2025-09-17@22:09:03 GMT
إجمالي نتائج البحث: 510

«Tabaraka Wa Ta ala»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Wani shafin yanar gizo na sojojin Amurka ya tabbatar da cewa dakarun kasar Yemen ne suka kaiwa jirgin Truman mai dakon jiragen sama hari Wani shafin yanar gizo na sojojin Amurka ya amince da cewa: Dakarun kasar Yemen ne suka lalata jirgin Truman. Shafukan yanar gizo na rundunar sojin Amurka Stars and Stripes sun watsa rahoton a yau Litinin cewa: Jirgin dakon jiragen sama USS Harry S da Truman sun dawo Amurka bayan da rikici ya yi tsanani a yankunan da suke shawagi. An lura cewa manyan bangarorin jirgin dakon jiragen saman Amurka a teku sun samu matsalolin fashe-fashe wanda hakan ke bayyana cewa; Jirgin Ruwan Truman da ma’aikatansa sun samu matsalolin ne a cikin tekun Bahar Maliya. Shafukan Stars...
    Ministan harkokin wajen Iran ya tattauna da Grossi kan sabbin abubuwan da suka shafi tattaunawar nukiliyar Iran Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi da Darakta Janar na Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya Rafael Grossi sun tattauna batutuwan baya-bayan nan da suka shafi tattaunawar nukiliya da kuma dage takunkumin da aka kakabawa Iran a wata tattaunawa ta hanyar wayar tarho. A yayin tattaunawar, bangarorin biyu sun yi nazari kan sabon ci gaban da aka samu a shawarwarin nukiliyar da kuma dage takunkumin. Sun kuma tattauna rahoton da hukumar ta IAEA ta fitar kan Iran. Haka nan kuma yayin da yake ishara da yadda Iran ke ci gaba da ba da hadin kai ga hukumar ta IAEA, da aiwatar da...
    A wancan lokacin, sojojin Nijeriya sun musanta batun Shehun Borno, amma wasu na ganin cewa akwai kashan gaskiya dangane da wannan al’amari, sakamakon irin yadda ‘yan ta’addan ke cin karensu babu babbaka a wadannan yankuna. Shi ma a nasa bangaren, mai sharhi kan kungiyoyin ta’addanci a Cibiyar Tony Blair, Barista Bulama Bukarti, ya ce, “A binciken da muke da shi, mun gano yadda Boko Haram suke amfani da jirage marasa matuka wajen kai wasu hare-hare a sansanonin sojojin Nijeriya.” Idan an yi la’akari da wadannan bayanan sun nuna cewa kungiyar Boko Haram tana ci gaba da fadada ayyukanta a fannoni daban-daban ba tare da an taka mata birki ba. Bisa ga wannan ne, Sanata Mohammad Ali Ndume, mai wakiltar kudancin...
    Likitocin Iran sun yi bikin murnar nasarar da ta samu na dasa na’urar dawo da ji da inganta shi ga masu matsalar kurmantaka da raunin ji a lardin Khuzestan na kasar Ƙaunar sana’a, dagewa, da sadaukarwa sune sirrin nasarar kowane aiki da hidimar jin kai. Waɗannan kalaman ne Farfesa Nadir Al-Saki ya fara bude jawabinsa a yayin bikin nasarar da aka yi na aikin tiyatar dashen na’urar magance matsalar Rashin ji da rauninsa sau 1,500 a lardin Khuzestan dake kudu maso yammacin ƙasar. Wadannan tiyata sun bayyana kwarewar aikin likita da basirar likitoci a lardin, wajen maido da ji da magana ga wadanda suka rasa jin tun da fari. Bikin dai ya samu halartar likitoci da ma’aikatan jinya da yara...
    Alkaluma daga hukumar lura da kudin musaya ta kasar Sin, sun nuna yadda kasar ta samu karuwar darajar cinikayyar waje ta fuskar hajoji da hidimomi, wadda a watan Afirilun da ya gabata ta kai kudin Sin yuan tiriliyan 4.37, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 606.8, karuwar da ta kai ta kaso 6 bisa dari a shekara.   Alkaluman da hukumar ta fitar a Juma’ar nan, sun nuna karuwar darajar hajoji da hidimomi da Sin ta fitar ketare zuwa dala biliyan 326.5, yayin da darajar wadanda ta shigo da su ta kai dala biliyan 280.3, inda aka samu rarar dalar Amurka biliyan 46.2. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran yayi tsokaci kan hasashe game da kusancin cimma yarjejeniyar nukiliyar da ke gudanarwa tsakanin Amurka da Iran Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Hanyar diflomasiyya tana bukatar a dage dukkan takunkumai da aka kakabawa Iran da kuma mutunta hakkin mallakar makamashin nukiliyar Iran, yana mai cewa: Hanyar cimma yarjejeniya ta ta’allaka ne ta kan teburin tattaunawa, ba ta hanyar kafafen yada labarai ba. Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya fada a jiya Alhamis cewa: Kafafen yada labarai na yada jita-jita game da yarjejeniyar da ake shirin kullawa tsakanin Iran da Amurka. Araqchi ya ci gaba da yin tsokaci a shafinsa na Twitter a dandalin Twitter, inda ya ce: “Muna shakkar...
    Sanarwar bayan taron koli na hadin gwiwar Sin da kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN, da kwamitin hadin gwiwar kasashen Larabawa na yankin Gulf wato GCC, ta jaddada burin sassan uku na bunkasa hadin gwiwar raya tattalin arziki, musamman ta hanyar gudanar da cinikayya marar shinge, da kammala yarjejeniyar gudanar da cinikayya cikin ’yanci tsakanin Sin da da GCC. Idan mun waiwayi wannan sanarwa ta hadin gwiwa, za ku gano manufofin da sassan uku ke fatan cimmawa, wadanda suka hada da fatan dunkule shiyyoyinsu waje guda, da kara yin tafiya tare, da neman samun ci gaba mai dorewa. Karkashin wadannan burika, sassan uku za su yi amfani da fifikonsu wajen cimma moriyar juna da karfafa kawance a...
    Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-Husi ya bayyana cewa; Harin da “Isra’ila” ta kai wa filin saukar jiragen saman Sanaa, manufarsa  ita ce yin matsin lamba akan matsayarmu ta taimakawa al’ummar Falasdinu da ake zalunta.” Sayyid Abdulmalik al-Husi ya kara da cewa;  Komai girman hare-haren da Isra’ilan za ta kai ba zai yi tasiri akan matsayarmu ta taimakawa Gaza ba,sannan kuma ya kara da cewa; Abinda Isra’ila makiya ke son yi, shi ne a kyale ta yi yadda take so da Falasdinawa ba tare da an mayar mata da martani ba daga kowace kasa ta musulmi.” Shugaban kungiyar ta Ansarullah ya kuma ce; Matsayar da kasar Yemen take dauka na taimakawa Falasdinawa, matsaya ce ta addini.” Haka...
    Mataimakin ministan ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin Ling Ji, ya ce gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da zurfafa dunkule rawar da yankunan raya tattalin arziki da fasahohi mallakin gwamnati ke takawa, a fannin janyo jarin waje, a gabar da kasar ke kara fadada matakanta na bude kofa ga kasashen waje. Ling Ji, wanda ya bayyana hakan a Talatar nan yayin wani taron manema labarai da ya gudana, ya ce a halin yanzu yanayin hada-hadar tattalin arziki da cinikayyar kasa da kasa na cikin wani halin ha’ula’i, kuma sakamakon haka, matsayar yankunan raya tattalin arziki da fasahohi na muhimmin jigon daidaita hada-hadar cinikayyar waje, da zuba jari na kara bayyana a fili. Ya zuwa shekarar 2024, adadin irin wadannan...
    Mijinta mai suna Ibrahim Mohammed ne ya gano ta, inda aka garzaya da ita asibiti, daga bisani aka tabbatar da mutuwarta.   “Wanda ake zargin ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa, inda ya amince da haurawa cikin gidan matar, inda ya shake ta, sannan ya daba mata wuka a wuya, wanda ya yi sanadiyar mutuwarta.   Sanarwar ta kara da cewa “Za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wani bafalasdine ya rasa ransa, bayan da harsasai da sojojin yahudawa suka cilla masa a garin Ariha na yankin yamma da kogin Jordan sun fada a kansa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran Falasdinawa WAFA ya na fadar haka a yau Talata, ya kuma kara da cewa Mohammed Yahya Asi Jalaytah ya yi shahada ne bayan da albarusan da sojojin suka cilla masa sun fada a kansa sun kuma ji masa munanan raunuka. Labarin ya kara da cewa bayan tsakiyar dare ne sojojin yahudawan suka soma barin wuta da bindigogi da kuma jefa hayaki mai sa hawaye a kan Falasdinawa a garin Ariha, Inda albarusai suka sami Asi Jalaita suka kuma kasashe shi. WAFA...
    Bayanai daga Falasdinu na cewa wani hari da jiragen yakin Isra’ila suka kai cikin dare a wata makarantar Gaza dake zaman matsugunni ga masu neman mafaka ya yi sanadin shahadar Falasdinawa 30, ciki har da yara da dama, a cewar jami’an kiwon lafiya da na fararen hula. Da sanyin safiyar yau litinin ne sojojin gwamnatin Isra’ila suka kai hari a makarantar Fahmi al-Jarjawi da ke yankin Daraj na zirin Gaza, inda daruruwan iyalai da suka rasa matsugunansu daga garin Beit Lahia da ke arewacin kasar da Isra’ila ke fama da hare-haren bama-bamai suka samu mafaka.   Hukumar tsaron farar hula ta Gaza ta ce masu aikin ceto sun tsamo gawarwakinmutum 20 daga makarantar, ciki har da yara da dama. A...
    Ya ce: “Ya kamata ku nazarci Shugaban Ƙasa sosai. Za ku iya faɗin ra’ayoyin ku; zai saurare ku, amma a ƙarshe shawarar da zai yanke tasa ce. Ina ganin ya dace mu gane hakan.”   Yayin da yake bayani kan taken taron, ministan ya ce Shugaba Tinubu na da cikakkiyar niyya wajen aiwatar da Shirin Sabunta Fata — wanda tsari ne da ya mayar da hankali kan jin daɗin talaka da fitar da cikakken ƙarfin Nijeriya.   “Shirin Sabunta Fata na da nufin kawo sauyi mai ma’ana ga rayuwar al’ummar Nijeriya ta hanyar muhimman matakai da za su fitar da cikakken ƙarfin Nijeriya, ta hanyar da ba a taɓa gani ba,” inji ministan.   Idris ya bayyana cewa Shugaba Tinubu...
    Wasu hare-haren da HKI ta kai kan gaza sun fada kan wata makaranta wacce aka maida ita wurin kwana, inda ya zuwa yanzu mutane 46 suka yi shahada a yayinda wasu 31 suka ji rauni. Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu har da yara kanana. Tashar talabijan ta Presstv ta bayyana cewa zana ganin yara suna gudu a cikin wuta suna kokaron kubutar da kansu. Labarin ya kara da cewa makarantar tana unguwar Daraj na birnin Gaza, mai suna Fahmi al-Jarjawi. Majiyar kungiyar kula da fararen hula a gazar ta bayyana cewa yahudawan kai hare haren a safiyar yau litinin a lokacinda suke barci. Labarin ya kara da cewa a cikin wadanda yahudawan suka kashe a Gaza, akwai Mohammad Al-kasih...
    Mainistan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin kasar Faransa bata da hakkin sukar wata kasa a duniya dangane da abinda ya shafi kare hakkin bil’adama. Bayan matsayinta a kissan kiyashin da HKI take aikatawa a gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa ministan yana maida martani ne ga tokwaransa na kasar Faransa Jean-Noel Barrot ya fada bayan da wani ba’irane ya sami lambar yabo mafi girma a gasar fina-fina mafi girma a duniya da ake kira ‘ Cannes Film Festival’ . Jafar Panohi dan kasar Iran ya lashe kyauta mafi girma a gasar ne saboda wani film da ya yi, wanda ya bashi makin samun wannan kyautar. Aragchi ya bayyana cewa, Faransa...
    Ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran ta gayyaci jakadan kasar Faransa dake nan Iran domin nuna masa kin amincewa da furucin ministan harkokin wajen kasarsa da ya shafi batunci ga Iran. Muhammad Tanhaye wanda shi ne mai kula da bangaren kasashen turai a ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran,  ya bukaci Karin bayani a hukumance dangane da abinda ministan harkokin wajen Faransa Jean Nuel Barrot ya fada akan Iran a yayin bikin ” Cannes” na fina-finai a da wani daga cikin fina-finan Iran ya sami kyauta. Har ila yau, Tanhaye ya yi suka akan yadda gwamnatin ta Faransa ta yi amfani da bikin fina-finan domin yada manufofinta na siyasa. Haka nan kuma ya ce; Faransa wacce kasa ce...
    Ministan ‘yan sandan kasar Afirka ta kudu, ya ce, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na cewa an yi wa fararen fatar kasar kisan kiyashi a yayin ziyarar da shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa ya kai. A yayin ganawar da ya yi da shugaban kasar Afirka ta kudu, shugaban kasar Amurka ya kunna wani faifen bidiyo da a ciki  aka  nuna  gicciye a gefen hanya domin tunawa da fararen fata manoma da aka yi wa ksian gilla. Ministan ‘yan sandan kasar ta Afirka ta kuku Senzo Mchunu ta cewa; Wadannan gicciyen ba su nuni da cewa suna akan kabarurruka ne, ko wani wuri na tunawa da matatu, an Sanya su ne a 2020 domin tunawa da dukkanin...
    Don haka, CHINADA tana nuna matukar adawarta ga duk wani yunkuri na bayyana shan kwayoyi masu kara kuzari a matsayin wai ci gaban kimiyya, tare da yin kira ga daukacin masu ruwa da tsaki a harkar wasanni na duniya da su tashi tsaye, su hada kai wajen yin fatali da wasannin da aka amince a sha kwayoyin kara kuzari. (Abdulrazaq Yahuza Jere)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana sabbin ci gaban da aka samu a tattaunawar da aka yi a birnin Roma Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya jaddada cewa: Ana gudanar da zagaye na biyar na tattaunawa ba na kai tsaye ba tsakanin tawagar Amurka da na Iran a cikin yanayi na kwarewa. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana a yau Juma’a cewa: Tattaunawar tana gudana cikin kwarewa da kwanciyar hankali, yana mai cewa abin da ake yadawa a kafafen yada labarai hasashe ne da baya da tushe ko inganci kuma baya da bambanci da shaci fadi. A yau Juma’a da yamma ne aka fara shawarwarin da ba na kai tsaye ba karo na biyar...
    Daga Bello Wakili Dukkan ‘yan majalisun tarayya daga Jihar Katsina sun bayyana goyon bayansu ga Gwamna Umar Dikko Radda domin ya sake tsayawa takara a wa’adin mulki na biyu karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben shekarar 2027 mai zuwa. An bayyana wannan matsaya ne a lokacin wani taron hadin gwiwa da ‘yan majalisar suka gudanar, inda Honourable Sada Soli, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Jibia da Kaita, ya yi magana a madadin takwarorinsa. Ya bayyana cewa wannan shawara ta samo asali ne daga nazarin hadin gwiwa da suka yi kan nasarorin da gwamnan ya samu da kuma goyon bayan da al’ummar jihar suka nuna daga kowane bangare. ‘Yan majalisar sun yaba da irin salon shugabanci na Gwamna...
    “Tsohon abin da ake zargin Sanata Natasha – duk karya ne,” in ji Obinna a fili. Har yanzu babu wata sanarwa daga ‘yansanda kan lamarin kama Obinna ya haifar da fushi a tsakanin masu fafutukar kare ‘yancin kafofin watsa labarai, waɗanda ke ganin harin ne kan ‘yancin faɗin albarkacin baki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Masana sun yi kira ga hukumomi da su yi bincike mai zurfi don gano waɗanda ke taimaka wa Boko Haram sannan a hukunta su domin kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankin Arewa maso Gabas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “An jawo hankalin gwamnatin jihar Zamfara kan munanan labaran ƙarya da ke yawo a kan wata mata mai suna Zainab Muhamadu ‘yar shekara 22, wacce ke fuskantar hukuncin kisa saboda ta shiga addinin Kirista.   “Muna so mu bayyana cewa aikin maƙiya zaman lafiya ne, waɗanda suke neman hanyar haifar da tashin hankali a inda ake zaman lafiya.   “Labarin ƙaryar, wanda wani dandali na yanar gizo da ya yi ƙaurin suna wajen yaɗa labaran bogi ya yaɗa, ba wani abu ba ne illa yunƙurin dagula zaman lafiya da ba za a yi nasara ba.   “Gwamnatin jihar Zamfara ta yi gaggawar ɗaukar matakin gayyato dukkan hukumomin da abin ya shafa da jami’an tsaro domin tabbatar da sahihancin labarin, wanda...
    “An jawo hankalin gwamnatin jihar Zamfara kan munanan labaran ƙarya da ke yawo a kan wata mata mai suna Zainab Muhamadu ‘yar shekara 22, wacce ke fuskantar hukuncin kisa saboda ta shiga addinin Kirista.   “Muna so mu bayyana cewa aikin maƙiya zaman lafiya ne, waɗanda suke neman hanyar haifar da tashin hankali a inda ake zaman lafiya.   “Labarin ƙaryar, wanda wani dandali na yanar gizo da ya yi ƙaurin suna wajen yaɗa labaran bogi ya yaɗa, ba wani abu ba ne illa yunƙurin dagula zaman lafiya da ba za a yi nasara ba.   “Gwamnatin jihar Zamfara ta yi gaggawar ɗaukar matakin gayyato dukkan hukumomin da abin ya shafa da jami’an tsaro domin tabbatar da sahihancin labarin, wanda...
    Sakataren harkokin wajen Amurka ya bayyana cewa: Gwamnatin rikon kwaryar Siriya na iya rugujewa cikin ‘yan makonni Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa: Gwamnatin rikon kwarya a Siriya na iya rugujewa cikin ‘yan makwanni, lamarin da zai sa kasar ta fada cikin yakin basasa matukar Amurka ba ta ba ta hadin kai ba. A yayin zaman Majalisar Dattijan Amurka, Sakataren harkokin wajen kasar Rubio ya yi furuci da cewa: Idan Amurka ta yi aiki da gwamnatin Siriya, yana iya yiwuwa, gwamnatin ta samu nasara, ko kuma gwamnatin ta kasa samun nasara idan Amureka ba yi aiki da ita ba, kuma tabbas ba zata taba samu nasara ba. Ya kara da cewa: “A hasashen Amurka, idan aka yi...
    Babban Mufti na kasar Oman ya bayyana cewa: Matakin taron kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ya fi kankara sanyi da rashin muhimmanci Babban Mufti na masarautar Oman, Sheikh Ahmed bin Hamad Al-Khalili, ya jaddada yabonsa ga fitaccen matsayi na kasar Yemen da kuma matsin lamba da dakarun kasar Yemen suke yi na kai kayan agaji a zirin Gaza. A gefe guda kuma, ya nuna rashin jin dadinsa da raunin kudirin taron kasashen Larabawa kan daukan matakan matsin lamba kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da take aiwatar da kashe-kashen gilla kan al’ummar Falasdinu. A wani rubutu da ya yi a dandalin X, Al-Khalili ya bayyana godiyarsa ga jaruman kasar Yemen da kuma kasashen da suka bayar da gudumawa wajen matsin lamba...
        Cikakkue bayanai daga baya… Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wasu shugabannin kasashen Yamma suna barazana ga gwamnatin mamayar Isra’ila kan daukan matakan ladabtarwa kanta Shugabannin kasashen Faransa da Birtaniya da kuma Canada sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa inda suka bukaci mahukuntan haramtacciyar kasar Isra’ila da su dakatar da kai farmakin da suke kai wa Zirin Gaza tare da yin barazanar daukar matakin hukunta Isra’ila. Wannan bayani dai ya samu karbuwa daga fadar shugabancin hukumar cin kwarya-kwaryan gashin kan Falasdinawa da kungiyar Hamas, amma fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi watsi da shi. Wannan dai ya zo daidai da gargadin da kasashen duniya suka yi na fuskantar bala’in jin kai da ke kara tabarbarewa a Gaza sakamakon killace yankin da bullar masifar yunwa...
    Kyaftin din kungiyar, Achu Gabriel, ya yabawa takwarorinsa da suka nuna kwazo, inda ya kara da cewa tawagar za ta ci gaba da mai da hankali wajen kwato kofin da ta lashe a shekarar 2018, tawagar ta Abuja za ta kara da mai masaukin baki, jihar Ogun a wasan rukuni na biyu a ranar Talata. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Iran ta yi watsi da zarge-zargen taron kasashen Larabawa game da tsibirai uku na Tekun Fasha Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi watsi da zarge-zargen da ke kunshe a cikin bayanin karshe na taron kasashen Larabawa a Bagadaza dangane da tsibiran Iran guda uku na Babban Tunb, Karamin Tunb da Abu Musa. Isma’il Baqa’i ya tabbatar a jiya Litinin 19 ga watan Mayu cewa: Tsibiran nan uku na Babban Tunb, Karamin Tunb da Abu Musa wasu bangarori ne na kasar Iran, yana mai cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana ganin duk wani da’awar a wannan fanni ya sabawa ka’idojin yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya da dokokin kasa da kasa, da kuma keta mutuncin yankunan kasa da ka’idojin...
      Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood? Kin san komai a rayuwa akwai abin da Allah ya tsara maka kuma duk abin da Allah ya tsara maka za ka ga sai ya tabbatu, ni dai farko mahaifiya ta zan iya ce miki tsohuwar furodusa ce ta taba ‘producing film’ a da’, Momi Jamila Haruna Allah ya ji kanta kawar ta ce tare suke tun muna yara ba mu san za mu shiga harkar ba, har muka shiga harkar. Ya gwagwarmayar shiga cikin masana’antar ta kasance? Eh! to, kin san ita rayuwa ba za ka ce baka samu irin akasi ko damuwa da wannan ba, amma ni dai gaskiya zan iya ce miki Alhamdulillahi ni dai...
    Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya yi watsi da wasu kalaman shugaban kasar Amurka Donal Trump a ziyar da ya kammala a wasu kasashen larabawa na yankin Tekun farisa, ya kuma bayyana wasu kalamansa a matsayin kungiya ga kansa da kuma mutanen Amurka. Har’ila yau Jagoran ya kara da cewa da dama daga cikin maganganunsa basu cancanci maida martani ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jagoran yana fadar haka a yau Asabar, a lokacinda yake ganawa da wasu malaman makaransu daga larduna daban daban na kasar, a Husainiyyar Imam Khonaini (q) a nan Tehran. Jagoran ya kara da cewa : Trump yace yana son amfani da karfin da Amurka...
    Shugaban kasar Iran ya jaddadacewa: Sun yi Imani da tattaunawa, amma ba su jin tsoron duk wata barazana Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa: Tabbas Iran tana gudanar da zaman tattaunawa da Amurka amma ba ta tsoron duk wata barazanarta, yana mai nuni da kalaman Trump da ke cin karo da juna, wani lokaci yana magana kan zaman lafiya sannan a wasu lokutan yana barazana da yaki. A jawabin da ya gabatar a wajen bikin cika shekaru biyu da samun nasarar tawagar “Rukunin Jirgin Ruwa na 86” na sojojin ruwan Iran, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yaba da sadaukarwar da jaruman da suka yi wannan hidimar, yana mai cewa: “Suna alfahari da kasancewar dakarunsu, yana mai...
    An samu bullar rikicin da ba a taba ganin irinsa ba a dangantaka tsakanin Aljeriya da Faransa Rikicin ma’aikatan harkokin diflomasiyya tsakanin Aljeriya da Faransa ya dawo kan gaba a fagen dakaddamar da ke tsakaninsu. Rikici dai na kara kamari ne tsakanin Aljeriya da Faransa, tun daga rikicin korar ‘yan kasar Aljeriya daga Faransa zuwa rikicin korar ma’aikatan diflomasiyyar Faransa daga Aljeriya. Kasashen biyu sun tsaya a gaban nauyin tarihin mulkin mallaka ba tare da shawo kan shi ba. Aljeriya ta gayyaci mukaddashin jakadan Faransa domin sanar da shi aniyarta ta korar karin jami’an Faransa da ke aikin taimakon wucin gadi daga kasarta. Wannan kiran ya biyo bayan maimaita cin zarafi mai tsanani da bangaren Faransa ya yi ne, yana...
