Gwamna ya aike wa majalisa dokar haramta auren jinsi ɗaya a Kano
Published: 12th, September 2025 GMT
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da mika kudirin dokar haramta auren jinsi daya, luwadi da madugo ga Majalisar Dokokin Jihar domin amincewa da shi a matsayin doka.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Juma’a, ya ce gwamnan ya bayar da umarnin ne yayin zaman majalisar zartarwar jihar karo na 31 da aka gudanar a reshen gidan gwamnati da ke Kwankwasiyya City a Kano.
Gwamna Yusuf ya ce gwamnatinsa ba za ta sassauta kan koyarwar addinin Musulunci ba, yana mai jaddada cewa dole ne Kano ta ci gaba da kare al’adu da addinin mutanen jihar.
Ya ce kudirin dokar ya haramta auren jinsi da kuma wasu dabi’u na madugo da luwadi, wadanda gwamnati ke dauka a matsayin haramtattu.
“Babu wani yanayi da za mu amince da ayyukan da suka sabawa addininmu da al’adunmu su samu gindin zama a Kano. Wannan gwamnati na da alhakin kare mutuncin zamantakewarmu,” in ji gwamnan.
Da zarar majalisar dokoki ta amince da kudirin ya zama doka, duk wanda aka samu da laifin aikata ko tallata auren jinsi da makamancin haka zai fuskanci hukunci mai tsauri.
Gwamna Yusuf ya nuna kwarin gwiwarsa cewa ‘yan majalisar za su amince da kudirin cikin gaggawa, la’akari da muhimmancinsa ga tarbiyya da zamantakewar mutanen jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Luwadi
এছাড়াও পড়ুন:
Yanzu-yanzu: Shugaba Tinubu Ya Ɗage Dokar Ta-ɓaci A Jihar Ribas
A yau, 17 ga watan Satumba, Shugaba Tinubu ya ɗage dokar ta-ɓaci da ya ƙaƙaba wa al’ummar jihar Ribas biyo bayan rashin jituwa da yaƙi ci yaƙi cinyewa da ya dabaibaye ɓangaren zartarwa da na dokokin jihar. Cikakken bayani na nan tafe…
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp