Leadership News Hausa:
2025-09-18@00:41:31 GMT

An Fara Gangamin Babban Taron LEADERSHIP Da Karrama Gwarazan 2024

Published: 7th, March 2025 GMT

An Fara Gangamin Babban Taron LEADERSHIP Da Karrama Gwarazan 2024

LEADERSHIP tana da mabiya kusan miliyan 3.7 a shafukan sada zumunta daban-daban, ciki har da dandalinta na Hausa.

Tun daga ranar Lahadi, da yawa daga cikin masu bibiyar wadannan manhajoji ko dai suna ba da alamar dangwale, ko kuma taya murna kan labaran da suka shafi bikin karramawar da ke tafe.

A makon da ya gabata, jaridar ta ce ta kara samun wani matsayi na musamman a bikin na bana, wanda kuma ke bikin cika shekaru 20 da kafa kamfanin, ta hanyar baje kolin abin da ke tafe a jaridar Financial Times, babbar jaridar kasuwanci da hada-hadar kudi ta duniya.

Gangamin wanda aka fara a makon farko na watan Fabrairu, zai ci gaba da kasancewa har zuwa watan Maris, wanda zai kare a daidai lokacin da ake shirin gudanar da taron LEADERSHIP da bada kyaututtuka karo na 17 da aka shirya gudanarwa a ranar 8 ga watan Afrilu a dakin taro na Bankuet dake fadar shugaban kasa, Abuja.

Kamfanin ya ce za a ga tallan taron da aka yi a jaridar Financial Times ta hannun manyan jami’an gwamnati da kuma mutanen da ke kan manyan mukamai da suka karanta Financial Times a kasashen Amurka da Birtaniya da Kanada da Nijeriya da Ghana da kuma Afirka ta Kudu.

Kamfen din ya kuma shafi Masar, Aljeriya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Saudiyya, Kenya, da Habasha.

Sama da masu biyan kudi 35,000 na Financial Times a cikin wadannan kasashe suna iya danna tallan don ziyartar intanet na taron LEADERSHIP da kyaututtuka.

Idan za a iya tunawa, Hukumar Editocin LEADERSHIP, a watan Nuwamba, 2024, ta zabi fitattun mutane da kungiyoyi 26 da suka bayar da gudunmawa ta musamman ga harkokin mulki, kasuwanci, tasirin al’umma, da hidimar jama’a a Nijeriya a shekarar 2024 don ba da kyauta ta gwal na jaridar.

Wadanda aka zaba sun hada da Alhaji Aliko Mohammad Dangote, fitaccen dan kasuwan Nijerita kuma mai taimakon jama’a, a matsayin wanda ya lashe kyautar gwarzon shekara saboda dimbin gudunmawar da ya bayar ga tattalin arzikin kasar. Kokarinsa na taimakon jama’a da kwazo ya sa ya zama wanda ya cancanci a ba shi wannan babbar daraja.

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Barista Nyesom Ezenwo Wike, ya lashe lambar yabo ta Kuinkuennial for Gobernance and Infrastructure a 2024, lambar yabo da ba kasafai ake samu daga LEADERSHIP Group Limited ba, lambar yabo ce da ake bayarwa sau daya a duk shekara biyar.

Har ila yau, a shekarar 2024, baya ga gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, tare da wasu gwamnoni biyar ne aka tsayar da su a matsayin gwarazan gwamnonin shekara. Bala Mohammed na Bauchi; Fasto Umo Bassey Eno na Akwa Ibom; Dr Peter Ndubuisi Mbah na Jihar Enugu; Mallam Umar A. Namadi na Jihar Jigawa da Ademola Nurudeen Jackson Adeleke na Jihar Osun.

Gwamnonin sun samu karbuwa ne wajen samar da ci gaba mai dorewa, samar da ababen more rayuwa, da sabbin tsare-tsare a jihohinsu.

Tsohon gwamnan Jihar Edo, Sanata Adams Oshiomhole (CON) ya lashe kyautar gwarzon dan siyasa na shekara saboda rawar da ya taka a siyasar Jihar Edo inda ya jagoranci yakin neman zaben da ya kai ga zaben gwamna Monday Okpehbolo, da kuma neman ci gaban dimokradiyya a Nijerita.

Benedict Peters, wanda shi ne ya kafa kuma shugaban kamfanin AITEO, ya lashe kyautar gwarzon dan kasuwa na shekara, saboda zuba jari mai yawa a fannin hakar ma’adanai da makamashin ruwa a Afirka, yayin da Dame (Dr) Adaora Umeoji, GMD/Shugaba ta Bankin Zenith Plc, ta lashe kyautar gwarzuwar bankin shekara saboda rawar da ta taka wajen kawo sauyi a harkar banki.

Babban Kwanturolan Hukumar Kwastam, Alhaji Bashir Adewale Adeniyi (MFR), ya zama gwarzon ma’aikacin gwamnati na shekara saboda irin jagoranci na musamman da ya yi wajen inganta ayyukan Hukumar Kwastam ta Nijerita (NCS).

