Babu Wata Tsokana Da Sojojin Amurka Za Su Yi Da Za Ta Iya Canza Matsayin Yankin Taiwan
Published: 14th, February 2025 GMT
Yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin, Zhang Xiaogang ya fitar da sanarwa kan batutuwan da suka shafi aikin soja a baya-bayan nan. Ya ce, Taiwan wani bangare ne na kasar Sin. Kuma babu wata tsokana da sojojin Amurka za su yi da za ta iya canza wannan lamari, sabanin haka, za ta iya nuna munafuncin da Amurka ta dade ta na yi ga al’ummomin duniya, kuma za ta iya kara karfafa niyyar jama’ar kasar Sin ta kare ikon kasa da cimma cikakkiyar dunkulewar yankunan kasar baki daya.
Game da zarge-zarge marasa tushe da sabon ministan tsaron Amurka ya yi kan Sin, Zhang Xiaogang ya ce, Sin na adawa sosai da hakan. Kuma jama’ar kasar Sin na son zaman lafiya. Bugu da kari, ya ce a ko da yaushe, bangaren Sin ba zai tayar da yaki don habaka kasar ba, kuma ba zai yi watsi da iko da moriyarsa ba, kana zai tsaya tsayin daka kan tinkarar duk wata barazana da kalubale.(Safiyah Ma)
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma
A nata bangare, Amurka za ta dage aiwatar da matakai bisa bincikenta karkashin sashe na 301 na dokar cinikayya ta 1974, wanda zai shafi sashen jiragen ruwa na Sin, da hidimomin sufurinsu, da na kirar jiragen ruwan na Sin da karin shekara daya. Sakamakon hakan, ita kuma Sin za ta dage aiwatar da matakan martani ga sashen Amurka a wannan fanni da shekara daya, da zarar Amurkan ta aiwatar da na ta matakan.
Kakakin ya ce “An Kai Ruwa Rana” kafin cimma wannan sakamako, kuma Sin na fatan ganin ta ci gaba da aiki tare da tsagin Amurka, ta yadda za su hada karfi wajen tabbatar da an aiwatar da sakamakon, da ingiza karin tabbaci, da daidaito cikin dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin sassan biyu, da kuma tattalin arzikin duniya baki daya. (Saminu Alhassan)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA