Shugaban Kasar Iran Yace Kasar Ba Zata Jada Baya Saboda Takunkuman Amurka Ba
Published: 8th, February 2025 GMT
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshiyan ya bayyana cewa, kasar Iran ba zata jada baya ba, kuma ba zati yi rauni ba saboda takunkuman zaluncin da kasashen yamma suka dorawa kasar. Ya ce kasar tana da arzikin da zata ci gaba da kasancewa a gaba da kasashen da dama a yankin Asiya ta kudu, duk tare da wadannan takunkuman.
Tashar talabijin ta Press tv ta nakalto shugaban yana fadar haka a yau Asabar a garin Sirjan, daga na kudu masu gabacin lardin Kerman. Inda ya gabatar da kamfanoni da ayyukan jama’a wadanda aka kammala, wadanda suka hada har da sabbin wuraren yawon bude ido da kuma shakatawa.
Shugaban y ace, kasar Iran ba zata jada baya ba, sannan makiyan kasar sun yi kuskura sun kuma kara yan wata, juyin juya halin musulunci wanda ya sami nasara a shekara 1979 a halin yaanzu ya ciki shekaru 46 da yardarm All..wadannan sararo zasu ci gaba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Da Iraki Sun Ce An Kammala Shimfida Layin Dogo Daga Shalamcheh Zuwa Basra
A wani taro wanda ya hada ministan riko na tattalin arziki da kudade na JMI da kuma mai bawa firai ministan kasar Iraki shawara, bangarorin biyu sun tabbatar da cewa an kammala aikin shimfida layin dogo tsakanin garin Shalamcheh na kasar Iran da kuma birnin Basra a kasar Iraki.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jami’an gwamnatocin kasashen biyu na fadar haka, sun kuma jaddada muhimmancin layin dogon da kuma samar da kasuwar babu kudaden fito a kan iyakokin kasashen biyu.
Labarin ya kara da cewa harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu ya zuwa yanzu ya kai dalar Amurka biliyon $11a ko wace shekara kuma anan saran nan gaba zai iyakaruwa zuwa dalar Amurka biliyon $25.
Rahmatollah Akrami, ministan riko na tattalin arziki da kudade na JMI, da kuma Hazem Majid Naji Al-Khalidi mai bawa firai ministan kasar Iraki shawara sun jaddada muhimmancin kammala layin dogo tsakanin kasashen biyu, da kuma kasuwar ba kudaden fito tsakanin kasashen biyu. Da kuma fatan zasu yi kokarin amfanar juna gwagwadon abinda zasu iya.