2025-07-11@00:20:57 GMT
إجمالي نتائج البحث: 599
«watan Ramadan»:
Labaran da suke fitowa daga kasar Yemen sunn bayyana cewa sojojin ruwan kasar sun nutsar da wani karin tankar dakon mai mallakin HKI a cikin tekun Red sea. Sojojin kasar sun bayyana cewa jigin ya sabawa Haramcin don haka sun tsutsar da ita. Sun yi haka ne don nuna goyon bayansu ga al-ummar Falasdinu wadanda ake zalinta a Gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa jirgin yana nufin zuwa ummu Rash Rash ko Ilat kamar yadda yahudawan suke kiransa. Sojojin kasar Yemen sun kara da cewa sun dauki wannan matakin kan jirgin ne bayan an gargade shi da ya koma amma yaki sauraro. Da wannan talilin sojojin ruwa na kasar yemen suka yi amfani da jiragen...
Mai magana da yawun matatar Dangote, Mista Anthony Chiejina, ya tabbatar da rage farashin a Legas. Ya ce, “Farashin man fetur ya ragu daga Naira 840 zuwa Naira 820 kan kowace lita.” Ya bayyana cewa rage farashin da aka yi a baya zuwa Naira 840 ya faru ne sakamakon hauhawar farashin ɗanyen mai a duniya sanadiyyar rikicin da ya auku a Gabas ta Tsakiya. Kamfanonin da ke haɗa kai da Dangote irin su MRS, Heyden, Ardova (AP), Hyde, Optima, da Techno Oil za su fara sayar da fetur a sabon farashin. Haka kuma, wasu sabbin kamfanonin da ke dillancin mai sun shiga jerin masu rarraba man Dangote. Kamfanonin sun haɗa da: TotalEnergies, Garima Petroleum, Sunbeth Energies, Sobaz Nigeria Ltd., Virgin...
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya ce kimanin kaso 90 cikin 100 na ’yan bindigar da suka hana jiharsa sakat ba baki ba ne, ’yan cikinta ne. Ya bayyana haka ne lokacin da ya bayyana a cikin shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels a ranar Talata. Ya ce tuni gwamnatinsa ta kafa rundunar tsaro mallakin jihar mai suna Katsina Community Watch Corps, inda aka debi matasa daga yankunan da ke fama da matsalolin tsaron domin a dakile ta tun daga tushe. DAGA LARABA: Shin Ko Zafin Nema Na Kawo Samu? Malaman firamare sun janye yajin aiki a Abuja Katsina dai na daya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da ke fama da matsalar ’yan bindiga, inda mutane dauke...
Kakakin dakarun rundunar Izzudden-Qassam ya bayyan cewa: ‘Yan gwagwarmaya sun tarwatsa wani mutum-mutumi da sojojin mamayar Isra’ila suka makare da harsashai dauke da makami mai linzami a lokacin da ake shirya shi A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, kakakin rundunar sojin Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas Abu Obeida, ya yi bayyana cewa: ‘yan gwagwarmaya sun nuna jarumtaka wajen tunkarar makircin ‘yan mamaya mai sarkakiya a gwagwarmayar Beit Hanoun, inda suka kara raunana martabar sojojin mamaya tare da rusa makircinsu.. Kakakin rundunar sojin Qassam Abu Obeida, ya kara da cewa: Hadadden aikin na Beit Hanoun wani karin mataki ne da ‘yan gwagawarmaya suka dauka na raunana makiya tare da rusa martabar sojojin mamayar Isra’ila. Yana...
Ministan harkokin wajen kasar Aran Abbas arachi ya bayyana cewa mutanen kasarsa a shirin suke su ci gaba da kare kasarsu daga Amurka da kuma HKI . Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Abbas Aragchi yana fadar haka a jiya litinin a lokacinda yake ganawa da tawagar kasar Brazil a gefen taron kungiyar BRICS karo 17 wanda ke tafiya a halin yanzu a birnin Rio de Jenero na kasar Brazil. An gudanar da wannan taron ne saboda hare-haren da HKI da kuma Amurka suka kaiwa JMI a baya bayan nan, da kuma tasirinsa a cikin al-amuran siyasa da kuma tattalin arziki a yankin Asiya ta yamma da kuma duniya gaba daya. Abbas Aragchi ya bayyana cewa hare-haren...
ADC ta tunatar da Tinubu cewa da gwamnatin Goodluck Jonathan ba ta jure hamayya ba a baya ba, shi ma ba zai kai matsayin shugaban ƙasa ba, kuma APC ba za ta lashe zaɓe ba. Jam’iyyar ta ce ya kamata shugaban ƙasa ya nuna cewa yana goyon bayan gaskiya da ‘yancin jam’iyyu a tsarin dimokuraɗiyya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
(ENT) Aikin Hanci , Makogaro da Kunne (Dental) Hakori (Fibroid) Qarin mahaifa, (Urology) Aikin Mafitsara Asibitin ya zakulo zakakuran likitoci domin gudanar da wannan ayyukan daga yau Litinin 8, ga watan Yuli 2025, ga duk masu bukatar wannan ayyukan, akan farashin kaso 50% cikin 100 shima za a biya. Labari Mai Daɗi: Asibitin Kwararru Mai Zaman Kansa A Kano Ya Rage Kaso 50 Na kuɗaɗen Ayyukansu Asibitin Aminu Kano Ya Musanta Cire Mahaifar Mara Lafiya Ba Tare Da Izini Ba Hakan na kunshe ne cikin wata sanar da shugaban asibitin Alh Auwal Muhd Lawal ya bayyanawa jaridar Alfijir Labarai a safiyar Litinin. Lawal yace sun yanke wannan hukuncin ne sakamakon buƙatar da al’umma suke da ita a wannan bangarorin ga...
(ENT) Aikin Hanci , Makogaro da Kunne (Dental) Hakori (Fibroid) Qarin mahaifa, (Urology) Aikin Mafitsara Asibitin ya zakulo zakakuran likitoci domin gudanar da wannan ayyukan daga yau Litinin 8, ga watan Yuli 2025, ga duk masu bukatar wannan ayyukan, akan farashin kaso 50% cikin 100 shima za a biya. Labari Mai Daɗi: Asibitin Kwararru Mai Zaman Kansa A Kano Ya Rage Kaso 50 Na kuɗaɗen Ayyukansu Asibitin Aminu Kano Ya Musanta Cire Mahaifar Mara Lafiya Ba Tare Da Izini Ba Hakan na kunshe ne cikin wata sanar da shugaban asibitin Alh Auwal Muhd Lawal ya bayyanawa jaridar Alfijir Labarai a safiyar Litinin. Lawal yace sun yanke wannan hukuncin ne sakamakon buƙatar da al’umma suke da ita a wannan bangarorin ga...
A taron ƙungiyar BRICS na karo na 17 da aka gudanar a Brazil, ƙasashen mambobi da suka haɗa da China, India, Rasha, Saudi Arabia, Iran da wasu sun soki hauhawar haraji da manufofin kariya ta ciniki da wasu ƙasashe ke aiwatarwa. A sanarwar da suka fitar, sun nuna damuwa kan rikicin Gabas ta Tsakiya, amma sun kaucewa sukar Rasha kai tsaye dangane da rikicin Ukraine. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Olubadan na Ibadan, Oba Owolabi Olakulehin ya rasu, yana da shekara 90 a duniya. Kakakin iyalan basaraken ne ya tabbatar da mutuwarsa da safiyar yau Litinin cikin wani saƙo da ya aike wa manema labarai. Kwanaki biyu da suka gabata ne basaraken ya gudanar da bikin cikarsa shekara 90 a duniya a wani ƙasaitaccen biki da aka gudanar a fadarsa. A shekarar da ta gabata ne aka naɗa Sarki Olakulehin a matsayin Olubadan na Ibadan bayan rasuwar wanda ya gabace shi Sarki Alli Okunmade II.
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya ce an samar da isassun matakan tsaro domin kawar da wasu gungun miyagu da ke aikata munanan laifuka a jihar. AbdulRazaq ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana wa masu ruwa da tsaki daga yankin Lafiagi na jihar Kwara ta Arewa kan dimbin kokarin gwamnatin jihar a wani taro da aka gudanar a Ilorin. Gwamnan ya amince da damuwar al’ummar tare da tabbatar musu da matakin da gwamnati ke jagoranta kan lamarin. Ya ce sojojin Najeriya za su ci gaba da kai hare-hare a dazuzzukan da aka gano a matsayin sansanin ‘yan ta’adda a Kwara ta Arewa da Kudu. Gwamna AbdulRazaq ya ce ayyukan za su hada da sabbin...
A wani yunkuri na bunkasa samar da wutar lantarki da kuma bunkasar tattalin arziki, gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da rabon kashi na farko na taransfoma 500 ga al’ummomin karkara a fadin kananan hukumomin jihar 44. Gwamna Abba Yusuf ne ya kaddamar da shi a hukumance a Kano a wani shirin da nufin magance kalubalen rashin samar da wutar lantarki. Gwamna Yusuf ya ce samar da taransfoma wani shiri ne na bunkasa masana’antu da zaburar da harkokin kasuwanci musamman a yankunan karkara. “Wannan rabon shi ne kashi na farko na aikin samar da wutar lantarki a yankunan karkara, ba wai kawai wani aikin samar da wutar lantarki ba ne, wani muhimmin mataki ne na inganta samar da...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sojojin Ukraine sun kama wani ɗan Nijeriya da ke taimaka wa Rasha a yaƙin da suke gwabzawa sama da shekaru biyu biyo bayan mamayar ƙasarsu. Wani bangaren sojin da ke ƙunshe da mayaƙan Rasha da ke goyon bayan Ukraine a wannan yakin, wanda ake kira ‘Freedom Of Russia Legion ne ya kama Kehinde Oluwagbemileke mai shekaru 29 a yankin Zaporizhzhia bayan shafe watanni biyar yana yaƙi a cikin mayaƙan Rasha. Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 41 a Nijar Kwankwaso ba zai yi mana takara a 2027 ba — NNPP Oluwagbemileke ya shafe shekaru huɗu yana zaune a ƙasar Rasha kafin a kama shi akan laifin da ke da nasaba da miyagun ƙwayoyi. An ruwaito cewa matashin ya amince ya shiga...
Rashford dai ya fi son komawa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona domin yana ganin zai iya buga abin a zo a gani a kakar wasa mai zuwa sai dai ita kuma Barcelona ta fi son dan wasa Nico Williams na kungiyar Athletico Bilbao ta kasar Spaniya, wanda shima yake son komawa Bardelona da buga wasa idan har Barcelonan za ta iya biyan kudin da aka yi masa farashi. Kungiya ta kwana-kwanan nan da ta nemi Rashford ita ce kungiyar Bayern Munchen ta Jamus, bayan da Liberpool ta ce ba za ta sayar mata da Luiz Diaz ba, ana ganin yanzu kungiyar za ta karkata akalarta zuwa neman Rashford. Kungiyoyi irinsu Newcastle United da Tottenham da kungiyoyi daga Saudiyya duka sun...
Majiyar kafafen yada labarai na Amurka sun bayyana cewa akalla mutane 52 suka rasa rayukansu sanadiyyar ambaliyar ruwan sama a jihar Texas. Jaridar US Today ta bayyana cewa an kubutar da daruruwan mutane daga halaka, amma kuma har yanzun ba san makamon daruruwan mutane ba. Sannan kungiyoyin bada agaji suna ci gaba da neman masu sauran shanruwa. Ruwan sama kamar da bakin kwarya ne ya sauka a jiya Asabar ya kuma ciika kogin Guadalupe wanda yayi ambaliya ya kuma rufe garuruwa da dama da suke bakin kogin. Gwamnatin Jihar Tezas Dan Patrick ya bayyana cewa an kubutar da mutane kimani 850 amma yawan matattu kuma yana karuwa a lokacinda jami’an agaji suke ci gaba da neman gawaki da kuma masu...
Rukunin farko: Morocco da Zambiya da Senegal da kuma Jamhuriyar Congo Rukuni na biyu: Nijeriya da Tunisia da Algeria da kuma Botswana. Rukuni na uku: Afirka ta Kudu da Ghana da Mali da kuma Tanzania. Bayan karawar bude labulen gasar, akalla za a rika buga wasanni bibiyu kowacce rana a fafatawar cikin rukuni har zuwa ranar Litinin 14 ga watan Yuli. Sannan a lokacin wasannin cikin rukuni za ake buga su daga 13:00 da 16:00 da kuma19:00 daidai da agogon GMT. Za a fara karawar zagaye na biyu daga ranar Juma’a 18 ga watan Yuli. Shekara ukun da ta gabata, Morocco ta gudanar da gasar cin kofin Afirka ta mata, kuma filaye ukun da ta yi amfani da su,...

Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN Ta Nuna Goyon Baya Ga Fadadar Kungiyar BRICS A Matsayin Hanyar Bunkasa Hadin Gwiwa
Taron farko na tsarin hadin gwiwar kungiyar BRICS, tun bayan shigar Indonesia da sauran abokan huldar kungiyar 10, ya ja hankulan sassan kasa da kasa. Har ma wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, ta nuna cewa kaso 91.2 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyi na ganin hadin gwiwa karkashin tsarin hadakar BRICS, ya zamo wani muhimman karfi na ingiza nasarar samar da duniya mai mabanbantan tasiri, wadda za ta wanzu bisa daidaito da adalci, da kuma tsari mai game dukkanin sassa, da tattalin arziki da dukkanin duniya za ta ci gajiyarsa. Kasashe mambobin BRICS, sun yi aiki tukuru wajen ingiza tsarin cinikayya da kudaden juna, da gina tsarin hada-hadar kudade mai zaman kansa,...
‘Yan kasuwa sun yi hasashen cewa za a yi sabon tsarin farashin daga ranar Lahadi. Tun a ranar Talatar da ta gabata, wakilinmu ya lura cewa sauran masu gidajen man da masu shigo da kaya sun daidaita farashinsu domin nuna sabon tsarin farashin da ya biyo bayan tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Iran. Daga Naira 920, akasarin gidajen sun rage farashin zuwa matsakaicin farashin Naira 845 akan kowace lita. A cewar Petroleumprice.ng, RainOil, Pinnacle, Matrid, Emadeb, Wosbab da First Royal suna sayar da man fetur a kan Naira 845 a Legas ranar Talata. Hakazalika, NIPCO, Aipec sun sayar da mai akan Naira 850 akan kowace lita. A sauran defot da ke wajen Legas, irin su Warri da Fatakwal, ana sayar...
Yakubu ya jaddada kokarin hukuma wajen yin adalci. “Za mu duba dukkan bukatun cikin adalci ba tare da la’akari da matsayin wadanda suka kawo su ba, lallai hukumar zabe ba za ta taba karya ka’idojinta ba.” Shugaban INEC ya musanta zarginsu cewa hukumar kokarin hada kai da wasu domin saba ka’ida wajen yin ragisara, ya tunawa da irin wannan zargin da ba tare da hujja ba da aka yi a shekarar 2013. Ya bayyana cewa hukumar ta amince da dukkan wasikun da aka karba illa guda shida, wadanda za a yi aiki a kai kafin karshen mako. Haka nan ya lura cewa dokoki da ka’idojin zabe ta 2022 kan jam’iyyun siyasa yana nan a shafin intanet na hukumar. Yakubu ya...
Bayan Plato sai kuma masani Aristotle shi ma ya zo da ta shi fahimtar, a shekara 340 kafin zuwan Annabi Isah (AS). A tunani irin Aristotle, yawaitar al’umma ba ta da wani alfanu, don haka hakki ne da ya rataya kan gwamnati ta kayyade yawan iyalin da mutum zai iya haifa. Idan matar mutum ta samu juna biyu (ciki) bayan sun kai adadin da gwamnati ta shardanta, ba su da wata mafita, in ji Aristotle, da ya wuce a zubar da cikin. Shi kuwa masani Abdurrahman Ibn Khaldun wanda aka haifa a ranar 27 ga watan Mayun 1332 ya na daga cikin wadanda ke goyon bayan yawaitar al’umma. Ibn Khaldun ya ce, rashin tunani da hangen nesa ne ma mutum...
Ya bayyana cewa, kungiyar na ci gaba da nazartar na rabar da man kai tsare, na shirin na matatar man ta Dangote, wanda daga baya, kungiyar za ta shiga cikin shirin gadan-gadan. Clement, ya sanar da cewa, kafin kungiyar ta shiga cikin shirin kai tsaye, yana da kyau a fara tattaunawa da Dangoten da kuma sauran da hukumomi. A cewarsa, ta hanyar tattaunawar ce, za ta sanya kungiyar ta shiga cikin shirin, domin a yanzu, muna ci gaba da yin nazari ne, kan shirin na Matatar ta Dangote. Sakataren ya ci gaba da cewa shirin da matar ta Dangote ta bullo dashi na rabar da man kai tsaye, musamman iskar Gas, abu ne da kungiyar take gani ya dace. “Shirin...
Kwamatin Harkokin Kananan Hukumomi na Majalisar Dokokin jihar Jigawa ya fara rangadin kwanaki biyu a karamar hukumar Roni a ci gaba da rangadin kananan hukumomin jihar 27 da kwamatin ya kaddamar. A jawabin sa a sakatariyar karamar hukumar Roni, Shugaban kwamatin Alhaji Aminu Zakari, ya ce tsarin mulkin kasa ya bai wa majalisa ikon dubawa da kuma tantance yadda bangaren zartaswa ke aiwatar da manufofi da shirye shiryen gwamnati. Ya ce ziyarar za ta mayar da hankali ga dubawa da kuma tantance kundin bayanan sha’anin mulki da na harkokin kudi da suka hada da kundin kasafin kudi na shekarar 2024 zuwa 2025 da Asusun kula da matsalolin muhalli da kundin bayanan kwamitocin karamar hukumar da takardun biyan kudade wato Voucher...
Rasha ta zama ƙasa ta farko da a hukumance ta amince da gwamnatin ƙungiyar Taliban da ke mulkin ƙasar Afghanistan. Wannan na zuwa ne bayan Rashar ta karɓi takardun shaidar kama aiki na sabon jakadan Afghanistan, wanda hakan ya sa ta zama ƙasa ta farko da ta amince da gwamnatin Taliban a ƙasar. Ambaliya da iska sun rushe gidaje 171 a watanni biyu a Gombe – SEMA Majalisar Mali ta ƙara wa Goita wa’adin mulkin shekara biyar “Mun yi imani cewa wannan matakin na amincewa a hukumance da gwamnatin Daular Musulunci ta Afghanistan zai ba da damar haɓaka haɗin gwiwa mai amfani tsakanin ƙasashenmu a fannoni daban-daban,” in ji Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis....
