Yobe na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya mafi zaman lafiya – Buni
Published: 24th, April 2025 GMT
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ce a yanzu jihar na ɗaya daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a Najeriya.
Ya ce, a matsayinsa na babban jami’in shari’a da tsaro a Jihar Yobe, yana da haƙƙin ganin an bi doka don tabbatar da cewa jihar ta samu zaman lafiya.
An kama mata 2 na ƙoƙarin sayar da ƙananan yara da aka sace An fara raba wa almajirai tabarma da gidan sauro a YobeGwamnan ya bayyana hakan ne a yayin karɓar lambar karramawa da aka yi masa shi da wasu shugabnnin da Ƙungiyar Inganta zaman lafiya ta “Peace Building Development Consult” (PBDC) ta yi musu.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin babban lauya kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Yobe, Barista Saleh Samanja, ya bayyana hakan ne ga manema labarai ranar Laraba a Abuja, bayan da ya karɓi lambar yabon ta zaman lafiya.
“ina tabbatar muku kai tsaye cewar, Jihar Yobe tana ɗaya daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a Najeriya, hakan yana yiwuwa ne saboda haɗin kan da muke bai wa jami’an tsaro da kuma namijin ƙoƙarin da Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ke yi na bada gudummawa kan harkokin tsaro da duk abin da hukumomin tsaro ke son gwamnati ta yi.
“A matsayinsa na babban jami’in shari’a da tsaro na jihar, yana jin cewa yana da haƙƙin ɗabi’a da na shari’a don ba da haɗin kai ga hukumomin tsaro domin mu samu cikakken zaman lafiya a Jihar Yobe,” in ji shi.
A cewarsa wannan karramawar na ƙara ƙarfafa gwiwa ne, inda ya ce Gwamnan zai ci gaba da yin abin da yake yi domin ganin an dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: zaman lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon ba barazana ba — Kwankwaso
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan kalaman da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi game da Najeriya.
Kwankwaso, ya yi wannan magana ne bayan Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin yaƙi game da zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci.
Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da AmurkaA cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso, ya ce Najeriya ƙasa ce mai cikakken ’yanci, wadda ke fama da matsalar tsaro daga miyagu a sassa daban-daban na ƙasar.
“Matsalar tsaron da muke fuskanta ba ta bambanta tsakanin addini, ƙabila ko ra’ayin siyasa,” in ji shi.
Ya buƙaci gwamnatin Amurka da ta tallafa wa Najeriya da sabbin fasahohi domin yaƙar matsalar tsaro maimakon yin kalaman da za su iya raba kan ’yan ƙasa.
“Amurka ya kamata ta taimaka wa hukumomin Najeriya da ingantattun fasahohi don magance matsalolin tsaro, maimakon yin barazanar da za ta ƙara raba ƙasar,” in ji Kwankwaso.
Haka kuma, ya shawarci Gwamnatin Najeriya da ta naɗa jakadu na musamman domin inganta hulɗar diflomasiyya da Amurka da kare muradun ƙasar a matakin duniya.
Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su zauna lafiya, inda ya bayyana cewa wannan lokaci ne da ya dace a fifita haɗin kan ƙasa ba abin da ke raba ta ba.
“Wannan lokaci ne da ya kamata mu mayar da hankali kan abin da zai haɗa kanmu ba wanda zai raba mu ba. Allah Ya albarkaci Najeriya,” in ji shi.