NAJERIYA A YAU: Halin jama’a za su shiga idan Kamfanin Kaduna Electric ya ki sauraren ma’aikatansa?
Published: 27th, February 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Wutar lantarki a Najeriya ta zama ginshiƙin rayuwa da al’umma ba sa iya rayuwa ba tare da ita ba. A duk lokacin da aka ɗauke ta al’umma kan shiga matsanancin hali.
Mutane da dama sun dogara ne da wutar lantarki wajen tafiyar da harkokinsu na yau da kullum, kai har ma da na kasuwanci.
A kwanakin baya ne jihohin Kaduna, Sakkwato, Zamfara da kuma Kebbi suka fuskanci ɗaukewar wutar lantarki na tsawon kwanaki, wanda ya jefa al’ummar jihohi cikin halin ni-’yasu.
NAJERIYA A YAU: Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa Da Shi? DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son HaihuwaShirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan halin da al’ummar jihohin da ke ƙarƙashin kulawar kamfanin rarraba wuta na Kaduna Electric za su shiga idan ma’aikatan kamfanin suka shiga yajin aiki.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Lantarki Wutar Lantarki
এছাড়াও পড়ুন:
Hauhawar farashi ya ragu a watan Agusta — NBS
Hukumar ƙididdigar a Najeriya NBS ta bayyana cewa an samu raguwar hauhawar farashin kaya a watan Agusta idan aka kwatanta da watan Yulin da ya gabace shi.
Cikin sabbin alƙaluman da NBS ta fitar a ranar Litinin sun nuna cewa an samu raguwar kashi 1.76 a watan Agustan saɓanin watan Yulin, wanda ya nuna karo na hudu ke nan a jere hauhawar farashin yana sauka.
NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a Legas Kundin Bajinta na Guinness ya taya Hilda Baci murnaRahoton na hukumar NBS na zuwa ne kwanaki bayan da Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin karya farashin kayan abinci ƙasar.
A watanin baya-bayan an riƙa samun raguwar hauhawar farashin kayyaki a ƙasar.
Ko alƙaluman da NBS ta fitar a watan Yuni, ta bayyana cewa hauhawar farashi a Najeriya ya sauka zuwa kashi 22.22 daga 22.97 da aka samu a watan Mayu.
A baya dai dai an yi ta kiraye-kirayen gwamnatin ƙasar ta ɗauki matakan rage hauhawarar farashi domin magance tsadar rayuwa da ake fuskanta a ƙasar.