Kwara Ta Ware Naira Miliyan Dubu Biyar Don Kula Da Cibiyoyin Lafiyar Jihar
Published: 14th, February 2025 GMT
Gwamnatin jihar Kwara ta ware naira biliyan 5 domin inganta cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda 70 a kananan hukumomin uku na jihar.
Babban Sakatariyar Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Kwara (KWHCDA), Farfesa Nusirat Elelu ce ta bayyana haka a lokacin rattaba hannu kan kwangilolin da aka yi a hedikwatar Hukumar da ke Ilorin.
Ta ce matakin zai hada da inganta ababen more rayuwa, samar da lantarki ta amafani da hasken rana, da samar da wuraren zama na ma’aikata, da samar da ruwan sha da samar da kayan aikin asibiti na zamani a duk wuraren da ke amfana da cibiyoyin kiwon lafiya na farko.
Farfesa Elelu ya bayyana cewa shiga tsakani na zuwa ne tare da tallafin da Bankin Duniya ke tallafawa.
Ta yi nuni da cewa shirin zai sa cibiyoyin kula da lafiya matakin farko su kasance masu inganci don samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya a matakin farko a fadin jihar.
Kwamishinan ya ce gaba daya makasudin shi ne a mayar da dukkan cibiyoyin PHC ‘daidai da manufa’ tunda tsarin PHC shi ne farkon tuntuɓar tsarin kiwon lafiyar ƙasa.
Farfesa Elelu ya roki duk wadanda suka yi nasara da su tabbatar sun samar da ingantattun ayyuka don tabbatar da amanar da aka ba su.
A nasa bangaren manajan shirin na IMPACT, Dr. Michael Oguntoye, ya ce za a bayar da kwangilar ne cikin watanni 3 kuma jihar ba za ta lamunci tsaikon wajen aiwatar da aikin ba.
Dr.Oguntoye ya kara da cewa wadanda suka fara cin gajiyar shirin na IMPACT su ne yara da mata ‘yan kasa da shekaru biyar, inda ya ce aikin zai kuma inganta samar da ayyukan kiwon lafiya ga daukacin mazauna jihar.
Cov/Ali Muhammad Rabiu/Wababe
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Gyara Kwara Lafiya a matakin farko kiwon lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar Kula da Da’ar Ma’aikata Za Ta Fara Daukar Bayanai Ta Yanar Gizo
Hukumar kula da da’ar ma’aikata ta sanar da cewa, a halin yanzu ana iya bayyana kadarorin ma’aikatan ta hanyar yanar gizo, wani mataki da aka tsara domin saukaka aikin da kuma kara yin lissafi.
Daraktan ofishin na jihar Jigawa Abubakar Bello ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Muhammad K. Dagaceri a ofishin sa.
Abubakar Bello ya jaddada cewa sabon shirin na da nufin rage dinbin aikin dake gaban ma’aiakata da kuma saukaka tantance kadarorin domin yaki da cin hanci da rashawa a cikin tsarin.
“Mun sauya dabara zuwa rajista ta yanar gizo don bayyana kadarorin, muna ba wa mutane damar kammala aikin daga gidajensu. Duk da haka, muna neman goyon bayan ku don tabbatar da cewa an sanar da jami’an gwamnati tare da karfafa gwiwar su bi wannan sabon tsari,” in ji shi.
Da yake mayar da jawabi, shugaban ma’aikata na jiha Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ya yi alkawarin wayar da kan jami’an gwamnati cikin tsanaki game da muhimmancin bayyana kadarorin su, kamar yadda hukumar da’ar ma’aikata ta ba su umarni.
Ya tunatar da cewa rashin yin biyayya ga kundin tsarin mulkin kasa ne.
Dagaceri ya bada tabbacin bada goyon baya da hadin kai domin cimma burin da ake so na wannan shiri.
USMAN MZ