2025-09-18@03:45:53 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2643
«Kwalejin Koyon Tukin Jiragen Sama»:
Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Batun cikin gidan kasar Labanon ya jaddada cewa, kungiyar ba za ta taba mika makamanta ba matukar dai Isra’ila na mamaye da wani yanki na Lebanon, ko kuma akwai barazana a kan kasar. A yayin jawabin nasa, Sheikh Naim ya nanata katsalandan din wuce gona da iri da...
Ministan harkokin wajen Masar Badr Abdel Aty ya tattauna da takwaransa na Tunisiya Mohamed Ali Nafti kan batutuwa da dama da suka shafi yankin gabas ta tsakiya a gefen taron majalisar ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC a birnin Jeddah na kasar Saudiyya. Dangane da ci gaban da halin da ake...
“Mun yi tattaunawar gaskiya, amma gwamnati tana yi mana wasa,” in ji shi. Ya ce an yi watsi da rahotanni masu muhimmanci, an kafa manufofin da ke cutar da ilimi, sannan an jefa malaman da suka yi ritaya mummunan hali. “Wannan gwamnati ta raina ilimi da malamai. Mun gaji,” in ji shi. Shugaban ASUU ya...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiyan ya godewa kasar Rasha saboda goyon bayanta ga kasar kan hakkinta na tace makamashin uranium, musamman a taron kwamitin tsaron MDD wanda za’a gudanar nan gaba dangane da kudurin kwamatin mai lamba 2231 dangane shirin nukiyar kasar Iran ta JCPOA, Inda kasashen turai 3 wato triko wadanda suke bukatar sake...
Wata mata mai aikin shara da goge-goge, Fa’iza Abdulkadir, ta mayar da kuɗi har N4.8m da aka yi kuskuren tura wa asusun bankinta a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno. Da take zantawa da News Central a Maiduguri, Fa’iza wadda take ɗaukan albashin Naira dubu 30 duk wata ta ce ta yanke shawarar mayar da kuɗin...
Sojojin Najeriya sun kashe ’yan ta’adda kimanin 35 da ake zargin mayakan kungiyar ISWAP ne a kusa da iyakar Najeriya da Kamaru. ’Yan ta’addan sun taru a yankin Kumshe, wani gari da ke kan iyaka a Jihar Borno, da safiyar Asabar domin kai hari kan sansanin sojoji da ke yankin. Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa...
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa: Hadin kan al’umma, jami’ai, da sojojin da ke dauke da makamai, jan layi ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa: Bayan da makiya suka kasa murkushe al’ummar Iran ta hanyar yaki, a halin yanzu suna neman cimma manufarsu ta...
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Gudanar da hidima wa mutane aikin kowa ne Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa yi wa al’umma hidima aiki ne na kowa da kowa, yana mai bayanin cewa hadin kai da fahimtar juna kan kasa suna samun nasarar gudanar da mulki da tsayin daka wajen tunkarar makiya....
Kwamandan sojojin Iran ya yi barazanar mayar da martani mai muni da zai haifar da nadama ga makiya Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya jaddada cewa: Sojojin kasar Iran da jarumtarsu suna tsayawa da dukkan karfinsu wajen fuskantar barazanar makiya. A yayin ziyarar da ya kai Jami’ar Kimiyyar Sojin Ruwa ta...
Kafofin yada labarai na yahudawan sahayoniyya sun yarda da gazawar dakile Yemen daga ci gaba da ayyukan soji kan Isra’ila Kafofin yada labaran Isra’ila, wadanda tashar 12 da tashar ta 13 ke wakilta, sun amince da cewa: Hare-haren da makiya ke kaiwa kasar Yemen, ya gaza hana sojojin Yemen harba makamai masu linzami zuwa yankunan...
Isra’ila ta kaddamar da wani farmaki ta sama a kan babban birnin kasar Yemen Sanaa a jiya Lahadi, inda ta kai hare-hare a yankin kudu maso gabashin birnin San’a. Wakilin tashar Almayadeen ya bayyana cewa, Isra’ila ta kai harin ne kan wani gidan mai a kudu maso gabashin birnin San’a mallakin kamfanin mai na kasar...
Ɗariƙar Tijjaniyya a Jihar Gombe, ta yi babban rashi bayan rasuwar ɗaya daga cikin fitattun malamanta, Sheikh Umar Bojude. Sheikh Bojude shi ne babban limamin Masallacin Juma’a na Alhaji Gidado Dalibi Yahaya (AG Dalibi). Japan za ta bai wa Najeriya rancen $190m don inganta wutar lantarki Rikici ya kunno kai a jam’iyyar ADC a Gombe...
Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa Najeriya za ta karɓi rancen dala miliyan 190 daga Ƙasar Japan domin inganta wutar lantarki. Wannan na cikin wata sanarwa da ma’aikatar lantarki, yayin da ake gudanar fa taron ƙasashen Afirka da ke gudana a birnin Yokohama na Ƙasar Japan. Mutum 6 sun rasu yayin tsere wa ’yan...
Aƙalla mutane shida sun rasa rayukansu, yayin da har yanzu an nemi wasu uku an rasa, sakamakon kifewar kwale-kwale a Garin Faji na Ƙaramar Hukumar Sabon Birni da ke Jihar Sakkwato. Lamarin ya faru ne lokacin da mazauna yankin ke tsere wa wani harin ‘yan bindiga da misalin ƙarfe 5:30 na safiyar Alhamis, 21 ga...
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) a jihar Kano ta bayyana cewa akwai katin zaɓe na dindindin (PVC) sama da dubu 367,000 da jama’a ba su karɓa ba har yanzu a jihar. Kwamishinan INEC na Kano, Ambasada Abdu Zango, ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi tawagar kwamitin gwamnatin jihar kan rajistar...
Mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Fluminense Fabio a ranar Talata ya zama mutum na farko a tarihin wasan kwallon kafa na maza da ya buga yawan wasanni a tarihi, lokacin da dan Brazil din ya buga wasa karo na 1,391. Dan wasan mai shekaru 44 a ranar Asabar ya yi daidai da tarihin...
Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran, Imam Sayyid Aliyul Khaminae, yace mafarkin da gwamnatin Amurka take yi na JMI ta yi biyayya a gareta, abu ne wanda ba zai taba faruwa ba. Ya kuma yi gargadi ga mutanen kasar su yi hattara da kokarin raba kansu. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran...
Dakarun kare juyin juya halain Musulunci a nan Iran sun nuna goyon bayansu ga gwamnatin JMI, sun kuma yaba da ayyukan da gwamnatinn take yi na kawo ci gaban kasar. Tashar talabijian ta Prestv a nan Tehran ta nakalto dakarun na IRGC na bayyana haka a wani rahoton da suka fitar wanda yayi dai dai...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin kasar Armenia ta yi alkawalin cewa babu wani sojojin Amurka da zai shiga yankin kaukas ta kudu kusa da kanika da kasar Iran. Musamman ta san cewa Iran bata son haka hakama kasar Rasha. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Arachi...
Jakadann Amurka na musamman a kasar Lebanon Tom Barrack ya bayyana cewa ya yarda da matakan da gwamnatin kasar Lebanon take dauka don kwance damarar kungiyar Hizbulla ta kasar, Shafin yanar gizo na Alarabia na kasar Saudiya ya bayyana cewa Barrack ya shaidawa gwamnatin kasar Lebanon kan cewa yana kirin kungiyar Hizbullah da kuma kasar...
Gwamnatocin kasashen Iran da Pakisatan sun amince su ninninka yawan kayakin noma na kasuwanci a tsakaninsu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto minitan noma na kasar Iran Jihad Gholam reza Nouri yaqna fadar haka a jiya litinin ya kuma kara da cewa kasashen biyu zasu karfafa harkokin siyasa da kuma tattalin arziki...
Gwamnatin Tarayya ta rage farashin jinyar ciwon ƙoda daga kimanin N50,000 zuwa N12,000 a Asibitocin Tarayya — ragin da ya kai kashi 76 cikin 100. Wannan saukin farashi ya samu ne bayan amincewar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, kamar yadda mai ba shi shawara kan harkokin sadarwa da manufofi, Daniel Bwala, ya bayyana a cikin...
Allah Ya yi wa Alhaji Ahmed Momohsani Ododo, mahaifin Gwamna Ahmed Usman Ododo na Jihar Kogi, rasuwa yana da shekara 83 a duniya. Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa na Jihar Kogi, Kingsley Femi Fanwo, ya sanar da rasuwar a yammacin ranar Litinin, 18 ga Agusta, 2025. Gwamnatin jihar ta bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga...
Wani mutum ya soka wa budurwarsa mai suna “Ima” wuka har lahira a unguwar Okereke Street da ke garin Fatalkwal na Jihar Ribas. Mutumin, wanda ake wa lakabi da “Doctor” ya daba wa budurwar tasa mai suna “Ima” wuka ne bisa zargin tana cin amanarsa. Lamarin ya faru ne da yammacin Lahadi, wanda shaidu a...

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Ce: Gwamnatin Mamayar Isra’ila Barazana ce Ga Tsaron Yanki
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan sahayoniyya barazana ce ga wanzuwar tsaron yankin Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Yahudawan sahayoniyya suna wakiltar wata barazana ga wanzuwa tsaro da zaman lafiyar yankin da kuma kasashensu. Idan ba a dakile wannan barazanar ba, to babu shakka yankin zai...
Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya yi ta’aziyya ga gwamnatin Jihar Kebbi da al’ummar jihar bisa rasuwar Sarkin Zuru, Mai Martaba, Manjo Janar Muhammadu Sani Sami (Gomo II). A cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasan shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Bayo Onanuga ya fitar, ya bayyana rasuwar Sarkin a...
Mama Lydia Yilwatda, mahaifiyar shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ta rasu. Mai magana da yawun jam’iyyar APC a Jihar Filato, Shittu Bamaiyi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Jos ranar Lahadi. Jirgin ruwa ya nutse da mutum 30 a Sakkwato Adam A. Zango ya auri jarumar Kannywood...
Mama Lydia Yilwatda, mahaifiyar shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ta rasu. Mai magana da yawun jam’iyyar APC a Jihar Filato, Shittu Bamaiyi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Jos ranar Lahadi. Jirgin ruwa ya nutse da mutum 30 a Sakkwato Adam A. Zango ya auri jarumar Kannywood...
Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da rabon sabbin baburan hawa ga shugabannin jam’iyyar APC na mazabun kananan hukumomi 12 na shiyyar Jigawa ta Arewa maso yamma wadda Sanata Babangida Hussaini Kazaure ya bayar da kyauta. A jawabin sa, Gwamna Umar Namadi ya yaba da kokarin Sanatan tare da shawartar shugabannin da suka sami ababan...
Gwamnatin Jihar Jigawa tace tana gudanar da ayyukan gyara da ginawa da kuma inganta hanyoyin mota domin cimma kudirin ta na bunkasa bangaren aikin noma. Gwamna Umar Namadi ya bayyana haka yayin kaddamar da aikin sanya kwalta akan hanyar Dandi da Farin Daba zuwa Gada a karamar hukumar Kazaure. Ya ce gwamnatin jihar ta...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Suna sa ido kan abubuwan da ke faruwa a Kudancin Caucasus cikin lura Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, Ismail Baqa’i, ya yi nuni da yadda Iran ke daukan abubuwan da ke faruwa a yankin arewa maso yammacin kasar da muhimmanci, yana mai jaddada cewa: “Suna...

Babban Sakataren Majalisar Tsaron Kasar Iran Ya Bayyana Cewa; Ba Zasu Amince Da Shiga Tsakanin Iran Da Iraki Ba
Babban sakataren majalisar kolin tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Ba zasu yarda wasu kasashe su shiga tsakanin Iran da Iraki ba Yayin da yake magana game da rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro tsakanin Iran da Iraki, babban sakataren majalisar koli na tsaron kasar Iran Ali Larijani ya yi nuni da cewa: Bai kamata a...

Gwamnatin DR Kongo Ta Nuna Rashin Amincewarta Da Zabin Kenya Kan Wajen Da Zata Bude Karamin Ofishin Jakadancinta A Kasarta
Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ta ki amincewa da nadin sabon karamin ofishin jakadancin Kenya a birnin Goma Gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango ta sanar da kin amincewa da nadin sabon karamin ofishin jakadancin Kenya a birnin Goma da ke gabashin kasar, duba da matakin da ya saba wa ka’idojin diflomasiyya, duba da yadda Kongo ke ganin ci...
Al’ummar unguwar Jauro Jatau da ke hanyar Bypass a Ƙaramar Hukumar Akko, Jihar Gombe, sun koka kan tsawon watannin da suka shafe ba tare da wutar lantarki ba. Sun roƙi gwamnati, ’yan siyasa da masu hannu da shuni su kawo musu ɗauki cikin gaggawa. Gwamnonin Arewa sun yi ta’aziyyar rasuwar Sarkin Zuru Adam A. Zango...
Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, ta bayyana alhininta game da rasuwar Sarkin Zuru na Jihar Kebbi, Mai Martaba Manjo Janar Muhammadu Sani Sami (mai ritaya) Gomo II, wanda ya rasu yana da shekaru 81. Shugaban ƙungiyar, Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ce marigayin jagora ne mai kishin ƙasa, dattijo nagari kuma basarake mai daraja wanda...
Sarkin Zuru, Alhaji Mohammed Sani Sami Gomo II, ya rasu a ranar Asabar, 16 ga Agusta, 2025, a wani asibiti da ke birnin London bayan gajeruwar rashin lafiya. Ya rasu yana da shekaru 82. A cewar majiyoyin danginsa, ana sa ran za a kawo gawarsa daga London zuwa Najeriya nan da gobe (Litinin), domin gudanar...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya aika da jajensa ga mutane da Firai ministan kasar Pakisatan kan ambaliyar ruwa da ta faru a kasar bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 300 da kuma bacewar wasu. Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran ya bayyana cewa shugaban y...
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian na Shirin wata kai wata muhimmiyar ziyara a kasashen Armeniya da Belarus. A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, mai baiwa shugaban kasar shawara Mahdi Sanaei, ya ce Pezeshkian zai bar Tehran zuwa Yerevan a ranar Litinin din nan, sannan ya wuce Minsk. Ya kara...
Firaministar kasarDenmark Mette Frederiksen, wadda a halin yanzu kasarta ke rike da shugabancin kungiyar Tarayyar Turai ta bayyana a wata sanarwa ga manema labarai a jiya Asabar cewa, kasarta na shirin kakabawa Isra’ila takunkumi, sakamakon yakin da take yi a zirin Gaza da yammacin kogin Jordan. A wata hira da ya yi da Jyllands-Posten, Frederiksen...
Jakadan Iran a Saudiyya Alireza Enayati ya tabbatar da ci gaba da tuntubar juna tsakanin babban hafsan hafsoshin sojin Iran da ministan tsaron Saudiyya. A wata hira da kamfanin dillancin labarai na IRNA Alireza Enayati ya yi nuni da cewa, Saudiyya na kallon alakar ta da Iran a matsayin alaka mai matukar muhimamnci, kamar yadda...
Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu a Zirin Gaza ta sanar a yau cewa akalla mutane 70 suka yi shahada da suka hada da 8 da aka gano gawarwakinsu, yayin da wasu 385 suka jikkata a cikin kasa da sa’o’i 24 da suka gabata, sakamakon hare-haren da Isra’ila a sassa daban-daban na yankin. Ma’aikatar ta yi nuni...
Gwamnatin Jihar Kwara ta ce za ta yi haɗin gwiwa da Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa (FAAN) da sauran masu ruwa da tsaki domin mayar da jihar cibiyar fitar da kayan gona da na kasuwanci. Kwamishinan Noma da Ci gaban Karkara na jihar, Dakta Afees Abolore, ne ya bayyana haka a wani taron da...

Jami’in Harkokin Shari’ar Kasa Da Kasa Na Iran Ya Yi Tofin Allah Tsine Kan Furucin Jami’ar Shari’ar Kasa Da Kasa
Mataimakin ministan harkokin waje kan harkokin shari’a da kasa da kasa ya mayar da martani ga son zuciya da wani jami’in kasa da kasa ke yi game da mamayar ‘yan sahayoniyya Mataimakin ministan harkokin waje kan harkokin shari’a da kasa da kasa, Kazem Gharibabadi, ya yi tsokaci game da kalaman mataimakiyar shugaban kotun kasa da...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa; Suna godiya ga Iraki saboda karimcin da ta yi wa masu ziyarar Arba’een na Imam Husain {a.s} Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yaba da kokarin gwamnati da al’ummar Iraki wajen karbar bakwancin masu ziyarar juyayin Arba’een na Imam Husaini {a.s}. A yayin da yake...
A wasu yankunan Jihar Katsina da suka daɗe cikin fargaba da hare-haren ’yan bindiga, zaman lafiya ya fara dawowa sakamakon sulhu da al’umma suka yi da masu tayar da ƙayar baya. Wannan sulhu, wanda ba a haɗa gwamnati ba, ya bai wa manoma damar komawa gonakinsu cikin daminar bana. Manoma sun fara noma cikin...
An kammala taron tattaunawa tsakanin shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Amurka Donald Trump a birnin Alaska na kasar Amurka, inda bangarorin biyu suka bayyana taron a matsayin mai matukar amfani. Fadar Kremlin ta tabbatar da cewa tattaunawar ta yi armashi, yayin da manzon musamman na Rasha Kirill Dmitriev ya bayyana cewa yanayin...
“Tsarin mulkin ADC ta bayyana cewa duk wanda ke neman zama shugaban jam’iyyar, dole ne ya kasance mamba nagari na jam’iyya. Wannan shi ne muhimman bukata ta asali wadda ba za a iya yin watsi da ita ko kauce mata ta kowace hanya ba. “A cewar tsarin mulkin ADC, hanyar da ta dace don cike...
Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka yi a garin Potiskum a daren Juma’a zuwa safiyar yau Juma’a ya haifar da ambaliya, wanda ya haifar da tashin hankali ga mazauna garin. Kamar yadda majiyar da ke garin ta shaidawa Aminiya cewa, ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka fara shi tun kusan tsakar...
“Sama da yara miliyan 10.1 ne ba su kai makaranta, kashi 70 masu zuwa makarantar kuma ba su da dabarun koyo, kuma fiye da kashi 60 na malaman firamare na gwamnati ba su da ilimin dijital,” in ji ta Da take yaba wa gwamnatin Koriya ta Arewa bisa tallafin da ta samu ta hannun hukumar...
“Manufar ita ce a ninka adadin likitoci, ma’aikatan jinya, masu hada magunguna, kwararrun dakunan gwaje-gwaje da sauran kwararru a fannin kiwon lafiya. Wannan ko shakka babu zai kara habaka harkokin kiwon lafiya a kasar,” in ji shi. Tsohon gwamnan Jihar Katsinan ya bayyana cewa, a bana, TETFund ta samu tallafinta mafi girma na Naira Tiriliyan...