2025-07-31@18:32:54 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1414

«hawan sallah»:

    Gwamnatin Jihar Jigawa ta horas da Malaman makarantun sakandare kimanin dubu 20 ilimin fasahar sadarwar zamani (digital). Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ne ya bayyana hakan a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawaga daga Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta ƙasa (NITDA) da Cibiyar Zaman Lafiya ƙarƙashin jagorancin Farfesa Hauwa Ibrahim da take Amurka, a ziyarar ban girma da suka kai a gidan gwamnati da ke Dutse. Peter Obi zai lashe jihohin Arewa idan ya koma PDP – Jerry Gana Mun yi asarar shanu 340 a hannun ɓarayi a Yuli — Miyetti Allah Ya ce: “Mun gabatar da cibiya ta dijital don malamai, don sadarwa da kuma kula da ilmantarwa a matakin farko, mun sanya hannu kan haɗin gwiwa na...
    A nasa tsokaci game da batun, wakilin musamman na kasar Sin a yankin kahon Afirka Xue Bing, ya ce Sin ta dade tana goyon bayan matakan wanzar da zaman lafiya da ci gaba a yankin. Ya kuma jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa ta fuskar shawo kan tarin kalubale dake addabar duniya. (Saminu Alhassan)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Amurka ta bada sanarwan kakabawa gwamnatin jeka na yi ka ta Falasdinawa takunkuman hadawa jami’anta visar shiga kasar a safiyar yau Alhamis. Shafin yanar gizo na labarai ‘abrabNews’ na kasar Saudiya ya bayyana cewa majiyar fadar white House ta bayyana cewa gwamnatin Palasdinawa musamman Mahmood Abbas suna zagon kasa ga kokarin da kasar Amurka ta ke yi don samar da zaman lafiya a Gaza. Labarin ya kara da cewa gwamnatin Falasdinawa tana mu’amala da wasu kasashen wai don amincewa da samuwar kasar Falasdinu a cikin watan satumba mai zuwa a MDD. A yau Alhamis ne wakilin Amurka na musamman a gabas ta tsakiya Steve Witkoff  Yake isa HKI don tattauna da gwamnatin saboda rage matsin lambar da wa HK...
    Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙarin wa’adin shekara guda ga shugaban hukumar Kwastan ta Nijeriya, Bashir Adewale Adeniyi. Kafin wannan ƙarin wa’adin, aikin Adeniyi zai kare ne a ranar 31 ga Agusta, 2025. Sai dai sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis ta ce wannan mataki na Tinubu zai ba Adeniyi damar kammala muhimman gyare-gyare da ayyuka da gwamnatin ke aiwatarwa a hukumar. Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Ziyarci Jama’a, Ya Daina Sauraron Gwamnoni — ADC Tinubu Ya Karrama Mata ‘Yan Ƙwallon Nijeriya Da Lambar Girmamawa (OON), Dala Dubu 100 Da Gidaje A cikin manyan ayyukan da ake son a kammala akwai shigar da...
    Shugaba Bola Tinubu ya ƙara wa Bashir Adeniyi, Shugaban Hukumar Kwastam ta Ƙasa, karin shekara ɗaya a kan wa’adin da ya kamata ya yi na shugabancin hukumar. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa a ranar Alhamis. Mutum 9 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa NNPCL ya sake haƙa sabbin rijiyoyin man fetur 4 a Kolmani A cewarsa, wa’adin Mista Adeniyi zai ƙare ne a ranar 31 ga watan Agusta, 2025. Amma yanzu Shugaba Tinubu ya amince da ƙara masa shekara ɗaya, wanda hakan ke nufin zai ci gaba da zama a kan kujerarsa har zuwa watan Agustan 2026. Sanarwar ta bayyana cewa ƙarin wa’adin zai ba shi damar kammala wasu...
    Shugaba Bola Tinubu ya ƙara wa Bashir Adeniyi, Shugaban Hukumar Kwastam ta Ƙasa, karin shekara ɗaya a kan wa’adin da ya kamata ya yi na shugabancin hukumar. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa a ranar Alhamis. Mutum 9 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa NNPCL ya sake haƙa sabbin rijiyoyin man fetur 4 a Kolmani A cewarsa, wa’adin Mista Adeniyi zai ƙare ne a ranar 31 ga watan Agusta, 2025. Amma yanzu Shugaba Tinubu ya amince da ƙara masa shekara ɗaya, wanda hakan ke nufin zai ci gaba da zama a kan kujerarsa har zuwa watan Agustan 2026. Sanarwar ta bayyana cewa ƙarin wa’adin zai ba shi damar kammala wasu...
    Aƙalla mutum tara ne suka rasu, yayin da wani kwale-kwale ɗauke da fasinjoji 17 ya kife a Jihar Jigawa. Yawancin fasinjojin da hatsarin ya rutsa da su ’yan mata ne. Kamfanin NNPCL ya sake haka sabbin rijiyoyin man fetur 4 a Kolmani Samar da makamashi mai tsafta na zamani shi ne fatanmu — Guterres Lamarin ya faru ne da ranar yammacin Lahadi, 27 ga watan Yuli, 2025, lokacin da kwale-kwalen ya taso daga ƙauyen Digawa a Ƙaramar Hukumar Jahun zuwa ƙauyen Zangon Maje da ke Ƙaramar Hukumar Taura. Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis. Ofishin NEMA na Kano, ya bayyana cewa kwale-kwalen ya kife ne a tsakiyar kogin. Wasu mazauna...
    Manchester United ta soma tattaunawa da Paris St-Germain kan golan Italiya Gianluigi Donnarumma, mai shekara 26, amma Chelsea da Manchester City na cikin masu sha’awar golan. (Telegraph – subscription required, external) Yayin da ɗanwasan gaba na Sweden Alexander Isak, mai shekara 25, ya amince ya koma Liverpool, Newcastle ta saka ɗanwasan Brazil Rodrigo Muniz, mai shekara 24 cikin lissafinta. (Mail – subscription required, external) Crystal Palace ta sanar da Arsenal cewa sai ta fara biya aƙalla fam miliyan 35 kafin ta ɗauko Eberechi Eze, daga baya ta cike sauran kuɗin. (Guardian, external) Palace a shirye take ta biya fam miliyan 27.6 domin ɗauko ɗanwasan baya na Jamus Yann Bisseck, mai shekara 24 daga Inter Milan domin maye gurbin Marc Guehi, da ake alaƙantawa da Liverpool. (Gazzetta dello Sport – in Italian, external) Chelsea na ci gaba da matsi kan Alejandro...
    Tawagar Iran ta fice daga taron majalisun dokokin kasashen duniya kafin fara jawabin jami’in gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a zaman taron A wata gagarumar nuna rashin amincewa da tushen zaluncin da ya addabi duniya, tawagogin kasashen Iran, Yemen, da Falasdinu sun fice daga zaman taron Majalisar Dinkin Duniya a Geneva, bayan da shugaban majalisar dokokin Isra’ila “Knesset” zai fara gabatar da jawabinsa mai kunshe da bayanai neman tunzura jama’a, wanda kuma bayanai suka haifar da cece-kuce a tsakanin wadanda suka zauna suka saurara. A cikin jawabin shugaban majalisar dokokin Isra’ila “Knesset” ya bayyana cewa; Akwai yiwuwar samar da ‘yantacciyar kasar Falasdinu a wajen yankunan Falasdinu, musamman a biranen London da Paris na kasashen Birtaniya da Faransa. Wannan matakin na nuna...
    Bayo Onanuga, Mai Bai Wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai, ya ce wasu ’yan siyasa na sukar Tinubu ne kawai saboda ya fito daga Kudancin Najeriya. Yayin wata hira da Trust Radio, Onanuga ya ce maganar cewa ana yi wa Arewacin Najeriya wariya ba gaskiya ba ce, face tsantsar siyasa kawai. Tinubu ya karɓi baƙuncin Abdulmumin Jibrin Kofa Za a kammala shimfiɗa layin dogo daga Kaduna zuwa Kano a 2026 — Gwamnatin Tarayya Ya ce ƙorafin da Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), ta yi na cewa an yi watsi da Arewa wajen naɗe-naɗen muƙaman gwamnati da ayyukan ci gaba, wata dabara ce kawai don rage ƙimar shugabancin wanda ya fito daga Kudu. Ya shawarci ’yan siyasar Arewa...
    Shugaban kwamitin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa, Alhaji Aminu Zakari, ya ce kwamatin ya jinkirta rangadin kananan hukumomin jihar 27 a Zango na uku na shekarar 2024 ne a sakamakon zaben kananan hukumomi, don haka akwai bukatar ba su damar gudanar da ayyuka kafin tantance kwazon su.   Alhaji Aminu Zakari ya yi wannan tsokaci ne a sakatariyar karamar hukumar Sule Tankarkar a ci gaba da rangadin kananan hukumomi da kwamatin yake yi.   A cewar sa, kwamatin zai tantance kasafin kudin karamar hukumar na shekarar 2024 da 2025 na ayyuka ta da jerin ayyukan raya kasa, da  takardun biyan kudaden ayyukan da littafin ta’ammalin kudaden na banki.   Yace kwamitin zai tantance takardun kudaden shiga tare da...
    Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da shirin tallafi guda biyu da suka kai fiye da naira miliyan 392, ga membobin kungiyar direbobi ta NURTW da kuma ƴan kungiyar mahauta a jihar Jigawa. Wannan tallafi wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatinsa na inganta rayuwar masu sana’o’in  da ke taka muhimmiyar rawa a rayuwar yau da kullum. A wajen kaddamar da shirin a filin wasa na Dutse, Gwamna Namadi ya bayyana cewa shirin yana da manufa ta musamman domin tallafa wa jama’a kai tsaye. Ya ce ƙungiyoyin NURTW da mahauta suna da matuƙar tasiri, ba kawai ga membobinsu ba, har ma da al’umma gaba ɗaya, shi ya sa gwamnatinsa ta ga dacewar tallafa musu. Gwamnan ya kara da cewa taimakon...
    Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta bada sanarwan cewa falasdinawa 7 ne suka mutu a zirin gaza saboda yunwa a cikin sa’o’i 24 da suka gabata  wanda ya sa adadin mutanen fa yunwa ta kashe a Gaza kai kai 154. Tashar talabijan ta Prersstv a nan Tehran ta nakalto Asbitin Nasir na Gaza na cewa yawa wadanda yunwa ta kashe sanadiyyar kofar ragon da HKI ta yiwa Gaza ya kai  154 sannan 89 daga cikinsu jarirai ne suka fi yawa ya zuwa yau Laraba. A makon da ya gabata ne hukumar abinci ta duniya wato ‘, the United Nations World Food Program (WFP)” ta bada sanarwan cewa 1/3 na mutanen gaza suna kwana da yunwa saboda rashin abinci sanadayar hana...
    Sanata Aniekan, ya gargaɗi jama’a da su daina yaɗa jita-jita ko bidiyo na ƙarya da ka iya tayar da hankali, tare da yaba wa da ƙoƙarin da ofisoshin jakadancin Nijeriya da Ghana da kuma ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya ke yi wajen warware matsalar. Ya ƙara da cewa: “Zaman lafiya, haɗin kai da girmama juna su ne ci gaba da zama ginshikin dangantakar ƙasashenmu biyu.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A ci gaba da hare-haren da dakarun Isra’ila ke kai wa a Zirin Gaza, yanzu adadin Falasdinawan da suka kashe ya kai 60,034. A cewar wasu alkaluma daga Ma’aikatar Lafiya ta Gaza, baya ga wannan, adadin wadanda aka raunata kuma a yanzu sun haura 145,870. Ma’aikatar ta kuma ce har yanzu ana zargin akwai mutanen kuma da ke karkashin baraguzan gine-ginen da aka rusa, wadanda ba za a iya ciro su daga ciki ba. Fiye da kaso daya cikin uku na mutanen yankin na shafe kwanaki ba su ci abinci ba, kamar yadda wani rahoton samar da abinci mai lakabin IPC na Majalisar Dinkin Duniya ya tabbatar. Rahoton ya ce ana samun karin hujjoji da ke nuna ana fama da...
    Da safiyar yau Laraba Yahudawa ‘yan share wuri zauna sun kutsa cikin masallacin kudus a karkashin kariyar jami’an tsaron ‘yan sahayoniya, tare da yin ayyukan bautar yahudanci a ciki. Wannan kutsen dai yana zuwa ne a daidai lokacin da sojojin HKI suke ci gaba da kai wa Falasdinawa hare hare  a cikin yankuna mabanbanta na Gaza da yammacin kogin Jordan. Rahotanni da suke fitowa daga Falasdinu sun ce ya zuwa yanzu adadin wadanda su ka yi shahada sun haura 18. Daga cikin wadanda su ka yi shahadar da akawi Fursunonin da aka ‘yanto su a musayar fursunoni tsakanin Hamas da HKI. A yankin Khalil sojojin HKI sun kutsa cikin kauyen Ummul-Khair tare da kame mutane 8 bayan yin kutse a...
    An yi kira ga manoma a jihar Kwara da su yi taka tsan-tsan domin hasashen za a samu ruwan sama da kuma tsawa da ake hasashen nan da kwanaki masu zuwa.   A wata sanarwa da kwamishinan noma da raya karkara na jihar, Dr, Afees Abolore ya fitar, ya ce a cewar hukumar kula da yanayi ta Najeriya, NiMet, ana sa ran wasu sassa na jihar za su fuskanci ruwan sama da kuma yiwuwar tsawa.   Ya ce za a fuskanci ruwan sama ne da rana da yamma, tsakanin Litinin 28 ga Yuli da Laraba 30 ga Yuli, 2025.   Ya yi bayanin cewa duk da cewa ba a sami ruwan sama ba tukuna, yanayin da ke gaba zai iya...
    Sanarwar New York ya jaddada alƙawarin kasa da kasa na kawo ƙarshen yaƙin a Gaza da aiwatar da hanyoyin samar da ƙasashe biyu Majalisar Dinkin Duniya ta sanar a cikin “Sanarwar New York” da yarjejeniyar kasa da kasa kan matakan dole da suka dace don kawo karshen yakin Gaza da aiwatar da Shirin samar da kasashe biyu da zai kai ga kafa kasar Falasdinu mai cikakken ‘yanci, da sake gina Gaza, da tura tawagar tabbatar da zaman lafiya ta kasa da kasa karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya. Sanarwar karshe da taron Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar kan sasanta rikicin Falasdinu cikin lumana ya sanar da amincewar kasashen duniya kan daukar matakai na bai daya don kawo karshen hare-haren wuce gona...
    Ma’aikatar Harkokin Wajen Faransa ta bayyana cewa: Laifukan da aka aikata a Yammacin Kogin Jordan na Falasdinu ayyukan ta’addanci ne Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta tabbatar da cewa tashe-tashen hankula da laifuffukan da tsagerun yahudawan sahayoniyya suke yi a yammacin gabar kogin Jordan da aka mamaye sun zama ayyukan ta’addanci, biyo bayan kashe wani mai fafutukar yaki da mamayar da tsagerun ‘yan sahayoniyya suka yi. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ya ce: “Faransa ta yi Allah-wadai da wannan kisan gilla da kakkausar murya, da kuma dukkan ayyukan ta’addanci da gangan da masu tsattsauran ra’ayi ke yi kan Falasdinawa, wanda ke karuwa a ko’ina cikin yankunan Gabar Yammacin Kogin Jordan.” Ya kara da cewa, wadannan ayyukan wuce gona da irin, hakikanin ayyukan...
    Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da naɗa Muhammad Fa’iz a matsayin Kwamanda Janar na farko na Hukumar Hisbah ta Jihar. Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ne ya tabbatar da naɗin ga manema labarai a Dutse. Ya bayyana cewa hakan na daga cikin ƙoƙarin Gwamna Namadi na ƙarfafa ayyukan sabuwar hukumar Hisbah da inganta aikinta. A cewar sa, naɗin ya haɗa da Dr. Husaini Yusuf Baban a matsayin Babban Mataimakin Kwamanda Janar, da Lawan Danbala a matsayin Mataimakin Kwamanda Janar da hedikwatar hukumar, da kuma Yunusa Idris Barau a matsayin Mataimakin Kwamanda Janar naYankin Dutse. Sauran su ne Abdulkadir Zakar, Mataimakin Kwamanda Janar, Yankin Hadejia, da Suraja Adamu, Mataimakin Kwamanda Janar, Yankin Gumel, da...
    Kwamitin neman sabuwar Karamar Hukumar Kanya Babba daga Karamar Hukumar Babura ta Jihar Jigawa, ya gabatar da takardar bukatarsa ga kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da kirkiro jihohi da kananan hukumomi a zaman da aka yi a jihar Kano. A yayin mika takardar, Shugaban kwamitin kuma Hakimin Kanya Babba,  Makaman Ringim, Malam Mohammed Ibrahim ya bayyana cewar wannan yunkuri ya bi duk sharuddan da kundin tsarin mulki ya shimfida don kafa sabuwar karamar hukuma.   Makaman na Ringim ya kara da cewar, daukacin al’ummar yankin Kanya Babba, ciki da wajen mazabar na matukar goyon bayan hakan domin bunkasa ci gaban tattalin arziki da al’umma a yankin. Da yake karbar takardar, Shugaban kwamitin Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibril,...
    Shugaban Ivory Coast, Alassane Ouattara wanda ke jagorantar ƙasar tun daga shekarar 2011, na fuskantar suka na neman mayar da shugabancin ƙasar mutu ka raba. Wannan dai na zuwa ne bayan Ouattara mai shekaru 83 ya tabbatar da aniyar sake takara wa’adi na hudu a zaben da za a yi ranar 25 ga watan Oktoba. Za mu halasta kafa ƙasar Falasɗinu muddin Isra’ila ba ta cika wasu sharuɗa ba — Birtaniya Nijar da Rasha sun ƙulla yarjejeniyar makamashin nukiliya A wani takaitaccen bayani da ya yi, Ouattara ya ce takararsa ta samo asali ne daga buƙatarsa ta kiyaye zaman lafiyar ƙasa a daidai lokacin da ta ke fuskantar kalubalen tsaro da na tattalin arziki. Ya bayyana cewa, “Ni dan takara...
    Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta ce akwai kwamitoci guda 30 da aka daurawa nauyin bibiyar yadda ma’aikatu da hukumomin gwamnatin Jihar ke sarrafa kudade domin gudanar da harkokin yau da kullum, gami da ayyukan raya kasa.   Shugaban Kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar, Alhaji Aminu Zakari, ya bayyana hakan lokacin wata ziyarar aiki a karamar hukumar Babura. Yayi bayanin cewar, an dorawa Kwamatinsa alhakin duba kananan hukumomi domin tabbatar da shugabanci nagari a yankunan karkara.   A cewarsa, kwamatin yana duba kundin bayanan sha’anin mulki da na harkokin kudi da suka hada da jadawalin kudaden da karamar hukuma ke samu daga kason arzikin kasa, da littafin hulda da banki,da takardun biyan kudade na voucher da kundin bayanan...
    Dan majalisa mai suna muhammad Mirzai ya ce; Kasashen turai sun zaku, akan su sami bayanai akan girman asarar da aka yi wa cibiyoyin Nukiliyar Iran don haka ya zama wajibi Iran din ta yi amfani da siyasar barinsu a cikin duhu. A yayin zaman da majalisar shawarar musulunci ta Iran ta yi a yau Talata, dan majalisar ya kuma yi bayani akan kallafaffen yakin kwanaki 12, ya yi ishara akan yadda HKI ta yi amfani da kirkirarriyar fasaha da kuma wasu hanyoyi na leken asiri,amma duk da haka ta ci kasa, saboda jagoranci mai cike da fasaha na jagora, da kuma yadda al’ummar kasar ta yi tsayin daka da goyon bayan tsarin musulunci. Haka nan kuma ya ce; Daga...
    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da naɗa Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin sabon Sarkin Gusau kuma Sarkin Katsina na Masarautar Gusau. Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Malam Abubakar Mohammad Nakwada ne ya sanar da hakan, inda ya bayyana cewa an yi naɗin ne bisa ga shawarwarin da masu zaɓen sarakuna na masarautar Gusau suka bayar, tare da bin al’ada da dokokin da suka dace. A wata sanarwa da mai taimakawa na musamman kan harkokin yaɗa labarai a ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Sulaiman Ahmad Tudu, ya fitar, ya ce sabon Sarkin, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello, shi ne ɗa na farko ga marigayi Sarki, kuma kafin naɗin nasa yana riƙe da mukamin Bunun Gusau. Alhaji Abdulkadir ya hau karagar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya bayyana halin da aka shiga mara daɗi, inda ya jajanta wa iyalan waɗanda suka mutu da waɗanda suka yi asarar dukiyoyi, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta tallafa musu wajen sake gina musu gidajen su da sauya muhallinsu. Fintiri ya kuma soki waɗanda ke yaɗa rahotannin ƙaryar game da lamarin, ba tare da fahimtar ainihin abin da ke faruwa ba, inda ya ce hakan yana da nasaba da tuggun siyasa da son zuciya. Ya bayyana cewa maƙasudin ambaliyar sun haɗa da ruwan sama mai yawa da toshewar hanyoyin ruwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
    Yau Litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Guo Jiakun, ya shirya taron manema labaru na yau da kullum. A wajen taron, wani dan jarida ya yi tambaya game da sabuwar yarjejeniyar kasuwanci da aka kulla tsakanin Amurka da kungiyar EU. A yayin da yake ba da amsa, Guo Jiakun ya ce, kasar Sin a ko da yaushe tana ba da shawarar cewa, ya kamata dukkan bangarori su warware bambance-bambancen tattalin arziki da cinikayya ta hanyar tattaunawa, domin kiyaye yanayin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa. Bugu da kari, dangane da taron tattauna batun tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka a kasar Sweden, Guo Jiakun ya bayyana cewa, matsayin kasar Sin kan batutuwan da suka...
    Umarnin NYSC ta amince da sanya siket ga mata masu hujjar sanya wa saboda addininsu. Umarnin NYSC ta dawo da su ta ‘yan matan da suka shigar da ƙarar tare da ba su takardar shaidar kammala NYSC. Kotun kuma ta bayar da umarnin bai wa kowacce daga cikinsu kuɗaɗe har ₦500,000 a matsayin diyya saboda tauye musu ‘yancin su. Kotun ta kuma bayyana cewa cin zarafi da muzantawar da suka fuskanta daga hannun jami’an NYSC ya ci karo da ‘yancinsu na yin addini da bayyana shi a aikace. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
    Shugaban kungiyar Hamass ya bayyana cewa HKI da gwamnatin kasar Amurka sun janye daga tattaunawa tsakaninsu da kungiyar ne don sake komawa yaki har zuwa lokacinda zasu shafe falasdinawa a gaza. Tashar talabijin nta Presstv a nan Tehran ya nakalto Kkalilul Hayya, yana fadar haka a wani jawabin da aka watsa a tashoshin talabijin nay au Litinin. Alhayya ya bayyana cewa akwai ci gaba a tattaunawar tsagaiuta wuta tsakanin kungiyar da HKI da kuma Amurka, amma janyewar HKI da kuma Amurka a wannan tattaunawar wata dasisa ce don ci gaba da kissan kiyashi a gaza. Ya ce: masu shiga tsakanin sun tabbatar da cewa akwai ci gaba a tattaunawar da ake yi a doha, sai dai sun janye ne don...
    Shugaba Bola Tinubu ya karrama ’yan wasan tawagar ƙwallon ƙafa ta mata ta Nijeriya da lambar yabo ta OON. Shugaban ya bai kowacce ’yar wasa  a tawagar ta Super Falcons kyautar gida mai ɗakuna 3 a rukunin gidaje na Renewed Hope da kuɗi dala dubu 100. Haka kuma, shugaban ya kuma bai wa masu horas da tawagar kyautar dala dubu 50.  
    Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana alhinin sa kan rahotannin ambaliya mai tsanani da ta faru a Yola, Jihar Adamawa, wacce ta yi sanadiyar  mutuwar mutane, da asarar dukiyoyi da kuma raba dimbin jama’a da muhallansu. A cikin wata sanarwa, Gwamna AbdulRazaq ya ce kungiyar NGF na jajantawa gwamnatin Jihar Adamawa ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri yayin da suke kokarin tara kayan agaji da daukar matakan rage illar wannan iftila’in. Sanarwar ta kara da cewa, kungiyar ta yaba da matakin gaggawa da ‘yan sanda da kuma dakarun sojin Najeriya suka dauka na tura rundunonin ruwa, bisa gayyatar gwamnatin jihar, domin taimaka wa al’ummar da abin ya shafa a wannan lokaci...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Majalisar Dokokin Jihar Kano ta ba da shawarar a soke ko kara inganta aikin titin gina hanya mai tsawon kilomita biyar a karamar hukumar Gabasawa. Wannan mataki ya biyo bayan karɓar rahoton da Kwamitin  Majalisar kan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci ya gabatar dangane da ambaliyar da ta afku a Zakirai, cikin karamar hukumar ta Gabasawa. Da yake gabatar da rahoton, Shugaban Kwamitin, Alhaji Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana wasu muhimman shawarwari da suka hada da: Umurtar kamfanin da ke aikin gina hanyar da ya faɗaɗa magudanar ruwa a yankin da abin ya shafa da kuma gaggauta kai agajin gaggawa ga waɗanda ambaliyar ta shafa. Sauran shawarwarin sun haɗa da tura tawagar ƙwararru daga ma’aikatun ayyuka da muhalli na jihar...
    Ministan Harkokin Tsaron Ƙasa, Dakta Bello Mohammed Matawalle, ya baiwa iyalan marigayi Sarkin Gusau, Alhaji Ibrahim Bello, gudummawar naira miliyan biyar da kuma kayan abinci, bayan rasuwarsa a ranar Alhamis da ta gabata a birnin Abuja sakamakon gajeruwar rashin lafiya.   Dakta Matawalle, ya bayyana alhininsa bisa wannan rashi na Mai Martaba.   Baya ga gudummawar kuɗi, ministan ya kuma bada buhunan shinkafa 20, gero 10, masara 10 da kuma dawa 10 ga iyalan mamacin.   Wata tawaga mai ƙarƙashin jagorancin Sanata Hassan Muhammad Nasiha, tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara a zamanin mulkin Matawalle ne suka miƙa gudummawar a madadin ministan. Dakta Matawalle ya bayyana marigayi Sarkin Gusau a matsayin shugaba mai ɗabi’a ta gari, wanda ya kasance...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa;Yunwar da mutanen Gaza suke fama da ita na tsawon watanni biyar, laifi ne maras tamka da HKI take tafkawa, da ya zama wajibi kungiyar kasashen musulmi ta yi taron gaggawa akansa. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran Dr. Isma’ila Baka’i wanda ya gabatar da taron manema labaru a yau Litinin ya kuma yi Magana akan tattaunawar da Iran ta yi da kasashen turai akan shirinta na makamin Nukiliya, ya ce: Tattaunawar da aka yi ta da kasashen turai manufarta ita ce dauke wa Iran takunkuman da aka kakaba mata akan shirinta na Nukiliya. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya kuma ce; Kasashen na turai ba su da hakkin su kakabawa Iran...
    A yau Litinin ne za a yi jana’izar sanannen mawakin kasar Lebanon wanda ya yi fice da wakokin gwgawarmaya da kishin kasa wanda zai sami halartar wakilan gwamnatin kasar da kuma al’umma. Jana’izar za ta kasance ne a majami’ar  Raqad Sayyida dake garin Bakfaya. Asibitin Khuri da Rahbani ya rasu ya cika da mutane tun da safiyar yau domin daukar jana’izarsa zuwa garin Bakfaya. A ranar Asabar din da ta gabata ne dai Rahbani ya rasu yana dan shekaru 69 bayan da ya yi gajeruwar rashin lafiya. A lokacin rayuwarsa ya shahara da wakoki na gwgawarmaya da kishin kasa, daga cikin da akwai wakar da ya yi wa Shahid Sayyid Hassan Nasarallah.
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba ’Yan Najeriya da dama ne dai aka bayyana ba sa fitowa kaɗa kuri’a a duk lokacin da zaɓe ya zagayo. Wasu daga cikin ’yan ƙasar sun bayyana rashin jin daɗin abun da hukumar zaɓe ke yi, rashin yarda da sakamakon zaɓuɓɓukan da suka gabata da dai sauransu a matsayin dalilansu na rashin kaɗa ƙuri’a. Ko waɗanne matakai Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) take ɗauka don ƙarfafawa ’yan Najeriya gwiwan fitowa su kada ƙuri’a a zaɓen 2027? NAJERIYA A YAU: Yadda masu yi wa kasa hidima za su ci arzikin yankunan da suke aiki DAGA LARABA: Abubuwan da ya kamata yara su yi yayin hutun makaranta Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A...
    Janar majid Khatami Shugaban Bangaren Leken Asiri Na dakarun IRGC masu kare juyin juya halin musulunci ya bayyana cewa, rundunarsa tana sa ido akan take –taken kasashen Turai dangane da ayyukan sharrin da HKI take gudanarwa a yankin. Ya kuma kara da cewa rundunarsa tana da hanyoyin wadanda zata yi amfani da su , wanda daga karshe turawan ne zasu cutu a goyon bayan da suke bawa HKI. Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya nakalto Janar Majid Khatami yana fadar haka a lokacinda yake jawabi a taron addu’a da girmama Ghulam Hussan Ghaiba a nan Tehran. Dangane da marigayin ya bayyana cewa ya kasance cikin wadanda suka je yakin kare kasa na shekaru 8, kuma a cutu da makaman guban da...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya zanta ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Afganistan Amir Khan Muttaki a yau Lahadi inda bangarorin biyu suka tattauna dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma al-amuran yankin wadanda suka hada da batun gaza da kuma halin da take ciki. Kamfanin dillancin labaran Tasnima na kasar Iran ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi yana cewa kasar Iran ta kira taron gaggabawa na kungiyar OIC ta kasashen musulmi don tattauna wannan batun. A nashi bangaren muttaki ya bukaci gwamnatin kasar Iran ta maida yan kasar Afganistan wadanda suke zauna a kasar zuwa gida tare da mutuntasu. Kafin haka dai a lokacin yakin kwanaki 12 tsakanin HKI da Iran jami’an tsaro a kasar...
    Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutane da dama tare da lalata gidaje a Ƙananan Hukumomin Yola ta Arewa da ta Yola Kudu a Jihar Adamawa. Ruwan sama mai ƙarfi da ya fara sauka tun da safiyar ranar Lahadi, ya haifar da ambaliya mai tsanani a sassan birnin. An gabatar da kundin dokar hana cin zarafin mata a Gombe Rashin abinci mai gina jiki ya kashe yara 650 a Katsina — MSF Yankunan da lamarin ya shafa sun haɗa da Yola Bye Pass, Sabon Pegi, Yolde Pate, da Modire. Gidaje da dama sun nutse, gonaki sun lalace, hanyoyi kuma sun katse, lamarin da ya hana mutane da ababen hawa zirga-zirga. Rahotanni sun nuna cewar mutane da dama sun rasu, ciki har...
    Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana farin cikinsa bisa nasarar da tawagar ƙwallon ƙafa ta mata ta Nijeriya (Super Falcons) ta samu a gasar cin kofin Afrika na mata (WAFCON) 2025, inda ya ce yana sa ran karɓar kofin daga hannunsu a Abuja. A cikin wata hira ta bidiyo da aka yi da shugaban ƙasa jim kaɗan bayan wasan, tare da kyaftin din tawagar, Rasheedat Ajibade, da wasu ‘yan wasan da jami’an tawagar, Tinubu ya taya su murna bisa lashe kofin karo na 10. Ya ce wannan nasara wata hanya ce da ke ɗaukaka darajar Nijeriya a idon duniya. Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata  Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Shugaban APC...
    Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana farin cikinsa bisa nasarar da tawagar ƙwallon ƙafa ta mata ta Nijeriya (Super Falcons) ta samu a gasar cin kofin Afrika na mata (WAFCON) 2025, inda ya ce yana sa ran karɓar kofin daga hannunsu a Abuja. A cikin wata hira ta bidiyo da aka yi da shugaban ƙasa jim kaɗan bayan wasan, tare da kyaftin din tawagar, Rasheedat Ajibade, da wasu ‘yan wasan da jami’an tawagar, Tinubu ya taya su murna bisa lashe kofin karo na 10. Ya ce wannan nasara wata hanya ce da ke ɗaukaka darajar Nijeriya a idon duniya. Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata  Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Shugaban APC...
    An gudanar da gagarumin tattaki a kasar Tunisiya domin nuna adawa da yunwar da aka kakaba wa al’ummar Falasdinu a Gaza Masu zanga-zangar Tunusiya a wani gagarumin tattaki da suka gudanar a tsakiyar babban birnin kasar, sun tabbatar da goyon bayansu ga gwagwarmayar Falasdinawa tare da bayyana cewa shiru da duniya ta yi kan killace Gaza da aka shafe sama da kwanaki 140 ana yi, abu ne da ba za a amince da shi ba. A ci gaba da nuna goyon baya ga yunkurin da kasashen duniya ke yi na yaki da yunwa a zirin Gaza da aka killace, al’ummar Tunisiya sun fito kan tituna suna gudanar da gagarumin jerin gwano, suna daga tutar kungiyoyin ‘yan gwagwarmaya da kuma rera...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta kaddamar da dashen itatuwa na shekarar 2025 tare da sabunta kudirin farfado da fiye da hekta 5,000 da ta lalace a fadin jihar. Gwamna Umar Namadi ne ya bayyana haka a wajen bikin kaddamar da shirin da aka gudanar a shatale-tale na Pentagon da ke Dutse babban birnin jihar.   Ya bayyana aikin dashen itatuwan a matsayin ɗaya daga cikin alkawuran da gwamnatinsa ta ɗauka domin ci gaban al’umma, inda ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen raya muhalli da kare shi. Ya ce: “Wannan yana da alaƙa da manufofinmu da suka shafi ƙaddamar da tsare-tsare da suka dace da kare muhalli, da ƙarfafa juriya da dorewar muhalli, da kuma...
    A baya-bayan nan Robert Tarjan, Ba’amurke masanin kimiyyar na’ura mai kwakwalwa, wanda ya taba lashe lambar yabo ta “Turing”, ya ce Sin ta kafa tsarin bunkasa ilimin kimiyya a matakin farko, a matsayin dabara ta tsawon lokaci da kasar ke baiwa fifiko, kuma hakan abu ne mai matukar ban sha’awa. Kazalika, a halin yanzu, Sin ta cimma manyan nasarori, yayin da a gaba kuma, ake sa ran ganin karin ci gaba da kasar za ta cimma. Tarjan wanda ya bayyana hakan yayin wata zantawa da kafar CMG ta Sin, ya ce a matakan ingiza ci gaban basirar AI, Sin na da manyan damammakin takara, wadanda suka hada da dagewa wajen cimma burika na tsawon lokaci, da tsarin bayar da ilimin...
    Firai ministan kasar Burtaniya Keir Starmer ya bayyana cewa ya fara tuntubar wasu kasashen turai kan nshirin jefawa Falasdinawa abinci daga sama tare da taimakon kasar Jordan. Shafin yanar gizo na Arab News ya nakalto Starmer yana fadar haka a yau Asanar ya kuma kara da cewa ya yi magana da kasashen Faransa da Jamus kan wannan shirin. Labarin ya kara da cewa banda jefa masu abinci kasashen zasu sauka su dauki marasa lafiya musamman yara kanana don jinyarsu.. Tun kimani watanni 4 da suka gabata ne gwamnatin HKI ta rufe kofofin shiga zirin gaza ta kuma hana shigowar abinci da magunguna, da nufin kashe dukkan falasdinawa kimani miliyon biyu a Gza, don ginawa yahudawa matsugunai a yankin. Tun fara...
    Sanata Dickson ya ƙara da cewa duk da wasu jami’an gwamnati ba su bi umarnin shugaban ƙasa ba, amma shi ya lashe zaɓen, kuma ya gode wa Buhari. Hakazalika, ya ce bayan ya kammala wa’adinsa a 2020, a lokacin da APC ke shirin karɓar mulki a Bayelsa, kotun ƙoli ta yanke hukunci cewa ɗan takararsu bai cancanta ba, amma Buhari bai matsa lamba kan kotun ta sauya hukuncin ba. “A lokacin mutane sun shirya rantsar da ɗan takarar APC a Bayelsa, amma cikin ƙasa da awa guda, kotun ƙoli ta soke nasararsa. Duk da haka Buhari ya karɓi hukuncin,” in ji shi. Ya ce Buhari shugaba ne na gari, wanda duk da bambancin siyasa da ra’ayi, bai taɓa nuna bambanci...
    Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Ƙarfin kariya da makamai masu linzami na Iran ne suka tilasta wa abokan gaba neman tsagaita wuta Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa: Karfin kariya da makamai masu linzami na Iran, sune suka tilasta wa makiya neman tsagaita wuta. Wannan dai ya zo ne a cikin wata sanarwa da ministan harkokin wajen kasar ta Iran Abbas Araqchi ya fitar a lokacin da ya ziyarci gidan tsohon kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci nak are tsaron sararin samaniyar Iran, Manjo Janar Amir Ali Hajizadeh, inda ya mika ta’aziyyarsa da taya shi murnar rabauta da shahada tare da nuna girmamawa ga daukakarsa. Araqchi ya yi ishara da irin kokarin...
     Al’ummar kasar Yemen suna ci gaba da nuna goyon bayansu ga Gaza, miliyoyin mutane suka jaddada kiran zafafa kai hare-haren daukan fansa kan ‘yan sahayoniyya Dubun dubatan jama’ar kasar Yemen ne suka fito kan tituna a jiya Juma’a a dandalin Al-Sab’en da ke tsakiyar fadar mulkin kasar Sanaa, da kuma dandali da dama a duk fadin sauran jahohin kasar, domin nuna goyon bayansu ga gwagwarmayar al’ummar Gaza, kuma a matsayin wa’adi na shugabancin kasar Yemen, wanda ya sha alwashin daukar wasu zabukan kara kaimi wajen nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu. Yemen ta ga wata rana ta musamman tare da jama’a da ba a taba ganin irinsu ba, suna amsa kiran Sayyed Abdulmalik Badr al-Din al-Houthi tare da nuna girman...
