Sahun farko na Alhazan Najeriya zai tashi zuwa kasa mai tsarki a ranar 9 ga watan Mayun 2025.

Hakan na kunshe ne a cikin bayanin bayan taro da Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON, ta yi da Shugabannin Hukomomin Kula da Jin Daɗin Alhazai na Jihohi a  ranar 22 ga watan Afrilun 2025.

Manufar taron ita ce tantance matakin shirin da kowace Hukumar Alhazai ta Jiha ta kai.

Wata sanarwa da mataimakiyar daraktar watsa labarai ta hukumar NAHCON, Fatima Sanda Usara ta fitar, ta ce shugaban hukumar, Farfesa Abdullah Saleh Usman, ya tunatar da mahalarta taron cewa harkar Hajji na cikin matakin karshe na shirye-shirye kafin fara aikin Hajjin shekarar 2025.

Ya bukaci jihohi da su sanar da NAHCON matsayin da suka kai wajen samar da biza, rigakafi, sayen jakunkuna da sauran batutuwa  da suka jibancu aikin hajji.

A yayin taron, Kwamishinan Ayyuka na NAHCON, Prince Anofiu Elegushi, ya bayyana cewa kamfanin Air Peace  zai yi jigilar alhazai 5,128 daga jihohin Abia, Akwa Ibom, Anambra, Rundunar Sojoji, Bayelsa, Benue, Borno, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, Ekiti, Enugu, Imo, Kogi, Ondo, Rivers, da Taraba.

Yayin da kamfanin FlyNas zai dauki alhazai 12,506 daga Birnin Tarayya Abuja, Kebbi, Legas, Ogun, Osun, Sokoto da Zamfara. Kamfanin na FlyNas ya ware jirage tara domin gudanar da wannan aikin.

Sai kamfanin Max Air da zai dauki alhazai daga jihohin Bauchi, Gombe, Jigawa, Kano, Katsina, Kwara, Oyo da Filato.

Kamfanin na Max Air ya yi alkawarin kammala jigilar alhazai  15,203 zuwa ranar 24 ga Mayu, inda zai yi amfani da jirage biyu,  jirgin B747 mai daukar mutum 400, da wani mai daukar mutum 560.

Haka zalika, kamfanin Umza zai yi jigilar alhazai 10,163 daga jihohin Kaduna, Adamawa, Nasarawa, Neja da Yobe. Shi kuma zai yi amfani da jiragin B747 mai daukar mutum 477 da B777 mai daukar mutum 310.

Wadanda kamfanonin jiragen sama 4 za su yi jigilar alhazan Hajjin 2025 su 43,000.

Kwamishinan Tsare-tsare, Bincike, Kididdiga, Labarai da Ayyukan Laburare (PRSILS), Farfesa Abubakar Yagawal, ya bayyana wa mahalarta taron irin shirin da hukumar ta yi dangane da samar da asibitoci a Makka da Madina, rabon kati na Yellow Card ga jihohi, tare da tunatar da su da su guji yi wa mata masu ciki rijistar  aikin hajji.

Sanarwar ta kara da cewa yayin da aka cimma matsaya cewa ranar 9 ga Mayu za a fara tashi, ana kuma sa ran kammala jigilar a ranar 24 ga watan Mayu.

Har ila yau, sanarwar ta ce za a fara dawowa daga kasar mai tsarki a ranar 13 ga watan Yuni zuwa 2 ga watan Yuli, idan Allah ya yarda.

 

 

Safiyah Abdulkadir 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigilar Alhazai mai daukar mutum

এছাড়াও পড়ুন:

Hajj 2025: Kaduna Ta Gaddamar Da Ayarin Likitoci Da Za Su Kula Da Alhazan Jihar

Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya kaddamar da ayarin likitoci su tara domin kula da lafiyar maniyata aikin hajjin na wannan shekaran.

Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Kaduna, Malam Salihu S. Abubakar, ne ya bayyana hakan bayan ganawar farko da ayarin da kuma shugabannin hukumar.

Ayarin likitocin ƙarƙashin jagorancin Dr. Bello Jamoh, za su gudanar da cikakken binciken lafiyar maniyata kafin tafiyar su zuwa kasa mai tsarki da zai gudana a sansanin alhazai da ke Mando, Kaduna.

Sannan kuma za su bayar da taimakon gaggawa a kasar Saudiyya tare da haɗin gwiwar Ayarin likitocin daga Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON).

Shugaban hukumar ya ce mambobin ayarin za su kasance cikin tsari na duba lafiyar mahajjata a tsawon lokacin aikin hajjin.

“Lafiya maniyata aikin hajjin tana da matuƙar muhimmanci, mun zaɓi ayarin ne bisa ƙwarewarsu, kuma muna da tabbacin za su bayar da ingantaccen kulawa ta lafiya a lokacin aikin hajjin,” In ji shi.

Shugaban ya ƙara da cewa za a gudanar da cikakken gwajin lafiya ga dukkan masu niyyar zuwa aikin Hajj, musamman don gano mata masu juna biyu.

Babu sassauci ko kaɗan wajen barin mata masu juna biyu su tafi Hajj.” in ji Malam Salihu, yana mai jaddada cewa gudunmuwar da ayarin likitocin za su bada wajen tabbatar da wannan doka, na da muhimmanci don bin ƙa’idodin aikin Hajjin.

Ya ja hankalin ayarin likitocin su gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa da sadaukarwa, domin tabbatar da cewa mahajjata sun samu aikin hajji mai sauƙi cikin koshin lafiya.

 

Adamu Yusuf

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu gobe Alhamis
  • Hajj 2025: Kaduna Ta Gaddamar Da Ayarin Likitoci Da Za Su Kula Da Alhazan Jihar
  • Jihar Kebbi Ta Kammala Shirye-shiryen Aikin Hajjin 2025
  • Hajjin 2025: An Fara Yi Wa Maniyyata Allurar Rigakafi A Jigawa
  • Hajjin 2025: Jihar Kwara Ta Fara Allurar Rigakafi Ga Maniyyata
  • Hajjin 2025: Gwamna Namadi Ya Nada Sarkin Kazaure Amirul Hajj
  • Sama Da Masu Sayayya Daga Ketare 220,000 Ne Suka Halarci Bikin Baje Kolin Canton Karo Na 137
  • Talata ce ɗaya ga watan Zhul Qi’ida — Sarkin Musulmi
  • Sarkin Musulmi Ya Ayyana Ranar Talata 1 Ga Watan Zulki’ida
  • Aikin Hajji: Za A Fara Jigilar Alhazan Jihar Kwara A Ranar 12 Ga Watan Mayu