Nigeria: An Kafa Kwamitin Bincika Hanyoyin Kare Hatsurra Akan Doron Ruwa A Cikin Kasar
Published: 4th, March 2025 GMT
Kwamitin ya kunshi Bola Oyebamiji a matsayin shugaba, wanda kuma shi ne babban darakta na hukumar dake kula da sufuri akan doron ruwa ( NIWA), sai kuma wakilai daga gwamnatocin jihohi, da hukumar matuka kwale-kwale ta cikin gida, hukumar kwararru ta kula da lafiyar zirga-zirga akan doron ruwa. An kuma zabi Adams Offie a mastayin sakataren kwamitin wanda dama shi ne mataimakin darakta na hanyoyin ruwa na cikin gida a wannan ma’aikata.
Ministan ma’aikatar tattalin arziki na ruwa, Adegboyega Oyetola ne ya kaddamar da kwamitin da zai yi aiki tukuru domin kare hatsurran kwale-kwale da kananan jiragen ruwa a cikin kasar.
Ministan da yake Magana a wurin kaddamar da wannan kwamitin a birnin Abuja, ya yi kira da a yi aiki tukuru domin magance yawan hatsurran da ake samu na jiragen ruwa a cikin gida wanda yake haddasa asarar rayuka da dama.
A Nigeria dai ana yawan samun hatsarin kananan jiragen ruwa masu jigilar mutane musamman ma dai a cikin arewacin kasar, da hakan yake haddasa asarar rayuka da yawa. Cunkoson mutanen da suke hawa knanan jiragen da kuma rashin rigunan tsira idan hatsari ya faru, suna cikin dalilin asarar rayuwa masu yawa da ake samu. Haka nan kuma karancin masu ceto mutane da za su zama aikinsu kenan a gabar ruwa, idan aka sami bullar hatsurra.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ambaliyar Mokwa: An sake gano gawa guda bayan kwanaki 8
Kwanaki takwas bayan wata mummunar ambaliyar ruwa da ta mamaye garin Mokwa, hedikwatar Ƙaramar hukumar Mokwa a Jihar Neja, an gano gawar mutum ɗaya daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su.
Mazauna garin sun shaida wa Daily Trust cewa, an tsinci gawar ne a ranar Alhamis a wata gona da ke kan hanyar wucewa kusa da wani wuri da aka fi sani da ‘dam’.
Ambaliya: Gwamnatin Kano ta fara tsaftace magudanan ruwa Abin da muke da shi a Najeriya ba cikakkiyar dimokuraɗiyya ba ce — FayemiA cewar shaidun gani da ido, an kasa tantance wanda abin ya shafa saboda gawar ta lalace. An binne shi ne a inda aka gano gawarsa.
Wata mazauniyar yankin mai suna Tswata Mai Rubutu da ta zanta da Aminiya ta wayar tarho, ta ce an tsinci gawar a kan hanyar da ruwa ke wucewa.
“Gawar wani babban mutum ne, amma ba za mu iya gane shi ba saboda tuni ya fara lalacewa. An binne shi a wurin tun da ba a iya motsa gawar,” in ji shi.
An yi ƙoƙarin jin ta bakin Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Abdullahi Baba Arah, domin ƙarin bayani lamarin ya ci tura.
Tun da farko hukumar ta tabbatar da mutuwar mutane 161, yayin da wasu da dama suka ɓace bayan iftila’in ambaliyar.