    Shugaban kasar Ukraine ya nuna sha’awar ganawa da shugaban Rasha kan neman hanyar warware rikicin da kasashen biyu ke fama da shi Ana ci gaba da yakin Ukraine musamman ta hanyar kai hare-hare da jiragen sama marasa matuka coiki. Ma’aikatar tsaron Rasha ta sanar da kakkabo jiragen sama marasa matuka ciki guda 105 na Ukraine da aka harba zuwa yankuna tara, a tekun Azov, da kuma cikin kasar Rasha a daren jiya. Shugaban kasar Ukraine Zelenskyy ya ce: Kasarsa tana da kudade don sarrafa tsarin makamai masu linzami na Patriot guda uku kuma yana neman samar da karin kudade don sarrafa wasu bakwai na daban, gami da taimakon abokan huldarsa na kasashen Turai. A cikin wata sanarwa da ofishinsa ya...
    Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta Jihar Jigawa (ALGON) ta yi alkawarin kafa kyakkyawar haɗin gwiwa da ƙungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar, domin inganta ƙwarewar jami’an hulɗa da jama’a a fadin jihar. Shugaban ALGON, Farfesa Abdurrahman Salim ne ya bayyana hakan yayin da ya karɓi shugabannin NUJ a wata ziyarar girmamawa da suka kai masa a sakatariyar ALGON da ke Dutse, babban birnin jihar. Farfesa Salim ya jaddada muhimmancin yada bayanai a harkokin mulki da kuma isar da ayyuka ga jama’a, yana mai cewa samun ingantacciyar sadarwa na da matuƙar muhimmanci. A cewarsa, bai wa jami’an hulɗa da jama’a horo da ƙwarewa zai taimaka wajen sauƙaƙe isar da sahihan bayanai ga al’umma. Farfesa Salim ya tabbatar wa NUJ...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta fara aikin gina shaguna guda dubu daya a cibiyar kasuwanci ta Farm Centre da ke Kano, wanda zai lakume  kudi Naira Biliyan Uku da rabi (N3.5bn), domin bunkasa kudaden shiga na cikin gida na jihar.   Shugaban Kungiyar Hadaka kan Tsaro, Zaman Lafiya da Warware Rikice-rikice a Jihar Jigawa, Muhammad Musbahu Basirka, ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a sakatariyar NUJ da ke Dutse, babban birnin jihar.   Ya bayyana cewa, hukumar EFCC ce ta mika filin hannun gwamnatin jihar Jigawa a matsayin wani bangare na dawo da kadarorin da jihar ta gada  daga tsohuwar jihar Kano.   Ya ce: “Wannan fili da ke a tsakiyar  birnin Kano, na daga cikin...
    A kokarin ta na inganta jin dadin al’umma, Gwamnatin jihar Jigawa ta gudanar da aikin tantance masu bukata ta musamman 200 a yankin Karamar Hukumar Birnin Kudu. A jawabin daya gabatar, shugaban Karamar Hukumar, Dr Builder Muhammad Uba ya godewa gwamnatin jihar bisa kula da jin dadin masu bukata ta musamman a yankin da ma jihar baki daya. Dr. Builder Muhammad, yace a baya akwai masu bukata ta musamman mutum 61 da ke con gajiyar shirin a yankin amma a yanzu kuma gwamnatin jihar ta amince a kara 139 da za a zabo daga mazabu 11 na yankin. Builder, wanda ya sami wakilcin Kansila mai kula da shirin walwalar jama’a na yankin, Alhaji Ahmed magaji Bashir, yace Karamar Hukumar za...
    Jami’an diblomasiyya na kasashen Iran da kuma na tarayyar Turai 3 wato Faransa da Jamus da kuma burtaniya sun fara tattaunawa gaba da gaba bayan yakin kwanaki 12 wanda Amurka da HKI suka kai mata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta kara da cewa wannan tattaunawar yana da matukar muhimmanci don zasu tattauna kan shirin makamashin nukliyar kasar Iran da kuma dauke mata takunkuman tattalin arzikin da su dora mata saboda shirinta na makamshin nukliya. Har’ila yau ana ganin tattaunawar ta Istambul shi zai fayyace makomar dangantaka tsakanin Iran da tarayyar Turai gaba daya nan gaba. Labarin ya kara da cewa tarunn yana gudana ne a cikin ofishin jakadancin kasar Iran dake birnin Istambul kuma Majid Takht-ravanci da...
    Namadi ya bayyana fatan cewa ayyukan hukumar ta Hisbah za su kawo kyakkyawan tsarin zamantakewa da tarbiyya a jihar. Ya kuma bukaci jami’an Hisba da su gudanar da ayyukansu cikin tsoron Allah, adalci, da sadaukarwa. Gwamnan ya kuma yaba wa ‘yan kwamitin kafa hukumar Hisbah bisa jajircewa, kwazon da suka yi, da sadaukarwa wajen gudanar da aikin da aka dora musu. “Kokarin da suka yi ya taka rawar gani wajen ganin an aiwatar da kudurin,” in ji shi. Ya kara da cewa, “Tare da sanya hannu kan wannan doka, a yanzu hukumar Hisbah ta samu cikakken ikon gudanar da ayyukanta a fadin Jihar Jigawa bisa aikinta na inganta kyawawan halaye, tabbatar da adalci ga al’umma, da kyautata rayuwar al’umma. “Kafa...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Taron Istanbul wata dama ce ta gyara matsayar Turai kan shirin makamashin nukiliyar Iran Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i, ya yi la’akari da taron na yau tsakanin Iran da kasashe uku mambobin kungiyar hadin gwiwa ta JCPOA a matsayin wata muhimmiyar dama ta gyara ra’ayoyinsu da gwada hakikaninsu kan batun makamashin nukiliyar kasar Iran. A cikin wata sanarwa da ya aikewa kamfanin dillancin labaran IRNA, Isma’il Baqa’i ya bayyana fatansa na cewa wadannan kasashe uku za su yi amfani da wannan damar wajen gyara tsarin da suka bi a baya wanda bai dace ba, wanda ya lalata martabar Turai da matsayin tattaunawa, tare da mayar da ita a matsayin...
    Hukumar ba da agaji da kula da ‘yan gudun hijirar Falasdinawa ta “UNRWA” tana karkashin wuta sakamakon ma’aikatan 330 da suka yi shahada kuma aka lalata cibiyoyinta 300 a Gaza! Inas Hamdan, mai magana da yawun hukumar ta UNRWA a birnin Alkahira, ta tabbatar da cewa; Yunwar da ke faruwa a zirin Gaza, wani bala’i ne da ba a taba ganin irinsa ba, wanda ya shafi mutane sama da miliyan biyu, ciki har da akalla yara miliyan daya. Wannan ya saba wa duk dokokin jin kai da ka’idoji, kuma abin takaici, lamarin yana da kara muni. Hamdan ta yi nuni da cewa, a lokacin da suke magana kan matsalar agajin jin kai ko shigar da kayan abinci zuwa zirin Gaza,...
    Mutane akalla 27 ne aka kashe a wani hari da dakarun kai daukin gaggawa suka kai a yammacin Kordofan na kasar Sudan Kafofin yada labaran kasar Sudan sun rawaito cewa: Mutane 27 ne suka mutu kana wasu 43 suka jikkata a wani hari da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka kai kan wasu kauyukan arewacin garin Nahud na jihar Kordofan ta yamma. Kungiyar likitocin Sudan ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da jaridar Sudan Tribune ta buga, inda ta bukaci daukar matakin kasa da kasa na dakatar da abin da ta bayyana a matsayin “cin zarafin fararen hula da bude hanyoyin jin kai don ceto wadanda aka tilastawa gudun hijira daga yankunansu.” A cewar jaridar,...
    “Rasuwar Sarkin Zamfara babban rashi ne ga al’ummar jihar Zamfara, Arewa da ma ƙasar nan baki ɗaya. “Sarkin ya sadaukar da rayuwar sa a shekarun nan 10 da ya ya yi hana mulki a matsayin Sarkin Gusau na 15, wanda ya hau a ranar 16 ga watan Maris na shekarar 2015. Ya yi mulki cikin jajircewa da sadaukarwa. “Marigayin, kafin ya zama Sarki, ƙwararren ma’aikacin gwamnati ne, wanda har sai da ya kai matsayin Babban Sakatare a gwamnatin tsohuwar jihar Sakkwato da ta Zamfara. “Na rasa murshidin Uba mai basira, wanda ke nuna mani hanya, tare da sauran shugabanni a jiha. Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki ya gafarta masa kura-kuran sa, ya sa aljanna ce ce makoma. Daga kanmu,...
    Kasashen Iran da Bangaladesh sun yi kakkausar suka ga cin zarafin da Isra’ila ke ci gaba da yi a zirin Gaza, tare da yin kira ga al’ummar musulmi da su dauki matakin gaggawa na dakatar da yakin kisan kare dangi da Haramtacciyar Kasar Isra’ila take yi wa al’ummar Palasdinu. A wata tattaunawa ta wayar tarho a jiya Alhamis, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da takwaransa na Bangladesh Md. Touhid Hossain sun yi musayar ra’ayi kan halin da ake ciki a yankin. Araghchi ya yi Allah wadai da laifukan da Isra’ila take tabkawa,  musamman manufofinta  na hana Falasdinawa abinci da Ruwan sha. Ya kuma jaddada muhimmancin kiran taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da kuma samar...
    Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya fada a wannan alhamis cewa yana shirin aikewa da tawaga zuwa kasar Senegal a cikin watan Augusta domin tattauna yadda aza magance matsalar basussukan da ke kan kasar  da kuma fara tattaunawa kan tsarin sabon shirin lamuni. Kasar Senegal na fama da bashin biliyoyin daloli da gwamnatin da ta shude ta karba, lamarin da ya sanya asusun lamuni na duniya IMF ya dakatar da shirin ba da lamuni ga kasar. A nasa bangaren kuma, wani mai magana da yawun IMF ya ce, “Asusun na bukatar karin bayanai kafin ya karfafa kimanta halin da ake ciki na basussukan kasar Senegal, sannan yana bukatar yarjejeniya kan muhimman matakan gyara.” Ya kara da cewa, “Da...
    Da yammacin yau Alhamis ne firaministan kasar Sin Li Qiang, ya shugabanci taron tattaunawa tsakanin shugabannin Sin da EU karo na 25, tare da shugaban majalisar EU Antonio Costa, da shugabar hukumar EU Ursula von der Leyen a nan birnin Beijing. A yayin taron, Li Qiang ya bayyana cewa, Sin da EU suna da moriya iri daya wadda babu rikici a cikinta. Bisa yanayin sauyi da ake ciki a halin yanzu, ya kamata Sin da EU su kara yin hadin gwiwa. Kuma kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da bangaren EU a fannonin cinikayya, da zuba jari, da kiyaye muhalli, da kimiyya da fasaha da sauransu, don tabbatar da samar da kayayyaki a tsakaninsu yadda ya kamata, da...
    Majiyar asibitocin yankin Gaza ta tabbatar da cewa, Falasdinawa 115 sun yi shahada sanadiyyar yunwa saboda karewar abinci a cikin yankin. Ita kuwa hukumar Agajin MDD dake aiki a Falasdinu “Unrwa” ta sanar da cewa tana da dubban manyan motoci da suke cike da kayan abinci suna jiran a ba su umaranin shiga Gaza.” Motocin suna dauke da kayan abinci, ruwa da magani a cikin kasashen Jordan da Masar.  A wani bayani da ofishin gwamnatin Gaza ya fitar a yau Alhamis, a cikin yankin Gaza duk wani abinci, ruwa da magani duk sun kare, don haka a halin yankin yankin yana da bukatuwa da buhunan filawa 500,000 a kowane mako.  An shiga kwanaki 145 da HKI ta rufe dukkanin mashigar...
    Shugaban Kwamatin kananan hukumomi na majalisar Dokokin jihar Jigawa, Alhaji Aminu Zakari, ya bayyana cewa gudanar da ayyukan raya kasa sosai a yankunan karkara zai kara daga martabar jihar a idon sauran jihohin kasar nan. Ya yi wannan tsokaci ne yayin ziyarar aiki a sakatariyar karamar hukumar Dutse, inda ya ja hankalin shugaban karamar hukumar game da bukatar bada fifiko ga bangaren ayyukan raya kasa fiye da harkokin yau da kullum domin karfafa matakin cigaban karamar hukumar. A cewar sa, kwamatin na rangadin kananan hukumomin jihar 27 ne domin bibiyar yadda ake aiwatar da tanade tanaden kasafin kudi domin tabbatar da kashe kudaden gwamnati ta hanyar da ta dace, Inda Kwamatin ke duba kundin bayanan sha’anin mulki da na harkokin...
    Shahararren ɗan kokawa ɗan ƙasar Amurka mai ritaya Terry Gene Bollea wanda aka fi sani da Hulk Hogan ya rasu yana da shekara 71 a duniya. A cewar TMZ da sauran rahotanni, likitoci sun mayar da martani a gidansa na Clearwater, da ke Florida da sanyin safiyar Alhamis kan Hulk Hogan ya kamu da bugun zuciya da ya yi ajalinsa. An rantsar da Nentawe sabon shugaban APC na ƙasa Kwalara: Mutum 13 sun mutu sama da 236 na jinya a Neja Daga nan an ɗauki Hogan da wuri aka saka shi cikin motar ɗaukar marasa lafiya. Duk da damuwa na kwanan da aka bayyana game da lafiyarsa – ciki har da larurar wuyansa a farkon wannan shekara, matarsa ​​Sky ta...
    Ayatullah Makarem Shirazi ya jaddada cewa: An kara samun karfafan hadin kan al’umma Iran bayan wuce gona da irin ‘yan sahayoniyya da Amurka kan kasarsu Ayatullah Nasser Makarem Shirazi, babban malamin addinin Musulunci a birnin Qum mai tsarki na kasar Iran ya jaddada cewa: An kara samun hadin kan kasa bayan yakin wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya da Amurka suka kaddamar kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A yayin ganawarsa da shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a jiya Laraba a birnin Qom mai alfarma Ayatullah Makarem Shirazi ya yi ishara da yakin tunani da gwamnatin ‘yan Sahayoniyya da Amurka suka yi kan Iran yana mai cewa: Wadannan makiya sun yi zaton za su haifar da rudani ta hanyar kai...
    Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fara tattauna masifar da ta faru a Gaza tare da jaddada kawo karshen kisan kiyashi  yanki Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da wani sabon zama domin tattauna batutuwan da suke faruwa a Gaza da kuma tabarbarewar al’amuran jin kai a yankin, inda ake ci gaba da yin kiraye-kirayen gaggauwa da kuma kira ga kasashen duniya da su dauki kwararan matakai na kawo karshen bala’in da ya biyo bayan yakin kisan kare dangi a yankin. Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a hanzarta dakatar da tilastawa al’ummar Gaza gudun hijira kamar yadda ta bukaci gwamnatin mamayar Isra’ila da ta ba da damar kai agajin jin kai ga al’ummar Zirin Gaza. Mataimakin babban...
    Gwamnatin mamayar Isra’ila tana ci gaba da karya dokokin kasa da kasa, inda ta fara mamaye yankunan Gabar Yammacin Kogin Jordan da kwarin Jordan! Majalisar Dokokin yahudawan sahayoniyya ta Knesset ta kada kuri’a kan wani kudirin doka da ba shi da tushe don tilastawa gwamnatin mamayar Isra’ila cikakken ikon mallakar yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan da kuma kwarin Jordan. Kuri’ar dai ta samu amincewar ‘yan majalisu 71, yayin da 13 suka nuna adawa da shi. Kungiyar Hamas ta dauki matakin a matsayin maras halacci a doka. A wani mataki da ya janyo ce-ce-ku-ce a cikin gida da na waje, Majalisar dokokin Isra’ila ta Knesset ta kada kuri’ar amincewa da wani kudirin doka da bai taka kara ya karya ba na...
    Sanatoci da dama sun goyi bayan wannan buƙata. Sun bayyana cewa hakan ya shafi dukkanin yankunan ƙasar nan kuma yana daidai da yadda sauran ƙasashe ke gudanar da ci gaban tattalin arziƙi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tawagar kwararru daga hukumar makamashin Nukliya IAEA zata ziyarci kasar Iran nan ba da daewa ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Kazem Gharibabadi mataimakin ministan harkokin wajen kasar a bangaren sharia da kuma harkokin kasashen waje ne ya bayyana haka. Ya kuma kara da cewa tawagar zata tattauna da Jami’an gwamnatin kasar Iran kan yadda mu’amalar hukumar zata kasance da Iran.  Gharibabadi ya bayyana cewa idan kasashen yamma sun yi kokarin amfani da shrin SnapBack na yarjeniyar JCPOA zasu gamu da maida martani mai tsanani, sannan ya kara da cewa mu’amala da hukumar IAEA da kasar Iran zata sauka saboda amfani da karfi kan cibiyoyin nukliyar kasar Iran wanda Amurka da HKI suka yi a kallafeffen...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata adadin falasdinawan da su ka yi shahada saboda yunwa sun kai 10.  Daga lokacin da HKI ta fara amfani da yunwa a matsayin makamin yaki,adadin falasdinawan da su ka yi shahada sun kai 111. Wannan adadin yana nuni da yadda rashin abinci ya tsananta a cikin yankin na Gaza saboda yadda Isra’ila ta killace yankin ta hana a shigar da abinci a ciki. A gefe daya, HKI tana ci gaba da kashe Falasdinawa ta hanyar yi musu kisan kiyashi, da a yau kadai fiye da mutane 80 ne su ka yi shahada. Mafi yawancin wadanda su ka yi shahada a cikin sa’oin nan...
    Babban abin dubawa a nan shi ne ko mene ne hikimar tura irin wadannan bakin haure zuwa kasashen Afirka? Misali kamar bakin hauren da Amerika take son turawa Nijeria, ’yan asalin kasar Venezuela, ko kuma bakin hauren da Sudan ta kudu ta karba ’yan asalin Myammar, da Cuba da Vietnam, al’adunsu da harshensu sun sha banban da na ’yan Afirka. Sabo da haka babu wata alaka tsakanin juna. To idan ba domin isgilanci da gadara ba, ta yaya Mr. Trump zai nemi tursasawa kasashen Afirka karbar irin wadannan bakin haure maimakon ya tasa keyarsu zuwa kasashensu na asali?(Lawal Mamuda) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
    Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya zargi Shugaba Bola Tinubu da amfani da hukumomin gwamnati wajen danne ’yan adawa. Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da manema labarai a Kano. Uwa ta kashe ’ya’yan cikinta biyu saboda kuncin rayuwa An kone babur din ‘barayin waya’ a Kano Lamido, ya ce hukumomi irin su EFCC ana amfani da su ne wajen matsa wa ’yan adawa lamba. Ya bayar da misalin tsohon Gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, wanda ke fuskantar tuhuma kan zargin aikata almundahana. A cewarsa bayan Okowa ya koma jam’iyyar APC, an daina tuhumarsa. Ya kafa misali da wata magana da Sanata Adams Oshiomhole ya taɓa yi. Ya ce: “Da zarar ka shiga APC, an yafe...
    Wani sabon salon gwamnatin mamayar Isra’ila na neman kashe Falasdinawa ‘yan gudun hijira da tsananta yunwa kansu Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun rufe tekun ga masunta da ‘yan gudun hijira a zirin Gaza, matakin da ke kara dagula al’ummar Gaza da aka killace. Gabashin tekun kudancin Gaza shi ne mashigar da mazauna yankin da kuma ‘yan gudun hijira a dukkanin yankunan zirin Gaza, musamman a kudancin zirin Gaza, biyo bayan umarnin ficewa da sojojin mamayarr Isra’ila suka bayar ga mazauna yankin Al-Mawasi da ke yammacin yankin. Tekun ya zama mafaka daya tilo ga ‘yan gudun hijira da mazauna yankin saboda hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila ke kaiwa kan Falastinawa. Sai dai rundunar sojin mamayar Isra’ila ta sanya sabbin takunkumi...
    An miƙa batun zuwa Rundunar ‘yansandan Jihar don ci gaba da bincike kafin gurfanar da wanda ake zargin a kotu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Dakatacciyar Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta lashi takobin sake maka shugabancin Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio a gaban kotun daukaka kara bayan an hana ta shiga harabar majalisar a ranar Talata. Cikin bacin rai, Natasha ta shaida wa ’yan jarida cewa za ta tattauna da lauyoyinta cikin gaggawa domin fara shigar da karar, tana mai cewa matakin ya saba da hukuncin kotun da ta bayar da umarnin a mayar da ita kan kujerarta. Lamarin dai ya biyo bayan yadda jami’an tsaron da ke gadin majalisar suka tare hanya suka hana tawagar motocinta shiga majalisar, duk kuwa da umarnin kotu na mayar da ita. HOTUNA: An ƙaddamar da aikin sabunta ginin Majalisar Dokokin Bauchi Majalisar Dattawa ta sahale wa Tinubu...
    Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya sanya hannu kan kudurin dokar da ta kafa Hukumar Hisba a matsayin hukuma ta dindindin a ƙarƙashin gwamnatin jihar. Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na gwamnan Hamisu Muhammad Gumel ya fitar ga manema labarai a Jigawa. Sanarwar ta bayyana cewa bikin sanya hannun ya gudana ne a zauren majalisar zartarwa na fadar gwamnati dake Dutse, inda manyan jami’an gwamnati suka halarta, ciki har da Mataimakin Gwamna, Injiniya Aminu Usman, da mambobin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa karkashin jagorancin Mataimakin Kakakin Majalisar, Hon. Sani Isyaku. Ta ce Gwamna Namadi ya bayyana cewa wannan rana na ɗaya daga cikin manyan nasarorin da aka cimma, bayan kai-komo na sama...
    Kwamatin kananan hukumomi na Majalisar Dokokin jihar Jigawa ya duba ayyukan raya kasa da karamar hukumar Kirikasamma ta samu nasarar gudanarwa daga watan Oktobar 2024 kawo yanzu. Shugaban Kwamatin, Alhaji Aminu Zakari, ya kafa kananan kwamitoci guda biyu domin samun nasarar tantance ayyukan a cikin garin   Kirikasamma da kauyuka. Karamin Kwamati na daya bisa jagorancin wakilin mazabar Kanya Babba Alhaji Ibrahim Hashimu Kanya, ya duba aikin sanya soma da tona riniyar tuka tuka a mayanka da magudanin ruwa a garin Marma da aikin gina rumfunan kasuwa a garuruwan Tasheguwa, Marma, Dilmari da Madaci. Alhaji Ibrahim Hashim Kanya ya bayyana wa shugaban kamsilolin karamar hukumar wanda ke yiwa tawagar rakiya, Malam Isyaku Abdullahi, muhimmancin ziyarar duba ayyukan Gwamnati dan tabbatar da...
    Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Shugaba Bola Tinubu ta karɓo bashin ƙasashen waje da ya haura dala biliyan 21 domin aiwatarwa da cike giɓin kasafin kuɗin shekarar 2025 zuwa 2026. Majalisar ta bayyana cewa za a yi amfani da bashin ne wajen aiwatar da muhimman ayyukan ci gaban ƙasa, musamman a fannonin ababen more rayuwa, da tsaro, da noma da kuma gina ɗan Adam. UNICEF na zargin Gwamnatin Nijeriya da cin zarafin ƙananan yara Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 151 a Nijeriya bana — NCDC Shugaban kwamitin Majalisar Dattawa kan basussukan cikin gida da na waje, Sanata Aliyu Wamako ne ya gabatar da rahoton karbar bashin yayin zaman majalisar a yau Talata. Sanata Wamakko wanda yake wakiltar shiyyar Sakkwato...
    Kungiyar ta malaman musulumi ta fitar da fatawa da a ciki ta bukaci gwamnatoci da al’ummar musulmi da su yunkura cikin gaggawa domin kawo karshen killace yankin Gaza da aka yi, da kuma wajabcin kai musu abinci da magunguna. Kungiyar malaman musulmin ta kuma bayyana abinda HKI take yi na killace mutanen Gaza fiye da miliyan biyu da haka su abinci da magani,musamman mata, yara da manya,wani babban laifi ne da ba shi da tamka a cikin tarihi, tana mai yin kira ga al’ummu da gwamnatoci da su motsa saboda su taimaki raunana. Kwamitin fatawa da yake a karkashin wannan kungiyar ta malaman musulmi, ya dogara da ayoyin alkrur’ani da hadisan ma’aiki ( s.a.w) da manufofi na shari’a da ka’idoji...
    Na san zuwa yanzu kowa zai amince cewa, kasar Sin ta bullo da sabuwar dabara ta abota da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa da ya bambanta da ta masu son cin zali da neman iko. Koyar da fasahohin da za su taimakawa kasashe masu tasowa musamman kasashen Afrika, zai kai su ga habaka ayyukansu da samar da sabbin dabarun ci gaba ta yadda za su habaka noma a cikin gida da sarrafa albarkatu har ma da shigar da su kasuwannin duniya. Wannan zai kai su ga samun wadata da ba su damar tsayawa da kafarsu. Tabbas wannan ya nuna cewa, kasar Sin aminiya ce ta kwarai mai son ganin dorewar ci gaban kasashe maimakon amfani domin mayar da su...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar Hisbah ta ce ta kama tare da lalata barasa da ta kai kimanin naira miliyan 5.8 a karamar hukumar Kazaure ta Jihar Jigawa. Kwamandan Hisbah a jihar Malam Ibrahim Dahiru ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a Dutse, babban birnin jihar. Jami’an tsaro sun dakile yunkurin Sanata Natasha na shiga harabar Majalisa Kamfanonin lantarki za su katse wuta kan bashin N5.2trn da suke bin gwamnati  Ya ce an gudanar da aikin ne karkashin jagorancin shugaban hukumar da ke Kazaure, Mansur Dabuwa, inda aka lalata katan 400 na barasa da darajar kudinsu ya kai naira miliyan 5.8. Ya bayyana cewa an kama barasa da aka kona a lokacin samamen da aka kai a sassa daban-daban a...
    Jami’an tsaro sun hana Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da ’yan rakiyarta shiga haramar Majalisar Dokoki ta Kasa, inda ta je da niyyar halartar zaman Majlasiar Dattawa a ranar Talata. Jami’an tsaro a daukacin kofofin shiga harabar majalisar sun hana ta shiga harabar majalisar ne a lokacin da ta yi yunkurin shiga domin halartar zaman ranar Talata, a yayin da magoya bayanta suka rako ta domin nuna goyon bayansu gare ta kan dakatarwar da majalisar ta yi mata. A watan Maris ne da Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha na tsawon wata shida kan zargin rashin da’a da kuma rashin bin tsarin wurin zaman da aka tanadar da mambobin majalisar a ranar 20 ga watan Fabrairu, 2025. A kana haka ne...
    Lauyanta, SAN West Idahosa, ya ce kotu ta tabbatar da cewa Natasha na da damar komawa majalisa ba tare da wata matsala ba. Amma majalisar dattawa ta dage cewa har yanzu tana nan kan matsayinta na dakatar da Natasha har sai wa’adin dakatarwar ya cika. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya ce ya dinga ƙorafi ne domin gwamnatin Buhari ba ta ɗauki matakin da ya dace ba game da kashe-kashen da ake yi a Benuwe. “Ba zan iya zama na yi shiru ina ci gaba da binne mutane ba. Dole ne na faɗi gaskiya,” in ji shi. “Amma ban tsaya a magana kawai ba, gwamnatina ta kawo hanyoyin magance matsalar da muka ga za su taimaka.” Ortom ya ƙara da cewa da gwamnatin Buhari ta karɓi shawararsa kuma ta yi aiki da ita, da matsalar tsaro a Benuwe ta ƙare. Ya ce ya sha kokawa a lokacin, kuma shirye-shiryen da gwamnati ta kawo kamar Ruga ba su da amfani. Ya ce ba wai rikici ne tsakanin makiyaya da manoma kawai...
    Ya ce PDP ce kaɗai ke da ƙarfin gina ƙasa. “Wannan gwamnati ce da ke cewa mutane su yi azumi alhali su suna cin abinci sannan suna jin daɗi. Babu ɗan Nijeriya mai kishin ƙasa ko wata jam’iyya mai jin zafin halin da mutane ke ciki da za ta goyi bayan Tinubu a 2027. Gwamnatinsa kasuwanci ne mara riba,” in ji Ologunagba. Kakakin PDP ya kuma nuna damuwa kan halin rashin tsaro, inda ya ambaci kisan gillar da aka yi wa mutane a Jihar Filato da kuma hari kan ɗan takarar PDP daga Anambra a Abuja, a matsayin alamu cewa rashin tsaro ya zama ruwan dare. Ya ce ƙarfin PDP yana hannun talakawa, ba sai da manyan ’yan siyasa ba....
      Manoma a Jihar Kaduna sun bayyana gamsuwarsu da yadda iri na TELA Hybrid Maize daga kamfanin EcoBasic Seeds ke samar da amfanin gona ba tare da amfani da maganin kwari ba.   Sun bayyana hakan ne a Jaji, Jihar Kaduna, lokacin da ‘yan jarida suka kai ziyara gonakin gwaji da kamfanin EcoBasic Seeds ya kafa.   Wani daga cikin manoman, Mallam Sabitu Abdullahi, ya bayyana Irin Masara na TELA Hybrid a matsayin masara mai ban mamaki, yana cewa tana bada amfanin gona mai yawa da kuma girbi cikin kwanaki 70 kacal.   “Idan duka manoman Najeriya suka rungumi wannan iri, zai taimaka wajen tabbatar da wadatar abinci a kasa,” inji shi.   Ya ce ya shafe shekaru uku yana...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta nuna matukar gamsuwa tare da yabawa Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu, Dr Builder Muhammad Uba bisa kokarin sa na ayyukan raya kasa. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da bude ofishin shugaban karamar hukumar da kuma dakin taro na karamar hukumar da aka gudanar a sakatariyar karamar hukumar ta Birnin Kudu. Ya ce shugaban karamar hukuma, Dr Builder Muhammad Uba mutum ne mai kwazo da himma wanda ya zamto abin koyi a bangaren shugabanci. A don haka, Malam Umar Namadi ya yi kira ga sauran shugabanin kananan hukumomin jihar da su tashi tsaye wajen gudanar da ayyukan kyautata rayuwar al’ummar su domin sharbar romon mulkin dimokradiyya. A jawabinsa na...
    Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, tare da wasu mutane goma sha biyu na samun kulawa a asibiti bayan tsira daga wani hadarin mota da ya faru a kan hanyar Katsina zuwa Daura, a Jihar Katsina. Hatsarin ya faru ne sakamakon taho-mu-gama da wata motar haya kirar Volkswagen a kusa da Tashar Motoci ta KTSTA da ke Daura. Duk da cewa hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) ba ta fitar da sanarwar hukumance dangane da lamarin ba, shaidu da hotunan da aka dauka daga wurin sun tabbatar da cewa motocin biyu sun lalace matuka. Shaidun gani da ido sun shaida wa Radio Nigeria cewa motar gwamnan ba ta cikin sahun motocin rakiyar gwamnati a lokacin da hadarin ya...
    Hukumar kula da ayyukan jin-ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce umurnin da sojojin Isra’ila suka bai wa Falasɗinawa na ficewa tsakiyar Gaza, babban koma baya ne ga ƙoƙarin ceton rayukan al’ummar yankin da yaƙi ya ɗaiɗaita. A ranar Lahadi ne Isra’ila ta umarci Falasɗinawa a Deir el-Balah, da su koma kudancin Gaza saboda ayyukan soji. MDD ta sake nanata gargaɗin da ta yi cewa al’ummar Gaza da dama na mutuwa saboda yunwa kuma suna buƙatar agajin abinci cikin gaggawa yayin da Isra’ila ke ci gaba da taƙaita shigar da kayan agaji.
    Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Hajiya Amina Mohammed, ta yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa kokarinsa wajen inganta ci gaban zamantakewar al’umma da kuma tallafawa aiwatar da Muradun Cigaba mai Dorewa (SDGs). Hajiya Amina Mohammed ta kai ziyara Jihar Kano ne domin yin ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar jihar bisa rasuwar fitattun dattawan nan  biyu, wato Alhaji Aminu Alhassan Dantata da tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. A yayin ziyarar tata, Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniyar ta nuna gamsuwa da wasu daga cikin shirye-shiryen Gwamna Yusuf na cigaban al’umma, musamman wadanda suka yi daidai da muradun ci gaban duniya. Daga cikin wadannan shirye-shirye akwai sanya fitilu masu amfani da hasken rana a titunan Kano, kafa cibiyar kula...
    Jami’in harkar shari’ar kasa da kasa ya bayyana cewa: Harin da aka kai wa Iran babban laifi ne kuma jarrabawa ce ta tarihi ga kwamitin sulhu Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan harkokin shari’a da kasa da kasa, Kazem Gharibabadi, ya ce: Harin da aka kai wa Iran babban laifi ne, kuma jarrabawa ce ta tarihi ga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya. A yayin wani taron manema labarai da ya yi da wakilan kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya fiye da 110 a birnin New York na kasar Amurka a jiya Litinin, Gharibabadi ya bayyana ma’auni na wuce gona da iri da gwamnatin yahudawan sahayoniyya da Amurka suka dauka kan yankin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma sakamakonsa ga zaman...
    Jami’in kungiyar Hamas ya bayyana cewa: Kamen da hukumar Falasdinawa ta yi wa ‘yan gwagwarmaya a yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan yana nuna goyon baya ne ga ‘yan mamayar Isrta’ila Jami’in kungiyar Hamas Abdel Rahman Shadid ya bayyana cewa: Kamen da jami’an tsaron Hukumar Falasdinawa suka yi na wani gungun ‘yan gwagwarmaya a Nablus da Jenin, da kwace makamansu, da kuma ci gaba da fatattakar ‘yan gwagwarmaya a duk fadin yankin gabar yammacin kogin Jordan, yana nuni da ci gaba da goyon bayan gwamnatin mamayar Isra’ila ce da murkushe al’ummar Falastinu. A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, Shadid ya jaddada a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa: Kamen da jami’an tsaron hukumar cin gashin kan Falasdinawa suka yi kan...
    Mataimakin shugaban kasar Iran na farko ya jaddada cewa; Ra’ayin gwamnati shi ne tattaunawa akan fagen yadda al’amura zasu karfafa Mataimakin shugaban kasar na farko na kasar Iran Mohammed Reza Aref ya bayyana cewa: Babu wani bambanci tsakanin diflomasiyya da fannin, inda ya ce har yanzu ra’ayin gwamnati shi ne tattaunawa kan hanyoyi kyautata gudanar da madafun iko. A yayin ganawarsa da malaman jami’ar Shariff ta fasahar kere-kere, Aref ya yaba da irin rawar da al’ummar Iran suka taka a yakin kwanaki 12 da yahudawan sahayoniyya da Amurka suka dorawa Iran, inda ya ce: Matsayin al’ummar Iran da kasancewarsu a fagen kare kasar ya kasance mai karfi wajen yakar makiya, saboda dabarun makiya shi ne cewa bayan harin da aka...
    Shugaban kasar Amurka ya dauki matakin matsin lamba kan shugabannin Afirka dangane da tarbar ‘yan gudun hijira da wadanda ya koro su daga Amurka Gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump, ta matsa lamba kan shugabannin Afirka 5 kan su yi maraba da bakin haure daga wasu kasashe a lokacin da Amurka ta kori su. A wata sanarwa da kamfanin dillancin labaran Reuters ya fitar bayan ya nakalto daga wasu jami’ai da suke da masaniya kan ganawar shugaban Amurka da shugabannin kasashen Afirka biyar ya bayyana cewa; Gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump, ta sanya matsin lamba a wannan makon kan shugabannin Afirka biyar da su yi maraba da bakin haure daga wasu kasashe idan za su bar Amurka.” A ranar Laraba ne...
     Shugaban kasar Korea ta Arewa ya bayyana goyon bayan sag a kasar Rasha a yakin da take fafatawa da kasar Ukraine. Kafafen yada labarai na Korea ta Arewa sun bayyana cewa Kim Jong Un ya fadawa ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Layrov, a cikin xiyarar kwanaki 3 da ya kai ziyara kasar. Kasar korea ta Areawa dai ta sha taimakawa kasar Rasha da sojoji da kuma makamai ma yakin da take fafatawa da kasar Ukraine fiye da shekaru uku da suka gabata. Kim ya hadu Lavrov ne a kan iyakokin kasashen biyu na ruwa da ke Wonsan . Kasashen bi yu sun tattauna karin taimakawa juna a bangaren tsaro.  KCNA ya bayyanan cewa shuwagabannin biyu sun tattauna al-amura da...
     Shugaban kasar Korea ta Arewa ya bayyana goyon bayan sag a kasar Rasha a yakin da take fafatawa da kasar Ukraine. Kafafen yada labarai na Korea ta Arewa sun bayyana cewa Kim Jong Un ya fadawa ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Layrov, a cikin xiyarar kwanaki 3 da ya kai ziyara kasar. Kasar korea ta Areawa dai ta sha taimakawa kasar Rasha da sojoji da kuma makamai ma yakin da take fafatawa da kasar Ukraine fiye da shekaru uku da suka gabata. Kim ya hadu Lavrov ne a kan iyakokin kasashen biyu na ruwa da ke Wonsan . Kasashen bi yu sun tattauna karin taimakawa juna a bangaren tsaro.  KCNA ya bayyanan cewa shuwagabannin biyu sun tattauna al-amura da...