Sanarwar ta ƙara da cewa, a yayin taron an sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin gwamnatin jihar Zamfara da Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta Yankunan Karkara, sannan aka tattauna da masu ruwa da tsaki, tambayoyi da amsoshi, ra’ayoyi, da kuma alƙawura. A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya ce ya gaji matalauciyar gwamnatin a bangaten lantarki. Ya ci gaba da cewa, “An katse ƙananan hukumomi da yawa daga babban lantarkin ƙasa. An sace wayoyin lantarki da dama, wasu kuma sun lalace, wasu muhimman ababen more rayuwa sun durƙushe a cikin shekaru saboda watsi da su, sannan masana’antu da kasuwancinmu sun gurgunta saboda rashin ingantaccen wutar lantarki. “Duk da haka, mun zaɓi kada mu shiga wasan zargi,...
Amurka ta dakatar da tallafin makaman da take bai wa Ukraine, tana mai bayyana damuwa kan raguwar makamanta a rumbun adana su. Mai magana da yawun Fadar Gwamnatin Amurka, Anna Kelly a watan sanarwar da ta fitar, ta ce a halin yanzu muradun Amurka ne kan gaba ta bangaren tsaro, don haka dole ne ta dakatar da duk wani tallafin makamai da take bai wa Ukraine din. Hamas ta karɓi tayin tsagaita wuta a Gaza Za mu ɗauki mataki kan mambobinmu da ke shirin shiga haɗakar ADC — PDP Wannan na zuwa ne daidai lokacin da Rasha ke ci gaba da fadada hare-harenta a kan kasar, yayin da aka kwashe sama da shekaru biyu ana gwabza yaki tsakanin kasashen da...
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha ya bayyana cewa: Kasarsa na da niyyar karfafa hadin gwiwa da Iran da kuma kara karfin tsaron kasar ta Iran Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Riyabkov ya jaddada cewa: Kasar Rasha za ta karfafa hadin gwiwa da Iran a dukkan fannoni, gami da kara karfin tsaron kasar ta Iran. Riyabkov ya shaidawa manema labarai a ofishin jakadancin Iran da ke birnin Moscow cewa: “Za su karfafa hadin gwiwa a aikace tare da Jamhuriyar Musulunci ta Iran a dukkan fannoni, yana mai jaddada cewa: Dole ne a karfafa karfin tsaron kasar Iran, saboda Rasha tana da gogewa mai kima a wannan fanni, kuma za ta ci gaba a kan hakan.” A ofishin jakadancin...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa hare-haren HKI da Amurka a yankin yammacin Asiya ya kara rashin zamn lafiya a yankin. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadin haka ne a lokacinda yake zantawa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Girka a jiya talata . Ya kuma kara da cewa hare-haren sun yu watsi da hanyar zaman lafiya da kuma zaman lumana a yankin. Ya kuma yi sanadiyyar karin tashe tashen hankula a yankin. Ministan ya bukaci kasashen duniya gaba daya su yi tir da HKI da kuma Amurka wadanda suka keta hurumin kasa mamba a MDD ba tare da wani daloli nay an haka ba. Ya ce hare-haren da...
A yayin zaman, ana sa ran tattauna batutuwa da dama da suka haɗa da ’yancin ƙananan hukumomi, ƙirƙiro hukumar zaɓe ta ƙasa don kula da zaɓen ƙananan hukumomi, kafa ƴansanda na jihohi, da ƙara yawan kujerun mata a majalisun dokoki domin samun wakiltar jinsin mata. Haka kuma, za a duba ƙuduri guda shida da suka shafi inganta gaskiya da rikon amana a harkokin kuɗi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hakazakika, an zakulo Mata dalibai daga wasu zababbun makarantun sakandare a jihar da kuma wasu daidaikun Mata a kananan hukumomi 23 na jihar Kaduna. Da yake kaddamar da Rabon Kayan, Shugaban Ma’aikatar Fadar Gwamnatin jihar Kaduna Malam Liman Sani Kila, ya bayyana gamsuwarsa dangane da kokarin uwargidar shugaban kasa Remi Tinubu na tallafawa Mata Da Matasa a fadin kasar baki daya. Hakazakika, ya jinjinawa Uwargidar Gwamnan jihar Kaduna Hajiya Hafsat Uba Sani bisa bubbasar da takeyi wajen tallafawa Mata Da dalibai Mata Da masa abin a Yaba ne Yana Mai bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar Kaduna Ta himmatu wajen ciyar da aikin Noma a jihar Kaduna. Kila ya kuma jinjinawa Hajiya Hafsat Uba wajen jajircewata wajen...
Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kassim ya ce; Tsayin dakar da kungiyar gwagwarmaya ta yi, ya samo asali ne daga koyi da Imam Hussain ( a.s). Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah wanda ya gabatar da jawabi a daren jiya a yayin zaman Ashura, ya kuma kara da cewa; tafarkin Imam Hussain ( a.s) shi ne wanda ya samar da gwarazan mazaje na musamman da shahidai da su ka fuskanci ‘yan mamaya. Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Matasan da su ka yi watsi da duniya su ka shiga fagen jihadi, sun sadaukar da kansu. Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma ce; kungiyar Hizbullah tana a matsayin kare kai ne,domin wannan kasarmu ce, don haka hakkinmu...
Wani ɗan Fashi da makami ya rasa ransa bayan da yayi yunƙurin yin fashi a unguwar Dorayi Babba, Unguwar Jakada, Kano. Rahotanni sun bayyana cewa ɓarawon, wanda aka gano sunansa Musa Nuhu, ya kutsa cikin wani gida riƙe da makami, wata wuka da nufin yin fashi a wani gida. Bayan shiga cikin gidan, ɓarawon ya kai hari kan wasu mata biyu tare da jikkata su. Sai dai wani namiji daga cikin iyalan gidan yai taho mu gama da ɓarawon a cikin wata fafatawa mai zafi da ta jawo raunika a tsakaninsu duka biyu. Gwamna Yusuf Ya Jagoranci Tawagar Kano Zuwa Jana’izar Marigayi Aminu Dantata A Madina An Sauya Sunan Makarantar Wasanni Don Girmama Ƴan Kano Da Suka Yi Hatsari Kakakin...
Hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin, ta yi watsi da bangaren rahoton kwamitin SAGO, na masana kimiyya mai bayar da shawara game da asalin kwayar cutar da ta haddasa annobar COVID-19, wanda hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar. Wata sanarwa da hukumar ta fitar a Litinin din nan, ta ce a ranar 27 ga watan Yunin nan, kwamitin SAGO, ya wallafa wani rahoto game da tushen kwayar cutar SARS-CoV-2, wadda ta haddasa barkewar annobar COVID-19. Sanarwar ta ce, duk da yake bincike mai zaman kansa da kwamitin SAGO ya gudanar bai nuna wata sabuwar shaida game da asalin kwayar cutar ba, bai kuma bayyana wani abu da ya saba da sakamakon binciken hadin gwiwa tsakanin Sin da WHO na...
Dalibai 29 ne suka rasa rayukansu sakamakon turmutsitsin a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya yayin tserewa fashewar taransifoma Akalla dalibai 29 ne suka mutu a birnin Bangui na kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a wani turmutsutsu sakamakon fashewar tiranfomar lantarki a lokacin jarrabawar sakandare, a cewar ma’aikatar lafiya ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Wata takarda daga ma’aikatar lafiya ta ce: “Mutane 29 ne suka rasa rayukansu bayan an kai su asibitocin birnin Bangui.” Ba a samu ingantattun bayanan yawan wadanda suka mutu ba har zuwa yammacin ranar Larabar da ta gabata, a lokacin da fashewar ta faru, sama da dalibai 5,300 ne ke zana jarrabawar kwana na biyu na jarabawar sakandare.
Adadin mambobin JKS na ci gaba da karuwa, inda rassanta ke ci gaba da ingantuwa. Baya ga haka, sassanta a matakin farko na kara karfi. Wannan na kunshe ne cikin rahoton kididdiga da sashen shirye-shirye na kwamitin kolin jam’iyyar ya fitar yau Litinin, gabanin bikin cika shekaru 104 da kafuwar jam’iyyar. Zuwa karshen 2024, jam’iyyar na da mambobi sama da miliyan 100.27, karuwar kusan miliyan 1.09 kan na shekarar 2023. Zuwa karshen 2024 kuma, JKS na da sassa miliyan 5.25 a matakin farko, karuwar 74,000 idan aka kwatanta da shekarar 2023. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Rwanda sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya bayan shafe shekaru 30 suna rikici Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Rwanda sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, shekaru talatin bayan rikicin da ya barke a shekara ta 1994 da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane daga bangarorin biyu. An rattaba hannu kan takardar ne a gaban sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ministar harkokin wajen Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Teresa Kayumba, da na Rwanda Olivier Nduhungirehe. Yarjejeniyar da Amurka da Qatar suka wakilci shiga Tsakani ta hada da tanade-tanade kan mutunta yankunan kasa, haramta ayyukan soji, kwance damarar makamai da hadewar kungiyoyin da ba na gwamnati ba, da kuma samar da wani tsari na hadin gwiwa don daidaita...
Masanan sun kuma bayyana cewa, kashi 25 cikin 100 na manya a Nijeriya na dauke da kwayar cutar Sikila. Ana bikin ranar Sikilar ne a kowace shekara, ranar 19 ga Yuni, domin wayar da kan jama’a game da cutar da kuma yadda ake sarrafa ta. Wasu iyayen da suka bayyana irin abubuwa na renon yara masu fama da cutar, sun bayyana cewa; ba don an yaudare su da kuskuren sakamakon gwajin da aka yi musu kafin aure ba, da sun kaucewa matsalolin da suke fuskanta a halin yanzu. Wata uwa mai ‘ya’ya uku daga unguwar Dagbana da ke babban birnin tarayya Abuja, ta bayyana wa LEADERSHIP yadda aka ba ta takardar shaidar cewa; ita da maigidanta za su iya yin...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran ba ta san mika wuya ba, kuma tana rubuta tarihin mutunci da jinin shahidanta A jawabin da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi bayan halartar jana’izar shahidan Quds ya jaddada cewa: Iran ba ta san ma’anar mika wuya ba, yana mai fayyace cewa tarihi zai shaida cewa Iraniyawa sun zubar da jininsu tare da kin ba da kasarsu da mutuncinsu. Araqchi ya bayyana a shafinsa na Instagram cewa: “Duk da zafi da rashi na shahidansu kwatsam, amma tunaninsu yana nan a cikin zukatan masu hankali, da kuma zukatan al’ummomi masu zuwa, kuma suna sane da yin riko da Imani da hanyarsu, kuma za su ci gaba da bin tafarkinsu.”...
Atiku, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP a 2023, ya bayyana Dantata a matsayin jarumin da ke ɗaukar kasada a harkokin kasuwanci, wanda ya ce wata muhimmiyar ɗabi’a ce ta manyan masu saka hannun jari. Ya yaba da yadda Dantata ya sauya kasuwancin danginsu daga saye da sayarwa ta hanyar gargajiya zuwa aikin gine-gine da injiniyanci na zamani, wanda hakan ya samar da dubban ayyukan yi ga ‘yan Nijeriya. Atiku ya kuma nuna girmamawa ga Dantata bisa irin taimakon da yake yi wa jama’a cikin sirri ba tare da neman ɗaukaka ko yabo ba. “Ya kasance mai dukiya sosai amma bai taɓa nuna girman kai ba, wannan ɗabi’a ce da ba kowa ke da ita ba,”...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Alhaji Sabo ya yaba wa shugaban majalisar wakilai kuma Iyan Zazzau, Dakta Abbas Tajuddeen, na yadda a tsarinsa ake koya wa matasa sana’a da zarar sun kammala yana ba matasa kayayyaki da kuma kudade domin dogaro da kai. Ya shawarci gwamnonin arewa da su duba matsalar durkushewar kamfanin yin tamfoli da ke Zariya, wanda a shekarun baya a fadin Nijeriya, wanna kamfanin ke yin tamfol da sojoji da kuma sauran al’umma ke amfani da sh a ayyuka daban- daban. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
Ya kuma yi watsi da ikirarin da ake yi na cewa ‘yansanda na taimakawa wajen magudin zabe, yana mai bayyana irin wadannan zarge-zarge a matsayin mara tushe, tare da cewa aikin ‘yansanda a lokacin zabe ya takaita ne kawai wajen samar da tsaro da tabbatar da zaman lafiya. “Mu ba ’yan bangar siyasa ba ne, mu kamar alkalan wasa ne, aikin ‘yansanda ya takaita ne kuma ya ta’allaka ga samar da tsaro a lokacin zabe, gwargwadon yadda ya kamata, ba za mu yi zabe ba, jama’a ne za su kada kuri’a, INEC ta kidaya, muna sa ido. “Kuma wannan ita ce matsayarmu, sannan kuma hanyar da za a bi domin cimma nasara ita ce, sake sabunta hadin gwiwa tsakanin hukumomi,...

Gwamnan Jigawa Ya Kaddamar Da Rumbun Sauki Don Sayar Wa Ma’aikata Kayayyakin Abinci A Farashi Mai Rahusa A Sakkwato
Tun da farko, Gwamna Aliyu ya ce, gwamnatinsa ta bullo da shirin ne domin ta saukaka farashi da kashi 20 ta hanyar saukar da farashin kayan abinci kasa warwas. Gwamnan ya ce, an tsara shrin ne domin saukakawa ma’aikatan jiha, na kananan hukumomi da masu karbar fansho ta hanyar samar da nau’ukan kayan abinci kamar shinkafa, gero, alkama, masara, dawa, man girki da taliya a cikin farashi mafi sauki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnan ya buƙaci kamfanin da ke aikin da ya yi aiki mai kyau kuma ya kammala a kan lokaci. Ya ce dole ne a gina gidajen cikin inganci domin taimakawa wajen rage matsalar rashin gidaje da jama’a ke fuskanta a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sanarwar ta ƙara da cewa, aikin Sahara ba wai kawai aikin jaridar bogi ba ne; ya samo asali ne zuwa da suna ‘Gonzo’, wanda ke da alaƙa da ƙarairayi wajen bayar da rahoto. Sanarwar ta ci gaba da cewa: “An ja hankalinmu kan labaran ƙarya da Sahara Reporters ke yaɗawa, shafin da ya shahara wajen yaɗa labaran ƙarya domin tayar da ƙura a intanet. “A yayin tattaunawa da manema labarai kai tsaye a makon da ya gabata, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana ƙudirinsa na ɗaukar nauyin kasafin kuɗi, inda ya tabbatar da cewa bai karbi lamuni na cikin gida ko na ƙasashen waje ba tsawon shekaru biyu da ya yi yana mulki. “Amma abin ya ba mu...
Shugaban Ƙasar Rasha, Vladimir Putin, ya ce babu wata hujja ko dalilin kai wa Iran hari. Putin ya yi wannan furuci ne yayin wata tattaunawa da Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Agarachi a fadar Kremlin da ke birnin Moscow. Akwai ƙasashen da ke shirin bai wa Iran makaman nukiliya — Rasha Fararen hula sun yi garkuwa da sojoji 57 a Columbia A jawabin da ya gabatar a farkon tattaunawar wanda aka yada a gidan talabijin na gwamnatin Rasha, shugaba Putin ya ce: “Babu wata hujja ko dalili da zai sa a kai wa Iran farmaki.” Ya ƙara da cewa “na ji daɗin zuwan ka [Agarachi] Moscow a yau. Wannan zai ba mu damar tattauna waɗannan batutuwa masu wahala da kuma...
Wani babban jami’in Rasha, Dmitry Medvedev ya yi iƙirarin cewa akwai wasu ƙasashe da ke shirin bai wa Iran makaman nukiliya domin kare kanta daga abokan gaba. A ranar Lahadi, Dmitry Medvedev wanda tsohon Firaministan Rasha ya yi iƙirarin cewa wasu ƙasashe sun shirya domin bai wa Iran makaman nukiliya kai-tsaye bayan hare-haren Amurka kan tashoshin nukiliyarta. Matashi ya yi wa maraya ɗan shekara 10 kisan gilla a Zariya Amurka ta roƙi China ta sa baki kada Iran ta rufe mashigar tekun Hormuz “Wasu ƙasashe sun shirya domin bai wa Iran makaman nukiliyarsu kai-tsaye,” kamar yadda Medvedev, Mataimakin Majalisar Tsaron Rasha, ya bayyana a wasu jerin saƙonni da ya wallafa a shafin X. Medvedev ya ce da alama wuraren da...
Ɗan wasan gaban Manchester United Marcus Rashford ya ce zai so ya taka leda tare da matashin ɗan wasa Lamine Yamal a Barcelona, Rashford mai shekaru 27, wanda ya shafe rabin kakar wasan bara ya na zaman aro a Aston Villa, a halin yanzu yana atisayen ƙara kuzari a ƙasar Sifaniya kafin a fara wasannin share fage na kulob ɗin, yayin da ake ta raɗe raɗin makomarsa a United. Lokacin da aka tambaye shi game da yiwuwar yin wasa tare da Yamal, Rashford ya ce: “E, tabbas, kowa yana so ya yi wasa tare da mafi kyawun dan wasa, don haka nima inada wannan burin kuma zamu gani, Yamal, mai shekaru 17, ya taka rawar gani sosai yayin da Barcelona...
Mahaifin fitacciyar jarumar nan a masan’antar Kannywood, Rahama Sadau, ya riga mu gidan gaskiya. Jarumar ta wallafa wani saƙo a shafinta na Facebook tana mai cewa “Allah Ya yi wa mahaifina rasuwa…” sannan ta ɗora wani hoto da aka rubuta Inna lilLahi wa inna ilaiHi raji’un har sau uku a ƙarƙashin saƙon. Shi ma abokin sana’arta, Ali Nuhu, a saƙon da ya wallafa mai ɗauke da hoton Rahama tare da mahaifinta, ya sake tabbatar da rasuwar. Bayanai sun ce Alhaji Ibrahim Sadau ya rasu ne a garin Kaduna, inda nan gaba kaɗan za a yi masa jana’iza.

Babban Al’amari Ne A Samu Ƴar Shekara 6 Ta Haddace Qur’ani A Makarantar Raudatul Jannah – Mai Sikeli
Ya kara da cewa wannan sauka ita ce karo na hudu wanda aka yi walimar dalibai 45, maza da mata, inda mafi kankanta daliba ita ce mai shekaru shida da rabi da makarantar ta yaye jimlar dalibai 90 kenan tun daga 2018 zuwa wannan shekara 2025. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Sin A Shirye Take Ta Yi Aiki Da Rasha Don Daukaka Amincewar Juna Ta Fuskar Siyasa Da Karfafa Muradun Juna
Mataimakin firaministan kasar Sin Ding Xuexiang, ya bayyana a jiya Jumma’a cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasar Rasha don ci gaba da daukaka amincewa da juna a fannin siyasa da karfafa dankon zumunci na cin moriyar juna. Ding ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin. Mataimakin firaministan ya ce, a yayin da ake fuskantar gagaruman sauye-sauye a yanayin duniya, ya kamata Sin da Rasha su kiyaye cikakken tsarin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, da kare adalci a matakin kasa da kasa, da tallafa wa tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban na kungiyar WTO, tare da kiyaye gudanar da harkokin tsarin samar da kayayyaki cikin lumana, da zurfafa...
Manyan kungiyoyin kwallon kafa a Turai Tottenham Hotspur da West Ham United na fafatawa wajen ganin sun dauki tauraron dan wasan Nijeriya dake buga kwallo a Club Brugge, Raphael Onyedika, ana alakanta Onyedika da barin kungiyar Club Brugge sakamakon rawar gani da ya taka a bana. Dan wasan na Nijeriya ya samu dimbin masu sha’awar raba shi da Brugge saboda bajintar da ya nuna a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai ta bara, a cewar Transferfeed, kungiyoyin biyu na son siyan dan wasan tsakiyar a wannan bazarar, West Ham na son ya maye gurbin Tomas Soucek dan kasar Czech, wanda ke kan hanyarsa ta barin kungiyar. Nico Williams Ya Amince Da Komawa Barcelona Akan Kwantiragin Shekaru 6 Diaz Ba Na...
Abbas ya kuma jaddada bukatar da dauki matakai, kan aukuwar sauyin yanayi, musamman duba da matsalar talauci da kuma ci gaba da fuskantar kalubalen rashin tsaro, da kasar nan, ke fuskanta. Bugu da kari, Hukumar kula da ‘yan cirani ta duniya wato IOM ta sanar da cewa, gurbata muhalli da robobin da aka sarrafa zuke haifarwa, suna taka gudunmwa, wajen aukuwar dumamar yanayi da kuma gurbata muhalli. A cewar Hukumar, matsalar na kuma lalata kasar noma da lalata hanyoyin ruwa, tare da kuma tilasta alumma, tashi daga matsugunan su, zuwa wasu gurare, domin su ci gaba da gudanar da rayuwarsu. Hakazalika, a cikin wasu rahotanni da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, sun bayyana cewa, a fadin duniya, ana yin amfani...
A ranar 27 ga Mayu, 2025, Indomie Arewa ta ƙara ɗanɗano da armashi a cikin tasowar yara. Babban kamfanin abincin tana alfaharin ƙaddamar da Indomie AI Career Generator, wata dandalin zamani irinsa na farkon da aka ƙirƙira don nuna irin baiwar da yara ke da ita ta hanyar ba su damar ganin makomarsu ta wata sabuwar hanya. Indomie tun da dadewa tana da kaimin ciyarwa da abincin dake gina jiki da kuma cincidar Mafarkin kowanne yaro. Wannan dandalin na Indomie AI Career Generator ya tunkari wannan manufa, na taimakawa yara su fahimci ƙarfin gwiwarsu, su yi manyan mafarkai, kuma su san cewa makomarsu tana gab da su. “Indomie ta tallafa wa yarada dama wajen girma, koyo, da zama ababen Alfahari. Tare...
FCCPC ta lura cewa, waɗannan sassan dokar suna kare ‘yan Nijeriya daga “rashin adalci, rashin sanin ya kamata, daga kwastomominsu.” A wata wasika mai ɗauke da kwanan watan 13 ga watan Yuni 2025, FCCPC ta yi amfani da sashe na 32 da na 33 na FCCPA, inda ta bukaci kamfanin da ya gurfana a gaban hukumar a hedikwatar ta Abuja a ranar Litinin 23 ga watan Yuni 2025. Hukumar ta yi gargaɗin cewa, rashin bin wannan umarni na iya haifar da tsauraran takunkumai da suka hada da tara da ɗauri kamar yadda aka bayyana a sashe na 33(3) na dokar. Har yanzu Air Peace ba ta amsa sammacin ba har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto. ...
Martanin Iran game da ta’addancin haramtacciyar kasar Isra’ila na ci gaba a rana ta biyu Ana ci gaba da mayar da martani mai girma na Iran game da harin da haramtacciyar kasar Isra’ila take kaiwa da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka ciki. ‘Yan mintoci da suka gabata a zaman wani bangare na biyu na “Alkawarin Gaskiya Na 3”, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta harba daruruwan makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka kan haramtacciyar kasar Isra’ila. An harba wadannan makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka ciki da kuma jiragen sama masu saukar ungulu daga Tehran da sauran garuruwan kasar Iran a matsayin wani mataki na murkushe laifuffukan da yahudawan sahayoniyya suka aikata a kan...
Sannan shi ne ya fi kowanne danwasa yunkurin cin kwallo a gasar, inda ya kai hari (attempt) sau 64, 23 daga cikinsu akwai munana (on target) 23. Ya yi nasarar yanka abokan hamayyarsa har sau 62, sannan ya yi bugun kwana 45. Rapinha Zakakurin danwasan gaba na Barcelona da Brazil, Rapinha, na cikin ‘yanwasan da suka fi bai wa mabiya harkokin wasa mamaki a kakar wasa ta bana baki daya – ba a Champions League ba kawai. Tare da dan wasan kungiyar Borussia Dortmund, Serhou Guirassy, su ne kan gaba a cin mafi yawan kwallaye da 13 kowannensu. Sai dai Rapinha ya zarta shi da yawan bayar da kwallo a zira a raga, inda yake da guda 9, Guirassy...

Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Shaida Gamsuwa Da Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Tsakiyar Asiya
Yayin da taro na biyu na tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya ke kara matsowa, sakamakon kuri’un jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, sun nuna gamsuwa da hadin gwiwa bisa matsayin koli dake tsakanin Sin da kasashen nan biyar na yankin tsakiyar Asiya, a matsayin wata hadaka ta al’umma mai kyakkyawar makomar bil’Adama, wadda ke kara shigar da sabon kuzari, na daidaito cikin yanayin duniya dake kara shiga yanayin tangal-tangal. Tun dai taro na farko na tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya, hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen biyar ya shiga wani sabon zango na ci gaba. Har ma kuri’un na jin ra’ayin jama’a suka nuna yadda kaso 90.4...
Da yake maida martani, Mokwa ya ce gwamanti ta fara biyan bashin tallafin rage radadin ga ma’aikata. Ya ce za a ci gaba da biyan kudin ne kashi-kashi har zuwa nan da watanni hudu masu zuwa. “Mun fara biyan bashin nira 35,000 ga ma’aikata. Illar kawai wasu ma’aikatu da suka kasance masu cin kashin kansu da suke biyan tallafin kai tsaye, misali, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa. “Amincewa da tallafin naira 35,000 ga ma’aikata shi ne mafita ta wucin gadi da gwamnatin tarayya ta yi kafin amincewa da mafi karancin albashi na naira 70,000. “Wannan ya faru a cikin watanni biyar, amma kungiyar kwadago ta ce ba a fara biya a kan lokaci ba, yanzu kenan akwai bashin...
Lamarin ya ci gaba da raguwa har zuwa 2024, inda yawan kudaden da ake kashewa a yawon ketare ya fadi da kaso 14 a matakin shekara-shekara zuwa dala biliyan 2.66. Hakan na nuni da cewa ‘yan Nijeriya sun rage kashe kudaden da suke kashewa kan safarar jiragen sama da dala biliyan 1.12 ko kuma kashi 30 cikin dari a cikin shekaru biyun. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Duk da cewa, yanayin zafi ya yawaita a kasar ta Saudiyya, yayin gudanar da aikin Hajjin 2025, koda-yake; akasarin wadanda suka mutu daga Nijeriyar tsofaffi ne. Rasuwar farko da aka sanar ta wani Alhaji ce daga Jihar Oyo, Alhaji Sulaimon Hamzat, wanda ya rasu a ranar 17 ga Mayun 2025 a kasar ta Saudiyya. Na biye da shi kuma daga Jihar Abiya ne, mai suna Alhaji Saleh, Shugaban Kasuwar Shanu ta Lokpanta, wanda ya rasu a garin Makka a daren ranar Litinin 26 ga watan Mayun 2025. Bayan haka kuma, sai wata Hajiya mai shekaru 75 daga Jattu Uzairue a Karamar Hukumar Etsako ta yamma da ke Jihar Edo, Adizatu Dazumi, wadda ta mutu a ranar Litinin 26 ga Mayun...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Rashin aikin yi na daya daga cikin manyan kalubalen da najeriya ke fuskanta a wannan lokaci, musamman la’akari da yanda ake cigaba da samun matasa dake da karfi a jika amma babu aikin yi. Hukumar kididdiga ta kasa ta fitar da bayanan dake baiyana cewa rashin aikin yi ya karu a najeriya da kaso 5.3 a farkon wannan shekarar, kazalika binciken ya baiyana cewa wadanda basu yi karatu mai zurfi ba sun fi wadanda suka yi karatu mai zurfi samun aikin yi. NAJERIYA A YAU: 12 Ga Yuni: Me Ranar Dimokuraɗiyya Ke Nufi Ga Talakan Najeriya? DAGA LARABA: Dalilan Rashin Jituwa Tsakanin Marasa Lafiya Da Jami’an Kiwon Lafiya Wadansu dalilai ne ke kara...

Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN: An Yi Kira Ga Amurka Da Ta Cimma Daidaito Da Sin Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya
Zuzzurfar tattaunawa da ta wakana tsakanin tsagin Sin da na Amurka a birnin Landan, ta sa masu bayyana ra’ayoyin jin karfin gwiwa game da makomar shawarwarin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka. Kuri’un jin ra’ayin jama’a na kafar CGTN ta kasar Sin, sun nuna yadda masu bayyana ra’ayoyi suka amince cewa, shawarwari sun nuna kyakkyawan fata game da aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma yayin tattaunawar da suka yi ta wayar tarho, tare da sassauta sabani a batutuwan tattalin arziki da cinikayya tsakanin sassan biyu. Yayin kuri’un jin ra’ayoyin, masu bayyana mahanga sun goyi bayan matsayar Sin, inda kaso 87.1 bisa dari suka amince cewa ba wani batu na wa ya yi nasara, ko wanda...
A ranar dimokuraɗiyyar Najeriya ta 2025, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Alhamis, ya yi afuwa ga fursunoni 66 a babbar Cibiyar gyaran hali da ke Maiduguri. Ziyarar da Gwamna Zulum ya kai a gidan yari a ranar 12 ga watan Yuni, 2025, ya yi amfani da ikon da sashe na 212 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba wa gwamnonin jihohi, wanda ya ba da damar yin afuwa bayan ya tattauna da wata majalisar ba da shawara kan jinƙai. 12 ga Yuni: Najeriya na bikin ranar dimokuraɗiyya An hana hawa babur da daddare a fadin jihar Gombe “Dangane da ikon da aka bani a ƙarƙashin sashe na 212 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya (wanda aka gyara)...
A ranar dimokuraɗiyyar Najeriya ta 2025, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Alhamis, ya yi afuwa ga fursunoni 66 a babbar Cibiyar gyaran hali da ke Maiduguri. Ziyarar da Gwamna Zulum ya kai a gidan yari a ranar 12 ga watan Yuni, 2025, ya yi amfani da ikon da sashe na 212 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba wa gwamnonin jihohi, wanda ya ba da damar yin afuwa bayan ya tattauna da wata majalisar ba da shawara kan jinƙai. 12 ga Yuni: Najeriya na bikin ranar dimokuraɗiyya An hana hawa babur da daddare a fadin jihar Gombe “Dangane da ikon da aka bani a ƙarƙashin sashe na 212 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya (wanda aka gyara)...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rashin wutar lantarki a Arewa maso Gabashin Najeriya ya tilasta wa jama’a da ’yan kasuwa zaman ɗari-ɗari da asarar dukiya, sakamakon aikin da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Ƙasa (TCN), ke yi na aikin sabbin turakun wutar lantarki. Rashin wutar, wanda ya fara daga ranar 10 zuwa 14 ga watan Yuni, ya shafi layin wutar lantarki na Jos–Bauchi–Gombe mai ƙarfin 132kV. An kashe mutum 41 cikin mako ɗaya a Filato Hajjin 2025: Jihohi 11 sun kashe N6.2bn wajen tallafa wa Alhazai A Jihar Adamawa, musamman a birnin Yola, jama’a na cikin matsanancin hali. Hajiya Aisha Babangida daga Jimeta, ta ce rashin wutar ya tilasta masa soye dukkanin naman ragon sallarta domin babu wutar da za ta ajiye shi a firinji....
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba An ware ranar 12 ga watan Yuni a matsayin Ranar Dimokuraɗiyya a Najeriya domin tunawa da ranar da aka gudanar da zaɓen da ake ɗauka a matsayin mafi sahihanci da adalci a tarihin ƙasar. Sai dai, bayan sama da shekaru 30 da gudanar da wannan zaɓe da kuma gwagwarmayar da ta biyo baya, wasu masana na ganin har yanzu ba a kai ga amfanin da ake murad daga dimokuraɗiyyar ba. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Fara Sana’a Ba Tare Da Jari Ba NAJERIYA A YAU: Hanyoyin kauce wa ɓarnar ambaliyar ruwa Ko mene ne hujjar kowane ɓangare? Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau zai yi duba a wannan lokaci. Domin sauke...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba An ayyana 12 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin Ranar Dimokuradiyya a Najeriya don tunawa da ranar da aka gudanar da zaben da aka yi amanna cewa shi ne mafi sahihanci da inganci a tarihi. Sai dai bayan fiye da shekara 30 da wannan zabe da fafutukar da ta biyo baya, wasu masana suna ganin har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Magance Matsalar Kwacen Waya DAGA LARABA: Dalilan Rashin Jituwa Tsakanin Marasa Lafiya Da Jami’an Kiwon Lafiya Ko mece ce hujjarsu? Wannan ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
Ya ce ya fahimci haka ne bayan kallon wani shiri a talabijin inda ya ga wasu mutane na nuna rashin jin daɗi. Wike ya ce wannan baƙin ciki na su shi ne ke ba shi ƙwarin gwiwa. “Na ji wani irin abu a zuciyata, sai na kunna talabijin. A nan ne na gano cewa wasu na cikin baƙin ciki saboda abubuwan alheri da ake yi,” in ji shi. Ya ƙara da cewa: “Yanzu da na gane suna cikin baƙin ciki, zan ci gaba da sanya musu ƙarin ciwon zuciya. Farin cikinmu na ƙaruwa ne da jin haushinsu. Wannan shi ne sabon aikina na ci gaba da sa musu hawan jini.” Wike ya yi raha da cewa yayin da suke cikin...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Inganta sinadarin Uranium da ɗage takunkumai na iya sa tattaunawar ta yi amfani Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya rubuta cewa: A bayyane yake cewa cimma yarjejeniyar da za ta tabbatar da zaman lafiya na dindindin na shirin makamashin nukiliyar Iran abu ne mai yiyuwa, kuma ana iya cimma shi cikin sauri. Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya rubuta a shafinsa na Twitter game da sabon zagayen tattaunawa tsakanin Iran da Amurka da kuma matsayin Iran a kansu yana mai cewa: Shugaba Trump ya bayyana a lokacin da ya shiga fadar White House cewa ba lallai ne Iran ta mallaki makamin nukiliya ba, wannan matsayi ya yi daidai da akidar Iran...
Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, zai yi wa ’yan Najeriya jawabi da misalin ƙarfe 7 na safiyar ranar Alhamis, domin bikin ranar dimokuraɗiyya na 2025. A cewar wata sanarwa daga kwamitin shirya bikin, shugaban ƙasa zai kuma je zaman haɗin gwiwa da ’yan majalisar dokoki da rana. Na shirya yin haɗaka don ƙalubalantar Tinubu a 2027 – Amaechi Majalisar Dokokin Kuros Riba ta dakatar da shugabar ƙaramar hukuma na wata 3 Sanarwar ta kuma bayyana cewa ba za a yi faretin bikin a bana ba. A maimakon haka, za a yi muhawara da jama’a a fadar shugaban ƙasa da misalin ƙarfe 4 na yamma. Bikin bana na zuwa ne yayin da Najeriya ke cika shekara 26 a gwadaben mulkin dimokuraɗiyya...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sojojin HKI sun kai hari akan Falasdinawan da su ka yi cincirindo domin karbar abinci da hakan ya yi sanadiyyar shahadar da dama daga cikinsu. Tun da safiyar yau Laraba ne dai sojojin HKI su ka rika kai hare-hare akan cibiyoyin cibiyoyin raba agaji wadanda dama suna a karkashin kulawar su kansu ‘yan sahayoniyar da kuma Amurka. Har ila yau hare-haren sun shafi gidajen fararen hula a cikin wasu unguwanni na zirin Gaza. Majiyar Asibitin “Audah” ta sanar da cewa an kai shahida 4 da kuma wadanda su ka jikkata sanadiyyar hare-haren na sojojin mamaya a wurin raba kayan agaji dake kan titin “Salahuddin” a tsakiyar zirin Gaza. A arewacin yankin Gaza kuwa wasu samarin Falasdinawa 4 sun yi shahada...
Amma har zuwa yanzu, babu cikakken bayani daga Gwamnatin Tarayya. A watan Mayun 2025 ne Tinubu ya miƙa buƙatar samun amincewar majalisa domin karɓar rancen Dala biliyan 21 daga ƙasashen waje, ciki har da Dala biliyan biyar daga Aramco. Rahoton Reuters bai bayyana sunayen bankunan da za su taimaka ba, amma majiyoyi sun ce ɗaya daga cikin bankunan na nahiyar Afrika ne, sauran kuma daga Gabas ta Tsakiya. Idan aka cimma yarjejeniyar, wannan zai zama mafi girma daga cikin bashin da Nijeriya ta taɓa karɓa a irin wannan hanya daga Saudiyya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Asibiti ko dakin shan magani ko wani bigire mai kama da wadannan wuri ne da marasa lafiya kan je ko ake kai su don neman waraka a duk lokacin da bukatar haka ta taso. Wuri ne da akan ware domin ceto rayukan wadanda suka jikkata suke kuma bukatar agajin gaggawa. A bisa al’ada kuma, ana sa ran samun tausayi da jinkai da sadaukarwa wajen yin dukkan mai yiwuwa kuma a ko wane lokaci don ceton rayuka daga jami’an lafiya. Sai dai ’yan Najeriya da dama sun dade suna kokawa da yadda a cewarsu wasu jami’an kiwon lafiya kan nuna halin ko-in-kula, a wasu lokutan ma da sakaci, wanda kan kai rasa rayuka. NAJERIYA...
Tawagar fursinonin yaki na kasar Rasha daga kasar Ukrain sun koma gida, saboda yarjeniyar da kasashen biyu suka cimma a birnin Istambul na kasar Turkiyya. Kamfanin dillancin labaran Spunik na kasar Rasha ya bayyana cewa a taro na biyu tsakanin jami’an gwamnatocin kasashen biyu a birnin Istambul na kasar Turkiya wato ranar 2 ga watan yunin da muke ciki ce suka cimma yarjeniyar musayar fursinonin a karo na biyu. Labarin ya nakalto ministan tsaron kasar Rasha yana cewa fursinonin Rasha da suke hannun Ukraine sun isa kasar Rasha a jiya talata. Haka ma bangaren Rasha ta mikawa gwamnatin Ukraine wasu daga cikin fursinonin da suke hannunta. Ministan ya kara da cewa a halin yanzu firsinonin suna kasar Belerus inda aka...
LEADERSHIP ta tuna cewa, gwamnatin jihar da jami’an tsaro sun fuskanci matsin lamba daga mazauna yankunan da lamarin ya shafa domin shawo kan lamarin. Fanwo, ya ba da tabbacin cewa, gwamnati ta yi shiru, amma tana samun nasara a yakin da take da masu aikata laifuka ta karkashin kasa, musamman masu garkuwa da mutane a jihar. Ya ce, nasarar da gwamnati ta samu ya biyo bayan ingantattun tsare-tsare da zurfafa hadin gwiwar hukumomin tsaro da nufin tabbatar da tsaro da walwalar kowane dan jihar Kogi. Yayin da take jajantawa iyalan wadanda hare-haren na baya-bayan nan ya shafa, gwamnatin jihar ta jaddada cewa, bai kamata a yi amfani da irin wadannan kalubalen wajen yada labaran karya ko firgita...
Gidauniyar Hind Rajab (HRF), mai rajin kare hakkin Falasdinawa, ta shigar da kara kan laifukan yaki bayan farmakin da sojojin ruwan Isra’ila suka kai kan jirgin ruwan agaji na Birtaniya Madleen a ruwan kasa da kasa a yammacin Lahadi. Koken dai ya shafi rundunar sojin ruwa ta Isra’ila Shaytet 13 da kwamandan ta, Vice Admiral David Saar Salama. Gidauniyar ta HRF ta yi kira da a gaggauta sakin masu fafutuka 12 da ake tsare da su, ciki har da mai fafutukar kare muhalli Greta Thunberg, dan wasan kwaikwayo Liam Cunningham, da Rima Hassan ta faransa, wadanda ke hannun Isra’ila. Jirgin ruwan na Madleen, na kungiyar Freedom Flotilla Coalition, na dauke da kayayyakin jinya, da abinci, da madarar jarirai, da sauran...
Majiyar sojan Rasha ta sanar da cewa; Tun daga watan Febrairu na 2024, zuwa yanzu ta tarwatsa tankokin yaki samfurin ” Abrams” kirar Amurka da ta bai wa kasar Ukiraniya har guda 26. Ya zuwa yanzu adadin wadannan tankokin da su ka rage a tare da sojojin Ukiraniya ba su wuce 5, ba domin adadinsu 31 ne. Kamfanin dillancin labarun ” Sputnik” ne ya bayyana cewa; adadin tankokin yakin na Amurka da su ka saura a tare da sojojin Ukiraniya ba su wuce 5 ba. Tun a watan Janairu na 2023 ne dai tsohon shugaban kasar ta Amurka Joe Biden ya sanar da bai wa Ukiraniya tankokin yaki samfurin Abrams a karkashin taimakon kayan yakin da take bai wa kasar....
Wadanda suka shirya jirgin agaji zuwa Gaza mai suna Madleen sun bada sanarwan cewa HKI kai farmaki kan jirgin a safiyar yau Litinin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jami’an tsaron HKI sun kaiwa jirgin Madleen hare-hare a safiyar yau Litinin kafin iasar Jirgin agajin zuwa gabar tekun Medeterania a gaza. Labarin ya kara da cewa Thiago Avila, dan rajin kare hakkin bil’adama daga kasar Brazil a cikin Jirgin ya bayyana cewa sojojin yahudawan sun yiwa jirgin kofar rago . Y ace sojojin ruwa na HKI sun kaiwa jirgin agaji ” Madleen farmakai. Jirgi wanda yake kokarin keta kofar ragon da HKI ta yi wa Gaza tun shekara 2006. Labarin ya kara da cewa sojojin yahudawan...
Wadanda suka shirya jirgin agaji zuwa Gaza mai suna Madleen sun bada sanarwan cewa HKI kai farmaki kan jirgin a safiyar yau Litinin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jami’an tsaron HKI sun kaiwa jirgin Madleen hare-hare a safiyar yau Litinin kafin iasar Jirgin agajin zuwa gabar tekun Medeterania a gaza. Labarin ya kara da cewa Thiago Avila, dan rajin kare hakkin bil’adama daga kasar Brazil a cikin Jirgin ya bayyana cewa sojojin yahudawan sun yiwa jirgin kofar rago . Y ace sojojin ruwa na HKI sun kaiwa jirgin agaji ” Madleen farmakai. Jirgi wanda yake kokarin keta kofar ragon da HKI ta yi wa Gaza tun shekara 2006. Labarin ya kara da cewa sojojin yahudawan...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A masana’antar Nollywood dake Kudancin Nijeriya, manyan masu kudinsu, sarakuna, hukumomi da gwamnatoci na iyakar kokarinsu wajen ganin masana’antar ta cigaba, ta hanyoyi daban daban da suka hada da kayan aiki, wajen daukar fim, fadada ilimi, tallace tallace da sauran tallafi da masana’antar ke bukata, a wasu lokutan ma akan daukesu har kasashen Turai wajen koyon aiki da kuma tallata hajarsu ga manyan dillalan fim a Duniya wanda ta wannan hanyar sai su samu manyan kudade. T Y ya cigaba da cewa idan ana maganar masana’antar Kannywood ba haka abin yake ba, domin kuwa a nan yankin sai mai shirya fim ya nemi gida ko kamfanin da zai shirya fim din sa ya rasa, hakan zai sa ya je ya...
Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta wallafa tsokacinta kan rahoton babban darartan Hukumar IAEA ga kwamitin gwamnonin hukumar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fitar da ra’ayoyinta da tsokacinta kan sabon rahoton da babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa (IAEA) ya gabatar ga kwamitin gwamnonin hukumar ta IAEA a ranar 24- wannan shekara ta 2025. A cewar cibiyar diflomasiyya da ta yada labarai ta hukumar makamashin nukiliya ta Iran, an fitar da bayanin mai taken “Sa ido da Tabbatarwa a Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da kudurin kwamitin tsaro mai lamba 2231 (2015)” a ranar 31 ga Mayu, 2025. Bayanin ya fayyace cewa: Rahoton da babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa...

Rundunar Sojin Mamayar Isra’ila Ta Yi Furuci Da Karancin Sojoji Saboda Raguwarsu Sanadiyyar Mutuwa Ko Rashin Lafiya
Rundunar sojin mamayar Isra’ila ta amince da samun tauyaya a yawan adadin sojojin mamayar Isra’ila sakamakon halakar wasu daga cikinsu Rundunar sojojin Isra’ila ta yarda cewa: Suna fama da matsanancin karancin sojoji masu yawa, a halin yanzu akwai yawan 10,000, da aka rasa kuma ana neman fiye da rabinsu a fagen gudanar da yaki, a ci gaba da gudanar da ayyukan soji a zirin Gaza. Rundunar sojin ta ce suna fuskantar karancin sojoji fiye da 10,000, ciki har da kusan 6,000 na rukunonin yaki,” wannan rashin sojojin rashi ne maim ai tsanani da ake bukatar samunsu cikin gaggawa, don haka rundunar soji take gudanar da duk matkn da suka dace don toshe wannan gurbin, in ji kakakin rundunar sojin mamayar...
Kasar Rasha ta kai wasu gagaruman hare-haren jiragen saman yaki marasa matuka ciki kan birnin Kharkiv na kasar Ukraine Rasha ta kai wadannan gagaruman hare-haren ne ta hanyar amfani da jiragen saman marasa matuka ciki kan birnin Kharkiv na gabashin Ukraine. Magajin garin Kharkiv ya ce: Hare-haren da jiragen saman Rasha suka kai a tsakiyar birnin sun haddasa gobara da barna sosai. Takaddama tsakanin Rasha da Ukraine na kara kamari a kasa duk da ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin biyu ke yi. Mjiyar sojin Ukraine ta amince cewa: Sojojin Rasha sun kaddamar da gagaruman hare-hare kan birnin Kharkiv da ke gabashin kasar Ukraine ne, lamarin da ya haifar da fashe-fashe a birnin, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da...
Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham Hotspur ta sallami kocinta Ange Postecoglu ƙasa da wata daya bayan ya lashe kofin Uefa Europa League na bana, Ange wanda ya zo Tottenham daga Celtic ya shafe shekaru biyu ya na jan ragamar kungiyar. Shugaban Tottenham Levy ne ya bayyana wannan mataki na sallamar Ange bayan wani taro da mahukuntan ƙungiyar suka yi a ranar Juma’a, wanda ya ce hakan shi ne mafita ga ɓangarensu da kuma ɓangaren kocin wanda ya jagoranci wasanni 101 a matsayin koci. Liverpool Sun Zama Zakaran Gasar Premier Bayan Lallasa Tottenham Tottenham Ta Doke Manchester United A Wasan Karshe Na Europa A zahiri, alaƙar babban kocin da tawagarsa ta zama ɗaya daga cikin manyan dalilan da suka sa kocin...
Wani Lauya Okere Kingdom Nnamdi, wanda ya gabatar da takardu don samun rajistar Jam’iyyar Mutanen Kasa (PPP) a ranar 28 ga Maris, 2025, ya ce bayan wata daya sai INEC ta bayyana cewa ba ta bude adireshin fara yin rajistar sabbin jam’iyyun siyasa. Jami’an INEC da suka yi magana kan lamarin, sun musanta zarge-zargen. Sun bayyana cewa duk da cewa an karbi bukatar yin rajista har guda 104, ana ci gaba da gudanar da bincike, sannan kuma tsarin zai fara gudana nan ba da dadewa ba ta hanyar sadarwaar zamani don inganta gaskiya da ingancin aiki. “Hukumar ta amsa wa masu nema. Ba daidai ba ne a zargi INEC da jinkirin amsa bukatun yin sabbin rajistar. Za a bude Shafin...
A rana ta biyu tabukuwan babbar salla, sojojin HKI suna ci gaba da yi wa Falasdinawa kisan kiyasahi da kuma rusa matsugunansu a yankin Gaza. A yau Asabar kadai gwamman Falasdinawa ne su ka yi shahada a cikin sansanonin da Falasdinawa suke gudun hijira a cikinsu. An sami shahidai 5 da kuma wasu mutane biyu da su ka jikkata a kusa da cibiyar rana kayan agaji a yammacin Rafah dake kudancin zirin Gaza. A yammacin birnin Khan-Yunus kuwa wasu Faladinawa 12 ne su ka yi shahada, yayin da wasu 40 su ka jikkata saboda harin da ‘yan sayahoniyar su ka kai wa sansaninsu. A arewacin Khan-Yunus kuwa, sojojin mamayar sun ruguza gidajen Falasdinawa da dama. A kusa da cibiyar kiwon...
“Gwamnatin ta yi hakan ne, sakamakon tabbatar da ganin an fara aiki a kamfanin daga nan zuwa karshen watan Mayun shekarar 2025. “Gwamnatin Jihar da shude ce ta bai wa kamfanin kwangilar da kuma wani kamfani da ke Kasar Indiya aikin, inda gwamnatin ta zuba dala biliyan 12 a kamfanin,” in ji Hamza. Sai dai, ya bayyana cewa; saboda kasancewar wasu dalilai, ba a samu cimma wata gagarumar nasarar a zo a gani ba a kan aikin. Ya sanar da cewa, a watan da ya gabata ne, gwamnatin jihar ta sake yin nazari kan yarjeniyar ta baya da aka kulla, wadda kuma za a dawo, domin a ci gaba da yin aikin. Babban Sakaren ya kara da cewa, manyan batutuwan...
Kafafen yada labarai na HKI sun tabbatar da mutuwar wasu da dama daga cikin sojojin su a wani tarkon da dakarun Hamas suka yi masau a garin Khan Yunus na Gaza, wasu sun ji nrauni, sannan har yanzun akwai wadanda ba’a fito dasu daga karkashin burbushin gine-gine ba. Kamfanin dillancin labatan IP na kasar Iran. Majiyar yahudawan ta kara da cewa karfin da kungiyar Hamas ta tokwarorinsu suke da shin a halaka sojojin HKI kamar haka ya Sanya shakku a kan yiyuwar samun nasara a kansu. Kamfanin dillancin labaran Hadashot Bazman na yahudawan ya tabbatar da cewa an kashe yahudawa 5 sannan wasu 12 sun ji Rauni a yayinda har yanzun ba’a san halin da wasu daga cikin sojojin suke ciki...
Domin shawo kan wannan matsalar, ministan ya zayyana kokarin da ake yi a karkashin dabarun bunkasa kiwon dabbobi na kasa, wanda ya mayar da hankali kan ginshikai guda 10 da suka hada da bunkasa kimar dabbobi, inganta kiwo, kiwon lafiyar dabbobi, samar da kudi, sauya salon kiwo da karfafawa matasa da mata gwiwa kan dogaro da kai. Maiha ya yi tunin cewa zuwa yanzu ma’aikatar ta samu cimma wasu nasarori da suka hada da yin rajistar nau’in kiwo guda takwas, “na farko a cikin shekaru 48” da kuma samar da wani shiri na kasa kan albarkatun halittun dabbobi tare da hadin gwiwar FAO. “Dabbobinmu na cikin gida suna samar da lita 1-2 na madara a kullun, idan aka kwatanta da...
Kafafen watsa labarun kasar ta Zambia da kuma jam’iyyarsa ta “PFT” sun sanar da cewa; Tsohon shugaban kasar ya fadi ne a lokacin da yake motsa jiki a gidansa dake birnin Lusaka. Bayan da aka kai shi asibitin soja na “Maina Soko” likitoci sun tabbatar da cewa ya rasu. Gwamnatin kasar ta Zambia ta tabbatar da rasuwar tsohon shugaban kasar, tare kuma da shelanta ranakun alhini na kasa. Shi dai Lunga ya jagorancin kasar ta Zambia ne daga 2015 zuwa 2021 da ake yabonsa da gina muhimman cibiyoyi a kasar, sai dai kuma hakan ya bar kasar da dimbin bashi. Ya zuwa yanzu dai ba a sanar da lokacin da za a yi jana’izar tsohon shugaban kasar ba.
Hukumar Kula da Sufuri ta Jihar Kaduna tace shirin Bus Rapid Transit BRT da ake shirin kaddamarwa zai taimaka matuka wajen rage kudaden sufuri ga mazauna jihar, da zarar an fara aiwatar da shi. Daraktan Hukumar, Injiniya Inuwa Ibrahim, ne ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Kada Hive da ke Kaduna. An shirya taron ne domin wayar da kan jama’a game da shirin BRT, sannan matakan da aka dauka ya zuwa yanzu. Taron an gudanar da shi ne domin sauraron ra’ayoyin al’umma kan yadda za a aiwatar da shi cikin nasara. Injiniya Inuwa ya bayyana cewa tsarin BRT zai taimaka wajen rage cunkoson ababen hawa...
Jakadan kasar Iran a Mosco ya bayyana cewa shugaban kasar Rasha Vladimir Putin zai kawo ziyarar aiki Tehran nan ba da dadewa ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran. Labarin ya kara da cewa kasashen biyu sun kulla yarjeniyoyi masu yawa a tsakanin daga ciki har da masu dogon zango. Kazem Jalali ya bayyana a yau Alhamis kan cewa kasar Rashe ce kasa tilo wacce ta zuwa jarin dalar Amurka biliyon $8 a bangaren gas da man fetur. Kuma ya zuwa yanzu ta kashe dala $ 5bl daga cikinsu. Banda haka zata kashe kudade don kammala layin dogo wacce ake kira hanyar Arewa zuwa Kudu. Banda haka Rasha zata fara tura danyen man fetur daga Rasha zuwa Iran don...
Farfesa Jibril Amin Likita kuma tsohon malamin Jami’a, ya rasu a jiya Laraba yana dan shekara 85 a duniya. Jaridar Daily Trusta ta Najeriya ta nakalto majiyar iyalar mamacin na tabbatar da haka. Ta kuma bayyana cewa kwamishin gidaje a jihar Adama Hon Abdullahi Prambe ya tabbatar da labarin. Sannan ya kara da cewa an yi masa sallar Jana’iza a babban masallacin kasa a Abuja a yau Alhamis. Sannan za’a maida shi garinsa Song na jihar Adamawa inda za’a rufe shi. A rayuwarsa dai Farfesa AAmin likitan zuciya ne, sannan malami da shugaba Jami’ar Maiduri na Jahar bornin a wani lokaci, ya kuma karantar. Har’ila yau Farfesa Amin ya rike kujerar Ministan ilmi da manfetur, sannan jakadan Najeriya A Amurka...
Aliyu, ya bayyana cewa Jibrin manomi ne daga ƙauyen Gargai da ke ƙaramar hukumar Bebeji a Kano. Ya kuma ce yana fama da cutar gyambon ciki da hawan jini. Likitoci sun bayyana cewa rasuwarsa ta faru ne sakamakon bugun zuciya da gazawar zuciya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wata al’ada da ta zama gama gari a tsakanin matasa, ita ce yankewa da fige kaji a unguwanni, musamman a lokutan bukukuwan Sallah. A da, ana da wurare na musamman da ake yin irin wannan abu. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin kauce wa ɓarnar ambaliyar ruwa NAJERIYA A YAU: Mokwa: Tsakanin Taraddadin Rashin Matsuguni Da Jimamin Rashin ’Yan-Uwa Sai dai masana sun ce wannan abu na iya haifar da matsaloli ga lafiya da kuma gurɓata muhalli. Wannan shi ne abin da shirin Najeriya A Yau zai tattauna a kai, yayin da ake Bikin Ranar Muhalli ta Duniya kwana ɗaya kafin Babbar Sallah. Domin sauke shirin, latsa nan
A watan Oktoban 2024, wani jirgin ruwa ya kife da kusan mutum 300 a Mokwa, na Jihar Neja. Haka kuma, a watan Satumban 2023, mutum 24 sun mutu a wani hatsarin kwale-kwale a Jihar Neja. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp