’Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya, sun sace ɗan kasuwa a Kaduna
Published: 27th, August 2025 GMT
’Yan bindiga sun kai hari garin Hunƙuyi da ke Ƙaramar Hukumar Kudan, a jihar Kaduna, inda suka kashe mutum ɗaya tare da sace wani ɗan kasuwa.
Mutanen yankin sun ce maharan sun kai hari ne da misalin ƙarfe 12:30 na dare.
ACReSAL ya tallafa wa manoma da buhunan iri 6,220 a Gombe Babu ɗaya daga cikin buƙatunmu da gwamnati ta aiwatar — Shugaban ASUUMaharan sun shiga yankin ne ta ɓangaren Katsina ɗauke da bindigogi, inda suka dinga harbi a sama.
Sun harbe wani mutum mai suna Aminu Shehu har lahira, sannan suka yi awon gaba da wani ɗan kasuwa mai suna Alhaji Shehu Dakin.
Majiyoyi, sun bayyana cewa maharan sun yi amfani da wayar Alhaji Shehu wajen kiran iyalansa, inda suka nemi kuɗin fansa Naira Miliyan 100.
Wasu mazauna yankin sun ce wannan hari ya tayar musu da hankali tare da sanya su cikin fargaba.
Sun roƙi gwamnati da hukumomin tsaro su kai musu ɗauki cikin gaggawa.
Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya ci tura, domin ba ya ɗaukar waya har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Ɗan Kasuwa hari
এছাড়াও পড়ুন:
Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Jiang Bin, ya ce a baya bayan nan babban jirgin ruwan dakon jiragen sama na kasar Sin mai suna Fujian, ya doshi yankin tekun kudancin kasar, inda ya ratsa ta zirin Taiwan, a kan hanyarsa ta gudanar da gwaje-gwaje da samar da horo.
Jami’in wanda ya bayyana hakan a Talatar nan, ya ce hakan bangare ne na ayyukan da aka saba gudanarwa lokaci-lokaci a wani bangare na kirar jirgin.
Jiang Bin, ya yi tsokacin ne yayin da yake amsa wata tambaya mai nasaba da hakan da aka yi masa, yana mai cewa, bulaguron jirgin ya dace da dokokin kasa da kasa da ayyuka masu nasaba, kuma ba shi da wata nasaba da tunkarar wani sashe. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp