Gwamnatin Kuros Riba ta bankaɗo ma’aikatan bogi 800
Published: 13th, September 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Kuros Riba, ta ce ta gano ma’aikatan bogi har guda 800 a wasu ma’aikatun jihar.
Tun da farko, an daɗe ana zargin gwamnatin da ta gabata ƙarƙashin Farfesa Ben Ayade da biyan albashi ga wasu mutane da ba ma’aikatan gwamnati ba, musamman a ƙananan hukumomin jihar.
HOTUNA: Mahaifiyar Dangote ta halarci gasar karatun Alƙur’ani ta Shetty a Kano Hilda Baci ta kafa tarihin dafa shinkafa buhu 200 a tukunya gudaKwamishinan ma’aikata ƙananan hukumomi, Darlington Bassey Eyo ne, ya tabbatar da hakan a Kalaba ranar Juma’a.
Ya bayyana cewa gwamnati ta fara aikin tantance ma’aikata tun farkon shekarar nan, inda ta duba kowace ma’aikata ɗaya bayan ɗaya.
A cewarsa, wannan ne ya sa suka gano ma’aikatan bogi da yawansu ya kai 800.
Eyo, ya nanata cewa gwamnatin Bassey Otu, ta ƙudiri aniyar kawar da ma’aikatan bogi ta hanyar tantance ma’aikatan jihar baki ɗaya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gwamnati Kwamishina Tantancewa
এছাড়াও পড়ুন:
An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta sanar da samun nasarar cafke Ifeanyi Eze Okorienta, wanda aka fi sani da “Gentle de Yahoo”, ɗaya daga cikin manyan kwamandojin ƙungiyar IPOB, a wani samame da ta kai a yankin kudu maso gabashin ƙasar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito wata majiya daga hedikwatar rundunar sojin tana cewa an cafke Gentle de Yahoo ne yayin farmakin da sojojin suka kai a ranar Lahadi kan sansanonin ’yan ƙungiyar a cikin wani dajin da ke ƙaramar hukumar Okigwe a Jihar Imo.
An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a RibasMajiyar ta ce a yayin cafke jagoran na IPOB, an kuma ƙwato makamai da dama daga hannunsa, ciki har da bindigogi kirar Turai, harsasai, kakin sojoji da na ’yan sanda.
“Cafke wannan kwamanda babban ci gaba ne wajen murƙushe ayyukan ta’addanci da ƙungiyar IPOB ke aikatawa, musamman a yankunan da suke hana zaman lafiya,” in ji majiyar.
Kungiyar IPOB, wacce ke fafutukar ballewa daga Najeriya don kafa ƙasar Biyafara, ta kasance a gaba-gaba wajen aikata hare-hare da ta da tarzoma a jihohin kudu maso gabas, musamman ta hannun sashen rundunar da suka kafa da kansu mai suna Eastern Security Network (ESN).
Ana dai zargin cewa Eze yana ɗaya daga cikin jagororin da ke tsara harin kwantan bauna, da hana zirga-zirga a wasu sassan yankin, wanda hakan ya jefa al’umma cikin fargaba da zaman ɗar-ɗar.
Wannan nasara na zuwa ne bayan makonni kaɗan da wata kotu a ƙasar Finland ta yanke wa Simon Ekpa, wani babban jigo a ƙungiyar IPOB, hukuncin ɗaurin shekaru shida a gidan yari kan laifukan da suka shafi ta’addanci da tayar da zaune tsaye.
Masu sharhi na ganin cewa cafke Gentle de Yahoo wata alama ce da ke nuna cewa ana shirin ragargaza ƙungiyar IPOB gaba ɗaya, duk da cewar har yanzu akwai sauran rina a kaba, musamman ganin cewa wasu sassan yankin na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro.