Trump : “Mun yi ganawa mai kyau da Iran”
Published: 22nd, April 2025 GMT
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana gamsuwarsa da yadda tattaunawa tsakanin kasarsa da Iran ke gudana, yana mai bayyana ta a matsayin mai matukar kyau.
Da yake magana da manema labarai a fadar White House jiya litinin, Trump ya ce tattaunawa da akayi da jami’an Iran sun yi matukar inganci.
A ranar 12 ga watan Afrilu ne aka gudanar da zagayen farko na tattaunawar wacce ba ta kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka a shiga tsakanin kasar Oman a birnin Muscat.
Haka zalika a ranar Asabar 19 ga watan Afrilu bangarorin sun yi wa ta biyu a birnin Rome na kasar Italiya, a shiga tsakanin kasar Oman.
kasashen biyu sun bayyana kwarin gwiwar cewa za a ci gaba da tattaunawa, inda za a sake gudanar da mataki na gaba a kasar Oman a ranar Asabar mai zuwa.
Kafin nan kwararu daga kasashen na Amurka da Iran zasu hadu a kasar Oman a gobe Laraba inda zasu tattauna game da shirin nukiliyar na Iran na zaman lafiya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Wulayati: Hanyar Zangezur Wata Shirin Amurka Ne Don Matsa lamba Kan Kasashen Iran Da Rasha
Mai ba da shawara ga Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya bayyana cewa: Hanyar Zangezur wata shiri ne na Amurka don matsawa kasashen Rasha da Iran.
Ali Akbar Velayati mai ba wa Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran shawara kan harkokin kasa da kasa, ya dauki aikin Zangezur (arewa maso yammacin Iran) a matsayin wani aikin Amurka na matsawa kasashen Rasha da Iran lamba.
A cikin wani sako na tunawa da Sheikh Safi al-Din Ardebili, Velayati ya yi tsokaci kan batutuwan da suka shafi Azarbaijan da mashigar Zangezur, yana mai cewa, “Makiya Iran karkashin jagorancin ‘yan sahayoniyyan duniya da Amurka, suna neman ta hanyar tsare-tsare irin su mashigar Zangezur, don ciyar da manyan ayyukan siyasa a karkashin fakewa da wadannan tsare-tsare.”
Ya kara da cewa, manufar farko ita ce raunana gwagwarmaya da yanke alakar Iran da yankin Caucasus da kuma killace Iran da Rasha ta kasa a kudancin yankin.
Ya bayyana cewa: “Wannan aikin ba wai kawai wani bangare ne na shirin Amurka na maye gurbin Ukraine da yankin Caucasus a matsayin wani sabon fage na matsin lamba kan Rasha da Iran ba, amma ana aiwatar da shi ne tare da goyon bayan kungiyar tsaro ta NATO da kuma wasu kungiyoyin ‘yan kishin kasa na Turkiyya (Pan-Turkist).