Sauran manyan ‘yan kasuwa da suka hada da Shugaban Kamfanin NORD Automobiles Ltd, Oluwatobi Ajayi, shi ne ya lashe kyautar gwarzon shekara na kamfanoni masu zaman kansu, yayin da Bamanga Usman Jada, Manajan Darakta kuma Shugaba na Hukumar Kula da Yankin Mai da Gas, ya lashe kyautar Shugaba na Gwarzon Shekara a bangaren Jama’a.

A cikin wasu nau’o’in kyaututtuka, ABSATEL Communications Limited ta lashe kyautar Kamfanin na Shekarar, yayin da ARCO Engineering Limited ne Gwarzon samar da Mai da Ga Na Cikin Gida na Shekarar.

Za a ba wa Olori Ibie Atuwatse III lambar yabo ta Mutum Mafi Tasiri ga al’umma na shekarar saboda namijin kokarin da ya yi wajen daukar matakan ilimi da kiwon lafiya.

OPAY ta lashe lambar yabo ta kamfanin Fintech na shekara saboda inganta hada-hadar kudi a Nijerita, yayin da bankin Alternatibe ya samu lambar yabo ta Innobatibe of the Year saboda aikinsa na farko a fannin banki na zamani.

Ministan Muhalli Balarabe Abbas Lawal, za a karrama shi ne a matsayin Gwarzon Mutum mai Tasiri Tajen Ayyukan Tsaftace Muhalli saboda yadda ya jagoranci inganta manufofin muhalli da magance sauyin yanayi.

Kyautar kwararren matashin dan’adam na shekarar 2024 zai je kungiyar ENACTUS daga Jami’ar Joseph Sarwuan Tarka, Makurdi. An zabe su ne don habaka kima da dorewa. Terra Cube zai karbi kyautar Samfurin Sanadari dandano Na Shekara don sabunta hanyoyinsa a cikin rayuwa mai dorewa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Gwaraza Karramawa ya lashe kyautar gwarzon shekara saboda lambar yabo ta na shekarar

এছাড়াও পড়ুন:

Jihar Jigawa Ta Amince Da Karin Kasafin Kuɗi Na Naira Biliyan 75 Na Shekarar 2025

Gwamnatin Jihar Jigawa  ta amince da ƙarin kasafin kuɗi na Naira Biliyan 75 na shekarar 2025, ga gwamnatin jiha da kuma ƙananan hukumomi 27.

Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan zaman majalisar da aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse, babban birnin jihar.

Ya bayyana cewa, wannan ƙarin kasafin kuɗi ya samo asali ne daga ƙarin kuɗaɗen shiga domin biyan buƙatun kuɗaɗen da suka taso, da kuma ƙarfafa manyan fannoni da za su kawo ci gaba mai ɗorewa a faɗin jihar.

Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce, majalisar ta amince da Naira Biliyan 58 ga gwamnatin jiha da kuma Naira Biliyan 17 ga Kananan Hukumomi 27, wanda ya shafi kashe-kashen kudade na yau da kullum da kuma manyan ayyuka.

Ya ce, wannan ƙarin kasafin kuɗin zai inganta ayyuka da tsare-tsare da ake gudanarwa a muhimman fannoni irin su ilimi, kiwon lafiya, ababen more rayuwa, noma da sauran muhimman ayyukan ci gaba.

Sagir ya ƙara da cewa, za a mika ƙarin kasafin kuɗin ga Majalisar Dokokin Jihar domin tattaunawa da amincewa da shi, kamar yadda kundin tsarin mulki da ka’idojin kasafi suka tanada.

Kwamishinan ya ƙara jaddada cewa, wannan mataki ya nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen gudanar da mulki bisa gaskiya da adalci, da kula da kuɗaɗen jama’a yadda ya dace, da kuma tabbatar da samar da ingantattun ayyuka ga al’ummar jihar baki ɗaya.

 

Usman Muhammad Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwara ETF Ya Dauki Nauyin Karatun Fitattun Dalibai A Matakin Sakandare
  • Lakurawa Sun Hallaka Jami’in Kwastam A Jihar Kebbi
  • Jihar Jigawa Ta Amince Da Karin Kasafin Kuɗi Na Naira Biliyan 75 Na Shekarar 2025
  • ‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja
  • ALGON ta karrama Gwamna Buni da lambar yabo kan kawo ci gaba a Yobe
  • Najeriya Na Asarar Dala Biliyan 10 Bayan Girbi Duk Shekara- Gwamnatin Tarayya
  • NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano
  • An Fara Taron Hukumar Makamashin Nukliya Ta Duniya IAEA Karo Na 69 A Birnin Vienna
  • Gwamnatin Neja Ta Musanta Rahoton Hana Da’awa A Jihar
  •  Dan Kasar Iran Mai Kirkira Ya Sami Kyautar Yabo A Kasar China