2025-06-15@17:22:49 GMT
إجمالي نتائج البحث: 222

«rajistar layin»:

    Martanin Iran game da ta’addancin haramtacciyar kasar Isra’ila na ci gaba a rana ta biyu Ana ci gaba da mayar da martani mai girma na Iran game da harin da haramtacciyar kasar Isra’ila take kaiwa da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka ciki. ‘Yan mintoci da suka gabata a zaman wani bangare na biyu na “Alkawarin Gaskiya Na 3”, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta harba daruruwan makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka kan haramtacciyar kasar Isra’ila. An harba wadannan makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka ciki da kuma jiragen sama masu saukar ungulu daga Tehran da sauran garuruwan kasar Iran a matsayin wani mataki na murkushe laifuffukan da yahudawan sahayoniyya suka aikata a kan...
    Ministan harkokin wajen Omani Badr Albusaidi ya sanar da cewa, ba za a gudanar da zagaye na shida na tattaunawar nukiliya tsakanin Iran da Amurka ba. Yau Lahadi ne aka shirya gudanar da zagaye na gaba na shawarwari a Muscat babban birnin kasar Oman. A cikin wani sakon da ya wallafa a kan X (tsohon Twitter), Albusaidi ya tabbatar da sokewar, yayin da ya jaddada cewa “diflomasiyya da tattaunawa sun kasance hanya daya tilo ta samun zaman lafiya mai dorewa.” “Tattaunawar Iran da Amurka, wadda aka shirya gudanar da ita a birnin Muscat ranar Lahadin nan, ba za ta gudana a yanzu ba. Tattaunawar diflomasiyyar da aka faro kan shirin nukiliyar Iran, a watan Afrilu a shiga tsakanin masarautar Oman,...
    A yau Asabar ne kasar Sin ta yi nasarar harba tauraron dan Adam na lura da yanayin bala’u a doron kasa, wanda ake sa ran zai rika samar da bayanai ga kasar Sin dangane da aukuwar bala’u daga indallahi, ta aikewa da sakwanni tsakanin sararin samaniya zuwa doron duniya. An harba tauraron dan Adam din mai suna Zhangheng 1-02, ta amfani da rokar Long March-2D, daga tashar harba kumbuna ta Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar Sin, da karfe 4 saura mintuna 4 agogon Beijing, ya kuma shiga da’irarsa ba tare da wata matsala ba, kamar dai yadda hukumar kula da binciken sararin samaniya ta kasar Sin ko CNSA ta tabbatar. Kazalika, CNSA ta ce, wannan aiki muhimmin mataki ne...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya aike da sako ga al’ummar Iran bayan harin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasar A yammacin jiya ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gabatar da sakon ta gidan talabijin ga al’ummar Iran bayan harin ta’addanci na baya-bayan nan da yahudawan sahayoniyya suka kaddamar kan kasar Iran. Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana a cikin wani sakon da ya aike ta gidan talabijin ga al’ummar Iran cewa: Sojojin Iran za su yi aiki da dukkanin karfinsu, kuma za su mayar da martani kan wannan mugunyar aniya ta ‘yan sahayoniyya kaskantattu marasa tunani da basira. Jagoran ya jaddada cewa: Yahudawan sahayoniyya ba za su fita cikin wannan aika-aika ba,...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bude kofofin wuta a kan haramtacciyar kasar Isra’ila ta hanyar mayar da martani kan harin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasarta Iran ta bude kofofin jahannama kan ‘yan sahayoniyya a matsayin mayar da martani ga mummunan zaluncin da suka kaddamar kan lardunan Iran da dama, wanda ya yi sanadiyyar shahadan mutane da dama da jikkata. Bayan da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa: Wajibi ne gwamnatin mamayar Isra’ila ta jira mummunan hukunci mai tsanani da kuma makoma mai daci kan abin da aikata, kuma bayan da sabon kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci Manjo Janar Muhammad Pakpour ya bayyana cewa: Sojojin kasar Iran za su bude kofofin...
    Biyo bayan sauya sheka da aka yi kwanan nan, a zauren majalisar dattawa, APC na da kujeru 68; PDP na da 30; LP na da 5; SDP na da 2; NNPP na da 1; APGA na da 1 da kuma kujeru guda biyu da babu kowa, guda daya daga Jihar Edo da daya daga Jihar Anambra. Masana harkokin siyasa na ganin cewa bisa yadda lamura suke a halin yanzu, adadin na iya haurawa lokacin da majalisar tarayya ta dawo daga hutu, bayan sauya shekar Gwamna Umo Eno na Jihar Akwa Ibom daga PDP zuwa APC. Ana sa ran wasu daga cikin ‘yan majalisar tarayya na jihar za su iya bin sahunsa. A halin yanzu, Jihar Akwa Ibom tana da sanatan...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghaei, ya zargi Isra’ila da yin zagon kasa ga diflomasiyya ta hanyar tsallaka jajayen layukan kasar Iran, da kuma ta’azzara rikici da kasashen yammacin duniya, yana mai bayyana cewa, ba za a iya yin shawarwari a halin da ake ciki ba. Sanarwar dai na nuni da koma baya sosai a yunkurin diflomasiyya na Iran da kasashen Yamma, musamman yadda tashe-tashen hankula ke kara ta’azzara bayan matakin sojin Isra’ila. Matakin na Isra’ila da hadin kai tare da Amurka na a matsayin kokari na kawar da duk wata dama ta cimma sakamakon shawarwari. “Ba za a iya shawarwarin ba yayin da a lokaci guda ake barin gwamnatin kisan kare dangi ta kai hari kan Iran.” “Ba...
    Jagoran juyin musulunci na Iran wanda shi ne babban kwamandan rundunonin sojan kasar Iran, ya nada sabbin kwamandoji da maye gurbinsu da wadanda su ka yi shahada. Bayan shahadar kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci Shahid Hussain Salami, da kuma  babban hshahid Muhammad Hussain Bakiri, sai Shahid Gulam Ali Rashid wanda shi ne kwamandan Bakirin soja na “Khatamul-Anbiya, jagoran juyin ya sanar da sunayen wadanda su ka maye gurbinsu. Birgediya Muhammad Pakphur shi ne wanda jagoran ya sanar a matsayin sabon kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci, sai kuma  Manjo Janar Musawi a mastayin sabon kwamandan rundunar sojan kasar, yayin da aka nada janar Ali Shadmani a matsayin kwamandan Barikin soja na Khatamul-Anbiya.
    Bayan harin da gwamnatin Sahayoniya ta kai kasarmu, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya aike da sako ga al’ummar Iran. Ga sakon kamar haka Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai Al’ummar Iran masu daraja! Gwamnatin yahudawan sahyoniya ta hanyar aikata wani laifi da sanyin safiyar yau, ta sake bayyana munanan dabi’arta da fasadi. Ta hanyar kai hari dole ne wannan ya fuskanci hukunci mai tsanani. A wannan harin makiya, kwamandoji da masana kimiyya da dama sun yi shahada. Wadanda suka gaje su kuma da abokan aikinsu za su ci gaba da aiki nan take akan wannan tafarki, godiya ta tabbata ga Allah. Ta hanyar wannan danyen aiki, gwamnatin Sahayoniya ta kaddara akan ta cewa...
    Zuzzurfar tattaunawa da ta wakana tsakanin tsagin Sin da na Amurka a birnin Landan, ta sa masu bayyana ra’ayoyin jin karfin gwiwa game da makomar shawarwarin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka. Kuri’un jin ra’ayin jama’a na kafar CGTN ta kasar Sin, sun nuna yadda masu bayyana ra’ayoyi suka amince cewa, shawarwari sun nuna kyakkyawan fata game da aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma yayin tattaunawar da suka yi ta wayar tarho, tare da sassauta sabani a batutuwan tattalin arziki da cinikayya tsakanin sassan biyu. Yayin kuri’un jin ra’ayoyin, masu bayyana mahanga sun goyi bayan matsayar Sin, inda kaso 87.1 bisa dari suka amince cewa ba wani batu na wa ya yi nasara, ko wanda...
      Sai dai kuma shugaba Tinubu ya yi amfani da wannan damar wajen yi wa shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, da kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas ado da lambar yabo ta GCON, yayin da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin da mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Kalu, da lambar yabo ta CFR.   Ga cikakken jerin sunayen sabbin mutane 67 da aka karrama da lambar yabon, kamar yadda fadar shugaban kasa ta fitar:   Grand Commander of the Order of the Niger (GCON).   Shehu Musa Yar’Adua Rt Hon Tajudeen Abbas Senator Godswill Akpabio Wole Soyinka   Commander of the Order of the Niger (CON) Ghali Umar Na’Abba Salisu Buhari Umaru Dikko Uche Chukwumerije Bala Mohammed Gwagwarwa Aisha Yesufu Innocent Chukwuma...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba An ware ranar 12 ga watan Yuni a matsayin Ranar Dimokuraɗiyya a Najeriya domin tunawa da ranar da aka gudanar da zaɓen da ake ɗauka a matsayin mafi sahihanci da adalci a tarihin ƙasar. Sai dai, bayan sama da shekaru 30 da gudanar da wannan zaɓe da kuma gwagwarmayar da ta biyo baya, wasu masana na ganin har yanzu ba a kai ga amfanin da ake murad daga dimokuraɗiyyar ba. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Fara Sana’a Ba Tare Da Jari Ba NAJERIYA A YAU: Hanyoyin kauce wa ɓarnar ambaliyar ruwa Ko mene ne hujjar kowane ɓangare? Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau zai yi duba a wannan lokaci. Domin sauke...
    Shugaba Bola Tinubu ya soke shirin yi wa ‘yan kasa jawabi kai tsaye da aka shirya gudanarwar tun farko a ranar Alhamis, 12 ga watan Yuni, domin tunawa da cikar ranar dimokradiyyar Nijeriya shekaru 26. A maimakon haka, zai gabatar da jawabinsa na ranar dimokuradiyya a gaban wani zama na musamman na hadin gwiwa na majalisar dokokin kasar. An bayyana sauyin ne a wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na ofishin SGF, Segun Imohiosen ya fitar a ranar Laraba. Amma Duk da haka, sauran shirye-shiryen ranar Dimokradiyya za su ci gaba da gudana kamar yadda aka sanar a baya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
    Binciken ya nuna cewa, mutum biyu daga cikin wadanda ake zargin ma’aikatan Dangote ne kai tsaye, yayin da sauran ke aiki da kamfanonin da ke da alaka da safarar mai daga matatar Dangote zuwa wuraren ajiya na kamfanin da ke Ibese da Obajana. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ta sha bamban da majalisun da ke goyon bayan masu goyon baya masu laifi misalin masu kisan gilla a Gaza Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada a yau Laraba cewa: Matsayin majalisar shawarar Musulunci ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bambanta da kasashen duniya, kuma ya sha bamban da majalisar da ke goyon bayan zalunci, nuna wariya, banbance-banbancen ra’ayi da masu aikata laifuka irin su kisan gilla a Gaza. Yayin ganawarsa da mambobin majalisar shawarar Musulunci a ranar Laraba, Jagora ya yi la’akari da cewa: Majalisun dokokin duniya suna da kamanceceniya ta fuskar nauyi doka. Duk da haka, ya jaddada cewa ma’auni...
    Iran ta ce za a gudanar da zagaye na gaba na tattaunawa da Amurka a ranar Lahadi mai zuwa a Muscat, babban birnin kasar Oman. Kakakin ma’aikatar Esmail Baghai a wata sanarwa da ya fitar ya ce “An shirya zagaye na gaba na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka a ranar Lahadi mai zuwa a birnin Muscat.” Tun a watan Afrilu, Tehran da Washington ke gudanar da shawarwarin kan shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya. An yi shawarwari guda uku a tsakanin kasashen biyu a birnin Muscat, yayin da sauran biyun suka gudana a Rome, babban birnin kasar Italiya. Tehran da Washington sun gudanar da wadannan zagaye biyar na shawarwarin a shiga tsakanin kasar Oman, kan batun maye gurbin yarjejeniyar nukiliyar...
    Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar a yau Litinin 9 ga wata sun nuna cewa, a watan Mayun bana, ma’aunin farashin kayayyakin masarufi, watau CPI na kasar, ya ragu da kaso 0.1 bisa dari, bisa na makamancin lokacin bara, kuma farashin makamashi ya zama babban dalilin da ya haifar da raguwar. Kana, ma’aunin farashin sarrafa kaya na cikin gida, watau PPI shi ma ya ragu da kaso 3.3 bisa dari, bisa na makamancin lokacin bara, kuma adadin ya ragu da kaso 0.4 bisa dari, idan aka kwatanta da na watan Afrilun bana. Duk da cewa ma’aunin CPI na watan Mayu ya ragu kadan, amma farashin kayayyaki a wasu bangarori ya canza, al’amarin da ya shaida rawar da...
    Jakadan kasar Iran a MDD Amir Sa’eid Iravani ya musanta zargin kasar Amurka na cewa falasdinawa dauke da makamai a Gaza suna aiki ne tare da umurnin Iran. A kuma dukkan yankunan da HKI take mamaye da su a kasar Falasdinu da ta mamaye. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto Iran vani yana cewa Amurka ta dorawa iran wannan zargin ne saboda boye laifukan yakin da HKI take aikatawa a Gaza da kuma sauran yankunan Falasdinawa da take mamaye da su. A wani jawabin da ta gabatar a gaban kwamitin tsaro na MDD a ranar Laraba mai rike da mukamin jakadan Amurka a MDD Dorothy Shea ta bayyanawa kwamitin tsaro kan cewa dole kungiyar Hamas ta mika...
    Har ila yau, ya bayyana cewa, bangaren tekun kudancin kasar Sin gaba daya yana cikin kwanciyar hankali kuma babu wata matsala game da ‘yancin zirga-zirgar jiragen ruwa da na sama da dukkan kasashe ke morewa bisa doka. Ya ce, a ko da yaushe, kasar Sin na dagewa kan amfani da tattaunawa da tuntubar juna wajen warware sabani da magance abubuwan da aka sha bamban a kai game da teku yadda ya kamata a tsakanin kasashen da abin ya shafa kai-tsaye, bisa mutunta hakikanin tarihi na gaskiya. Haka nan, ya kamata kasashen da ba na yankin ba su mutunta kokarin da kasashen yankin suke yi na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tekun kudancin kasar Sin, maimakon haddasa fitina...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi wanda yake ziyar aiki a kasar Lebanon bayyana cewa kasarsa tana goyon bayan hadin kan mutanen kasar Lebanon. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka bayan ganawarsa da shugaban majalisar dokokin kasar ta Lebanon a yau Talata a birnin Beirut babban birnin kasar. Aragchi ya ce kasar Iran tana goyon bayan kasar Lebanon ta hanyar kungiyar Hizbullah. Kuma tana goyon bayanta kan HKI wacce take mamaye da wasu yankuna a kasar. Muna goyon bayan gwamnati da mutane a duk wani kokarin da zasu yi na kwato yankunan kasar wadanda HKI take mamaye da su.  Ministan kafin haka ya bayyana cewa JMI tana daga cikin kasashen da zasu...
    Wasu kuma sun ce akwai rashin jituwa tsakanin Gwamnan da mahaifinsa, Oba Akinruntan. Bayan saukar Akinruntan, an zaɓi Ololade Gbegudu daga Okitipupa a matsayin sabon mataimakin kakakin majalisar. Gbegudu, mai shekara 42, ya riƙe muƙamin shugaban kwamitin tsaro da ci gaban al’umma a majalisar kafin wannan sabon muƙamin. Oluwatoyin James daga Akoko ta Arewa Maso Gabas ne, ya ayyana sunansa, yayin da Chris Aiyebusiwa daga Okitipupa I ya mara masa baya. Haka kuma, tsohon jagoran majalisar, Ogunmolasuyi daga Owo I, ya sauya wajen aiki da Olatunji Oshati daga mazaɓar Ose, wanda yanzu shi ne sabon shugaban masu rinjaye. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
    Dillalan rago a jihar Kano sun nuna damuwarsu kan rashin zuwan masaya da suke fuskanta duk da ‘yan kwanaki da suka rage ayi bukukuwan Sallah.   Ziyarar da aka kai kasuwar dabbobi ta Gandun Albasa ta nuna cewa, da yawa daga cikin masu sayar da kayayyaki sun shafe tsawon yini ba tare da yin cinikin komai ba, inda masu saye kadan ke zuwa sayen dabbobin hadaya.   Da yake zantawa da gidan rediyon Najeriya shugaban kasuwar dabbobi ta Gandun Albasa, Alhaji Yusuf Ahmed Muhammad ya bayyana cewa duk da cewa mutane na zuwa kasuwar domin tambayar farashin, amma a zahiri kadan ne ke saye.   Ya bayyana cewa yayin da wasu kwastomomi ke siyan kananan raguna da farashinsu ya kai...
    Sojojin Yemen sun kai jerin hare-hare har sau 4 kan filin jirgin saman Ben Gurion tare da wasu wurare masu muhimmanci a cikin Isra’ila Sojojin Yemen sun sanar da aiwatar da hare-haren soji masu tsanani guda hudu a kan filin jirgin sama na Lod, wanda aka fi sani da “Ben Gurion” a haramtacciyar kasar Isra’ila, da kuma wasu muhimman wurare a yankunan Jaffa, Ashdod da Umm al-Rashrash a cikin Palasdinu da aka mamaye. Rundunar sojin Yemen ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau cewa: Rundunarta ta kai wasu hare-haren soji masu inganci a kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da aka mamaye da makamai masu linzami. Dakarun sojin sun tabbatar da cewa: wannan...
    Kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya sun bayyana rashin jin dadinsu ga Isra’ila, kan hana su ziyartar yankunan Falasdinawa Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa sun bayyana rashin jin dadinsu ga gwamnatin Isra’ila, game da rashin amincewa da tawagar kungiyar kasashen ta ziyarci yankin da aka mamaye a Gabar Yamma da kogin Jordan don tattaunawa da shugaban Falasdinawa. A wani taron manema labarai, ministan harkokin wajen Saudiyya, Yarima Faisal bin Farhan Al Sa’ud, ya ce matakin da Isra’ila ta dauka kamar watsi ne da tayin zaman lafiya. A dai tsara a wannan Lahadi ne ministocin kasashen Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Masar, Jordan, Qatar, da Turkiyya, karkashin jagorancin ministan harkokin wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan za su isa birnin Ramallah domin ganawa...
     Mahukuntan kasar Saudiyya sun sanar da cewa a ranar hawan arfa na bana, za a fassara hudubar da za a yi da harsuna 34 daga cikinsu da akwai Hausa da filatanci. Wasu harsunan Afirka da za a fassara hudubar ta Arfa da su, sun hada yarabanci, Sawahili, Somali da kuma Amharic na kasar Habasha. A bisa sanarwar da kasar Saudiyya ta yi na ganin watan zulhijja, a ranar 27 ga watan Mayu, za a yi hawan Arfa a ranar 5 ga watan na Mayu.
    Dakarun gwagwarmayar kasar Yemen sun bayyana cewa: Za su mayar da jiragen saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila abin ba’a Shugaban majalisar koli ta siyasar kasar Yemen Mahdi al-Mashat, ya tabbatar da cewa: Tsaron sararin samaniyar sojojin kasar Yemen zai iya tunkarar jiragen saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila da suke kai hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yemen. Shugaban majalisar koli ta siyasar kasar Yemen Mahdi al-Mashat ya shaidawa tashar talabijin ta Al-Mayadeen cewa: Kariyar tsaron sararin samaniyar sojojin Yemen za ta mayar da jirgin saman makiya ‘yan sahayoniyya abin izgili a cikin kwanaki masu zuwa. Al-Mashat ya jaddada cewa: Sojojin kasar Yemen za su iya tunkarar jiragen saman yakin yahudawan sahayoniyya ba tare da haifar da wata illa ga...
    Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Makaman nukiliya ba su da gurbi a cikin akidar Jamhuriyar Musulunci ta Iran Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran ba za ta taba yin watsi da haƙƙin da doka ta tanada ba ta fannin inganta sinadarin uranium, domin inganta harkar kiwon lafiya, aikin gona da masana’antu, yana mai jaddada cewa: makaman nukiliya ba su da gurbi a cikin koyarwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A yayin ziyarar da ya kai masarautar Oman, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, a wata hira da gidan talabijin na kasar, ya yi bayani kan batutuwan da suka shafi kasashen biyu, da kuma muradun yankin da na kasa da kasa na Iran da Oman, da kuma muhimman batutuwan...
    Sojojin Yemen sun kai hari kan filin jirgin saman Ben Gurion da makami mai linzami lamarin da ya tarwatsa cinkoson jama’a a filin jirgin Sojojin Yemen sun sanar da kai farmakin soji kan filin tashi da saukan  jiragen saman Ben Gurion tare da yin barazanar ci gaba da toshe hanyoyin zirga-zirgar jiragen sama da na ruwa na haramtacciyar kasar Isra’ila muddin bata kawo karshen killace Zirin Gaza da ta yi ba. Kakakin rundunar sojin kasar Yemen Birgediya Janar Yahya Sari’e ya tabbatar da cewa: Wannan farmakin ya samu nasarar cimma burin da aka sanya a gaba, wanda ya tilastawa miliyoyin ‘yan sahayoniyya ‘yan mamaya tserewa zuwa maboyar karkashin rami tare da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a filin jirgin. Sari’e...
    Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-Husi ya bayyana cewa; Harin da “Isra’ila” ta kai wa filin saukar jiragen saman Sanaa, manufarsa  ita ce yin matsin lamba akan matsayarmu ta taimakawa al’ummar Falasdinu da ake zalunta.” Sayyid Abdulmalik al-Husi ya kara da cewa;  Komai girman hare-haren da Isra’ilan za ta kai ba zai yi tasiri akan matsayarmu ta taimakawa Gaza ba,sannan kuma ya kara da cewa; Abinda Isra’ila makiya ke son yi, shi ne a kyale ta yi yadda take so da Falasdinawa ba tare da an mayar mata da martani ba daga kowace kasa ta musulmi.” Shugaban kungiyar ta Ansarullah ya kuma ce; Matsayar da kasar Yemen take dauka na taimakawa Falasdinawa, matsaya ce ta addini.” Haka...
    Gwamna Uba Sani ya amsa da cewa gwamnati ta kashe sama da Naira biliyan 100 cikin watanni shida don magance matsalar ƙarancin ruwa a faɗin jihar, tare da alƙawarin cewa za a maye gurbin dukkan kayan aikin da suka lalace. Ya ƙara da cewa an riga an kashe sama da Naira miliyan 400 wajen gyara da maye gurbin bututun ruwa da aka lalata, kuma kafin ƙarshen shekara Kaduna za ta fara samun ruwa ba tare da katsewa ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Majalisar dokokin kasar Iran ta sake zaben Mohammad Baqir Qalibof a matsayin shugaban majalisar dokokin kasar na wata shekara a zaben da aka gudanar a cikin majalisar a jiya Litinin. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran,  ya bayyana cewa ya sami kuriu 219 daga cikin Jimillan kuri’u 272, wanda ya bashi babban rnjaye a kan sauran wadanda suke takara da shi. Wannan kuma ya nuna cewa shugaban majalisar ya na da karbuwa a cikinta. Kuma yana da tasiri a cikin al-amuran gwamnati musamman a lokacinda kasar take fama da barazana a ciki da wajen kasar, musamman dangane da tattaunawa kan shirin makamashin Nukliyar kasar, wanda ake tattaunawa a kansa da Amurka. An gudanar da wasu zabubbuka a cikin majalisar...
          Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Kuma taron zai baiwa jama’a damar yi wa gwamna tambayoyi kai tsaye, kuma su sami bayani kan ayyukan gwamnati.” “Wannan shi ne ci gaba a siyasance, kuma ba sabon abu bane a duniya, amma a jihar Yobe, wannan wani sabon salo ne. Mataki ne na sauke nauyi, gaskiyar da jama’a suka baiwa gwamnati, samun hadin kai, da sauran jama’a kai tsaye.” In ji shi. Dakta Yabani ya jaddada cewa, taron an shirya shi ne domin baiwa al’ummar jihar Yobe kwarin gwiwa, a tafarkin gudanar da ayyukan da gwamnati take aiwatarwa na ci gaba da kyauta jindadin su, tare da basu dama wajen tofa albarkacin su wajen tsara manufofi gwamnati. “Maigirma Gwamna Buni a shirye yake ya amsa duk wata tambayar...
    Ministan gina hanyoyi da ci gaban kasa na JMI Farzaneh Sadegh ta ziyarci kasar Iraki don bin duddugin aikin layin dogo da ake ginawa tsakanin kasashen biyu. Farzaneh Sadegh ta isa bienin Bagdaza a jiya Asabar inda mataimakin ministan sifiri na kasar Iraki da kuma jakadan kasar Iran a Bagdaza suka yi maraba da ita. Ministan ta ziyarci inda sojojin Amurka suka kashe kwamandojin yaki da yan  ta’adda Janar Kasim Sulaimani da kuma Mahdi Almuhandis a cikin watan Jenerun shekara ta 2020. Farzaneh Sadegh zata gana da firai ministan kasar Iraki Mohammad shiaa Assudani, da wasu jami’an gwamnatin kasar Iraki. Sannan zata ziyarci aikin shimfida layin dogo mai tsawon kilomita 33 wadanda kasashen biyu suke yi don hada garin Chalamce...
    MDD ta bayyana cewa; Da akwai damuwa mai zurfi akan halin da ‘yan Hijirar Sudan suke ciki a gabashin kasar Chadi saboda rashin masu bayar da kudaden taimakon kula da su. Ma’aikatan MDD a fagen ayyukan ceto sun ce ana samun kwararar ‘yan hijira daga Sudan zuwa gabashin kasar ta Chadi, da kuma ‘yan kasar ta Chadi da suke komawa gida. Tun da yaki ya barke a Sudan zuwa yanzu an yi rijistar kwararar ‘yan Sudan masu yawa. A cikin wata daya kadai ‘yan Sudan  su dubu 55, sai kuma ‘yan asalin Chadi da su ka koma gida zuwa Jahar Inidy da yankin Fira, a gabashin kasar, da su kuma sun kai dubu 39. Sanarwar ta MDD ta ci gaba...
    An gudanar da Jana’izar Malam Maikudi Umar (Cashman) Shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Ƙasa a garin Zariya, Jihar Kaduna. Marigayin dan shekaru 62, jarumi ne, mai shirya finafinai kuma ma darakta da ke gudanar da aikace aikacen sa a masana’antar Kannywood da Nollywood. Dan uwan mamacin, Abdul Azeez Muazu, Talban Tudun Jukun yace Umar ya rasu ne bayan gajeriyar jinya a Asibitin Koyarwa Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Shika, Zariya. Yace rasuwar ya faru ne a daren ranar laraba sailin da akayi Jana’izar sa a ranar Alhamis a makabarta dake Zariya. Shi dai Marigayin har ilau malami ne a Kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli dake Zariya. Ya rasu ya bar yan uwanshi da dama Hoton...
    Iran ta sanar da lokaci da kuma wurin da za a yi sabon shawarwari tsakanin Iran da Amurka Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya sanar da cewa: A gobe Juma’a ne za a gudanar da zagaye na biyar na shawarwari tsakanin Iran da Amurka a birnin Roma. A lokacin da ya isa birnin Shiraz don halartar taron yankin kan harkokin diflomasiyya na cikin gida, Araghchi ya bayyana cewa, gudanar da wannan taro da ya fi mayar da hankali kan diflomasiyyar tattalin arzikin yankin, ya shiga cikin tsarin manufofin makwabtaka na Iran, yana mai jaddada cewa, ko shakka babu za ta yi tasiri. Araqchi ya kara da cewa “Za a gudanar da tattaunawar zagaye na biyar ranar Juma’a a Roma...
    Manyan kamfanonin jiragen sama na kasa da kasa da dama sun tsawaita dakatar da zirga-zirgar jiragensu zuwa yankunan Falasdinawa da Isra’ila ta mamaye, a daidai lokacin da kasar Yemen ta sha alwashin daukar mataki kan kasar. Kamfanin jirgin sama na Air France ya sanar cewa, bayan dakatarwar da aka yi na tsawon watanni, zai ci gaba da dage zirga-zirgar jiragensa zuwa yankunan Falasdinu da aka mamaye har zuwa ranar 24 ga watan Mayu. Da farko Air France ya yi niyyar dawo da zirga-zirgar jirage a wannan makon, amma ya zabi karin jinkirta hakan. Kamfanin Lufthansa da SWISS, Austrian Airlines, Brussels Airlines da Eurowings, su ma sun tsawaita dakatar da zirga-zirgar jiragensu zuwa yankunan da aka mamaye. “Saboda halin da ake...
    Ministan Harkokin wajen kasar Omman ya bada sanarwan cew za’a gudanar da tattaunawa zagaye na 5 tsakanin Iran da Amurka kan shirin Iran na makamshin nukliya a ranar 23 gawatan Mayun da muke ciki a birnin Roma nakasar Italiay. Tashar talabijin ta Presstv a nnan Tehran ta ce Har yanzun ba’a ji tabakin kasashen biyu ba bayan wannan sanarwan. Sai dai kafin haka Iran tace tana tunanin dakatar da halattan taron saboda yadda jami’an gwamnatin kasar Amurka suka bayyana cewa duk wata yarjeniya da Iran sai ta hada da hana ta tace Uranium. Amma iran ta dage kan cewa ba zata bar hakkinta wanda yarjeniyar NPT ta bata ba na tashe Uranium karkashin kula na hukumar IAEA ba.
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da fitar da kudi sama da naira miliyan 279 ga  Ƙungiyar Direbobin Motocin Haya ta Najeriya (NURTW reshen jihar Jigawa karkashin shirinta na tallafawa masu sana’o’i. Kwamishinan Muhalli, Sabunta Makamashi da Sauyin Yanayi na jihar, Dr. Nura Ibrahim ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai bayan taron majalisar zartarwa da Gwamna Umar Namadi ya jagoranta a gidan gwamnati dake Dutse. Ya bayyana cewa za a yi amfani da kudaden ne wajen siyan motoci Sharon guda goma sha shida da kuma motoci Golf Volkswagen guda ashirin domin raba wa mambobin ƙungiyar guda talatin da shida a matsayin tallafin dogaro da kai. Ya ƙara da cewa, majalisar ta kuma yanke shawarar fitar da...
    Wani harin kwanton bauna da rundunar sojin al-Qassam suka kai kan sojojin mamayar Isra’ila a Beit Lahiya ya yi sanadiyar halaka tare da jikkatan sojojin mamaya masu yawa Rundunar Izzuddeen al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, ta sanar da cewa: Mayakanta sun kai wani kazamin harin kwantan bauna a yankin al-Atatra da ke yammacin Beit Lahiya a arewacin zirin Gaza, inda suka yi nasarar ritsawa da sojojin mamaya masu yawa da suka yi sanadaiyyar halakar wasu daga cikinsu bayan jikkata wasu da dama. Rundunar ta Al-Qassam ta ce: Mayakanta sun kai hari kan motocin sojin mamayar Isra’ila uku da bama-baman Shawaz guda biyu da kuma makami mai linzami, sannan kuma suka yi arangama da wata rundunar mamayar Isra’ila....
    Gwamnatin kasar Masar na shirin yin arangama ta soji da haramtacciyar kasar Isra’ila Kafofin yada labaran Isra’ila, musamman tashar talabijin ta 14, sun watsa wani rahoto cewa: Gwamnatin kasar Masar na kokarin karfafa karfinta na soji a tsibirin Sinai, tana mai gargadin abin da ta bayyana a matsayin “yiwuwar rugujewar yarjejeniyar zaman lafiya” da aka rattaba hannu tsakanin kasashen biyu a shekara ta 1979. Tashar talabijin ta NAN ta nakalto Eliyahu Dekel, tsohon shugaban hukumar leken asirin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila kuma masani kan al’amuran Masar na cewa: Masar na cikin gaggawar shirin tunkarar rikicin soji, yana mai cewa “yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla tsakanin kasashen biyu a shekarar 1979 ta kasance cikin yanayi na rugujewa tun lokacin da...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, tattaunawar dake tsakanin Iran da Amurka za ta iya taka rawar gani wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. A yayin da yake zantawa da manema labarai a gefen dandalin tattaunawa na Tehran, Araghchi ya ce kasashen yankin suna goyon bayan tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Amurka. ” Zaman lafiya da kwanciyar hankali su ne batutuwa mafi muhimmanci ga dukkan kasashen yankin,” in ji shi. Ya nanata matsayar Iran kan turbar diflomasiyya da kuma muhimmancin da take baiwa manufofin kyakkyawar makobtaka ta hanyar tattaunawa. A wani bangare na jawabin nasa, ministan harkokin wajen na Iran ya ce dandalin tattaunawa na Tehran karo na shida ya samu...
    Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Na’im Kasim a wani jawabinda da ya gabatar don tunawa da cika shekara guda da shahadar shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi da abokan tafiyarsa, ya bayyana cewa shugaban ya kasance mai  kaunar falasdinawa ne har cikin zuciyarsa. Sheikh Qasim ya kara da cewa, shugaba Ra’isi ya rike makamai da dama a rayuwarsa a JMI amma wannan bai canza  shi ba, ya kasance yana tambaya ta dangane da gwagwarmaya da HKI a yankin Hizbullah da kuma sauran mujahidai a yankin. A lokacin shugabancinsa ya taimakawa kungiyar Hizbullah, sosai kamar yanda wadanda suka gabaceshi suka yi. A ranar 20 ga watan Mayun shekarar da ta gabata ce. Sayyid Ibrahim Ra’isi shugaban kasar Iran yayi...
    Iran ta yi kira da a kawo karshen neman shafe wata al’umma daga kan doron kasa tare da kawo karshen rashin hukunta shugabannin ‘yan sahayoniyya Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan hare-hare da laifukan da gwamnatin ‘yan sahayoniyya take ci gaba da yi a cikin ‘yan kwanakin nan a zirin Gaza, yana mai kira da a kawo karshen kisan kiyashi da rashin hukunta shugabannin gwamnatin ‘yan shayoniyya da kuma gurfanar da su a gaban kuliya don hukunta su. Baqa’i ya yi ishara da laifuffukan da ba a taba ganin irinsa ba da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta yi kan al’ummar Falastinu da ba su da kariya a Gaza da Yammacin Gabar Kogin Jordan, ya...
    An gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga al’ummar Falasdinu a sassa daban-daban na duniya, a yayin zagayowar cika shekaru 77 da ranar ‘’Nakba’’ cewa da masifa. A Faransa da Ingila duk an gudanar da wannan zanga zanga a wasu sassan kasar. A cikin jerin gwanon, an daga allunan da ke dauke da sakonni irin su “Falasdinu za ta rayu!” » ko “Dakatar da kisan kiyashi a Gaza”. “Nakba ba wani lamari ne da ya faru a baya ba, yana ci gaba da faruwa ta hanyar korar jama’a, da amfani da bama-bamai,” kan al’ummar Gaza. Masu zanga-zangar sun yi Allah wadai da tabarbarewar al’amuran jin kai a zirin Gaza tun bayan barkewar yakin kisan kiyashi da Isra’ila ta kaddamar a...
    A kokarin da yake yi na jigilar maniyyatan aikin hajjin bana, Kamfanin jiragen sama na Max Air yace zai kwashe daukacin Alhazan Jihar Jigawa cikin kwanaki biyu.   Mataimakin mai kula da ofishin kamfanin dake jihar kano, Mr Barnabas Anderson ya bayyana haka a lokacin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a shelkwatar hukumar Jin dadin alhazan jihar Jigawa dake Dutse babban birnin jihar. A cewarsa, ana sa fara jigilar maniyatan jihar  zuwa kasar Saudi Arabia a ranar 20 da kuma 21 ga watan Mayun 2025.   Ya ce jirgin Max air zai yi sawun farko da maniyata su 550 zuwa kasa mai tsarki a ranar 20 ga watan Mayu.   Mr Anderson yace a ranar 21...
    Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Amurka tana da hannu dumu-dumu a muggan ayyukan da gwamnatin ‘yan shayoniyya suka aikata nakisan kare dangi a Gaza Jakada kuma wakilin dindindin na Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani ya yi nuni da ire-iren laifuffukan da gwamnatin ‘yan sahayoniyya suke ci gaba da aikatawa kan al’ummar Falastinu, yana mai bayyana wadannan laifuka a matsayin wani misali karara na kisan kiyashi yana kuma daukar Amurka a matsayin babbar kawa a aikata wadannan muggan laifuka. A yayin zama na musamman a Majalisar Dinkin Duniya a yammacin jiya Alhamis kan batun boren Falasdinawa “Ankaba” na musamman ya bayyana cewa: Gwamnatin yahudawan sahayoniyya tana so da cikakken goyon baya...
    A jiya Laraba ne dai da aka rattaba hannu akan wata yarjejeniya a tsakanin sarkin Katar Tamim Bin Hamad ali-Thani da kuma shugaban kasar Amurka Donad Trump wanda ya kai Ziyara kasar. Shugaban kasar Amurka wanda ya bayar da labarin kulla wannan yarjejeniya ya kusa sanar da cewa, kasar ta Katar za ta sayi jiragen sama marasa matuki samfurin Mq-9 daga Amurka. Gabanin isarsa kasar ta Katar, shugaban kasar ta Amurka ya fara yada zango ne a kasar Saudiyya inda ya sami kyakkyawar tarba daga mahukuntanta, tare da kuma da kulla yarjejeniyar kasuwanci ta billiyoyin daloli. Saudiyyar ta yi alkawalin zuba hannun hajri a can Amurka da kudaden da su ka kai dala biliyan 500 zuwa biliyan 600. Haka nan...
    Ɗan wasan Manchester United, Leny Yoro da Matthijs de Ligt da kuma Ayden Heaven ba suyi atisaye ba, bayan da ƙungiyar ke shirin buga wasan karshe a Europa League da Tottenham a makon gobe. Ranar Juma’a United za ta je Stamford Bridge domin karawa da Chelsea a Premier, amma dai hankalinta yana wasan da za ta kara ranar Laraba a birnin Bilbao. Yoro ya ji rauni ranar Lahadi a wasan da West Ham ta doke United 2-0, shi kuwa De Light a wasan Brentford ya ji rauni. Shi kuwa Heaven ya yi atisaye shi kaɗai, sai dai Jonny Evans da Toby Collyer sun yi atisaye tare da ƴan wasan United. Diogo Dalot ya motsa jiki shi kaɗai, wanda ke fatan...
    Gwamnatin jihar Kwara ta shirya wani gagarumin horo ga likitocin kiwon lafiya a fadin cibiyoyin kiwon lafiya na jihar kan yadda za a shawo kan cutar zazzabin cizon sauro.   Da yake sanar da bude horon a Ilorin, daraktan kula da lafiyar jama’a na jihar, Dokta Oluwatosin Fakayode, ya jadadda bukatar gaggawar gano cutar da wuri da kuma gaggauta magance cutar zazzabin cizon sauro, musamman a cikin mutane masu rauni kamar yara ‘yan kasa da shekaru biyar da mata masu juna biyu.   A cewarsa shirin ya kasance wani bangare na faffadan kokarin yaki da cutar zazzabin cizon sauro a jihar, gami da shirye-shiryen yakin rigakafin cutar zazzabin cizon sauro na 2025 (SMC).   Dokta Fakayode ya bayyana cewa horon...
    Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Iran ba zata taba yin watsi da haƙƙinta na makamashin nukuliya na zaman lafiya ba a kowane yanayi Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Iran da gaske take yi wajen gudanar da tattaunawa domin neman cimma matsaya da zata gamsar da kowane bangare, amma neman yin watsi da cibiyoyin nukiliyarta ba abu ne da za a amince da shi ba. A yammacin jiya Lahadi ne jami’an gwamnatin kasar Iran suka gudanar da wani taro karkashin jagorancin shugaban kasar Masoud Pezeshkian, inda ya jaddada aniyar gwamnatin kasar na kare nasarorin da Iran ta a fagen ayyukanta na zaman lafiya, yana mai jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta taba neman mallakar makamin...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Tattaunawar Iran da Amurka ba zata shafi matakin jan layi da Iran ta gindaya ba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa da gaske kasarsa tana tattaunawa da Amurka, kuma tana neman cimma matsaya, amma batun neman yin watsi da cibiyoyin nukiliyarta wani zabi ne da ba za a taba amincewa da shi ba. A cikin rashin tabbas da ke tattare da ci gaba da aiwatar da tattaunawa tsakanin Iran da Amurka, biyo bayan cin karo da maganganun da jami’an fadar mulkin Amurka ta White House suka yi, da kuma karuwar bukatar Amurka kan Iran; Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kawo karshen matsin lambar da ake yi mata; Yayin da shugaban Iran Masoud...
    Kasar Siriya ta rikide daga Jihadi da zaluncin gwamnatin mamayar Isra’ila zuwa ga kulla kyakkyawar alaka da gwamnatin ‘yan mamaya Gaskiya ta fara bayyana daya bayan daya, sannan makirci da makarkashiyar kungiyoyin masu dauke da makamai bisa da’awar gudanar da jihadi a Siriya suka fara bayyana ga al’umma, masu da’awar jihadi sun kama hanyar fitar da Siriya daga cikin sahun masu fada da makirce-makircen yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya ta hanyar kulla kyakkyawar alaka da su, da janyewa daga duk hakkokin kasar Siriya da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta mamaye na Siriya a baya-bayan nan. Manufar samar da sabuwar gwamnatin masu da’awar jihadi, kamar yadda aka sani, ita ce tabbatar da tsaron babban sansanin Amurka mafi girma a yanking abas ta tsakiya,...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa tattaunawa ba kai tsaye ba tsakanin JMI da Amurka zagaye na hudu, yana tafiya kamar yadda ya dace. Kuma kasashen buyu sun kara fahintar ra’yin juna. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran da nakalto Aragchi yana fadar haka a wani hira da da ya gabatar bayan kammala zagaye na 4 na tattaunawar a jiya. Ministan y ace bangarorin biyu sun tattauna babututuwan da suke da zurfi a cikin matsalolin da kasashen biyu suke son su warware, na farko gamsar da Amurka kan cewa shirin makamashin Nukliya na kasar Iran ban a tsaro bane. Da kuma maganar daukewa Iran takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata. Yace tattaunawar jiya   yafi...
    Kungiyar Magajunan Gari Na Kasashen Asiya Ta Zabi Birnin Esfahan na tsakiyar kasar Iran a matsayin cibiyar yawan bude ido na wannan shekara ta 2025. Manufar zaben birnin Esfahan a wannan karon shi ne gabatar da shi ga kasashen Asiya saboda sa mutanen Nahiyar Asiya su su ziyarci kasar da kuma birnin don sanin dumbin wuraren tarihin da suke cikin birnin da kuma kewayensa. Labarin ya bayyana cewa birnin Esfahan ayana daga cikin birane mafi tsufa a kasar , sannan yana dauke da wuraren kallo da kuma bude ido a cikin birnin Har’ila yau labarin ya kammala da cewa ana da kayakin tarihi kimani 200,000 a cikin birnin, sannan wasu 1940 na kayakin tarihin kasar, hukumar UNESCO ta zama wurare...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bukaci shugaban kasar Ukraine ya amince da tayin shugaban Putin na Rasah na sun hadu a birnin Istambul na kasar Turkiya don tattauna yiyuwar  tsagaita budewa juna wuta. Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya nakalto shugaban Trump yana fadar haka a jiya Asabar ya kuma bayyana cewa wannan wata dama ce kawo karshen zubar da jinni tsakanin kasashen biyu na fiye da shekaru uku da suka gabata. Trump ya bayyana haka ne a shafinsa na yanar gizo, ya kuma kara da cewa, haduwar shuwagabannin biyu zai fayyace matsayin yakin, da kuma yiyuwar dakatar da shi nan kusa. Banda haka haduwarsu zai bawa kasar Amurka damar gane matakin da zata dauka nan gaba,...
    Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ba da shawarar yin  tattaunawa “kai tsaye” ba tare da sharadi ba” tsakanin kasarsa da Ukraine a ranar 15 ga Mayu a Istanbul. A martanin da ya mayar, shugaban na Ukraine ya ce a shirye ya ke don tattaunawa kai tsaye, amma ya zama dole a tsagaita bude wuta a gabanin haka, yana mai nuni da shawarar da kawayensa na yammacin duniya suka bayar na tsagaita bude wuta na kwanaki 30 ba tare da sharadi ba daga ranar Litinin. Ba tare da yin tsokaci a kai tsaye kan shawarar kasahen ba, shugaban na Rasha ya caccaki turawan da ya ce sun yi wa Rasha “rashin ladabi da kakkausan lafazi” ya kuma ce ya kamata...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Dole ne duniya ta dauki matakin kalubalantar laifukan ‘yan sahayoniyya da magoya bayansu kan zaluncin Gaza Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, yayin da yake karbar bakwancin dimbin ma’aikata a yau Asabar, a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan “Makon ayyuyka da Ma’aikata” ya bayyana cewa: A yau duniya ta shaida yadda ake daukar manufofin son zuciya kan wasu kasashe. Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa daga cikin wadannan manufofi na son zuciya da ake aiwatarwa a yau akwai kokarin mantar da al’umma batun da suka shafi Falasdinawa, yana mai cewa: Kada al’ummar musulmi su kuskura wannan kyale hakan ya faru, domin ko dan...
    A jiya Alhamis ne dai majami’ar Roman Katolika ta sanar da zabar Robert  Farncis wanda ya zabi sunan Leo 14,a matsayin shugabanta. Zabar Robert Francis a matsayin Paparoma na 267 ya zo ne bayan kwanabi 2  da manyan malaman addinin majami’ar Roman katolika su ka dauka suna yin zaben.  A bisa al’adar majalisar, farin hayaki yana fitowa daga saman majami’ar da yake nuni da cewa an zabi sabon Paparoman, da hakan ya sa a ka rika kada karaurawa a cikin maja’mi’un birnin Roma. Sabon Paparoman  dan shekaru 69 ya zabarwa kansa sunan  Leo 14 domin sake dawo da aiki da kyawawan halaye a cikin harkokin tafiyar da majami’ar kamar yadda Leo na farko ya yi a 1878 zuwa 1903.
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Ana nazarin lokacin gudanar da zagaye na huɗu na shawarwari tsakanin Iran da Amurka Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya sanar da cewa: Ana nazari kan lokacin gudanar da zagaye na gaba na tattaunawar Iran da Amurka wand aba na kai tsaye ba, kuma mai shiga tsakani na Oman zai sanar da karin bayani da zarar an tantance lokaci da wurin da za a yi. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya shaidawa kamfanin dillancin labaran kasar Iran cewa: Ana duban lokacin da za’a gudanar da zagaye na gaba na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka. Baqa’i ya kara da cewa: Mai shiga tsakani na Oman zai sanar da bayanai...
    Mamba a majalisar gudanarwa ta kungiyar Ansarulla ta kasar yemen Muhammad Bukhaiti ya bayyana cewa hare-haren da HKI da Amurka suka kai fararen hula a kasar yemen wuce jan layi, ko ketare haddi ne na kungiyar don haka su jira maida martani mai tsanani. Kamfanin dillancin labaran Iran ya nakalti yana fadawa tsahar talabijin ta Al-mayadeen ta kasar Lenamon a yau Talata.  Ya kuma kara da cewa hare-haren da Amurka suke kaiwa ma’aikatu da wuraren fararen hula a kasar Yemen na baya-bayan nan duk sun nuna cewa an sami nasara a kansu. Albukhaiti ya kara da cewa sadaukarwa da mutanen kasar Yemen suke yi saboda Gaza, ba zai tsaya ba, sannan muna son fadawa kasashen Amurka da ingila da kuma...
    Hukumar Kula da Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna za ta fara jigilar maniyyata zuwa kasar Saudiyya a ranar 14 ga watan Mayu, 2025. Shugaban hukumar, Malam Salihu S. Abubakar, ne ya bayyana hakan a wani shirin rediyo kai tsaye da aka watsa daga Kaduna, inda ya bayyana shirye-shiryen da jihar ta kammala domin aikin Hajjin bana. Ya bayyana cewa maniyyata 4,060 daga jihar Kaduna za su sauke farali a bana, kuma kamfanin jirgin sama na UMZA ne zai yi jigilarsu. Shugaban hukumar ya bayyana cewa domin kammala matakan da ake bi kafin tafiya, za a yi duk maniyya cikakken gwajin lafiya a sansanin alhazai da ke Mando. Wata mata ta auri maza biyu a lokaci guda a Kano NAJERIYA...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da zaluncin ‘yan sahayoniyya a kan kasar Yemen Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan harin wuce gona da iri da sojojin yahudawan sahayoniyya suka kai tashar jiragen ruwa na Hodeidah da sauran ababen more rayuwa na kasar Yemen, yana mai bayyana hakan a matsayin babban laifi da kuma keta ka’idoji da dokokin kasa da kasa. A cikin bayaninsa da sanyin safiyar yau Talata, Baqa’i ya yi nuni da cewa: Hare-haren da ‘yan sahayoniyya suka kai kan tashar jiragen ruwa, da masana’antu, da kuma wuraren zama a kasar Yemen, ana aiwatar da su ne tare da goyon baya da kuma taimakon Amurka. Ya bayyana wadannan hare-haren...
    Kotu ta yanke wa wani matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan kan laifin kashe wata karuwa bayan ya yi lalata da ita. Babban Kotun Jihar Ekiti ce ta yanke masa hukuncin bayan an gurfanar da shi kan zargin haɗa baki da kuma garkuwa da matar da kuma amfani da maganin kashe ciyawa wajen halaka ta a ranar 18 ga Afrilun 2024. Tun da farko mai gabatar da ƙara, Ibironke Odetola, ya bayyana wa kotun a ranar 6 ga watan Fabrairu, cewa wanda ake zargin ya haɗa baki d da wani abokinsa wajen sace matar da ke sana’ar kasuwanci. Wanda ake zargin, David Isaiah, mai shekara 26, ya shaida wa kotun cewa bayan ya yi lalata da matar ne ya...
    Sojojin Yemen sun sanar da killace sararin samaniyar Falasdinawa da yahudawan sahayoniyya suka mamaye Sojojin Yemen sun sanar a yammacin jiya Lahadi cewa: Za su kakaba wa haramtacciyar kasar Isra’ila cikakken takunkumi ta sama, yayin da kamfanonin jiragen sama na kasa da kasa suka yi gargadin hadarin da ke tattare da zirga-zirga daga filayen jiragen saman yankunan Falasdinawa da aka mamaye. Wannan dai na zuwa ne a matsayin martani ga karuwar hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai wa a zirin Gaza. Kakakin rundunar sojin Yemen, Birgediya Janar Yahya Sari’e, ya ce za su kakaba takunkumin ne ta hanyar kai hare-hare akai-akai kan filayen jiragen saman haramtacciyar kasar Isra’ila, musamman filin jirgin sama na Ben Gurion. Sanarwar ta yi...
    An rantsar da mista Brice Nguema a matsayin shugaban kasar Gabon, a birnin Libreville fadar mulkin kasar Shugabannin kasashen Senegal, da Equatorial Guinea, da Rwanda, da dai sauransu na dag cikin bakin da suka halarci bikin. An ce, bikin rantuwar kama aiki na wannan karo shi ne irinsa na farko a kasar Gabon mai bude kofa ga jama’ar kasar, don haka aka samu kimanin mutane 40,000 da suka je kallon bikin. Kafin hakan an rantsar da Brice Nguema bayan ya lashe babban zaben kasar da ya gudana a shekarar nan ta 2025, inda ya yi nasarar lashe kaso 94.85% na jimillar kuri’un da aka kada.
    Shugaban karamar hukumar Babura ta jihar Jigawa, Malam Hamisu Muhammad Garu, ya kaddamar da shirin karfafa aikin gona da nufin sanya matasa aikin noman shinkafa a wani bangare na kokarin inganta ayyukan yi da samar da abinci a yankin.   Da yake jawabi yayin bikin kaddamar da aikin aka gudanar a garin Babura, shugaban ya bayyana cewa, Gwamna Malam Umar Namadi ne ya bullo da shirin a matsayin wani muhimmin mataki na samar da guraben ayyukan yi ga matasa, da habaka tattalin arzikin kananan hukumomi, da karfafa samar da abinci a fadin jihar.   A cewarsa, gwamnatin jihar ta samar da muhimman kayayyakin amfanin gona da suka hada da takin zamani, magungunan kashe kwari, irin shinkafa mai yawan gaske, da...
    Kasar Yemen ta haramta fitar da man da Amurka ke fitarwa a matsayin mayar da martani ga wuce gona da irin sojojin Amurka kan kasarta Cibiyar kula da ayyukan jin kai da ke birnin Sana’a na kasar Yemen ta sanar da dakatar da fitar da mai da Amurka ke fitarwa daga ranar 17 ga watan Mayu, a matsayin martani ga hare-haren da Amurka ke kaiwa kasar Yemen. Cibiyar daidaita ayyukan jin kai da ke birnin Sana’a ta sanar a safiyar ranar Asabar, matakin hana fitar da danyen mai da Amurka ke yi daga cibiyoyin man fetur na kasar, wanda zai fara aiki daga ranar 17 ga watan Mayun wannan shekara ta 2025. Wannan shawarar dai ta zo ne a matsayin...
    Layukan dogo na kasar Sin sun gudanar da sufurin kusan fasinjoji miliyan 23.12 a jiya Alhamis, ranar farko ta bikin ranar ‘yan kwadago ta duniya da aka saba yi duk shekara a watan Mayu, kamar yadda kamfanin sufurin layin dogo na kasar Sin ya bayyana.   A cewar alkaluman da kamfanin ya fitar a yau Jumma’a, wannan adadi ya nuna karuwar kashi 11.7 cikin dari na adadin da ake samu a mizanin shekara-shekara. (Abdulrazaq Yahuza Jere)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin jihar Zamfara ta kammala biyan sama da naira biliyan 13 na garatuti, wanda ke nuna wani gagarumin mataki na inganta jin dadin ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya a jihar.   Mataimakin gwamnan jihar, Mani Malam Mummuni, ya bayyana hakan a yayin bikin ranar ma’aikata na shekarar 2025 da aka gudanar a Gusau, babban birnin jihar.   A cewar Mummuni, gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ta jajirce wajen ganin ta magance kalubalen da ma’aikata da masu ritaya ke fuskanta a jihar.   Ya bayyana cewa, gwamnatin jihar tana sane da korafin ma’aikatan da aka yi kuskuren cire su daga lissafin albashin sakamakon aikin tantance ma’aikatan da aka kammala.   “Gwamnati ta riga ta kafa wani kwamiti a karkashin jagorancin shugaban...
    Binciken LEADERSHIP ya nuna cewa, duba mara lafiya guda daya tak da ke dauke da cutar Maleriyar da ba ta yi karfi sosai ba a asibitin gwamnati, na lashe kimanin Naira 17,000, tsakanin ganin likita, yin gwaje-gwaje da kuma magunguna.   Wadannan kudade sun kai kimanin Naira tiriliyan 1.156 da ake kashewa a kan wannan cuta, amma asalin kudaden sun zarta haka, musamman idan Maleriyar ta yi kamari, za a iya kashe ninki uku ko sama da haka na wannan kudi.   Yayin da duniya ke yin wannan biki na ranar Maleriya, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta nanata cewa, cutar na ci gaba da zama barazana, musamman a yankuna masu fama da zafi, duk da cewa; cuta ce da...
    Ministan Tsaron kasar Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta zama babbar alamar ta’addanci a duniya Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh, yayin da yake yin Allah wadai da kisan gillar da yahudawan sahayoniyya suke yi wa al’ummomin Falastinu da na Lebanon a daidai lokacin da kungiyoyin kasa da kasa da tarurrukan kasa da kasa suka yi shiru, yana mai cewa: A yau al’ummar yahudawan sahayoniyya ta zama wata babbar alama ta ta’addancin kasa a duniya. Birgediya Janar Nasirzadeh ya furta haka ne a ganawarsa da ministan tsaron Jamhuriyar Zimbabwe Uba Muchinguri Kashiri a lokacin ziyararsa a kasar Iran, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi kasashen biyu. A cikin wannan ganawar, ministan tsaron na Iran ya...
    Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi Allah wadai da matsayin Amurka na goyon bayan haramta hukumar kula da ‘yan gudun hijira falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi Allah wadai da matsayin Amurka na goyon bayan haramtacciyar kasar Isra’ila kan haramta hukumar kula da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa da ayyukan ba da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya “UNRWA”, tana daukan wanan a matsayin Amurkia na ci gaba da nuna son kai da goyon bayan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ‘yar mamaya da kuma rashin mutunta dokokin kasa da kasa da yarjejeniyar jin kai. A cikin wata sanarwar manema labarai da ta fitar jiya Alhamis, kungiyar Hamas ta yi nuni da cewa: Shigar da Amurka...
    Ana sa alamar tambayar cewa: Shin gobarar da ta tashi a birnin Kudus… shin sako ne na ranar tunawa da kafuwar gwamnatin ‘yan sahayoniyya? Gobarar da ta tashi a tsaunin Kudus da aka mamaye ta bazu zuwa manyan yankuna a cikin haramtacciyar kasar Isra’ila, inda ta kewaye wani sansanin soji tare da cinye filayen masu girma da tsayi. Hakan ya sa hukumomin gwamnatin mamayar Isra’ila suka kafa dokar ta baci tare da neman taimakon kasashen duniya. Yayin da Ministan tsaron cikin gidan Isra’ila Itamar Ben-Gvir yake neman dora wa Falasdinawa, alhakin tashin gobarar. Gobarar ta kunno kai ne a daidai lokacin da yahudawan sahayoniyya suka fara gudanar da bukukuwan cika shekaru 77 da kafuwar gwamnatinsu ta mamaya a kasar Falasdinawa,...
    Babu tabbacin ko ya rasu sakamakon rashin lafiya ko kuwa an kashe shi. An ce ‘yan bindigar sun fara neman Naira miliyan 20 a matsayin kudin fansa, amma iyalansa sun iya haɗa Naira miliyan 11 ne kacal. Sun kuma buƙaci sabon babur da kayan abinci, duk a matsayin kuɗin fansa. Bayan da matar da ta tsere ta shaida wa jama’a abin da ya faru a ranar Litinin, sai aka yi masa sallar jana’iza a ranar Talata kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Rundunar ‘yansandan Jihar Zamfara, ta bakin kakakinta DSP Yazid Abubakar, ta ce har yanzu ba ta samu labarin tabbacin mutuwar limamin da iyalansa daga hukumomi ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce za a yi taro karo na hudu na shawarwari tsakanin Tehran da Washington kan shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a birnin Rome na kasar Italiya a ranar Asabar mai zuwa. M. Araghchi ya fadawa manema labarai a gefen taron majalisar ministocin gwamnatin kasar na mako-mako yau Laraba cewa, inda ya ce taron na Rome zai kasance gabanin wani taro a ranar Juma’a na tsakanin Tehran da kasashen Turan nan uku da ake wa lakabi da E3 wato – Ingila, Faransa da kuma Jamus wadanda suka sanya hannu kan yarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015. Ya ce rawar da kasashen Turai uku ke takawa ta ragu sakamakon manufofinsu a tattaunawar da aka dade...
    A wani taro wanda ya hada ministan riko na tattalin arziki da kudade na JMI da kuma mai bawa firai ministan kasar Iraki shawara, bangarorin biyu sun tabbatar da cewa an kammala aikin shimfida layin dogo tsakanin garin Shalamcheh na kasar Iran da kuma birnin Basra a kasar Iraki. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jami’an gwamnatocin kasashen biyu na fadar haka, sun kuma jaddada muhimmancin layin dogon da kuma samar da kasuwar babu kudaden fito a kan iyakokin kasashen biyu. Labarin ya kara da cewa harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu ya zuwa yanzu ya kai dalar Amurka biliyon $11a ko wace shekara kuma anan saran nan gaba zai iyakaruwa zuwa dalar Amurka biliyon $25. Rahmatollah Akrami,...
    Wata tsohuwa mai shekara 80 a kasar Turkiyya za ta shafe sama da shekara 4 a gidan yari, saboda ta daki jikarta ’yar shekara 18 da silifa a lokacin da suke takaddama. Asiye Kaytan na zaune tare da jikarta Vural a unguwar Topraklık da ke Denizli a Kudu maso Yammacin Turkiyya. Tuntuni dai iyayen yarinyar suka rabu, inda tsohuwar mai shekara 80 take kulawa da ita fiye da kanta. A ranar 9 ga Agustan bara, bayan Vural ta dawo daga aiki, ta fada wa kakarta cewa, za ta fita waje tare da wasu abokanta. Tsohuwar ta ji tsoron fitar don kare lafiyarta, ta ce ba za ta yarda ba, har ma ta kulle kofa don tabbatar da cewa Vural ba...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ya bayyana kalaman gwamnatin ‘yan sahayoniyya a matsayin wani rudu da ba shi da amfani da har zai yi tasiri a zaman tattaunawan Iran da Amurka Wanda ba na kai tsaye ba, yana mai cewa duk wani hari ko da karami ne za a kai kan Iran zai zama tamkar tartsatsin wuta da zai iya janyo tashin gobara da zai iya kona yankin gaba daya. A jawabin da ya gabatar yayin taron kolin majalisar shawarar Musulunci ta Iran a yau Talata, Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Firai ministan gwamnatin yahudawan sahayoniyya mai laifi ne mai zubar da jinin fararen hula, saboda neman hana mutuwarsa a fagen siyasa, kuma yanzu yana yin barazana ga al’ummar Iran...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Ci gaba da killace Gaza da kuma kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, laifi ne da ba a taba yin irinsa ba a tarihin dan Adam A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Masar Badar Abdel Ati a yammacin jiya Lahadin da ta gabata, Araqchi ya bayyana ci gaba da killace yankin Gaza da rashin abinci da magunguna, tare da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, a matsayin wani laifi da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin dan Adam. Ya dauki Amurka da sauran masu goyon bayan ‘yan sahayoniyya a matsayin masu hannu a kisan kiyashi da laifukan yaki...
    Fadar Kremlin ta kasar Rasha ta ayyana tsagaita wuta na kwana biyu ita kaɗai a yakinta da kasar Ukraine. Shugaba Vladimir Putin ya sanar a ranar Litinin cewa Rasha za ta aiwatar da tsagaita wutar ne daga tsakar dare na 8 ga Mayu zuwa tsakar dare na 10 ga Mayu. A ranakun da za a tsagaita wutar ne Rasha ke bikin karshen da yakinta da kasar Jamus a shekarun 1941 zuwa 1945, wanda aka fi sani da Yakin Duniya na Biyu a yawancin duniya. A Rasha ana kiran yakin na Duniya na biyu da sunan Babban Yaƙin Ceton Kasa. Shekara 10 ina sayar da sassan jikin ɗan Adam — Wanda ake zargi Dukan farar hula saboda sanya kayan sojoji laifi...
    A cewarsa, tuni aka shirya wuraren kwana da abinci ga maniyyatan a kasar Saudiyya.   Abdulkadir ya tabbatar da cewa, ana shirye-shirye, inda za a yi alluran rigakafi a ranar 28 ga Afrilu, za a raba tufafi a 30 ga Afrilu, sannan kuma za a raba jakunkuna a ranar 1 ga Mayu.   Ya kara da cewa maniyyatan da suka biya sama da Naira miliyan 8.4 na kudin aikin Hajji, za a biya su bayan sun dawo daga Saudiyya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
    Hakimin Kafin Hausa, Dan Amar na Hadejia, Alhaji Aliyu Usman Ginsau, ya yaba wa Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, bisa aiwatar da jerin manyan ayyuka a fadin jihar cikin shekaru biyu da suka gabata. Hakimin ya yi yabon ne yayin bikin kaddamar da wani littafi a garin Kafin Hausa. A jawabinsa yayin taron, Gwamna Umar Namadi ya yi jinjina ga marubucin littafin bisa rubuta cikakken tarihi da zai amfani al’umma, musamman matasa masu tasowa. Malam Umar Namadi ya kuma yi alkawarin umurtar ma’aikatar ilimi ta jihar da ta sayi kwafin littafin domin amfanin ɗalibai a makarantun gwamnati. Gwamna Umar Namadi ya kuma sayi kwafi bakwai na littafin a madadin iyalinsa kan kudi naira miliyan daya, yayin da...
    A dai-dai lokacinda kasashen Indiya da Pakisatn suke tada jijiyoyin wuta kan wani harin ta’addanci da ya kai ga mutuwar mutane 27 masu yawon shakatawa a yankin Kashmir na kasar Indiya, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya gabatar da tayin shiga tsakani don dai-daita tsakanin kasashen biy. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka, a shafinsa na X, ya kuma kara da cewa Iran tana da dangantaka mai karfi tsakaninta da kasashen biyu, kuma makobta ne kuma yan uwa wadanda suke da tsohuwar dangantaka ta al-adu a tsakaninsu na karnuka, ba za muyi kasa a guiwa wajen sasantasu ba, idan sun bamu wannan damar. A cikin makon da ya gabata ne wasu...
    Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah sayyid Ali Khamnei wanda ya gabatar da jawabi dangane da zagayowar ranar shahadar Imam Ja’afar Assadiq ( a.s) ya bayyana cewa: Tafarkin Imaman Ahlul-Bayti (a.s) ya kasance na gwgawarmaya da jajurcewa, kuma koyarwarsu ta ginu ne akan mandiki da kafa dalili. Jagoran juyin musuluncin na Iran ya ce; rayuwar Imam Ja’afar Assadiq           (  A. S ) ta ginu ne akan tafarkin koyar da ilimin addinin Allah, wacce ta kasace mai cike  da abin mamaki. Jagoran juyin musuluncin na Iran ya siffata mutanen Gaza da Lebanon da cewa suna tafiya ne akan wannan tafarki na Imaman shiriya.
    Sabuwar gwamnatin Siriya tana kara matsa lamba kan bangarorin ‘yan gwagwarmaya domin Isra’ila ta janye daga wasu yankunan kasarta Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da tura kayayyakin soji zuwa tsaunukan Dutsen Harmon, yayin da suke hanzarta gina abin da suka kira “Katangar tsaro.” Har ila yau, sun karfafa wuraren tsaro da suka kafa a cikin yankunan Siriya, a cikin abin da gwamnatin Isra’ila ta kira “yankin da ke da kariya,” wanda ya hada da mamaye wasu sassan garuruwan Quneitra da Dara’a. Majiyoyin cikin gida a garin Nawa da ke cikin karkarar Dara’a na cewa, mahukuntan kasar Siriya na ci gaba da daukan matakan matsin lamba, ta hanyar shugabannin kabilu da kwamandojin ma’aikatar tsaro a Dara’a, na tilastawa bangarorin da...
    A hukumance gwamnatin tarayya ta ayyana filin jirgin saman Bola Ahmed Tinubu dake Minna a matsayin mafita ga jiragen dake sauka Abuja.   Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ne ya bayyana hakan a yayin bikin kaddamar da jirgin saman na Overland Airways a filin jirgin sama na BAT dake Minna.   Festus Keyamo ya ce ana shirin daukar matakan da suka wajaba kamar su kwastam, shige da fice, ‘yan sanda, NDLEA da sauran su don sarrafa fasinjoji idan filin jirgin Abuja ya samu matsala.   Gwamnan jihar Neja Mohammed Umar Bago wanda ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa ci gaba da goyon bayan da yake baiwa jihar, ya bayyana cewa wannan nasara wani kokari ne na hadin...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jinjinawa kasashen Sin da Rasha a matsayin abokan hulda na kut-da-kut da kasar, yayin da ya isa birnin Beijing domin yin shawarwari da manyan jami’an kasar Sin, gabanin yin tattaunawa zagaye ta uku da Amurka kan shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Abbas Araghchi ya shaida wa kafar yada labaran Iran a babban birnin kasar Sin a ranar Laraba cewa, “Sin da Rasha abokan hulda ne na kut da kut da suka tsaya tare da mu a lokutan wahala, don yana da kyau da ma’ana mu ci gaba da tuntubar juna tare da su a bangarori daban-daban, musamman ma yanzu da ake tattaunawa da Amurka.” “Ya zama dole mu sanar da abokanmu a kasar...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: China da Rasha abokan hulda ne na tushe ga Iran bisa kyakkyawan tsari Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana kasashen China da Rasha a matsayin abokan huldar na tsari a kan tubalin manyan tsare-tsare ga Iran, kuma ya dace kasashen uku su ci gaba da tuntubar juna a fannoni daban daban. A yayin da ya isa birnin Beijing, yayin da yake amsa tambaya game da makasudin ziyararsa a kasar China a jajibirin shawarwarin da ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, Araqchi ya bayyana cewa: Kasashen China da Rasha abokan hulda ne na kut-da-kut da Iran. Sun kasance tare da Iran a lokutan wahala, kuma abu ne mai...
    Adadin Falasdinawa da suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da irin sojojin mamayar Isra’ila kan Gaza ya kai shahidai 51,266 Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da cewa: An isar da gawawwakin shahidai 26 da kuma wasu 60 da suka jikkata a asibitocin zirin Gaza cikin sa’o’i 24 da suka gabata. Ma’aikatar ta bayyana a cikin wata sanarwa a jiya Talata cewa adadin wadanda suka yi shahada da wadanda suka jikkata tun ranar 18 ga Maris, shekara ta 2025 ya kai shahidai 1,890 da kuma jikkata wasu 4,950 na daban. An tabbatar da cewa adadin wadanda suka yi shahada a sakamakon harin ta’addancin ‘yan sahayoniyya ya karu zuwa shahidai 51,266 da jikkatan wasu 116,991 tun daga ranar 7 ga...
    Sahun farko na Alhazan Najeriya zai tashi zuwa kasa mai tsarki a ranar 9 ga watan Mayun 2025. Hakan na kunshe ne a cikin bayanin bayan taro da Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON, ta yi da Shugabannin Hukomomin Kula da Jin Daɗin Alhazai na Jihohi a  ranar 22 ga watan Afrilun 2025. Manufar taron ita ce tantance matakin shirin da kowace Hukumar Alhazai ta Jiha ta kai. Wata sanarwa da mataimakiyar daraktar watsa labarai ta hukumar NAHCON, Fatima Sanda Usara ta fitar, ta ce shugaban hukumar, Farfesa Abdullah Saleh Usman, ya tunatar da mahalarta taron cewa harkar Hajji na cikin matakin karshe na shirye-shirye kafin fara aikin Hajjin shekarar 2025. Ya bukaci jihohi da su sanar da NAHCON matsayin da...
    A shekarar 2024, an kammala jigilar fasinjojin da yawansu ya kai biliyan 1.46 a filayen jiragen sama na kasar Sin yayin da yawan tashi da saukar jiragen sama ya wuce miliyan 12.4, adadin sun karu da kashi 15.9 bisa dari da kuma kashi 5.9 bisa dari, idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara. Hakan ya nuna cewa, duka alkaluma masu alaka da harkokin sufuri sun kafa tarihi.   Kazalika, a ranar 21 ga wata, kungiyar filayen jiragen sama masu daukar fasinja ta kasar Sin, da kwalejin nazarin kimiyya da fasahar jiragen sama masu daukar fasinja ta kasar Sin, da sauransu sun fitar da “Rahoton kimanta ingancin hidimar filin jirgin sama na shekarar 2024”, inda rahoton ya ce, akwai daidaito...
    Jamuhuriyar Musulunci ta Iran ta jaddada matsayinta kan batun tace sinadarin yuraniyo. Mai magana da yawun gwamnatin Iran Fatemeh Mohajerani ta bayyana cewa, Iran na kokarin yin shawarwari ne domin samar da amana da samar da gaskiya game da shirinta na nukiliya domin dage takunkumi kanta. A cikin taron manema labarai na mako-mako da ta gudanar a jiya litinin, Mohajerani ta mayar da martani ga wata tambaya game da tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Amurka, inda ta ce, shin bangarorin biyu sun cimma matsaya dangane da kasar da za a aike da hajojin uranium da Iran ta inganta? Shin Iran ta amince ta mika wadannan haja zuwa Rasha? Ta ce: Ina so in bayyana dangane da kashi na...
    Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa tace uranium din ta tamakar jan layi ne a tattaunawar dake wakana tsakaninta da Amurka. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar ne Kazem Gharibabadi ya bayyana hakan, inda ya ce hakkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ne inganta sinadarin Uranium, yana mai jaddada cewa, wannan batu a matsayin jan layi a tattaunawar da Amurka. Mista Gharibabadi ya bayyana haka ne a yayin taron kwamitin majalisar dokoki kan tsaron kasar da manufofin ketare, inda ya yi wa ‘yan majalisar bayani kan shawarwari zagaye na biyu tsakanin Tehran da Washington, wanda ya gudana a Rome, babban birnin kasar Italiya. Jami’in na iran ya kara da cewa tawagar kasar ta jaddada matsayinta na cewa Iran ba ta neman...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Tattaunawa da Amurka an yi ta ne cikin yanayi mai inganci da hangen nesa Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana tattaunawar da ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, wadda Oman ta shiga tsakani a birnin Roma na kasar Italiya, da cewa an gudanar da shi cikin yanayi mai ma’ana da hangen nesa. A cikin wata sanarwa bayan tattaunawar, Araqchi ya yi nazari kan yanayin tattaunawar, inda ya bayyana cewa: “Sun gudanar da shawarwari na tsawon sa’o’i hudu a ci gaba da zaman da aka yi a baya, kuma sun samu kyakkyawar fahimta kan ka’idoji da manufofi da dama.” Ya ci gaba da cewa: An amince da a ci...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Za a gudanar da zagaye na biyu na tattaunawar ba na kai tsaye ba da Amurka a birnin Roma a ranar Asabar Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya sanar da cewa zai tafi birnin Roma a ranar Asabar domin halartar zagaye na biyu na shawarwari ba na kai tsaye ba da Amurka, yana mai jaddada cewa sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya aikewa shugaban kasar Rasha ya kunshi muhimman batutuwa. A cewar kamfanin dillancin labaran IRNA, Araghchi ya ce: Roma ba ita ce mai masaukin baki ba, a’a, a maimakon haka, wajen da za a yi shawarwarin, gwamnatin Oman ce ta kasance mai daukar nauyin shawarwarin ba na...
    Sojojin mamayar Isra’ila sun sake aiwatar da wani sabon kisan kiyashi kan Falasdinawa 5 a sansanin Jabaliya da ke arewacin Gaza Fararen hula 5 da suka hada da yara biyu da mace daya ne suka yi shahada, wasu kuma suka bace sakamakon harin da rundunar sojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gida a sansanin ‘yan gudun hijira na Tal al-Za’atar da ke gabashin Jabaliya da ke arewacin Zirin Gaza. A cewar majiyoyin yankin, gidan da aka kai harin na dangin Nasiyo ne, kuma yana dauke da ‘yan gudun hijira daga iyalai sama da biyar a cikinsa, inda harin ya turbude su a karkashin baraguzan gine-gine.
    Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya yi kakkausar suka dangane da yawaitar kashe-kashen da ake yi a jihar Filato da sauran sassan Arewacin Nijeriya, inda ya dora laifin kitsa tashe-tashen hankula da nufin tada zaune tsaye a Nijeriya. A wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, Fani-Kayode ya yi ikirarin cewa wadanda ke haddasa tashe-tashen hankula ba wai kawai ’yan tada kayar baya ba ne, a’a, wasu ‘yan kasashen waje ne da ake zargin suna shigowa Nijeriya ta kan iyakokin kasar, da nufin raba kan al’ummar kasar ta hanyar addini da kabilanci. Fani-Kayode ya yi gargadin cewa, rikicin da ake fama da shi na da kamanceceniya da yadda aka kirkiri tashe-tashen hankula a zabukan shekarar...