar Kano da aka yi wa kisan gilla a garin Uromi da ke Jihar Edo sun yi zargin cewa gwamnati ta yi watsi da su. Wasu daga cikin waɗanda suka tsallake rijiya da baya a harin da kuma iyalan waɗanda aka kashe, sun bayyana cewa alƙawarin kuɗin magani da tallafi da...
    2. Gyaran zaɓe da shari’o’in zaɓe 3. Ƙirƙirar sabbin jihohi 4. Samar da Ƴansandan jihohi 5. Haɗa kai don gudanar da mulki Daga cikin muhimman shawarwari, akwai na kafa hukumar zaɓen ƙananan hukumomi (NALGEC), ƙara kujeru ga mata a majalisu, da ba wa ‘yan Nijeriya dake ƙasashen waje damar yin zaɓe. Hakanan, akwai shawarwarin sauya...
    Ya nanata cewa nasarar da aka samu ya zuwa yanzu ta samo asali ne sakamakon kyawawan tsare-tsare, ingantaccen jagoranci, da kuma kula da albarkatu.   Gwamnan ya bayyana cewa an samu ci gaba sosai a harkar tsaro a jihar idan aka kwatanta da abin da ya gada a shekarar 2023.   A cewar sa, inganta...
    Aƙalla mutum biyar ne aka tabbatar da rasuwarsu, yayin da wasu 15 suka jikkata sakamakon fashewar wani bam a Jihar Kano. Aminiya ta gano yadda fashewar bam ɗin ya haddasa firgici a yankin da lamarin ya faru, inda jami’an tsaro da na agajin gaggawa suka garzaya wajen don kai ɗauki. An yi wa ma’aikatan ƙananan...
    Idris, wanda shi ne ya jagoranci zaman, ya bayyana irin nasarorin da aka samu a ƙarƙashin jagorancin Babban Hafsan Tsaro da sauran Hafsoshin Sojin a matsayin mai tabbataccen tasiri da gamsasshen sakamako.   Ya ce: “Abin da muka gani ba wai kawai daƙile waɗannan barazanar ba ne, sai dai ma sake karɓe sararin ƙasar mu,...
    Kwamitin kasa mai lura da kasuwancin Amurka da Sin ko USCBC, ya gudanar da liyafar murna ta shekarar 2025, a ranar Laraba 18 ga wata a birnin Washington na Amurka, liyafar da jakadan kasar Sin a Amurka Xie Feng ya halarta tare da gabatar da jawabi. Cikin jawabin nasa jakada Xie ya ce cimma moriya...
    Barcelona ta amince da yarjejeniyar ɗaukar ɗan wasan gaba na ƙungiyar Athletic Bilbao Nico Williams, amma kuma har yanzu akwai ƙalubalen da zasu fuskanta kafin ɗan wasan ya samu damar rattaba hannu a ƙungiyar ta Catalonia, ɗan wasan na ƙasar Sifaniya Williams, wanda ya zura ƙwallaye 31 a wasanni 167 da ya buga wa Bilbao,...
    Brig.-Gen. Abu-Mawashi ya kara da cewa an kama ‘yan ta’adda 14,138 da sauran masu aikata laifuka yayin da aka ceto mutane 5,365 a cikin wannan lokaci.   Abu-Mawashi ya ci gaba da cewa, sojojin sun kwato daruruwan makamai da kuma harsashi da yawa duk acikin wannan lokaci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce matsalar da ke addabar jam’iyyar PDP ba ta tsaya kan Atiku Abubakar kaɗai ba, face tana da nasaba da girman kai tsakanin shugabannin jam’iyyar. Da yake magana da manema labarai a ranar Laraba, Gwamna Lawal ya ce: “Kowa yana da nasa matsalar; ba kan Atiku Abubakar kawai ba...
    Ya ce duk da cewa akwai damuwa kan yadda za a aiwatar da hakan, Gwamnatin Tarayya na da damar tsara ƙa’idoji da dokoki na musamman ga kowace jiha don hana amfani da ‘yansandan wajen cin zarafi. A halin yanzu, gwamnonin jihohi daga faɗin Nijeriya na gudanar da wani taron gaggawa a Babban Birnin Tarayya, wanda...
    A yayin ƙaddamar da asibitin ƙwararrun, tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya buƙaci gwamna Lawal da ya ci gaba da gudanar da ayyukan ceto har sai Zamfara ta kasance ɗaya daga cikin manyan jihohin Nijeriya.   Tsohon shugaban ƙasar ya ce: “A yau ina jihar Zamfara ne domin na ga ingantacciya, wadda ta ci gaba,...
    Alhazai 442 sun tsallake rijiya da baya, bayan jirgin da ya ɗauko su bayan sun kammala aikin Hajjin bana ya samu sakon cewa an dasa bom a cikinsa a yayin da yake sararin samaniya a ƙasa Indonesiya. A ranar Talata ne jirgin, mallakin kamfanin Saudia Air, ya yi saukar gaggawa a birnin Jakarta babban birnin...
    Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump ya ce yana neman ganin an kawo karshen rikicin nukiliyar ƙasar Iran gaba ɗaya, a yayin da aka shiga kwana na biyar a yaƙin da ya ɓarke tsakanin Iran da Isra’ila.  Trump ya bayyana shirinsa na tura manyan jami’an ƙasarsa zuwa birnin Tehran domin tattaunawa da hukumomin Iran a game...
    Ministan harkokin wajen kasar Rwanda Olivier Nduhungirehe ya bayyana cewa, kwakkwaran zumunci da ake sadawa a aikace a tsakanin Rwanda da kasar Sin na yin tasiri mai kyau ga al’ummar Rwanda. A cikin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, yayin bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya na Sin da Afirka karo na...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa: Babu wata tattaunawa da zata yi da Amurka a halin da take ciki na kare kanta A yayin da haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare kan yankunan kasar Iran, a hukumance Iran ta bayyana rashin yiwuwar ci gaba da zaman tattaunawa da Amurka kan batun...
    Ministan harkokin wajen Omani Badr Albusaidi ya sanar da cewa, ba za a gudanar da zagaye na shida na tattaunawar nukiliya tsakanin Iran da Amurka ba. Yau Lahadi ne aka shirya gudanar da zagaye na gaba na shawarwari a Muscat babban birnin kasar Oman. A cikin wani sakon da ya wallafa a kan X (tsohon...
    A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta fitar, ta yi tir da harin na Isra’ila akan Iran tare da bayyana cewa, ya haifar da rikici a tsakanin bangarorin biyu da kuma musayar harba makamai masu linzami. Gwamnatin ta Najeriya ta nuna bakin cikinta akan abinda ya faru, tare da kuma da yin kiran...
    Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci wanda ya tattauna ta wayar tarho da jami’ar harkokin waje ta tarayyar turai ya bayyana cewa, ci gaba da tattaunawa a tsakanin Iran da Amurka ba shi da wata ma’ana, kamata ya yi jami’an tarayyar turai din su yi Allawadai da wuce gona da irin HKI...
    Ba tare da saninmu ba, yawancin al’ummar Afirka musamman ma naYammacin Afirka suna fama da abinda ake kira da suna irin hali ko yanayin da aka shiga sanadiyar lamarin cinikin Bayi.Bayan shekara 100 da aka yi daga shekarar 1801 zuwa 1901, an yi wani kokarin da ake yi ma kallon tamkar wani takune na yadda...
    Jami’in kungiyar Hamas ya bayyana cewa: Kakkausan martanin da Iran ta mayar ya tabbatar da cewa babu mai girman kai da ba zai fuskanci mayar da martani ba Izzat al-Rishq mamba na ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya jaddada cewa: Kakkausan martanin da Iraniyawa suka mayar ya tabbatar da cewa; babu mai...
    Bayan hakan, Pogba ya kunce kwantiraginsa da Juventus a watan Nuwamban 2024, kuma tun watan Maris da ya gabata ya samu damar komawa fili domin shirya dawowarsa. Yanzu haka yana ci gaba da atisaye tare da fatan ƙulla sabuwar yarjejeniya da Monaco domin ci gaba da taka leda a ƙasarsa ta haihuwa. Daga kanmu,...
    A cewar Bawa, gwamnatocin da a karkashinsu aka wawashe dukiyar kasa, su ne na Mulkin Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo (daga 1999 zuwa 2006), sai Marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua (daga 2007 zuwa 2009), kazalika a mulkin Shugaba Goodluck Jonathan daga (2010 zuwa 2014), sai kuma mulkin Muhammadu Buhari (daga 2015 zuwa 2023). Wadannan bayanai...
    An sanar da tashin shi daga City kafin karshen kakar wasa ta bana, kuma De Bruyne ya yi bankwana da magoya baya a filin wasa na Etihad bayan wasansa na karshe a gida da suka buga da Bournemouth a watan Mayu, City ta yi kokarin cike gibin da De Bruyne ya bari, yayinda ta dauki...
    A yayin da ake tsaka da bikin Ranar Dimokradiyya a Najeriya, al’ummar jihar Gombe sun wayi gari da sabuwar dokar takaita zirga-zirgar babura daga ƙarfe 7:00 na yamma zuwa ƙarfe 6:00 na safe a duk faɗin jihar. Sanarwar da ta fito ne daga hannun Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sanda ta jihar, DSP...
    Haka kuma, ya zargi Matawalle da karɓar Naira miliyan 300 daga tsohon gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, don a sako ɗaliban, amma ya bai wa ‘yan bindiga miliyan 30 kacal. APC ta ƙaryata wannan zargi. Ta kuma bayyana cewa zargin Kaura yana shafar wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar kamar tsohon Gwamna Abdulaziz Yari, wanda yanzu ke...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Inganta sinadarin Uranium da ɗage takunkumai na iya sa tattaunawar ta yi amfani Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya rubuta cewa: A bayyane yake cewa cimma yarjejeniyar da za ta tabbatar da zaman lafiya na dindindin na shirin makamashin nukiliyar Iran abu ne mai yiyuwa, kuma ana...
    Mataimakin firaministan Sin He Lifeng, ya bukaci Amurka da ta warware takaddamar cinikayya da Sin ta hanyar tattaunawa, da hadin gwiwa da zai iya haifar da moriyar bai daya. He, ya ce Sin na jaddada burin ganin Amurka ta yi aiki da bangaren Sin, ta yadda za a martaba alkawura da matakai da aka amince,...
    Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, zai yi wa ’yan Najeriya jawabi da misalin ƙarfe 7 na safiyar ranar Alhamis, domin bikin ranar dimokuraɗiyya na 2025. A cewar wata sanarwa daga kwamitin shirya bikin, shugaban ƙasa zai kuma je zaman haɗin gwiwa da ’yan majalisar dokoki da rana. Na shirya yin haɗaka don ƙalubalantar Tinubu a...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sojojin HKI sun kai hari akan Falasdinawan da su ka yi cincirindo domin karbar abinci da hakan ya yi sanadiyyar shahadar da dama daga cikinsu. Tun da safiyar yau Laraba ne dai sojojin HKI su ka rika kai hare-hare akan cibiyoyin cibiyoyin raba agaji wadanda dama suna a karkashin kulawar su kansu ‘yan sahayoniyar da...