Aminiya:
2025-09-18@03:44:46 GMT

Dangote ya rage farashin man fetur zuwa N825 a Legas

Published: 26th, February 2025 GMT

Matatar Dangote ta rage farashin man fetur zuwa Naira 825 kan kowace lita a Jihar Legas.

Yanzu haka dai an samu ragin Naira 65, daga farashin da ake siyarwa a kan Naira 890 a baya.

Na gaji bashin 8.9bn a matsayin shugaban APC — Ganduje Boko Haram sun sace mutum 2 da kayan abinci a Borno

Sabon farashin zai fara aiki daga ranar 27 ga watan Fabrairun 2025.

Matatar ta ce wannan matakin na nufin rage wa ‘yan Najeriya wahalhalun da suke fuskanta, yayin da azumin watan Ramadan ke ƙaratowa, tare da tallafa wa manufofin tattalin arziƙi na Shugaba Bola Tinubu.

“Rage farashin man fetur wani ɓangare ne na ƙokarinmu na sauƙaƙa wa ‘yan Najeriya,” in ji matatar Dangote.

“Za mu ci gaba da tabbatar da wadatar man fetur a farashi mai sauƙi.”

Wannan ragi, na nufin za a sayar da man fetur a gidajen mai a Legas kan Naira 860 kan kowace lita, Naira 870 a Kudu maso Yamma, da Naira 880 a Arewacin Najeriya.

A gidajen mai na AP da Heyden, farashin zai kasance Naira 865 a Legas, sai Naira 875 a Kudu maso Yamma, da Naira 885 a Arewacin Najeriya.

“Muna kira ga ‘yan kasuwa su mara mana baya don tabbatar da cewa ‘yan Najeriya sun ci gajiyar wannan sauƙi,” in ji matatar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan Najeriya Matatar Dangote Rage Farashi Ramadan Tattalin Arziƙi

এছাড়াও পড়ুন:

Jihar Jigawa Ta Amince Da Karin Kasafin Kuɗi Na Naira Biliyan 75 Na Shekarar 2025

Gwamnatin Jihar Jigawa  ta amince da ƙarin kasafin kuɗi na Naira Biliyan 75 na shekarar 2025, ga gwamnatin jiha da kuma ƙananan hukumomi 27.

Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan zaman majalisar da aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse, babban birnin jihar.

Ya bayyana cewa, wannan ƙarin kasafin kuɗi ya samo asali ne daga ƙarin kuɗaɗen shiga domin biyan buƙatun kuɗaɗen da suka taso, da kuma ƙarfafa manyan fannoni da za su kawo ci gaba mai ɗorewa a faɗin jihar.

Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce, majalisar ta amince da Naira Biliyan 58 ga gwamnatin jiha da kuma Naira Biliyan 17 ga Kananan Hukumomi 27, wanda ya shafi kashe-kashen kudade na yau da kullum da kuma manyan ayyuka.

Ya ce, wannan ƙarin kasafin kuɗin zai inganta ayyuka da tsare-tsare da ake gudanarwa a muhimman fannoni irin su ilimi, kiwon lafiya, ababen more rayuwa, noma da sauran muhimman ayyukan ci gaba.

Sagir ya ƙara da cewa, za a mika ƙarin kasafin kuɗin ga Majalisar Dokokin Jihar domin tattaunawa da amincewa da shi, kamar yadda kundin tsarin mulki da ka’idojin kasafi suka tanada.

Kwamishinan ya ƙara jaddada cewa, wannan mataki ya nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen gudanar da mulki bisa gaskiya da adalci, da kula da kuɗaɗen jama’a yadda ya dace, da kuma tabbatar da samar da ingantattun ayyuka ga al’ummar jihar baki ɗaya.

 

Usman Muhammad Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Manyan Ma’aikatan FIRS 4 Sun Rasu Sakamakon Gobarar Da Ta Tashi A Ginin Afriland A Legas 
  • Jihar Jigawa Ta Amince Da Karin Kasafin Kuɗi Na Naira Biliyan 75 Na Shekarar 2025
  • DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya
  • Wata Ta Kashe ’Yar Uwarta Kan Bashin Naira 800 A Ondo
  • Jigilar Mai: Me Ya Haddasa Rikicin Dangote Da Ƙungiyar NUPENG?
  • ’Yan ‘Mafiya’ na ƙoƙarin kashe matatar man fetur da na gina —Ɗangote
  • NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba
  • Hauhawar farashi ya ragu a watan Agusta — NBS
  • NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a Legas
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa