2025-06-16@09:19:54 GMT
إجمالي نتائج البحث: 64
«Mista Parradang»:
Garkuwan sararin samnaiyar kasar Iran a lardin Zanjan ya bada labarin kakkabo jiragen yakin na HKI guda biyi wadanda ake sarrafasu daga nesa a sararin samaniyar. Kamfanin dillancin lbaran Tasnim na sojojin kasar Iran ya nakalto majiyar dakarunn juyin juya halin musulunci na kasar Iran tana fadar haka. Labarin ya kara da cewa rubuce rubucen da aka rubuta a jikin jiragen da aka tarwatsa sun bayyan cewa kirar kasar Amurka ce. Wannan yake tabbatar da irin hannun da Amurka take da shi a cikin yakin da Iran take fafatawa da HKI. A wani labarin kuma yansandar yanar gizo sun kama mutane biyu wadanda suke yada labaran karya dangane da yaki da kuma shuwagabannin kasar. Har’ila yau an kama wasu wadanda...
Wakilin dindindin na kasar Sin a hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ko IAEA Li Song, ya ce kasarsa na matukar Allah wadai da harin Isra’ila kan cibiyoyin sarrafa nukiliyar Iran da ake amfani da su domin ayyukan zaman lafiya. Li Song, ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a, yayin taron manyan jami’an majalisar gudanarwar hukumar ta IAEA, game da batun hare-haren da Isra’ila ta kaddamar kan cibiyoyin sarrafa nukiliyar Iran. Ya ce, har kullum Sin na mayar da hankali ga zakulo matakan wanzar da zaman lafiya, dangane da batun nukiliyar Iran ta hanyoyin siyasa da diflomasiyya, tana kuma adawa da kakaba takunkumai ba bisa ka’ida ba daga bangare guda. Har ila yau, Sin za ta ci gaba da...
Ciwon Olsa Ga mai fama da ciwon Olsa, sai ya nemi garin ‘ya’yan Gwanda cokalin shayi daya; ya zuba a kunu sau daya a rana, har tsawon kwana bakwai, za a rabu da ita da yardar Allah. Ruwan Maniyyi Ga masu fama da karancin ruwan maniyyi, sai ya nemi garin ‘ya’yan Gwanda da Madara ya hada ya rika sha, wannan hadi na matukar kara ruwan maniyyi. Ciwon Siga: Shan garin ‘ya’yan danyar Gwanda cokali daya a ruwan dumi, na sauke Siga cikin kankanin lokaci a jikin mutum da izinin Allah. Hana Daukar Ciki Ga masu son yin tsarin iyali, shan garin ‘ya’yan Gwanda cokalin shayi daya a ruwan dumi bayan yin jima’i, na hana ciki ya shiga. ...
Sai dai kuma shugaba Tinubu ya yi amfani da wannan damar wajen yi wa shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, da kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas ado da lambar yabo ta GCON, yayin da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin da mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Kalu, da lambar yabo ta CFR. Ga cikakken jerin sunayen sabbin mutane 67 da aka karrama da lambar yabon, kamar yadda fadar shugaban kasa ta fitar: Grand Commander of the Order of the Niger (GCON). Shehu Musa Yar’Adua Rt Hon Tajudeen Abbas Senator Godswill Akpabio Wole Soyinka Commander of the Order of the Niger (CON) Ghali Umar Na’Abba Salisu Buhari Umaru Dikko Uche Chukwumerije Bala Mohammed Gwagwarwa Aisha Yesufu Innocent Chukwuma...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karrama daya daga cikin masu kamfanin Microsoft, Bill Gates, da lambar girmamawa ta kasa — Commander of the Order of the Federal Republic (CFR), inda ya jaddada cewa Gates ya kasance abin koyi ga shugabanni a fadin duniya saboda yadda yake taimaka wa talakawa da masu bukata ta musamman. Shugaban ya kuma bayyana cewa Mista Gates, wanda shi ne Shugaban Gidauniyar Melinda da Gates, ya bada gudummawa a fannonin kiwon lafiyar mata, noma da bincike kan cututtuka masu yaduwa. Ya gode wa Bill Gates bisa gudummawar da yake bayarwa a duniya, musamman wajen saukaka rayuwa da kare lafiyar masu rauni da wadanda ke cikin bukata. Ministan Lafiya da Ci gaban Jama’a, Farfesa Ali Pate,...
A nasa jawabin, shugaban kwamitin shirya musabakar karatun alkurani na karamar hukumar Igabi, Malam Abubakar Sadik Muhammad (Abu Asim), ya ce duk irin nasarar da kwamitin ya samu, ya samu ne bisa goyon bayan da Honarabul Yusuf Ibrahim Zailani yake ba su. Ya ce shi ne kashin bayan samun nasarar da suka yi a fadin duniya. Ya bukaci daukacin iyaye da su kara zage damtse wajen ganin ‘ya’yansu sun samu ilimi nagartacce da kuma sanya ido wajen kula da tarbiyyarsu. Haka zalika, kwamitin shirya musabakar karatun alkurani ya karrama Zailani da lambar yabo bisa irin gudummawar da yake bai wa addinin Musulunci a ciki da wajen Jihar Kaduna. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
“Gane amfanin lamarin da ya shafi ilimi shi yasa, Gwamna Lawal ya kaddamar da dokar ta baci a bangaren ilimi a watan Nuwamba 2023,matakin da aka dauka an yi sa’a ya haifar da da mai ido a bangaren ilimi a Jihar Zamfara. “Fiye da makarantu 500 aka y masu kwaskwarima da samar masu abubuwan da suka kamata tun lokacin da aka kaddamar da dokar ta bacin.An horar da Malaman makarantun gwamnati,ana kuma ci gaba dayin hakan. “Saurin biyan kudaden bashi da Hukumomin WAEC da NECO ya kawo kwanciyar hankali ga daliban da suka kammala makaranta da rubiuta jarabawa, sai dai basu samu ci gaba da karatu ba saboda Hukumomin jarabawar sun rike masu sakamakon jarabawar da suka yi. Daga...
Ɗaruruwan ɗalibai ne suka suka tsallake rijiya da baya a lokacin da ajujuwan da suke rubuta jarabawar kammala sakandare (SSCE) a ranar Laraba. Lamarin ya faru ne a makarantar sakandiren gwamnati da ke Namne a Ƙaramar hukumar Gassol a Jihar Taraba. Ko kwabo ban ciyo bashi ba tun da na zama Gwamnan Kaduna – Uba Sani Ambaliyar ruwa ta kashe sama da mutum 50 a Neja Ajujuwan sun rufta musu a lokacin da aka yi ruwan sama kamar da baƙin ƙwarya da iska. Ɗaliban da masu kula da jarrabawar sun maƙale a cikin ajujuwan da suka rufta na tsawon sa’o’i kafin wasu mazauna garin su kuɓutar da su. Wani mazaunin garin Alhaji DanAzumi Lauris ya shaida wa Daily Trust cewa,...
Daga baya, hukumar WAEC ta fitar da sanarwa tana mai bada hakuri, inda ta ce wasu ƙalubale ne suka hana isar da kayayyakin jarrabawa akan lokaci. Wannan lamari ba sabon abu ba ne, domin a watan Afrilu, LEADERSHIP ta ruwaito cewa wasu masu rubuta jarrabawar UTME sun bar gida da asuba domin isa cibiyoyin jarrabawa kafin ƙarfe 6:30 na safe, ba tare da wadataccen tsaro ko sufuri ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Jaddada Cewa: Ba Zata Taba Amincewa Da Batun Dakatar Da Sarrafa Uranium Ba
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Iran ba za ta daina sarrafa sinadarin Uranium a kowane hali ba Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya tabbatar a wata hira da tashar CNN ta Amurka cewa: Iran ba za ta taba yin watsi da hakkinta na tace sinadarin Uranium a kowane hali ba. A yayin da yake mayar da martani game da kyakkyawan fata na shugaban Amurka Donald Trump game da shawarwarin nukiliyar da aka yi tsakanin gwamnatinsa da Iran da kuma yadda yake kallon ci gaban da aka cimma, Baqa’i ya ce: Idan manufar Amurka ita ce tabbatar da cewa shirin makamashin nukiliyar Iran ba zata yi amfani da shi wajen karfin soji ba, to yana ganin...
Kasar Najeriya ta sanar da Shirin fara aiki a wasu sabbin masana’antu domin sarrafa sanadarin Lithium Ministan ma’adanai na kasar ta Najeriya Daili Alaki ne ya sanar a ranar Lahadin da ta wuce cewa, a wannan shekarar da ake ciki ta 2025, da hakan zai samar da gagarumin sauyi a fagen kayan da kasar za ta rika fitarwa zuwa kasashen waje. Kamfanin dillancin “Reuters” ya ambato ministan ma’adanai na kasar yana ci gaba da cewa; ‘yan kasar China ne za su zuba hannun jari mafi grima a cikin wannan Shirin da hakan zai samar da ayyukan yi a cikin kasar da kuma bunkasar harkokin kere-kere. Haka nan kuma Alaki ya yi ishara da cewa; Msana’antar sarrafa Lithium din da za...
Gwamnatin Jihar Gombe ta sanya hannu kan yarjejeniyar Naira biliyan uku domin gina mayankar dabbobi ta zamani a garin Gombe. Hakan wani bangare ne na shirin inganta kiwon dabbobi da tsaftar abinci da kuma rage matsalolin kiwon dabbobi (L-PRES) wanda Bankin Duniya ke tallafa wa. Shirin L-PRES na da nufin kyautata harkar kiwon dabbobi da sarrafa nama cikin tsafta a jihar. An kulla yarjejeniyar ce tare da kamfanin Lubel Nigeria Limited da wa’adin kammalawa na watanni 9, zuwa watan Fabrairun shekarar 2025. An gudanar da bikin sanya hannu kan yarjejeniyar a ofishin L-PRES da ke G.R.A, a Gombe, inda shugaban shirin na jihar, Farfesa Usman Bello Abubakar, ya bayyana wannan aiki a matsayin babban ci-gaba a jihar. Sojoji sun kashe mayaƙan...

Nijeriya Na Da Karfin Tattalin Arzikin Sarrafa Kayan Dandanon Da Muke Bukata A Cikin Gida – Yahaya Yakubu
Na yi imanin za mu iya hakan Kuma muna fasahar da za mu iya aiwatar da hakan? Idan aka yi la’akari da albarkatun noma da Nijeriya ke da shi, musamman a cikin amfanin gona irin su rogo da rake, da kuma ta hanyar saka hannun jari kan ababen more rayuwa da fasahar kere-kere, akwai gagarumin yuwuwar bunkasa damar samar da MSG na cikin gida ta hanyar amfani da wadannan albarkatun kasa da ake samu. Muna da injiniyoyi da yawa wadanda za su iya gyara injinan. Muna da dukkan abubuwan da ake bukata a Nijeriya don samar da kayan dandano. Yawanci muna samun abubuwan da duk da muke bukata. Idan kana bukatar ruwa mai yawa, muna da madatsun ruwa a Shiroro,...
Samun Gurbin Shiga Jami’a Da Sauran Manyan Makarantu Samun damar shiga jami’a a Nijeriya na da matukar wahala a koda-yaushe, sai ga shi wannan shekara ta 2025 ta bullo da wasu sabbin kalubale. Daga kura-kuren da aka samu yayin yin rajista da kuma gwajin kwamfuta, don rage yawan masu shiga jami’ar, tsarin ragewar na wannan shekarar ya fi na kowace shekara. Sama da dalibai miliyan 1.9 ne suka rubuta jarrabawar a wannan shekarar, wanda hakan yasa ta zama jarrabawa mafi girma a tarihin hukumar shirya jarrabawar. Wannan karuwar, ta nuna karuwar yawan al’umma da kuma karuwar bukatar neman ilimi a tsakanin matasan Nijeriya. Har ila yau, wannan na nuni da cewa; adadin guraben da ake da su a jami’o’in kasar...
“Haƙiƙa muna alfahari da Dr. Sani Dauda Ibrahim da wannan ajin naku, musanman cewa akan ku na fara koyarwa a jami’a, kuma haɗin kan ‘yan wannan ajin ya zama na daban a cikin ƙungiyoyin tsofaffin ɗalibai, musanman saboda ayyuka da kuka gabatar na ci gaban ilimi a jami’ar Bayero da yadda kuke damuwar da al’amuran ilimi” cewar Dr. Almajir. Taron ya samu halartar Dr. Maimuna Isma’il da ke koyarwa a sashen da sauran mambobin ƙungiya da ‘yan uwa da abokan arzikin Dr. Sani Dauda Ibrahim da aka karrama a wajen taron. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin...

Wulayati Ya Ce Samun Kalamai Masu Karo Da Juna Tsakanin Trump Da Mukarrabansa Yana Zubar Da Kwarin Gwiwa
Mai ba da shawara ga jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Kalamai masu karo da juna na Trump da mataimakansa sun zubar da kwarin gwiwa ga gwamnatin Amurka Mai bai wa Jagoran juyin juya halin Musulunci shawara ya bayyana cewa: Sabani da ake ci gaba da yi a cikin maganganu da ayyukan Trump da takwarorinsa na haifar da rashin amincewa da gaskiyar gwamnatin Amurka. Ali Akbar Velayati mashawarcin Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya yi tsokaci a cikin wani sako da ya wallafa a dandalin X kan kalamai masu cin karo da juna da jami’an Amurka suka yi. Mai bai wa Jagoran juyin juya halin Musulunci shawara ya ce ci gaba da cin karo da juna...
An karrama Injiniya Dr. Mohammed Uba da lambar yabo ta kasa ta Rootswatch ta shekarar 2025, a matsayin girmamawa bisa gagarumin gudummawar da ya bayar wajen ci gaban al’umma, aiwatar da muhimman ayyukan raya kasa, da kuma kyakkyawan jagoranci. An mika wannan lambar yabo ne a yau a Cibiyar Karramawa ta Kasa da Kasa da ke Abuja. An karrama Dr. Uba tare da wasu shugabannin kananan hukumomi guda uku daga Jihar Jigawa da suka hada da Abdullahi Na Layi, Jarma na Garki, da Malam Madori, saboda hadin gwiwarsu wajen bunkasa ci gaban al’umma tun daga yankunan karkara. Taron ya jawo hankalin manyan baki daga sassa daban-daban na ƙasar, kuma ya kasance wata hanya ta ƙarfafa gwiwar shugabannin kananan hukumomi...
Shugaban Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB), Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana cewar an samu kura-kurai a sakamakon jarrabawar UTME ta shekarar 2025 da aka saki kwanan nan. A yayin wani taron manema labarai a Abuja, Farfesa Oloyede, ya fashe da kuka yayin da yake bai wa ɗalibai haƙuri, inda ya nuna nadamarsa kan wahalar da suka sha. Mutum 2 sun shiga hannu zargin yi wa ƙananan yara fyaɗe a Gombe ’Yan bindiga sun kashe jarirai, sun bai wa karnuka namansu a Zamfara A cewar JAMB, matsalolin fasaha sun shafi sakamakon ɗalibai 379,997. Waɗannan matsaloli sun fi shafar jihohin Kudu maso Gabas da kuma Jihar Legas. A Legas, ɗalibai 206,610 daga cibiyoyi 65 ne suka fuskanci matsalar, yayin da...
Kasar Sin ta harba wani rukunin taurarin dan adam daga cibiyar harba tauraron na Taiyuan dake lardin Shanxi na arewacin kasar. An harba taurarin ne jiya Lahadi da misalin karfe 9:27pm agogon Beijing, bisa amfani da samfurin rokar Long March-6 da aka yi wa ‘yan gyare-gyare. A cewar cibiyar ta Taiyuan, rukunin taurarin mai suna Yaogan-40 02, ya shiga da’irarsa cikin nasara. Za a yi amfani da taurarin ne wajen gwaje-gwajen fasahohi da gano yankuna masu tasirin haduwar maganadisu da lantarki. Aikin na jiya shi ne karo na 574 da aka yi amfani da samfurin rokar Long March. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
Hukumar JAMB mai shirya jarrabawar neman shiga makarantun gaba da sakandire a Nijeriya, ta sanar da sakin sakamakon jarrabawar da ɗalibai suka zana a bana. Wata sanarwa da shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede ya fitar ranar Juma’a, ta ce an riƙe sakamakon ɗalibai 39,834 wanda a cikin wannan adadi tana bincike kan sakamakon ɗalibai 1,426. An kama mutum 78 da makamai da kwayoyi a Kano Nijeriya ta soke ba da tallafin karatu a ƙetare A ranar Litinin ne JAMB ta fitar da alƙaluman sakamakon bana tana mai cewa yawancin ɗaliban da suka zauna jarabawar sun gaza samun maki 200 daga cikin maki 400. JAMB ta ce ɗalibai miliyan 1.95 ne suka rubuta jarabawar daga cikin 2,030,862 da suka yi rajista,...
Shugaban kamfanin Sarrafa Sinadaran man fetur na kasar Iran ya bayyana cewa kasarsa tana son da kasance cikin wadanda zasu gina kamfanin sarrafa sinadaran man fetur na jumhuriyar Nijer, iran tana son ta taimaka wajen samar da takin zamani ga kasashen Afirka. Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran ya nakalto Hassan Abbaszadeh yana fadar haka a lokacinda yake ganawa da ministan man fetur na Jumhuriyar Nijer a kasuwar baje kolin kayakin da aka kera a Iran wato Iran EXPO 2025 karo na 7 wanda aka kamala. Abbaszadeh ya kara da cewa sinarin Urea wanda JMI take samarwa zai amfani amfani kamfanin sinadaran man fetur na kasar Nijer don samar da takin zamani wanda zai sami kasuwa babba a kasashen...
Sun ƙara da cewa, “Samun shugabannin matasa masu jajircewa a wannan yankin babbar albarka ce ga al’ummarmu. “Hakan na nuna mana cewa akwai kyakkyawar makoma ta ci gaba a Arewa gaba ɗaya.” Sannan sun bayyana cewa sun aike wa ƙungiyoyinsu a dukkanin jihohi 19 na Arewa goron gayyata domin naɗin sabbin muƙamai a Masarautar Daura. “Za a gudanar da babban taron karramawa wanda ba a taɓa ganin irinsa ba a nan kusa, domin naɗin sabbin muƙamai da Masarautar Daura za ta yi.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe ...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hon. Ibrahim ya yi nuni da cewa a karkashin jagorancin Gwamna Abba an samu ci gaba sosai wajen tabbatar da samar da ingantaccen ilimi ga kowa da kowa da kyautata harkar lafiya da sufuri da biyan ma’aikata da ‘yan fansho hakkokinsu ba tare da jinkiri ba. Kwamishinan ya jaddada goyon bayansa ga irin ayyukan raya kasa da Gwamna Abba ke yi, musamman a fannonin ilimi, kiwon lafiya, bunkasa matasa da bunkasa harkar kasuwanci da sufuri a fadin Jiha Kano. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
A kokarinta na ganin an gudanar da jarrabawar hadin gwiwa ta hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta JAMB, gwamnatin jihar Kano ta dakatar da aikin tsaftar muhalli na watan Afrilun 2025. An dauki wannan matakin ne bayan nazari da tuntubar masu ruwa da tsaki, a kokarin baiwa daliban jihar Kano damar rubuta jarabawarsu ba tare da wata matsala ba. A wata sanarwa da Daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi, Ismail Garba Gwammaja ya fitar, ya ruwaito kwamishinan yana cewa. “Dakatar na da nufin hana duk wani cikas da zai iya kawo cikas ga aikin jarrabawar da kuma tabbatar da cewa ‘yan dalibai za su iya zana jarabawarsu ba tare da wani shamaki...
Sai dai Bukarti wanda ya shafe shekaru da dama yana gudanar da bincike kan kungiyar ta ‘yan ta’adda, ya kara nuna fargabar cewa, a halin yanzu ‘yan tada kayar bayan na yaɗa aƙidarsu a shafukan sada zumunta ta hanyar ɗora naɗaɗɗen faifan bidiyo da kuma gabatarwa kai tsaye. Ya ce, “Yanzu idan ka shiga TikTok, za ka ga shafukan ‘yan Boko Haram, suna gudanar da shirye-shirye kai-tsaye ko kuma su ɗora naɗaɗɗen bidiyo, inda suke yada akidar Boko Haram, suna kafa hujjar kashe-kashen da suke yi da harshen Hausa, suna amsa tambayoyi daga masu sauraro, suna amsa tsokaci da aka rubuta. “Ko a wannan makon ma, an samu wani dan Boko Haram da ya saka wani bidiyo na...
Da alama tsohon Shugaban Kasar Nijeriya, Muhammadu Buhari, yana nema karbe kambun ɗaukaka da ’yan siyasa a baya suka riƙa bai wa tsofaffin shugabannin ƙasar nan biyu, Janar Ibrahim Badamasi Babangida da kuma Cif Olusegun Obansanjo, wajen neman tabarrakinsu musamman a lokacin da zabe ya karato a kasar nan. Buharin wanda ya mulki kasar nan a tafarkin soja da kuma na farin hula daga bayabayan nan, a yanzu haka tauraronsa na haskawa, kuma yana ƙamshin turaren Ɗan goma, inda jiga-jigan ’yan siyasa daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP da SDP da kuma jam’iyyarsa mai mulki ta APC, suke nikar gari takanas zuwa gidansa da ke birnin Kaduna, tare da nuna irin kyakkyawan kusancinsa da su. Hakan dai na zuwa ne...
Hukumar Shirya Jarrabawa Shiga Manyan Makarantu ta Najeriya, JAMB, ta sanya Alhamis, 24 ga watan Afrilu, a matsayin ranar soma jarrabawar wannan shekarar maimakon ranar 25 ga wata da ta fara sakawa. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Dokta Fabian Benjamin ya fitar ranar Asabar. Manyan jami’an gwamnati sun halarci auren ’yar tsohon Gwamnan Bauchi NAJERIYA A YAU: Sabbin dabarun hana matasa aikata laifi A cewarsa, an samu sauyin ranar ne domin tabbatar da muhimman matakan da ta ɗauka sun yi daidai da tnade-tanaden sauran hukumomin da za su taimaka mata wajen gudanar da aikin. Dokta Benjamin ya ce a yanzu haka waɗanda za su rubuta jarrabawar za su iya fitar da katin shiga jarrabawar –...
A ƙarshe, wakilin Gwamna Abba Kabir Yusuf a taron, Sakataren Gwamnatin Jihar, Umar Faruk, ya nuna jin daɗinsa da ci gaban da aka samu wajen gyaran ɗaliban ta hanyar ilimi na yau da kullum, yana tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen ilimi na ‘yan gidajen yari a matsayin muhimmin mataki na dawo da su cikin al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Al’ummar Babura sun shirya gagarumin taron girmamawa domin karrama Dr. Salisu Mu’azu, bayan nada shi a matsayin Daraktan kuma babban likitan asibitin koyarwa na Rasheed Shekoni da ke jihar Jigawa, da kuma samun matsayin mamba na Cibiyar Kasa (mni). Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Kwamitin Shirye-shirye, Rabiu Umar, ya bayyana cewa an gudanar da taron ne domin nuna godiya ga Allah da kuma murnar manyan nasarorin da Dr. Mu’azu ya samu. Ya yaba da kokarin Daraktan wajen gudanar da aikinsa da kwarewa, da kuma ci gaba da tallafa wa al’umma. A sakon da aka gabatar a madadin Mai Martaba Sarkin Ringim, Alhaji Dr. Sayyadi Abubakar Mahmoud, wanda Mai Girma Alhaji Usman Sayyadi, Babban Hakimin Masarautar, ya wakilta,...
Sojojin kasar Yemen sun kakkabo jirgin yakin Amurka wanda ake sarrafashi daga nesa samfurin MQ-9 na 19 a jiya Lahadi da yamma a sararin samaniyar kasar. Tashar talabijan ta Presstv daga nan Tehran ya bayyana cewa sojojin kasar ta Yemen sashen UAV wato masu kula da abinda ake kira ‘Drones’ sun bada sanarwan kakkabo jirgin yaki na Amurka ne a lokacinda yake tattara bayanai a wasu yankuna a sararin samaniyar kasar. Masana sun bayyana cewa farashin ko wane jirgi yakin samfurin MQ-9 ya kai dalar Amurka miliyon $33, don haka ya zuwa yanzu kasar Amurka ta yi asarar dalar Amurka miliyon $600. Kafin haka dai sojojin Yemen bangaren makamai masu linzami sun bada sanarwan cilla makamai masu linzami samfurin Balistic ...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sanarwar ta ƙara da cewa, ƙungiyar ta karrama gwamna Lawal tare da gwamnonin Akwa Ibom, Kaduna, da kuma jihar Legas. “A jiya a Legas, ƙungiyar ‘yan kasuwa ta Nijeriya da Amurka (NACC) ta gudanar da bikin cika shekaru 65 da ƙaddamar da Alhaji Sheriff Balogun a matsayin shugaban ƙungiyar na 20. “Taron mai taken ‘Ƙarfin Haɗin Kai: Shekaru 65 na inganta dangantakar tattalin arzikin Nijeriya da Amurka’ ya samu halartar manyan jami’an Amurka da Nijeriya da kuma ‘yan kasuwa. “Ƙungiyar ta amince da goyon bayan da Gwamna Lawal yake baiwa harkokin kasuwanci a jihar Zamfara, musamman a fannin noma. “Karramawar da aka baiwa gwamnan na nuni ne da irin kwazonsa na jagoranci, da kwazonsa na inganta...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baqaei ya bayyana cewa, ma’a, kwana guda gabanin tattaunawar da ake jira a kasar Oman tsakanin Amurka da Iran kan shirin nukiliyar kasar Iran, damammaki da daman a diflomasiyya da Amurka za ta iya tabbatar da aniyarta a kansu Baqaei ya rubuta a dandalin X, “Ya kamata Amurka ta mutunta wannan shawarar da aka yanke duk da cewa ana fama da rikici.” “Ba za mu yanke hukunci ba, Muna da niyyar tantance niyyar dayan bangaren kuma za mu tabbatar da hakan a wannan Asabar,” in ji jami’in diflomasiyyar na Iran, ya kara da cewa Iran “za ta yi tunani kuma ta mayar da martani ga kowane mtaki.” A ranar Litinin shugaban Amurka Donald...
Dukkanin dangogin abinciccika masu kitse, na da matukar hadari ga lafiyar hantar Dan’adam. Abincin da ke da kitse, ya kan bai wa hanta wahala kwarai da gaske, kasantuwar cewa ita ce ke kula sarrafa dukkanin abin da ke shiga cikin Dan’adam. Don haka, yawan cin kitse na cutar da ita matuka gaya. 2- Siga Kadan daga cikin ayyukan hanta shi ne, sarrafa siga zuwa sinadarin kitse, sannan kuma kamar yadda muka bayyana a sama, yawan hakan na da matukar lahali ga lafiyar hantar. 3- Gishiri Binchiken masana ya nuna cewa, abinci mai gishiri kan yi lahali ga jiki, musamman ma dai kasantuwar hanta ita ce ke da alhakin sarrafa sinadarin. Yawan gishiri kan wahalar da hanta tare da sanya mata...
Duk da haka, ɗalibai masu kammala makaranta sai sun jira amincewar Majalisar Jami’ar kafin su samu damar duba sakamakonsu. Ana sa ran wannan ci gaba zai inganta ayyuka a Jami’ar da kuma sauƙaƙa wa ɗalibai gudanar da harkokin karatunsu cikin sauƙi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban Karamar Hukumar Jahun dake Jihar Jigawa, Alhaji Jamilu Muhammad Danmalam ya kaddamar da rabon kayan sallah da kuma kudin dinki ga al’ummar yankin. A jawabinsa wajen bikin da aka gudanar a garin Jahun, shugaban Karamar Hukumar yace Hakimai na gundumomin Jahun da Aujara da Gunka da Kadawawa da Limaman masalatan juma’a 79 na yankin za su amfana da kayan sallah da kuma kudin dinki. Jamilu Muhammad Danmalam ya bayyana rashin Jin dadinsa bisa yadda ake mantawa da iyayen kasa da Malaman Addini a irin wannan lokacin da ya kamata a taimake su. Ya ce yana daya daga cikin kudurorinsa na shigo da kowanne bangare na al’umma cikin tsarin shugabancinsa dan kowa ya anfana. Danmalam ya...
Ya kara da cewa cire Jami’oi daga tsarin albashi na (IPPIS),wanda hakan ne ya ba su Jami’oin tsayawa da kansu kan lamarin da ya shafi ayyukansu wanda har ila yau hakan ya sa ayyukamsu suka kara ingantuwa. Wike ya yi karin bayani,“akwai maganar amincewa da maganar kudaden bincike na Hukumar TETFund a cikin wasu makarantu, hakan ya kar bunkasa lamarin daya shafi bincike da kirkiro wasu abubuwa.” Su wadannan lamurran na ci gaba sun kara daidaita Jami’oi su maida hankali kan ilimin da suke samarwa domin ya cimma matsalolin da ake fuskanta a karni na ashirin da daya. da yake bayyana yadda ya ji dangane da karramawar da Hukumar Jami’ar kalaba ta yi masa na ba shi digirin digirgir,Wike ya...
Wani rahoto da aka fitar yau Talata, yayin zaman taron shekara-shekara na shekarar 2025, na dandalin tattaunawa na Asiya na Boao, ya nuna yadda kasar Sin ke ci gaba da kasancewa cibiyar rarraba hajojin da masana’antu ke sarrafawa. Rahoton mai taken “Nazarin tattalin arzikin Asiya, da hadadden rahoton ci gaba na shekarar”, ya nuna yadda tun daga shekarar 2017, hada-hadar cinikayya ta duniya a fannin rarraba matsakaitan hajoji, ke kara dogaro kan kasar Sin sama da dogaronta ga yankin arewacin Amurka. Kazalika a shekarar 2023, dogaron sassan kasa da kasa kan kasar Sin ta fuskar samar da matsakaitan hajoji ya kai kaso 16 bisa dari, sama da na yankin arewacin Amurka mai kaso 15 bisa dari. Bugu da kari, rahoton...
Majiyar gwamnatin kasar Yemen ta basa sanarwan kai hare-hare har sau biyu kan kataparen jirgin ruwa mai daukar jiragen yaki na kasar Amurka dake cikin Tekun Red sea, wato USS Harry Truman. Inda suka cilla makami mai linzami guda da kuma jiragen yake wadanda ake sarrafasu daga nesa kan jirgin. Har’ila yau sojojin yamen sun ce sun kaiwa wasu sojojin Amurka hare-hare da jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa duk a cikin sa’oi 48 da suka gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin sojojin kasar Yemen Burgediya Yahyah Saree ya na fadar haka a safiyar yau talata, ya kuma kara da cewa sojojin kasar za su ci gaba da maida martani da kuma hana jiragen...
Tsohon gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya fasa baragurbin ƙwai kan zargin sace Jafaru Sani, tsohon Kwamishina a gwamnatinsa. El-Rufai, wanda ya mulki Jihar Kaduna daga 2015 zuwa 2023 kafin ya miƙa mulki ga Sanata Uba Sani, wanda shi ne ɗan takarar da ya fi so ya gaje shi, ya bayyana wannan batu ne a shafinsa na Facebook da aka tantance sahihancinsa a ranar Alhamis. Tsaro: Shugaban Ƙaramar Hukuma ya tabbatar da haɗa kai da Sarakuna Galibin ’yan Najeriya na neman muƙaman gwamnati don arzuta kansu — Obasanjo A cewarsa, an tsare tsohon Kwamishinan na shi ne a kurkuku ba bisa ƙa’ida ba. El-Rufai ya ce, yana da tabbacin ana cin zarafin abokin nasa ne saboda ya fice daga...
Hukumar gudanarwar asibitin koyarwa na Aminu Kano ta ce ana kokarin ganin an dawo da ayyukan da masana’antar iskar Oxygen da asibitin ke yi. A cewar Mataimakin Daraktan sashen (Biomedical/ kuma Shugaban Kwamitin Kula da Oxygen), Engr Ahmed Usman a madadin Hukumar, an sanya hannu kan wata yarjejeniya ta fahimtar juna tsakanin asibitin da Dodams Medical Equipt don kula da aikin na tsawon shekaru 2. Ya bayyana cewa, a watan Janairun wannan shekara ne aka yi duk wani shiri da kuma biyan kudin jirgi, amma saboda hutun karshen shekara da Kamfanoni suka yi, an samu tsaiko wajen samar da wasu sassa musamman na’urar gudanarda aikin, wanda ya iso a ranar Litinin 10 ga Maris, 2025. Ya ci...
Ya kara da cewa an samu wasu kayayyaki a wurin, ciki har da babbar motar dakon kaya ɗauke da buhuna takwas na ‘Monazite’ da aka sarrafa, wanda nauyinsa ya kai kilogiram 1000, wanda darajar kowanne buhu ta kai naira miliyan hudu, da kuma wasu ma’adinai da ba a sarrafa ba da ake zargin an haƙo su ba bisa ƙa’ida ba. Ya ce ana ci gaba da bincike kan lamarin kuma da zarar an kammala za a gurfanar da waɗanda ake zargin a kotu domin su fuskanci hukunci. Idan ba a manta ba a kwanaki kaɗan da suka wuce gwamnatin Jihar Filato, ta sanar da sanya haramci kan harkokin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a faɗin jihar saboda...
Ƙungiyar Malaman Tsangaya a Jihar Gombe ta karrama Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya lambar yabo ta ‘Khadimul Qur’an’ a matsayin girmamawa ga goyon bayansa maras misaltuwa ga ilimin Alƙur’ani da kuma matakan da ya ɗauka wajen kyautata tsarin Almajiranci. Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta miƙa wannan girmamawa ga Gwamnan yayin wani taron buɗa-baki na musamman da aka shirya musu a Fadar Gwamnati da ke Gombe, wanda ya tattaro shugabannin malaman Tsangaya daga faɗin jihar. Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Yadda masana’antun Arewa suka koma kufai Wannan taron na cikin tsarin shekara-shekara na Gwamna Inuwa Yahaya na shirya shan ruwa tare da jama’a, wanda hakan wani mataki ne da yake ƙara haɗin kai, zaman lafiya, da hulɗa...
Daga ƙarshe sanarwar ta ƙara jaddada ingantattun ƙa’idojin karatu a BUK, wanda ta ce ba za ta lamunci satar jarrabawa ko laifuffuka makamantan haka ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
LEADERSHIP tana da mabiya kusan miliyan 3.7 a shafukan sada zumunta daban-daban, ciki har da dandalinta na Hausa. Tun daga ranar Lahadi, da yawa daga cikin masu bibiyar wadannan manhajoji ko dai suna ba da alamar dangwale, ko kuma taya murna kan labaran da suka shafi bikin karramawar da ke tafe. A makon da ya gabata, jaridar ta ce ta kara samun wani matsayi na musamman a bikin na bana, wanda kuma ke bikin cika shekaru 20 da kafa kamfanin, ta hanyar baje kolin abin da ke tafe a jaridar Financial Times, babbar jaridar kasuwanci da hada-hadar kudi ta duniya. Gangamin wanda aka fara a makon farko na watan Fabrairu, zai ci gaba da kasancewa har zuwa watan Maris, wanda...
A kasuwar Ariaria da ke Aba, NAFDAC, sun gano jabun magunguna da kudinsu ya kai na miliyoyin Naira. Bugu da kari, a kasuwar Idumota da ke a jihar Legas, NAFDAC sun garkame Shanguna sama da 3,000 bayan sun gano Shagunan shake da jabun magunguna. A kasuwar kan Gadar Onitsha, nan ma Hukumar ta sun kama manyan motoci goma shake da jabun magungana, inda a bayan kamen dilolin magungunan suka yi yunkurin bai wa jami’an na NAFDAC cin hancin Naira miliyan 135. Har ila yau, a kasurgumar kasuwar Cemetery da ke Aba, nan ma NAFDAC ta kama tare da kwace jabun magunguna da kudinsu ya kai na sama da Naira miliyan biyar. Bisa batun gaskiya, irin wannan bakar hada-hadar jabun magunguna,...
Parradang ya yi aiki a hukumar NIS fiye da shekaru 30, inda ya yi aiki a fadin jihohin kasar nan da suka hada da Kano, Legas, Kwara, Enugu, da Abuja. Ya halarci kwasa-kwasan ƙwararru da yawa a cikin gida da waje. Domin karrama shi da hidimar da ya yi, an karrama shi da lambar yabo ta kasa ta jami’in tsaro na Tarayya (OFR) kuma ya yi fice a Cibiyar Nazarin Siyasa da Dabaru (NIPSS). Hukumomin tsaro tuni suka fara gudanar da bincike kan kisan gillar da aka yi masa, inda ake kokarin zakulo wadanda suka aikata laifin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta sanar da cewa a ɗakin wani otel ta gano gawar wani tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Ficen Nijeriya, David Shikfu Parradang. A baya dai an ruwaito cewa wasu masu garkuwa da mutane ne suka kashe Mista Parradang bayan sun karɓe kuɗin da ya ciro a banki a yankin Area 1 da ke babban birnin ƙasar. Masu garkuwa sun kashe tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Fice a Abuja Tinubu ya naɗa Babatunde Ogunjimi Akanta Janar na Tarayya Sai dai wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Abuja, Josephine Adeh ta fitar a yammacin wannan Talatar, ta ce tsohon babban jami’in Hukumar Shige da Ficen ya mutu ne a ɗakin wani otel...

A ɗakin otel muka tsinci gawar tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Ficen Nijeriya — ’Yan sanda
Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta sanar da cewa a ɗakin wani otel ta gano gawar wani tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Ficen Nijeriya, David Shikfu Parradang. A baya dai an ruwaito cewa wasu masu garkuwa da mutane ne suka kashe Mista Parradang bayan sun karɓe kuɗin da ya ciro a banki a yankin Area 1 da ke babban birnin ƙasar. Masu garkuwa sun kashe tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Fice a Abuja Tinubu ya naɗa Babatunde Ogunjimi Akanta Janar na Tarayya Sai dai wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Abuja, Josephine Adeh ta fitar a yammacin wannan Talatar, ta ce tsohon babban jami’in Hukumar Shige da Ficen ya mutu ne a ɗakin wani otel...
Ana fargabar cewa wasu masu ta’adar garkuwa da mutane sun kashe tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya (NIS), David Shikfu Parradang a Abuja. Majiyoyi sun shaida wa ƙwararren mai sharhi kan yaƙi da tayar da ƙayar baya Zagazola Makama cewa ’yan ta’addan sun ɗauke Parradang a yankin Area 1 da ke babban birnin ƙasar da safiyar wannan Talatar. Tinubu ya naɗa Babatunde Ogunjimi Akanta Janar na Tarayya Muhimmancin ƙamshi a rayuwar mace Makama ya ce ’yan ta’addan sun biyo sawun tsohon babban jami’in Hukumar Shige da Ficen ne bayan ya ciro kuɗi a banki, inda suka karɓe kuɗin sannan kuma suka kashe shi. Wannan lamari dai ya sake ɗaga hankalin mazauna Abuja a fannin tsaro musamman yadda...
Kwanan baya, kwamitin kula da aikin lantarki na duniya (IEC) ya gabatar da ka’idar sarrafa mutum-mutumin inji mai kula da tsoffi. Ka’idar da kasar Sin ta ba da jagorancin tsarawa, ta tabbatar da yadda za a tsara da sarrafa mutum-mutumin injuna masu kula da tsoffi bisa halayen da tsoffi suke ciki, ta kuma tabbatar da yadda za a gudanar da bincike kan mutum-mutumin inji, yayin ba da izini gare su. Lamarin da ya ba da tabbaci ga bunkasuwar aikin sarrafa mutum-mutumin injuna masu kula da tsoffi yadda ya kamata. Bayanin ya nuna cewa, an tsara ka’idar bisa bukatun tsoffi a fannonin samun kulawa cikin harkokin yau da kullum, da kiwon lafiya da dai sauransu. Haka kuma, ana fatan tsara mutum-mutumin...
Hukumar bayar da gudunmawar fansho ta Jihar Jigawa da Kananan Hukumomin jihar ta kulla yarjejeniyoyi da wasu mashahuran Hukumomin Asusun Fansho guda shida (PFA) da nufin tabbatar da tafiyar da kudaden fansho na jihar yadda ya kamata. Shugaban ma’aikata na jiha Alhaji Muhammad K Dagaceri wanda ya jagoranci rattaba hannu kan yarjejeniyar a madadin gwamnatin jihar Jigawa a gidan fensho na Dutse ya ce taron yana kara jaddada kudirin gwamnati na tabbatar da gaskiya da inganci a tsarin tafiyar da fansho. Ya kuma jaddada mahimmancin kula da harkokin kudi da kuma bukatar samar wa wadanda suka yi ritaya kudaden fansho domin ci gaba da gudanar da rayuwarsu. “Wannan yarjejeniya ta nuna wani gagarumin ci gaba a kokarin da...
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), ta gargaɗi shugabannin ƙananan hukumomi da su guji almundahana tare da yin amfani da kuɗaɗen jama’a bisa gaskiya da adalci. Shugaban EFCC, Mista Ola Olukoyede ne, ya bayyana haka yayin wani taro da aka shirya a Jihar Gombe kan ’yancin cin gashin kai na ƙananan hukumomi. Jihar Gombe na ƙarfafa haƙƙoƙin yara masu nakasa — Ƙungiyar JONAPWD Na yi nadamar soke zaɓen 1993 — Babangida A cewarsa, samun ‘yancin cin gashin kai ba yana nufin cewa shugabannin ƙananan hukumomi ba za a iya hukunta su ba idan sun aikata ba daidai ba. “Shugabannin ƙananan hukumomi ba su da kariya a tsarin mulkin ƙasa. Idan aka samu rashin gaskiya wajen sarrafa kuɗaɗen jama’a,...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta dauki matasa fiye da 6,000 aiki a fannoni daban-daban a fadin jihar, a kokarinta na ganin ta inganta rayuwarsu. A saboda haka ne ma matasan da aka dauka aikin suka karrama Gwamnan Jihar, Malam Umar Namadi, bisa kokarinsa na samar da ayyukan yi da bunkasa tattalin arzikin al’ummar jihar. Wakilinmu Usman Mohammed Zaria ya ruwaito cewa, taron karramawar, wanda aka gudanar a gidan Gwamnati dake Dutse Babban Birnin Jihar, ya hada da wadanda suka ci gajiyar shirye-shiryen gwamnati da suka hada da J-Teach, da J-Agro, da J-Health, da J-Millionaires, da sabbin likitocin da aka dauka aiki a bangaren lafiya. A yayin taron, kowanne rukuni ya mika lambar yabo ga Gwamna Umar Namadi don nuna...
Ya kuma bayyana cewa, a halin yanzu ayyukan hukumar bai tsaya a kan kula da tsaftace muhalli da abinci kadai ba, suna kula da tasirin sauyin yanayi da kuma fadakar da al’umma yadda za su amfana da trallafin sauyin yanayin da ake samu daga Majalisar Dinkin Duniya. A nasa jawabin, Babban Manajan Daraktan kamfanin, Alhaji Mu’azu Elezah ya nuna bukatar hukumar ta kara kaimi wajen yayata wa al’umma ayyukanta domin zuwa yanzu mutane kadan ne suka san kasancewar hukumar da ayyukanta a sassan kasar nan, “Ya kamata ku zuba jari sosai wajen fadakar da al’umma irin ayyukanku, da kuma yadda mutane za su amfana daga tallafin yaki da sauyin yanayi na majalisar dinkin dunuya” in ji shi
Jiragen Yakin HKI Sun Kashe mutane 3 da kuma jikada wasu 4 a kudancin kasar a jiya Asabar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar kafafen yada labara na yankin kudancin kasar ta Lebanon suna fadar haka. Labarin ya kara da cewa HKI ta yi amfani da makamai masu linzami wanda jirgin yaki na ” Drone” ya cilla kan wata mota a kan titi a garin Jarjoun da Iqlim Attuffah inda suka kashe mutane 3 sannan wasu kusa da motar guda 4 sun ji rauni. Majiyar yahudawan ta bayyana cewa sun kashe wani kwamandan kungiyar Hizbullah ne, amma shaidu a yankin sun tabbatar da cewa duk wadanda HKI ta kashe ba mayakan kungiyar Hizbullah ne ba. Wannan...
Gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello ta sanar da cewa za a gudanar da taron Karrama Sir Ahmadu Bello karo na 11 a ranar Asabar, 22 ga Fabrairun 2025, a Bauchi. Wannan taron, wanda ke tunawa da rayuwa da gado na Sir Ahmadu Bello KBE, Sardaunan Sokoto da Firaministan tsohuwar Yankin Arewa, zai hada da jerin tattaunawa da ayyukan da zasu mayar da hankali wajen magance kalubalen tattalin arzikin yankin. Taken taron na bana, “Alherin Duniya: Sauyw Albarkatun Halitta na Arewa zuwa Cigaba Mai Dorewa”, na zuwa ne a lokacin da ake fuskantar karin damuwa kan talauci da rashin aikin yi da rashin ci gaba duk da kasancewar Arewa na da yalwar albarkatun halitta. ...

Thomas Bach Ya Bai Wa Cmg Izinin Sarrafa Watsa Labarun Gasar Olympics Ta Lokacin Hunturu Ta Milan Ta 2026
Albarkacin bikin bude gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Asiya karo na 9 dake gudana a birnin Harbin na Sin, shugaban kwamitin shirya gasar Olympics ta kasa da kasa, Thomas Bach ya ziyarci cibiyar yada labarai ta gasar a jiya Juma’a, kuma ya yi hadin kai da shugaban rukunin gidajen rediyo da talibijin mallakin kasar Sin, wato CMG, Shen Haixiong, don bai wa runkunin na CMG damar tsarawa da kuma sarrafa watsa labarun gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Milan da Cortina d’Ampezzo ta shekarar 2026. Shen Haixiong ya ce, gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Asiya da ake shiryawa a birnin Harbin, wata kasaitaciyyar gasa ce ta kasa da kasa da Sin ta shirya bayan...
Saka sunan Taye Taiwo a cikin jerin zakakuran yan wasan kungiyar ya nuna yadda dan wasan ya nuna bajinta da kuma yadda ita kanta kungiyar ta Marseille ta yaba da irin kokarin da ya yi a baya.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karrama wasu mutum 35 ’yan asalin Jihar Kano waɗanda suka yi fice a fannoni daban-daban na rayuwa. Daga cikin waɗanda gwamnan ya karrama akwai janar-janar ɗin soji 19, Farfesoshi 6 da wasu fitattun Kanawa 10. Asibitin Malam Aminu Kano ya hana motoci masu baƙin gilas shiga harabarsa Mahaifin ma’aikacin Aminiya ya rasu Aminiya ta ruwaito cewa, an bayar da lambobin yabon ne ga fitattun mutanen maza da maza a wani ƙwarya-ƙwaryan biki da ya gudana a Fadar Gwamnatin Kano ranar Asabar da daddare. Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce waɗanda suka samu lambobin yabon sun yi fice a fannoni daban-daban na rayuwa kuma a dalilin haka an samu ci...