Kiristoci sun yi addu’ar ɗorewar zaman lafiya a Kudancin Kaduna
Published: 29th, January 2025 GMT
Ƙungiyar Shugabannin Kiristoci na Kudancin Kaduna (SKCLA) ta yi kira ga al’ummar yankin da su rungumi haɗin kai da ƙaunar juna a matsayin tubalin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba.
Shugaban ƙungiyar SKCLA, Fasto Emmanuel Nuhu Kure ne ya yi wannan kiran ga mazauna yankin a wajen taron addu’ar shekara-shekara da ake gudanarwa a garin Kafanchan don kyautata alaƙarsu da Ubangiji tare neman ɗauki daga gare Shi don samun zaman lafiya da wadata.
“Lokaci ya yi da za mu haɗa kai da tunanin mu waje ɗaya da manufa ɗaya don sake gina al’ummomin Kudancin Kaduna,” inji Kure.
“Dole ne mu koyi son makwabtanmu musulmai ba tare da wariya ba. Idan har babu haɗin kai, ba za mu samu makoma mai kyau ba.”
Malamin ya jaddada buƙatar sake gina yankin inda ya yaba wa Gwamnatin Tarayya da ta jiha kan inganta tsaro a yankin.
“A cikin shekaru biyu da suka gabata zamu iya cewa mun samu zaman lafiya, yanzu za mu iya numfasawa da kyau kuma mu yi barci idanunmu biyu a rufe, muna jin daɗin zaman lafiyar da ke gudana,” inji shi.
Kure ya kuma yi kira ga manyan mutane daga Kudancin Kaduna da su yi amfani da wannan damar na zaman lafiya wajen kafa masana’antu da za su samar da aikin yi ga matasan yankin ba tare da jiran gwamnati sai ta yi komai ba.
Babban baƙo mai jawabi, Bishop Zakka Nyam na Cocin Anglikan da ke Kano, ya bayyana fatansa na kasancewar shekara 2025 da ta zamo shekarar sauyi ga Kudancin Kaduna.
Ya ce lokaci ya yi da jama’ar yankin za su yi watsi da dabi’ar yawaita gine-ginen Otal a yankin maimakon haka su fara gina masana’antu don sarrafa abubuwan da ake nomawa a yankin.
A nasa jawabin, Mataimakin Kakakin Majalisar Dokoki na Jihar Kaduna, Hon. Henry Magaji Danjuma ya bayyana yankin Kudancin Kaduna a matsayin yanki mai yalwar albarkatu, tare da yin kira ga mazauna yankin da su mara wa gwamnatinsu baya don samun ƙarin romon dimokuraɗiyya.
An gudanar da addu’o’i da waƙe-waƙen ibada musamman don ceto yankin, da Jihar Kaduna da kuma ƙasar baki ɗaya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: zaman lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Manyan makarantu 2 ne kacal ke da rajista a Katsina — Gwamnati
Kwamitin da Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umari Radda, ya kafa domin binciken ayyukan makarantun gaba da sakanadare masu zaman kansu na jihar, ya tabbatar da cewa, 37 cikin 39 ba su da rajista da gwamnati.
Shugaban kwamitin, Farfesa Ahmed Muhammad Bakori, ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ƙaramar hukumar Bakori da ke jihar.
Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Maiduguri Sojoji sun daƙile hari, sun kashe mayaƙan Boko Haram 9 a BornoBakori, wanda shi ne Kwamishinan Harkokin Noma na jihar, ya ce binciken kwamitin ya gano cewa makarantu biyu masu zaman kansu ne kacal a faɗin jihar ke da cikakkiyar rajista da hukumomin da suka dace.
“Jihar Katsina na da makaruntun gaba da sakanadare na gwamnati huɗu da ke bayar da takardar shaidar difloma da koyarwa, sai kuma ƙarin 39 masu zaman kansu.
“Sai dai bincikenmu ya bankaɗo biyu ne kacal a cikin 39 suke da cikakkiyar rajista da hukumomi.”
Kwamishinan, ya kuma ce shida daga cikinsu na buƙatar gyare-gyare domin kammala rajistar, yayin da 22 ke aiki ba tare da rajistar ba.
“Ƙarƙashin sabon tsarin da muka ɗauka yanzu, ya zamo dole makarantun da ke bayar da takardar shaidar digiri su yi rajista da Hukumar Jami’o’i ta Ƙasa (NUC).
“Masu difloma kuma da Hukumar Kula da Ilimin Fasaha (NBTE), sai masu koyarwa da Hukumar Kula da Kwalejin Ilimi ta Ƙasa (NCCE).
Bakori, ya jaddada cewa, duk makarantar da ta saɓa wa wannan tsarin, a shirye gwamnatin take ta rufe ta.
Sai dai ya yi wa ɗaliban da ke makarantun albishir ɗin cewa gwamnatin za ta tabbatar ta sauya musu makaranta zuwa masu rajista daga waɗanda ba su da su, idan buƙatar rufe su ta taso.