Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala
Published: 16th, September 2025 GMT
Hukumar Tace Fina-Finai da Dab’i ta Jihar Kano ta haramta shirya duk wata muƙabala tsakanin mawaƙan yabon Annabi (S.A.W), tare da gayyatar mawaƙa Usman Maidubun Isa da Shehi Mai Tajul’izzi su bayyana a gabanta.
Hukumar ta kuma gayyaci mawaƙan ne tare da sauran waɗanda suka jagoranci muƙabalar da fitattun mawaƙan biyu suka yi ranar Litinin, da su bayyana a gabanta cikin sa’o’i 24.
Hakan na zuwa ne ƙasa da kwana ɗaya bayan ɓullar wata muhawara da aka yi tsakanin Usman Maidubun Isa da Shehi Mai Tajul’izzi kuma ta karade shafukan sada zumunta, wacce hukumar ta bayyana a matsayin karya dokokin aikinta.
Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha ne ya sanar da hakan ranar Talata, inda ya ce ɗaukar matakin wani yunƙuri ne na tabbatar da zaman lafiya, daidaito da bin doka tsakanin mawaƙan nishaɗi da na addini.
El-Mustapha, a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar, ya kuma ce an haramta duk wata nau’in muƙabala daga mawaƙan addini a jihar ba tare da izinin hukumar ba.
A yayin da yake ƙaddamar da wani kwamitin bincike da shugaban hukumar ya naɗa karkashin Daraktan Ayyuka na Musamman a hukumar, Isah Abdullahi, El-Mustapha ya umarci waɗanda aka gayyatar da su bayyana a gaban kwamitin domin amsa tambayoyi.
Hukumar ta ce shirya irin waɗannan muhawara ba tare da izininta ba ya saɓa doka kuma zai iya jawo hukunci mai tsanani ga wanda suka karya.
Hukumar ta kuma jaddada ƙudirinta na ci gaba da kula da ayyukan mawaƙan da masu nishaɗantarwa a faɗin jihar tare da yin kira ga jama’a da su zauna lafiya sannan su ci gaba da ba ta haɗin kai a ayyukanta.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Hukumar Tace Fina Finai
এছাড়াও পড়ুন:
Babban Daraktan Sakatariyar APEC: Sin Tana Ba Da Gudummawar Ba Da Jagoranci A APEC
Za a gudanar da kwarya-kwaryan taron shugabannin kungiyar APEC karo na 32 a Koriya ta Kudu.
Eduardo Pedrosa, babban daraktan sakatariyar APEC, ya bayyana cewa tun bayan shigarta APEC, Sin ta kasance mamba mai himma da kwazo. Kuma a halin yanzu, tana taka muhimmiyar rawa wajen ba da jagoranci a karkashin tsarin APEC, haka kuma tana mai da hankali kan yadda za a inganta samar da manyan ci gaba a yankin da kuma duniya baki daya.
Eduardo Pedrosa ya bayyana haka ne kwanan nan yayin wata hira da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG a birnin Gyeongju dake Koriya ta Kudu. Ya kuma yaba da nasarorin da Sin ta samu a tafarkinta na zamanantar da kanta.(Safiyah Ma)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA