’Yan sanda sun sa dokar hana yawon dare a Gombe
Published: 7th, February 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta haramta yawon dare, ta hanyar takaita zirga-zirga daga kare 12 na dare zuwa 5 na asubahi.
Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ya sanar a ranar Alhamis cewa dokar za ta fara aiki ranar Juma’a, 7 ga Fabrairu, 2025.
Ya bayyana cewa an kafa dokar takaita zirga-zirgar ne bayan samun rahotannin barazanar tsaro.
Sanarwar ta ce, “takaita zirga-zirgar na da nasaba da karuwar barazanar tsaro da ke fuskantar al’ummar Gombe,” kuma a shirye rundunar take ta shawo kansu.
NAJERIYA A YAU: Dalilin Faɗuwar Farashin Tumatur A Kasuwa Majalisa na son ƙirƙiro sabbin jihohi 31 a Najeriya Mutuwar Almajirai: Tinubu ya buƙaci a samar da matakan kare ɗalibaiDSP Buhari ya kara da cewa rundunar za ta kara ba da muhimmanci ga tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma domin jihar Gombe ta kasance cikin aminci.
Ya bukaci jama’a su ba da hadin kai, yana mai kira ga iyaye da su gargadi ’ya’yansu su guji saba dokar domin duk mai kunnen kashin da aka kama zai yaba wa aya zaki.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
NBRDA Za Ta Hada Gwiwa Da KIRCT Domin Habaka Magunguna Da Yaki Da Cututtuka
Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyar ta na hadin gwiwa da Cibiyar Binciken Cututtuka ta Jihar Kano(KIRCT) a fannonin bincike, samar da rigakafi, habaka magunguna da kuma yaki da cututtuka masu nasaba da zafi (tropical diseases).
Darakta Janar na Hukumar Binciken Harkokin Halittu ta Kasa (NBRDA), Farfesa Abdullahi Mustapha ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar ban girma da ya kai hedikwatar KIRCT da ke Kano.
Farfesa Mustapha ya ce ziyarar na da nufin karfafa hadin gwiwa tsakanin NBRDA da KIRCT domin magance kalubalen da kasa ke fuskanta ta hanyar binciken zamani.
“A matsayina na shugaba a wata muhimmiyar hukuma da ke da alhakin bincike da ci gaban fasahar halittu a fannonin abinci da noma, lafiya, masana’antu da muhalli, muna da cikakken shiri na tallafa wa KIRCT don cimma manufofinta.”
Ya yaba da kayan aiki na zamani da ke cibiyar, yana mai cewa suna da babban amfani wajen kawo sakamako mai tasiri da kuma daga martabar Najeriya a fagen binciken kimiyya na duniya.
A nasa jawabin, Daraktan Janar na KIRCT, Farfesa Hamisu Salihu, ya bayyana cewa cibiyar na mai da hankali kan muhimman fannoni guda uku da suka hada da taimaka wa manyan masu bincike daga Jami’ar Bayero ta Kano da Jami’ar Northwest, da horar da sabbin masana bincike, wato masu tasuwa, da kuma kaddamar da wani shirin gwaji na horas da dalibai biyar mafi hazaka daga ajin karshe na sakandare kan ilimin fasahar halittu kafin su shiga jami’a.
Farfesa Hamisu ya jaddada muhimmancin kafafen watsa labarai da kuma Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano wajen bunkasa fasahar halittu da inganta tattalin arzikin ilimi.
Ya kuma sake nanata kudurin KIRCT na ci gaba da gudanar da bincike mai tasiri da amfani.
Wakiliyar Rediyon Najeriya ta ruwaito cewa an kafa Kano Independent Research Centre Trust(KIRCT) ne domin gudanar da bincike kan kiwon lafiya da cututtuka masu yaduwa da wadanda ba sa yaduwa, masu matukar muhimmanci ga lafiyar jama’a a Najeriya da ma fadin nahiyar Afirka.
Khadijah Aliyu