    Sai ya ce “Na riga na amsa wannan tambayar amma har yanzu kana sake maimaita ta. Idan dai za a iya tunawa, ‘yan jarida 43 mazauna Kaduna ne suka halarci taron, ciki har da wasu ‘yan jarida daga wasu jihohin da suka raka gwamnonin nasu. Don haka, ba daidai ba ne a ce na hana ‘yan jarida shiga taron gwamnonin Arewa. Duk jaridun kasar nan sun je a wurin. Duk gidajen rediyo da talbijin na Kaduna suna wurin. Duk wakilan manyan gidajen Talabijin da Rediyo da ke wajen Kaduna su ma suna nan. Kada ka dauki maganata a wani bangare daban, je ka bincika. Duk wadannan labarai ne irin na teburin mai shayi. Ni kuma ban sani ba. Abin da...
    Haramun ne ga mai harama namiji ya daura duk wani abu dinkakke, sai dai hirami kawai. Amma idan bai samu hirami ba, babu laifi ya daura wando kamar yadda Abdullahi bin Abbas (RA) ya ruwaito daga cikin hudubar da Annabi (SAW) ya yi a ranar Arfa. Idan mai harama bai samu silafas ba, zai iya sanya takalmi sawu-ciki, amma ya yanke shi zuwa karkashin idon sawunsa kamar yadda ake wa khuffi. Wannan duk an haramta ne ga namiji. Amma ita mace babu abin da ya haramta mata illa sanya turare, nikabi da safar hannu, kamar yadda Abdullahi bin Umar (RA) ya ruwaito daga Manzon Allah (SAW). Haka nan kar ta sanya kayan da aka yi musu rini da turare, amma...
    Wakilan kafafen yada labaran, sun tattauna kan kalubalen da fannin aikin noman kasar ke fuskanta da suka hada da rashin samar ainahin bayanai kan abin da ya shafi aikin noma. Rashin bayar da ingantaccen dauki ga fannin daga bangaren gwamnati, kalubalen rashin tsaro da zabar wasu ‘yan lelen kafafen yada labarai, musaman da gwamnatin kasar ke yi, wajen bayar da tallace-tallacen da suka shafi bangaren aikin noma, inda suka yi nuni da cewa, kafafen yada labarai; sun dogara ne kacokan a kan samun tallace-tallace, wanda akasari shi ne ke rike da su. Sun kuma bukaci a samar wa da kafafen yada labaran kasar, wata hanyar sadarwa ta bai daya, musamman domin su kara wallafa rahotannin da suka shafi ayyukan gwamnatin...
    Mun bijoro da wannan batun kalubalen da manoman ke ci gaba da fuskanta ne, musamman duba da cewa, kakar noman bana, ta karato, musamman ganin cewa, an fara samun saukar Ruwan sama, a wasu sassan kasar nan, inda kuma tuni, mahara suka mamaye wasu yankunan kasar da ake yin noma. Akasarin fadin kasar nan, musamman a yankunan Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma duba da cewa, wadannan yankunan biyu, sun yi fice wajen yin noma, amma abin takaici, ‘yan bindiga daji, ‘yan ta’adda da kuma wasu Fulani Makiyaya, sun mayar da wadannan yankunan fagen daga, inda suka kashe manoma da kuma lalata amfanin gonakansu. Bugu da kari, wadannan bata garin sun kuma kone wasu gidajen alumomin da ke a...
    Majalisar wakilai za ta binciki yadda aka samu mummunar faduwa a jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire (UTME) ta 2025 da hukumar shirya jarabawar (JAMB) ta gudanar kwanan nan. Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da dan majalisa, Adewale Adebayo ya gabatar a zauren majalisar a ranar Alhamis. Da yake gabatar da kudirin, ya koka da cewa, da yawa daga cikin daliban, sun yi tafiya mai nisa domin zana jarabawar UTME a cibiyoyin jarabawar. Amma abin takaici, sai ga sakamakon ya fito da koma baya da yawa. Duk da cewa, hukumar JAMB ta amince cewa, tangardar na’ura ce ta janyo faduwar amma akwai bukatar a binciki hukumar. Idan za a iya tunawa, sakamakon jarabawar UTME na 2025 da JAMB...
    Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta bayyana cewa hauhawar farashi a Najeriya ya sauka kaɗan a watan Afrilu 2025 zuwa kashi 23.71, daga kashi 24.23 da aka samu a watan Maris. Wannan na nuna cewa hauhawar farashi ya ragu idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, inda a watan Afrilun 2024 aka samu kashi 33.69. Sabon Hari: An kashe makiyayi da shanu sama da 100 a Filato Wuta ta kashe ɓarawon wayar lantarki a Jigawa Wannan ragi da aka samu a watan Afrilu ya kai kusan kashi 10. Har ila yau, hukumar ta ce hauhawar farashi daga wata zuwa wata ya ragu a watan Afrilu, inda aka samu kashi 1.86, ƙasa da kashi 3.90 da aka samu a watan...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi tir da zargin da shugaban kasar Amurka Donal Trump yayiwa JMI a lokacinda yake ziyarar aiki a birnin Riyar na kasar Saudiya a ranar talatan da ta gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar na fadar haka a jiya Laraba ta kuma kara da cewa zargin da shugaba Trump yakewa JMI na kokarin wargaza tsarin zamantakewa a yankin Asiya da yamma ba gaskiya bane, ta kuma kara da cewa kasashen yamma musamman Amurka ne suke son dagula al-amura a yankin tare da goyon baya HKI ta kashe mutanen yankin a gaza da lebanonm da kuma siriya. Inda a gaza kadai ya zuwa yanzu ta kashe Falasdinawa fiye dubu 52.
    Tsohon shugaban kasar Sin marigayi Mao Zedong ya taba bayyana cewa, ” Idan an dauki mataki mai karfi wajen neman zaman lafiya, to, za a samu. Amma idan an nuna sassauci a kokarin neman tabbatar da zaman lafiya, to, ba za a samu biyan bukata ba. ” Wannan tunani ya sa kasar Sin nuna ra’ayin kin amincewa da matakin kasar Amurka na karbar karin harajin fito ba tare da wasiwasi ba. Musamman ma ta la’akari da yadda kasar ba ta rasa “kati” a hannunta ba, inda karfin tattalin arzikinta, da manufar bude kofa da ta dauka, dukkansu suka kasance karfinta na tinkarar kalubale. Sai dai, idan babu “kati” a hannu, yaya za a yi? Ga shi, abu na biyu da...
    A cikin binciken jin ra’ayoyin, kashi 91 cikin 100 na masu bayyana ra’ayoyi, sun yi imanin cewa shaye-shayen miyagun kwayoyi na daga cikin manyan abubuwan da ke barazana ga rayuwar Amurkawa. An wallafa sakamakon binciken a dandalolin CGTN a cikin harsuna biyar da suka hada da Ingilishi, Sifaniyanci, Faransanci, Larabci, da Rashanci. A tsakanin sa’o’i 24 da kaddamar da binciken, masu amfani da intanet fiye da 12,000 ne suka shiga cikin binciken tare da bayyana ra’ayoyinsu. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
    Babu wata ’yantacciyar kasa da za ta hakura da muradunta domin wata ta biya bukatunta na son rai. Yayin da Amurka ta yi gaban kanta wajen kakabawa kasashe haraje-harajen kwastam na babu gaira ba dalili, kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen kin amincewa da salon cin zali, inda ta sha nanata cewa, sai ta ga abun da ya ture wa buzu nadi, a yakin cinikayya da Amurkar ta tayar. Lallai tsayuwar kasar Sin ya ba kasashe masu tasowa kwarin gwiwa, kuma ya nuna cewa, lokaci ya wuce da za a rika yi wa ’yantattun kasashe danniya da cin zali domin biyan bukatu na kashin kai. Hakika kasar Sin ta gina tubali mai karfi da ta dora tattalin arzikinta a...
    Wannan rangwamen farashin duk da cewa ba a hukumance yake ba, amma ya bai wa kwastomomin Dangote damar siyar da mai akan farashi mai rahusa a tsakanin Naira 830 zuwa N835 kan kowacce lita.   Wannan nasarar ta zo ne makonni kadan bayan da matatar ta yi ragin farashi sau biyu a jere a cikin mako guda a cikin watan Afrilu, inda ta rage farashin man ta daga N880 zuwa N835 kan kowace lita.   Ana kyautata zaton cewa, ragin na da nasaba da sabunta tsarin sayen danyen mai da takardar Naira, biyo bayan dakatarwar da aka yi na wucin gadi.   Kokarin samun wata sanarwa a hukumance daga Kakakin Rukunin Dangote, Anthony Chiejina, kan batun rangwamen ya ci tura...
    Kungiyar Hamas wacce take iko da yankin Gaza, ta bada sanarwan cewa a shirye take ta saki fursina mai suna Edan Alexander wanda yake da jinsiyar Amurka da HKI don bude kofa ga tattaunawar tsagaaita wuta a gaza da kuma bude kofar rafa don samar da kayakin abicni a gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Jami’an kungiyar tana fadar haka a jiya Lahadi. Khalil Al-Hayya shugaban kungiyar ya bayyana cewa Hamas ta amince da hakan ne bayan wata tattaunawa da Amurka kan batun. Ya kuma kara da cewa kungiyar tana son a fara tattaunawa da gaske tsakaninta da HKI ta hanyar masu shiga tsakani, don kawo karshen yakin da kuma ficewar sojojin yahudawa gaba daya daga...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana fatan ganin kasashen India da Pakistan sun kai zuciya nesa, tare da warware sabani ta hanyar shawarwari da tattaunawa, kana su gujewa sake rura wutar tashin hankali. Wang ya bayyana hakan ne a jiya Asabar, yayin tattaunawa ta wayar tarho da mashawarcin gwamnatin India ta fuskar tsaro Ajit Doval, inda ya ce Sin na goyon baya, da fatan sassan biyu za su kai ga cimma cikakken yanayi mai dorewa na dakatar da bude wuta ta hanyar tattaunawa, wanda hakan muhimmiyar moriya ce ta kasashen biyu, kuma zai cika burin sassan kasa da kasa. Ya ce Sin ta yi tir da harin ta’addanci da ya auku a yankin Pahalgam, tana kuma adawa...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kungiyar ya yi magana Ibrahim Yusuf Babayo,Shugaban kungiyar  Miyetti Allah masu kiwon dabbobi na kasa ya bayyanawa jaridar karshen mako cewar dukkan hare- haren da ake kaiwa dabbobin da kuma kashesu an sanar da jami’an tsaro daban- daban,da suka hada da Kwamanda na rundunar soja ta,3 kuma kwamandan Operation Safe Haben (OPSH), Manjo- Janar Foluaho Oyinlola,Kwamishinan‘yansanda na Jihar, Emmanuel Adesina,da kuma darekta na bangaren jami’an farin kaya DSS. Ya ce jami’an tsaro da suke a bangaren Karamar Hukuma an kai su can wuraren da aka kai hare- haren domin su ganewa idanunsu yadda lamarin yake. Sa Wa Shanu 110 guba Kamar yadda jagorancin kungiyar MACBAN a Jihar yace,an kashe Shanu a kalla 110 ta hanyar guba a hare- haren...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga taron musayar al’adu da cudanyar al’umma da aka shirya domin murnar cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiya da jama’ar kasar Sin suka yi a kan zaluncin Japan da kuma kazamin yakin ceton kasa na tsohuwar tarayyar Soviet. A cikin sakon nasa, Xi ya yi nuni da cewa, shekaru 80 da suka gabata, al’ummomin kasar Sin da na kasar Rasha sun bayar da gudummawa mai tarihi da ba za a taba mantawa da ita ba wajen samun nasarar yaki da zaluncin danniya a duniya, tare da kulla kakkarfar alaka da ba za a iya kassarawa ba ta hanyar sadaukar da jini, wadda ta kafa tubulin raya dangantakar...
    A cewar sa, wannan bita tana da nufin tantance yadda aka samu cigaba a aiki, da kuma tabbatar da cewa hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar suna tafiya daidai da abin da aka ɗora masu a matsayin nauyi.   Ya ce: “Muna nan ne don sauraron shugabannin hukumomi domin mu ga yadda suka aiwatar da muhimman abubuwan da muka rattaba hannu a kai. Idan akwai ƙalubale, za mu tattauna su. Idan akwai cikas, za mu duba abin da za mu iya yi domin shawo kansu.”   Ministan ya bayyana wannan taro a matsayin hanyar tantance kai kafin a kai tsakiyar wa’adin gwamnatin yanzu.   Ya ce: “Ku tuna cewa wannan gwamnati ta fara aiki kusan shekaru biyu da suka gabata. Cikin...
    Wannan nasara da Inter Milan ta samu ya sa ta kai wasan karshe na gasar Zakarun Turai a karo na biyu cikin shekaru 3, a shekarar 2023 Manchester City ta doke Inter Milan a wasan karshe na gasar, wannan rashin nasara da Barcelona ta yi ya bata mata burinta na lashe gasar a karon farko cikin shekaru 10. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya ƙara da cewa Ganduje mutum ne da kullum yana cikin yi wa ma’aikatansa fara’a. Ya ce masu yaɗa bidiyon na ƙoƙarin tada rikici ne domin dalilan siyasa. “Wannan ba zai rage farin jinin Ganduje ba,” in ji shi. “Ya yi wa Jihar Kano aiki tuƙuru, yanzu kuma yana yi wa ƙasa. ‘Yan adawa ba sa jin daɗin yadda APC ke ƙara ƙarfi a ƙarƙashin jagorancinsa.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da “Bankasar tattalin arzikin Iran duk tare da takunkuman tattalin arziki masu tsanani wadanda kasashen yamma musamman Amurka suka doramata, wanda ni tahir amin zan karanta. ////…A dai-dai lokacinda gwamnatin kasar Amurka take barazanar zata hana sayan danyen man fetur daga kasar Iran kwatakwata, sannan take barazanar zata farwa kasar da yaki saboda shirin na makamashin nukliya, sabbin rahotanni sun bayyana cewa iran tana gaba a fitar da kayaki kasuwanci zuwa kasar China sannan ita ce ta 9 a duniya wajen samar da kwan kaji da sauran tsuntsaye. Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya bayyana cewa, yawan danyen man fetur wanda kasar Iran take sayarwa kasar China...
    Kotun duniya ta yi watsi da karar da Sudan ta kai Hadaddiyar Daular Larabawa tana mai zarginta da hannu a kisan kiyashin da aka yi wa al’ummar wannan kasa. A yau Litinin ne kotun duniyar ta yi watsi da karar ta Sudan, tana mai wanke Hadaddiyar Daular Larabawa. Ita dai Sudan ta zargi Hadaddiyar Daular Larabawar da cewa ta hada baki da dakarun kai daukin gaggaawa wajen yi wa mutanen yankin Darfur kisan kiyashi. A nata gefen Hadaddiyar Daular Larabawan ta ki amincewa da tuhumar da Sudan ta yi mata  tana mai siffata ta da cewa; Farfaganda ce, kuma Sudan din ta yi hakan ne domin kawar da hankulan duniya daga kan laifukan da sojoji suke aikatawa.
    Ana ci gaba da gwabza kazamin fada a yammacin Sudan tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa na kasar Jiragen saman yaki marasa matuki ciki na dakarun kai daukin gaggawa sun kai hare-hare kan sansanin sojin sama na Osman Digna da ke gabashin Sudan, inda suka janyo bullar gobara a ma’ajiyar harsasai. Jiragen saman marasa matuka ciki dai sun kai hari kan filin jirgin na Kassala cikin kwanaki biyu. Yayin da a yammacin Sudan, sojojin Sudan sun yi ruwan bama-bamai a kan wani jirgin saman dakon kaya a filin jirgin sama na Nyala da ke yankin Darfur ta Kudu, wanda ke jigilar kayan aikin soji zuwa ga dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces. A yammacin Sudan na...
    Shugaban kamfanin Sarrafa Sinadaran man fetur na kasar Iran ya bayyana cewa kasarsa tana son da kasance cikin wadanda zasu gina kamfanin sarrafa sinadaran man fetur na jumhuriyar Nijer, iran tana son ta taimaka wajen samar da takin zamani ga kasashen Afirka. Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran ya nakalto Hassan Abbaszadeh yana fadar haka a lokacinda yake ganawa da ministan man fetur na Jumhuriyar Nijer a kasuwar baje kolin kayakin da aka kera a Iran wato Iran EXPO 2025 karo na 7 wanda aka kamala. Abbaszadeh ya kara da cewa sinarin Urea wanda JMI take samarwa zai amfani amfani kamfanin sinadaran man fetur na kasar Nijer don samar da takin zamani wanda zai sami kasuwa babba a kasashen...
    Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur da kuma kawayensu na wajen kungiyar sunce zasu kara yawan man fetur da suke haka da ganga 411,000 a cikin watan Yuli mai zuwa. Kamfanin dillancin labarai na kasar Saudiya ya bayyana cewa kungiyar da kawayenta sun gudanar da taro ta kafar sadarwa ta Bidiyo a ranar 3 ga watan mayu wato jiya inda suka tsaida wannan shawarar. Labarin ya kara da cewa kungiyar tana son ta maida ganga miliyon 2.2 da suke rage da radin kansu a shekarun bayana a hankali-a hankali. Sannan kungiyar zata ci gaba da gudanr da taro a farkon ko wani wata don sanin yadda kasuwar man take a duniya da kuma yadda zasu ci gaba da kara yawan...
    Rundunar sojojin Najeriya ta 1 karkashin jagorancin Birgediya Janar Timothy Opurum ta samu gagarumar nasara a yakin da take yi da ta’addanci da ‘yan bindiga a jihar Zamfara, musamman a kananan hukumomin Talata Mafara da Kaura Namoda.   A wata sanarwa da mukaddashin mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji, Kyaftin Sulaiman Omale ya fitar tace a farkon farkon watan Mayun 2025, dakarun su da ke sintiri na yaki sun ci karo da dimbin ‘yan ta’adda da suka kutsa kai kauyen Mai Kwanugga a karamar hukumar Talata Mafara.   Ya yi bayanin cewa, ‘yan ta’addan sun rika kai hari kan mutanen yankin tare da kona gidaje kafin isowar sojojin, inda ya ce, bayan tuntubar rundunar, sojojin sun yi nasarar...
    Wadanda ake tuhumar dai sun tabbatar wa kansu aikata laifin ba tare da kara yin wata shaida ba. Duk da haka, a kokarin janye ikirari nasu, sun yarda cewa abokai ne kuma suna zaune tare a wurin da suka aikata laifin, kuma aka kama su tare. Tawagar masu gabatar da kara karkashin jagorancin Barista Zainab M. Jabbo, DDPP daga ma’aikatar shari’a ta Jihar Kebbi, ta gabatar da karar a gaban kotun. A halin da ake ciki, wadanda ake kara sun samu wakilcin Barista Alhassan wanda ya fara kare su, Barista Rilwan M. Mayalo wanda ya kammala da kuma Barista Faruk Dauran, Kodinetan Agaji na shari’a, wanda ya wakilce su a yayin yanke hukunci. Lauyan wanda ake kara ya kalubalanci nauyin...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce duk wani ci gaba da za’a samu a tattaunawa da Amurka ya dogara ne da muhimmancin da Washington ta ba tattaunawar. A wata tattaunawa ta wayar tarho da Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, Araghchi ya ce barazana da kuma takunkumin da Amurka ke kakaba wa Iran, ya kara haifar da shakku game da aniyar Washington na neman hanyar diflomasiyya. “Don ci gaba a kan wannan tafarki dole ne dayan bangaren ya nuna kyakkyawar niyya cewa da gaske ya ke,” in ji shi, kafin ya ce: “Iran, a matsayinta na mamba a yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT), dole ne ta ci moriyar makamashin nukiliya don dalilai na zaman lafiya.” Ministan...
    Ya ci gaba da cewa, tuni aka fara gudanar da wasu manyan ayyukan a Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar, musamman a ta Lekki da ta Tin Can Island. Shugaban ya bayyana cewa, an kuma samar da kafar sadarwa ta zamani ga masu ruwa da tsaki a daukacin Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar, domin a rinka yin musayar Data, har da lokacin da ya dace, a fara gudanar da aiki. Ya sanar da cewa, idan an kammala wannan aikin, za su kara taimaka wa wajen kara inganta ayyukan Hukumar, na tsawon sa’oi 24. Dantosho wanda Manajan Sashen Tashar da ke a jihar Legas Lawal Ibrahim ya wakilce shi a wajen taron ya bayyana cewa, Hukumar ta kuma yi hadaka da Rundunar Sojin Ruwa,...
    Binciken LEADERSHIP ya nuna cewa, duba mara lafiya guda daya tak da ke dauke da cutar Maleriyar da ba ta yi karfi sosai ba a asibitin gwamnati, na lashe kimanin Naira 17,000, tsakanin ganin likita, yin gwaje-gwaje da kuma magunguna.   Wadannan kudade sun kai kimanin Naira tiriliyan 1.156 da ake kashewa a kan wannan cuta, amma asalin kudaden sun zarta haka, musamman idan Maleriyar ta yi kamari, za a iya kashe ninki uku ko sama da haka na wannan kudi.   Yayin da duniya ke yin wannan biki na ranar Maleriya, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta nanata cewa, cutar na ci gaba da zama barazana, musamman a yankuna masu fama da zafi, duk da cewa; cuta ce da...
    Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi Allah wadai da matsayin Amurka na goyon bayan haramta hukumar kula da ‘yan gudun hijira falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi Allah wadai da matsayin Amurka na goyon bayan haramtacciyar kasar Isra’ila kan haramta hukumar kula da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa da ayyukan ba da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya “UNRWA”, tana daukan wanan a matsayin Amurkia na ci gaba da nuna son kai da goyon bayan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ‘yar mamaya da kuma rashin mutunta dokokin kasa da kasa da yarjejeniyar jin kai. A cikin wata sanarwar manema labarai da ta fitar jiya Alhamis, kungiyar Hamas ta yi nuni da cewa: Shigar da Amurka...
    Haka kuma, kasar Sin ta yi nuni da cewa, matakan kasar Amurka kan harajin kwastam sun kawo illa ga cinikayyar duniya, da moriyar kasashe masu tasowa, amma kasar Sin a nata bangaren kokari take yi wajen tabbatar da bunkasar cinikayya ta duniya, da kuma tsayawa tare da kasashe masu tasowa. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya kai wannan mataki ne bayan lashe Copa del Rey a wasan ƙarshe da Real Madrid a filin wasa na La Cartuja a Seville. Yamal ya fara buga wasa a Barcelona a shekara ta 2023, inda ya fara a gasar La Liga a wasan da suka buga da Betis, yana da shekaru 15 da watanni tara a lokacin. Tun daga wannan rana, ya ci gaba da kafa tarihi a ƙungiyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya kai wannan mataki ne bayan lashe Copa del Rey a wasan ƙarshe da Real Madrid a filin wasa na La Cartuja a Seville. Yamal ya fara buga wasa a Barcelona a shekara ta 2023, inda ya fara a gasar La Liga a wasan da suka buga da Betis, yana da shekaru 15 da watanni tara a lokacin. Tun daga wannan rana, ya ci gaba da kafa tarihi a ƙungiyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Syria ta nuna kin amincewarta da tsoma bakin kasashen waje a rikicin da kasar take fuskanta. Sanarwar ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Syria ta kuma ce; gwamnatin kasar za ta kare dukkanin ‘yan kasar. Kasar Syria tana fuskantar fada a tsakanin ‘yan Duruz da kuma sojojin gwamnatin kasar a yankin Sahanaya da Ashrafiyyah a yankin Suwaida. Ya zuwa yanzu dai adadin wadanda su ka rasa rayukansu sun kai 70.
    Haka kuma Wang ya halarci taron ministocin waje na kasashe mambobin kungiyar BRICS da na kasashe kawayensu a wannan rana, inda aka tattauna game da yadda za a karfafa ra’ayin cudanyar bangarori daban daban.   Wang ya bayyana cewa, mafitar matsalolin da ake fuskanta a duniya ita ce kiyayewa da aiwatar da ra’ayin cudanyar bangarori daban daban. Ya ce bayan da ta habaka mambobinta, ya kamata kungiyar BRICS ta ci gaba yayata manufar yin shawarwari da juna da tabbatar da ci gaban juna da cin moriya tare, da kiyaye muhimman ka’idojin huldar kasa da kasa, da kuma kare tsarin ciniki tsakanin bangarori daban daban.   Wang ya jadadda cewa, amsar da Sin ta bayar game da yakin cinikayya a bayyane...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wannan ya sa wasan yau zai zama mai ɗaukar hankali, domin kowanne daga cikinsu na burin ɗaukar kofin a karo na farko, domin a dakatar da yawan dariyar da ‘yan adawa ke musu. A zagayen rukuni da suka haɗu a farkon wannan kakar, Arsenal ta lallasa PSG da ci 2-0. Kocin Arsenal yanzu, Mikel Arteta, ya taɓa buga wasa a duka ƙungiyoyin. Yana fatan ya zama kocin farko da zai jagoranci Arsenal ta lashe kofin Zakarun Turai. Wannan ya sa magoya bayan Arsenal ke fatan ganin ƙungiyarsu ta yi abin mamaki a wasan da za a fara da misalin ƙarfe 8 na dare agogon Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
    Sanata Ali Ndume, mai wakiltar yankin Borno ta Kudu, ya bayyana cewa hare-haren na ƙara ƙamari a yankin abun takaici ne. Ya ce ya samu rahoto tsakanin Hawul da Garkida inda aka ce an kashe ’yan sa-kai sama da 10 a ranar Litinin. A cewarsa, sama da mutane 100 aka kashe cikin wata guda a hare-hare da aka kai Sabon Gari, Izge, Kirawa, Pulka, Damboa, Chibok, Askira Uba da wasu garuruwa da dama. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ƙaddamar da shirin rigakafin mahajjata na shekarar 2025 a yankin Hadejia da ke shiyyar arewa maso gabas ta jihar. Shugaban hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Hadejia. Alhaji Ahmed Umar Labbo ya jaddada kudirin hukumar na ba da fifiko ga lafiya da kuma tsaron mahajjatan jihar. Ya ce, kare lafiyar mahajjatan jihar  nauyi ne da ya rataya a wuyan  hukumar. “Shirin rigakafin da muka fara yana nuna shirinmu na tabbatar da nasarar aikin Hajjin shekarar 2025. Ina ƙarfafa mahajjata su ba da haɗin kai tare da bin ƙa’idojin lafiya yayin wannan tafiya mai albarka.” “Ina kuma ƙarfafa ku da ku zama masu bin doka da...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a yau Litinin cewa, babu wata tattaunawa da aka yi ta wayar tarho tsakanin shugabannin kasashen Sin da Amurka a baya-baya nan, haka kuma bangarorin biyu ba su cimma wata yarjejeniya ko su tuntubi juna game da batun haraji ba. (Fa’iza Mustapha)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Iran ya nuna murnarsa da yin maraba lalai da masu zuba hannun jari daga kasashen waje a Iran Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana Iran a matsayin dandalin da ta dace wajen zuba hannun jari da gudanar da harkar kasuwanci, yana maraba da masu zuba hannun jari na kasashen waje da ‘yan kasuwa na duniya da su shiga harkokin tattalin arziki da zuba hannun jari a Iran. A yayin bikin bude baje koli karo na bakwai na baje kolin kayayyakin da Iran ke fitarwa zuwa kasashen ketare (Iran Expo 2025) a safiyar yau Litinin, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi maraba da baki na kasashen waje da suka halarci wannan baje kolin, yana mai cewa, “Ko...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wani wanda ake zargi da safarar sassan jikin ɗan Adam ya shaida wa jami’an tsaro cewa ya shafe sama da shekara 10 yana sayar da sassan jikin mutum don samun kuɗi. Dubun mutumin sun cika ne a ranar Asabar din da ta gabata inda sojoji suka kama shi a yankin Kulanla Odomoola da ke Jihar Ogun. A furucinsa da ya amsa laifin, wanda ake zargin ya amince da sayar da sassan jikin mutum ga masu buƙata don samun kuɗin shiga. “Na dogara ne da sayar da sassan jikin mutum tsawon shekaru 10 da suka gabata. Yawancin sassan da nake sayarwa ina tono su ne daga sabbin kaburbura a makabartu, yayin da wasu kuma nake samun su daga gawarwakin da aka...
    A cewarsa, tuni aka shirya wuraren kwana da abinci ga maniyyatan a kasar Saudiyya.   Abdulkadir ya tabbatar da cewa, ana shirye-shirye, inda za a yi alluran rigakafi a ranar 28 ga Afrilu, za a raba tufafi a 30 ga Afrilu, sannan kuma za a raba jakunkuna a ranar 1 ga Mayu.   Ya kara da cewa maniyyatan da suka biya sama da Naira miliyan 8.4 na kudin aikin Hajji, za a biya su bayan sun dawo daga Saudiyya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
    Shugaban kasar Siriya ya ki amincewa da bukatar kurdawan kasar daga dakarun Democradiyyan  kurdawa wato (SDF), na samar da tsarin tarayya a kasar bayan kifar da gwanatin Basshar Al-Asab. Jaridar The Nation ta nakalto shuga Al-Ahmad Sharaa yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa tsarin tarayyar barazana ce ga hadin kan kasar ta Siriya sannan tsarin tarayya ya sabawa yarjeniyar da aka kulla da kurdawan a baya-bayan nan. A wani taron da suka gabatar a makon da ya gabata,  jam’iyyar kurdawan kasar ta Siriya (SDC) ta fadawa “ The National  ”  bayan taron kan cewa suna bukatar tsarin tarayyar a kasar Siriya don shi ne kadai zai tabbatar da hakkinsu a kasar. A cikin watan maris...
    A nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya yaba da ziyarar da cibiyar ta kai Zamfara domin duba ƙoƙarin gwamnati na magance matsalar rashin tsaro a jihar.   “Ina yawan cewa, idan ku ka yi ƙoƙarin shawo kan Zamfara yadda ya kamata ta fuskar rashin tsaro, za ku magance kashi 80 na matsalolin tsaro a Arewa.   “Daga dukkan tsare-tsaren da na gani ya zuwa yanzu, mun mallaki abin da ake buƙata domin tunkarar waɗannan ƙalubale bisa tuntubar juna da haxin gwiwa tsakanin jihar Zamfara da ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, wannan abin a yaba ne.   “Na yi farin ciki da jin cewa Tarayyar Turai ta ware wasu kuɗaɗe, duk da cewa za mu samar da...
    Sun ƙara da cewa, “Samun shugabannin matasa masu jajircewa a wannan yankin babbar albarka ce ga al’ummarmu. “Hakan na nuna mana cewa akwai kyakkyawar makoma ta ci gaba a Arewa gaba ɗaya.” Sannan sun bayyana cewa sun aike wa ƙungiyoyinsu a dukkanin jihohi 19 na Arewa goron gayyata domin naɗin sabbin muƙamai a Masarautar Daura. “Za a gudanar da babban taron karramawa wanda ba a taɓa ganin irinsa ba a nan kusa, domin naɗin sabbin muƙamai da Masarautar Daura za ta yi.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe ...
    A wata hira da Jammaje ya yi da rfI Hausa an jiyo shi ya na cewa sunana Kabiru Musa Jammaje haifaffen Jihar Kano, nayi karatu a Bayero Unibersity da ke birnin Kano inda na karanci English kafin in tafi kasar Amurka domin zurfafa karatu, bayan na dawo gida Nijeriya kuma na shiga Jami’ar koyo daga gida ta NOUN inda na karanci ‘Education Administration and Planning’.   Jammaje ya ci gaba da cewa a yawace yawacen da na yi na tafi kasashe irinsu Afirika Ta Kudu da kasar Kenya inda a wancan lokacin sai na lura cewa mutanen wadannan kasashen biyu suna yi wa duk wani dan Nijeriya wani kallo na daban sakamakon abin da suka ga ana nunawa a wasu...
    Sunana Fatimah Zahra Mazadu Daga Jihar Gomben Nigeria: Ba abun da ke janyo haka sai sakaci da rashin wayo, ta wani fannin kuma aljihu da halin maza dan suma suna nan a gari, za ka ga wata ta birgeka amma taka ta gida ka gagara kashe mata dan tayi kyau, sannan ba yadda za a yi kina kara girma kina komawa jeji, ai a lokacin da ki ka dade da namiji a lokacin ne ya kamata ki kara wanka akan wanda ki ke dan maida hankalinsa kacokam a kanki, tsabta naki kwalliya naki jan hankali naki. Na daya zai fara hangen na waje, na biyu zai dinga nisanta dake, ko da ko ba mai ra’ayin kwalliya sosai bane, ba zai...
    “Abin takaici ne ganin yadda jami’an CJTF biyu da aka kashe a ranar Juma’a, sannan kuma wasu mutane 10 da suka je daji neman itace aka kashe su yau. “Mun riga mun birne mamatan kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, kuma an kwashe waɗanda suka ji rauni zuwa Maiduguri domin nema musu kulawar likitoci,” in ji Sarkin. Ya yi addu’a Allah ya jiƙan mamatan ya kuma bai wa waɗanda suka jikkata lafiya. Sarkin ya yaba wa gwamnati da sojoji bisa ƙoƙarinsu amma ya buƙaci a ƙara amfani da sabbin fasahohin zamani da kayan yaki masu ƙarfi domin yaƙar ‘yan ta’addan. Ya yi gargaɗin cewa waɗannan hare-hare na iya tsoratar da manoma wajen komawa gonakinsu yayin da lokacin shuka ke gabatowa....
    Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da magance cin zarafin da Amurka ke yi ita kadai, ba wai kawai don kare hakki da moriyarta ba, har ma da kiyaye moriyar kasashen duniya. Ya bayyana hakan ne a jiya Jumma’a yayin ganawarsa da takwaransa na kasar Tajikistan Sirojiddin Muhriddin. Ministocin harkokin wajen kasashen biyu sun yi musayar ra’ayoyi kan batutuwan da suka shafi harajin kwastam yayin da suka hadu a birnin Almaty domin halartar taron ministocin harkokin wajen kasashen tsakiyar Asiya da kasar Sin karo na shida. Wang, ya nanata cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da dukkan bangarori domin tabbatar da gudanar da kasuwanci cikin ‘yanci,...
    Zulum ya bayyana wasu matsaloli da ke kawo tsaiko, ciki har da ƙarancin sojoji a yankunan Timbuktu Triangle, Tumbus, tsaunin Mandara, da kan iyakar Nijeriya da ƙasashen Sahel. Ya roƙi Ministan Tsaro da ya turo ƙarin manyan makamai da motocin yaƙi na zamani zuwa Borno domin taimaka wa sojoji. A nasa jawabin, Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta tura ƙarin kayan aiki da jami’an soja don magance matsalar tsaro a Borno da Arewa Maso Gabas. Ya ce shugaban ƙasa ya umarce su da su tabbatar da samar da duk abin da ake buƙata domin murƙushe ‘yan ta’adda a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
    A jiya Juma’a, an gudanar da taron dandalin tattaunawar kirkire-kirkire na kafofin watsa labaru na duniya karo na 4, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, wato CMG a takaice da gwamnatin lardin Shandong dake gabashin kasar Sin suka dauki nauyin shiryawa a birnin Qufu na lardin.   Taron dandalin mai taken “Musanya da yin koyi da juna da ma amfani da kimiyya da fasaha na kasancewa karfin wayewar kai a yayin da ake neman sauye-sauye da ci gaba”, ya samu halartar wakilai kusan 300 daga kungiyoyin kasa da kasa da hukumomin watsa labarai na kasashe da yankuna 95, da cibiyoyin masana na kasar Sin da na kasashen waje, da ma kamfanonin ketare da dai sauransu ta...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Mazauna Ƙauyen Batakashi da ke ƙaramar hukumar Garki a Jihar Jigawa sun yaba wa Gidauniyar Aliko Dangote bisa tallafin abinci da ta kai musu. Wasu daga cikin mazaunan da suka tattauna da wakilinmu sun bayyana farin cikinsu kan wannan karamci, tare da fatan alheri ga gidauniyar. Daya daga cikin waɗanda suka amfana da tallafin, Malam Umar Abdullahi, ya ce gidauniyar ta kawo sassauci ga al’umma bayan iftila’in gobara da ya cinye gidaje kusan 45 a kwanan nan. Haka shi ma Malam Usman Auwal,  ya nuna farin cikinsa, inda ya yaba da gwamnatin jihar Jigawa da kuma Gidauniyar Dangote, bisa tallafinsu ga al’umma. A jawabinsa yayin kaddamar da rabon tallafin na buhunan shinkafa guda 500 masu nauyin kilogiram10, Shugaban ƙaramar...
    “Saboda ragin farashin litar man fetur da Dangote ya yi ne. Gidan man yana da tsohon mai da ya saya a farashin da ya fi wannan, kuma ba zai sayar da shi a asara ba.   “Wannan dalilin ne ya sanya muka rufe gidajen man tun ranar Talata. Da yiwuwar mu bude nan gaba.”   Kazalika, wani ma’aikacin gidan man, ya tabbatar da cewa suna ‘yan wasu gyare-gyare ne amma za su sake budewa. Ya kuma ce, gidan man zai fara sayar da man fetur ga jama’a a ranar Talata kan kudi naira 910 a kowace lita.   Rahotonni sun tabbatar da cewa sauran abokan huldar matatar man Dangote, kamar su AP, Ardoba, da Optima, sun yi ta sayar wa...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tsoffin kwamishinoni na Jihar Kano kamar su Hon. Diggol, Hon. Abbas Sani da Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Baffa Bichi su ma sun koma APC. Hakazalika, Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada wanda ya tsaya takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar ADP a zaɓen 2023, ya sauya sheƙa zuwa APC. Ana kallon wannan sauya sheƙar a matsayin wani babban tagomashi ga jam’iyyar APC musamman a Jihar Kano. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A daidai lokacin da sabani yake yin tsanani a tsakanin India da Pakistan, bayan wani hari da aka kai a Kashmir da ya yi sanadiyyar mutuwar  mutane 26, ministan tsaron kasar Pakistan Khajah Asif ya ce; matukar India ta keta hurumin kasarsa, to kuwa za ta fuskanci mayar da martani mai tsanani. Minista Khajah Asif ya kuma gargadi kasar ta India da ta guji keta hurumin kasar Pakistan. Asif ya kuma bukaci India da ta gudanar da bincike akan harin da aka yi a ranar Talata a yankin Kashmir, kuma ta nesanci yin wani abu wanda zai jefa yankin cikin yakin da ba a san yadda karshensa zai kare ba. Haka nan kuma ya ce; Tushen matsalar tana nan a...
    Ya buƙaci jama’a da su ci gaba da tallafa wa jami’an tsafta domin tabbatar da tsaftar muhalli a jihar. Aikin tsaftar muhalli na wata-wata, wanda ake yi a ƙarshen kowane wata, ana dakatar da zirga-zirgar ababen hawa na wasu awanni domin tsaftace muhalli a faɗin Kano. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sanarwar ta ƙara da cewa, ’yan kasuwa 1,000 za su samu jarin fara aiki na Naira 150,000 kowannensu, da nufin sauya akalar kasuwancin su zuwa sana’o’i na zamani a faɗin Jihar Zamfara.   A nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada cewa bayan hawansa mulki, gwamnatinsa ta bullo da shirye-shiryen ƙarfafawa da dama tare da samar da damarmaki don cimma manufofinsa na ceto.   “Waɗannan tsare-tsare ba wani kebantaccen abu ba ne, wani ɓangare ne na babban burinmu wajen samar da jihar Zamfara mai albarka don haɗa abokan hulɗa don magance ɗimbim matsalolin zamantakewa da tattalin arziki. “Yawancin tsare-tsare na rage raɗaɗin talauci da wannan gwamnati ta bullo da su sun yi tasiri ga rayuwar dubban ‘yan jihar, ƙudirin...
    Garuruwan da aka fi tsananta wa harajin sun haɗa da Gijinzama da aka tilasta musu biyan Naira miliyan 8.5, Dakolo da aka karɓi Naira miliyan 5 da buhun wake 20, sai Kibari da Kunchin Kalgo da suka biya Naira miliyan 20, Sungawa da Naira miliyan 15, da kuma Yalwa da aka tilasta su biyan Naira miliyan 2.7. Bayan rasuwar Isuhu Yellow, wani ƙasurgumin jagoran ‘yan bindiga mai suna Dogo Gide ya sa harajin Naira miliyan 100 a kan ƙauyuka 23 da ke ƙaramar hukumar Tsafe. A ƙarshen makon da ya gabata kuma, mazauna ƙauyen Dankurmi a ƙaramar hukumar Maru sun fuskanci sabon harajin Naira miliyan 60. Wani mazaunin ƙauyen Dan Jibga, Muhammad Dogo, ya bayyana cewa bayan kashe mutane biyu...
    “Yaron ya kuma ce akwai lokacin da ta ba shi wani lemun tsami da yake zaton an saka wani abu a ciki kafin abin ya faru. Ya bayyana cewa ta sha maimaita wannan aika-aikar a kansa,” Wakil ya ƙara da bayani. Wakil ya ce a yayin bincike, wadda ake zargin ta amsa laifin da ake zarginta da shi. Ya ce za a ci gaba da tantance bayananta, sannan a gurfanar da ita a gaban kotu bayan kammala bincike. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp