JAMB ta sauya ranar soma jarrabawar bana
Published: 19th, April 2025 GMT
Hukumar Shirya Jarrabawa Shiga Manyan Makarantu ta Najeriya, JAMB, ta sanya Alhamis, 24 ga watan Afrilu, a matsayin ranar soma jarrabawar wannan shekarar maimakon ranar 25 ga wata da ta fara sakawa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Dokta Fabian Benjamin ya fitar ranar Asabar.
A cewarsa, an samu sauyin ranar ne domin tabbatar da muhimman matakan da ta ɗauka sun yi daidai da tnade-tanaden sauran hukumomin da za su taimaka mata wajen gudanar da aikin.
Dokta Benjamin ya ce a yanzu haka waɗanda za su rubuta jarrabawar za su iya fitar da katin shiga jarrabawar – wadda ke ɗauke da muhimman bayanai dangane da jarrabawar.
Ya ƙara da cewa, akwai bayanin wuri da lokacin mutum zai zana jarrabawar da sauran muhimman bayanai game da yadda tsarin zaman ɗakin jarrabawar zai kasance duka a jikin katin.
Dubban ɗaliban Najeriya ne ke rubuta jarrabawar JAMB a kowace shekara, domin samun damar shiga makaratun gaba da sakandire.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Hukumar JAMB Jarrabawa
এছাড়াও পড়ুন:
Manyan Malaman Roman Katolika Sun Fara Taron Zabar Paparoma
Manyan malaman addinin darikar Roman Katolika za su fara Shirin zabar shugaban darikar tasu a fadar Vatican
Adadin manyan malaman addinin masu mukamin “Cardinal” 130 ne za su taru a fadar Vatican, domin su zabi wanda zai maye gurbin Paparoma Farancis da ya rasu.
Sai dai masu kusancin da fadar ta Vatican suna bayyana cewa, da akwai batutuwa da dama da su ka raba kawunan manyan malaman addinin na Roman Katolika da su ka batun auren jinsi, da rawar da mata za su taka a karkashin inuwar cocin.
Sai dai kuma wani mai sharhi akan abubuwan da su ka shafi cocin, Reese ya bayyana cewa, masu zaben za su mayar da hankali ne akan wanda zai kare ayyukan da mamacin Paparoma Francis ya bari.
Tare da cewa babu kafa ta yin yakin neman zabe a tsakanin masu mukamin na Cardinal, sai dai da akwai wasu siffofi da halaye da ake son gani da wadanda za su iya zama ‘yan takara.
Ana sanar da wanda ya zama sabon Paparoma ne ta hanyar samun kaso 2/3 na kuri’un da manyan masu zaben su ka kada.
A bisa ka’idar cocin, duk wanda aka yi wa wankan tsarki na ” Baptisma”zai iya zama paparoma,amma kuma tun daga 1378 ba a zabi wanda bai kai mukamin “Cardinal” ba.