Aminiya:
2025-04-30@19:23:36 GMT

Zaɓen 2027: Me ya sa jam’iyyu ke neman tabarrakin Buhari?

Published: 20th, April 2025 GMT

Da alama tsohon Shugaban Kasar Nijeriya, Muhammadu Buhari, yana nema karbe kambun ɗaukaka da ’yan siyasa a baya suka riƙa bai wa tsofaffin shugabannin ƙasar nan biyu, Janar Ibrahim Badamasi Babangida da kuma Cif Olusegun Obansanjo, wajen neman tabarrakinsu musamman a lokacin da zabe ya karato a kasar nan.

Buharin wanda ya mulki kasar nan a tafarkin soja da kuma na farin hula daga bayabayan nan, a yanzu haka tauraronsa na haskawa, kuma yana ƙamshin turaren Ɗan goma, inda jiga-jigan ’yan siyasa daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP da SDP da kuma jam’iyyarsa mai mulki ta APC, suke nikar gari takanas zuwa gidansa da ke birnin Kaduna, tare da nuna irin kyakkyawan kusancinsa da su.

Hakan dai na zuwa ne bayan kowanne daga bangarorin biyu — ’yan adawa da Jam’iyyar APC mai mulki wadda Shugaban Tinubu ke shugabanci a karkashin inuwarta — babu wanda bai yi ta dora laifin matsalolin da kasar nan ke ciki da mulkin Buhari ba, bayan saukarsa daga kan mulki, amma ba tare da ya tanka musu ba.

Ya zama sabuwar amarya

Buhari wanda bayan saukarsa daga mulki ake ganin tamkar ya yi adabo da al’amuran siyasa, sannu a hankali tasirinsa na sake bayyana a fagen, inda yanzu ɓangarorin daban-daban ke rububin neman tabarrakinsa, ko a kalla su nuna kusancinsa da shi.

Na farko a cikin jerin wadanda suka fara nuna alfaharinsu da Buhari, shi ne abokin alkarasa wato tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i, wanda ya sauya sheka zuwa Jam’iyyar SDP.

Bayan nan sai tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, wanda ya jagoranci wasu gaggan ’yan siyasa zuwa gidan Buharin — ciki har da El-Rufa’i da kuma tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, inda ya bayyana ziyarar a matsayin ta gaisuwar Sallah.

Tuni dai aka fara rade-radin cewa, abokan tafiyar tsohon shugaban ƙasar a tsohuwar Jam’iyyarsa ta CPC, suna shirin ficewa daga jam’iyya mai mulki ta APC.

A yayin da Atiku ya yi ƙoƙarin nesanta ziyarar tasa da siyasa, amma bayanin da El-Rufa’i ya yi a shafinsa na sada zumunta ya bar baya da ƙura, inda a cikin na ba’a ya ce bai kamata ba abokan hamayyarsu, su tayar da hankali a kan ziyarar tasu, kasancewar ba su da wani tasiri da ya rage masu a siyasa.

Gabanin ziyarar hadakar mambobin jam’iyyun adawa da Atiku ya jagoranta, akwai wadda Kungiyar Gwamnonin APC a karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, ta kai wa Buharin.

Wata ziyarar da ta ƙara jan hankalin masu sa ido a kan abin da kan kai ya kawo ita ce wadda ’yan majalisar gudanarwa ta Jam’iyyar APC da shuganta na kasa, tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ya jagoranta zuwa gidan Buharin ’yan sa’o’i kalilan bayan ziyarar su Atiku.

An ruwaito Ganduje na bayyana ziyarar ’yan adawar a matsayin marar tasiri wajen sauya matsayar Buhari daga matakin ci gaba da kasancewarsa a APC.

Haka kuma a cikin watan Ramadan dan shugaban kasa Tinubu, wato Seyi, ya ziyarci Buhari tare da wasu jagororin siyasa a Arewacin Najeriya da ya zama abin ce-ce-ku-ce a yankin.

Ziyarar ’yan adawa ta girgiza APC — Masani

Wani mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum, Mallam Shamsuddin Ibrahim, ya bayyana ziyarar da Ganduje ya jagoranci kai wa Buharin a matsayin alamar jin tsoron rasa yankin Arewa, wanda ya fi bai wa Shugaba Tinubu kuri’u a zaɓen da ya gabata na shekara ta 2023.

Ya ce ziyarar su Ganduje, “ta fi kama da jin fargaban rasa yankin fiye da na nuna dangantaka ko girmawa ga tsohon shugaban kasar kamar yadda jagororin jam’iyyar ta APC ke nunawa a matsayin dalilin yin ta.

Jam’iyyar na nuna wa duniya cewa Buhari na da tasiri a siyasa bayan a baya sun nisanta kansu da manufofin gwamnatinsa.”

Mallam Shamsuddin ya ce, “A kokarin ’yan siyasa na cigaba da kasancewa ko kaiwa ga karagar mulki, al’ummar kasa ne ke dandana ukuba,” sannan ya bayyana ’yan siyasan a matsayin wadanda ke karyata kansu da kansu.

Ya ce “Hakan ya sake nuna wa al’ummar Najeriaya cewa akidar siyasar Najeriya ta wucin gadi ce kawai, inda ra’ayinsu ke sauyawa kan abin da zai dadada masu.

“A daukacin ziyarar da aka kai wa Buharin, ya kasance a hali na natsuwa tare da rike bakinsa, watakila ma cike da mamakin yadda masu sukar sa suka rikide zuwa masu neman tabarrakinsa.”

Dalilin da ’yan adawa ke bukatar Buhari

Shi ma da yake tsokaci a kan rububin ziyartar Buharin, wani jigo a jam’iyyar adawa ta PDP, Malam Umar Sani, ya ce hadakar jam’iyyu da Abubakar ke jagoranta na bukatar Buhari saboda, “Na farko, kwashe ’yan barin toshuwar Jam’iyyar CPC da suka bi Buharin zuwa Jam’iyyar APC mai mulki.

“Wannan raunana APC sannan ya karfafa nasu bangaren. Sannan abu na biyu shi ne har yanzu Buhari na da karfin fada a ji a yankin Arewa.”

Umar Sani wanda a baya ya kasance mai taimaka wa tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Muhammad Namadi Sambo, kan al’amuran yada labarai, ya ce, “Har yanzu Buhari na da tasiri a siyasance a yankin Arewa duk da raguwar hakan da ake ganin ya fuskanta bayan mulkinsa na shekara takwas.”

“A bangarenta, APC na yi wa Buhari tuni kan sadaukarwar da ta yi masa da ta ba shi nasara a zaben da ya kai shi ga wa’adin mulinsa na farko a shekarar 2015, da kuma wanda ya kai shi ga wa’adi na biyu a shekara ta 2019, inda za ta bukaci saka alheri da alheri,” in ji Malam Umar Sani.

Ya ce duk da cewa Buhari ya yi ta samun masu kai masa ziyara tun gabanin ya taso daga mahaifarsa ta Daura bayan saukarsa daga mulki, dawowarasa Kaduna da ke da kusanci da cibiyar mulki – Abuja, na sanar da shi cewa ya shirya fuskantar komawa lamuran siyasa gadan-gadan.

Tasirin Buhari na musamman

Umar ya ce, “Duk da cewa har yanzu tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida na da tasiri a siyasa, tasirin Buhari na musamman ne.

“In banda takarar da ya yi da dan uwansa daga yankin Arewa Marigayi Malam Umaru Musa Yar Aduwa, Buhari ya samu zunzurutun kuri’u har miliyan 12 a zabuka daban-daban a baya, lamarin da ke nuna cewa yana da magoya baya.”

Masu sa ido a kan abubuwa da kan je ya zo na da ra’ayin cewa ’yan Najeriya da dama musamman daga yankin Arewa, da a baya suka soki gwamnatin Buhari gabanin saukarsa daga mulki, sun fara gwammace mulkinsa a kan na Tinubu, wanda kasa da shekara 2 da hawansa mulki, amma ake ganin manufofin gwamnatsinsa sun jawo matsananci yanayin tattalin arzikin kasa.

A tsokacinsa a kan lamarin, Dokta Sa’idu Dukawa ya ce ziyarar da ake kaiwa Buharin na nuna cewa harkar zaben shekara ta 2027 ta fara kankama.

Dakta Dukawa wanda babban malami ne a Jami’ar Bayero ta Kano ya ƙara da hasashen cewa ziyarce-ziyarcen za su kuma fadada zuwa wajen wasu tsoffin shugabannin ƙasar nan kamar Cif Obasanjo, da kuma takwaransa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Abdullahi Umar Ganduje Atiku Abubakar Muhammadu Buhari a yankin Arewa saukarsa daga Gwamnan Jihar a jam iyyar

এছাড়াও পড়ুন:

Ma’aikata 240 na karɓar albashi biyu, wasu 217 na amfani da lambar BVN ɗaya a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta gano ma’aikatanta 240 da ke ƙarɓar albashi sau biyu a duk wata, da wasu 217 da ke amfani da lambar tantance asusun banki (BVN) guda ɗaya.

Wani mai magana da yawun gwamnati, Dakta Sulaiman Wali Sani, ya gaya wa manema labarai a ranar Lahadi cewa an gano wannan badaƙalar ce a yayin da ake tantance tsarin biyan albashin gwamnati.

Dr. Sani ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi alƙawarin biyan ma’aikata daidai kuma akan lokaci, kuma gano waɗannan matsalolin wani ɓangare ne na gyara al’amura.

Ya ce sun duba bayanan ma’aikata ta hanyar amfani da hotunan yatsa a matakin jiha da ƙananan hukumomi.

“Tsohuwar hanyar biyan mutane tana da matsaloli. Mun gano ma’aikata 240 suna karɓar albashi sau biyu kuma mutane 217 suna amfani da BVN ɗaya, wanda zai iya nufin akwai ma’aikatan bogi ko kuma mutane suna amfani da BVN na wani,” in ji Dakta Sani.

Ya kuma ce ma’aikata 1,335 ba su zo don a tantance su ba a tsawon fiye da watanni shida, wanda ya sa suke tunanin ko waɗannan mutanen da gaske suna aiki da gwamnati.

Alhaji Umar Idi, wanda ya duba biyan kuɗin ƙananan hukumomi, ya ce sun gano sunaye 247 da babu tabbaci a kansu. Waɗannan sun haɗa da mutanen da suka yi ritaya, waɗanda suka mutu, ko kuma waɗanda aka ci gaba da biyan su ba tare da izini ba bayan lokacin barinsu aiki.

“Daga cikin waɗannan ma’aikata 247, takwas ne kawai suka zo don tabbatar da cewa har yanzu suna aiki. Za a goge sauran sunaye 239, wanda zai rage wa gwamnati asarar naira miliyan 27 a duk wata,” in ji shi, yana mai cewa za a mayar da kuɗaɗen da aka samu ga asusun gwamnati.

Dakta Sani ya ce gwamnati ba ta ƙoƙarin hukunta kowa ba, kawai dai tana gyara tsarin ne don ma’aikata na gaske da ’yan fansho su ci gaba da karɓar haƙƙoƙinsu ba tare da wata matsala ko yanka ba bisa ƙa’ida ba.

“Tun lokacin da Gwamna Abba ya fara aiki, ya tabbatar da cewa ana biyan ma’aikatan gwamnati da ’yan fansho a kan lokaci, ba tare da ɓoyayyun cire-cire da aka riƙa yi a baya ba,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa yanzu da suke tsaftace tsarin biyan kuɗi, ma’aikata su yi tsammanin samun biyan kuɗi mafi inganci a gaba.

Gwamnati ta ce za ta ci gaba da magana da duk masu ruwa da tsaki don tabbatar da cewa an magance duk matsalolin kuma jama’a sun sake amincewa da ayyukan gwamnati.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tsoffin ma’aikatan NECO na neman a biya su bashin haƙƙoƙinsu
  • Rawar da Arewa za ta taka a Zaɓen 2027
  • Dalilin da manyan ’yan siyasa ke barin NNPP — APC
  • Wang Yi: Neman Sulhu Da Ja Da Baya Riba Ne Ga Masu Son Cin Zali
  • Gwamna Namadi Ya Nada Aisha Mujaddadi Sabuwar Shugabar Hukumar InvestJigawa
  • Nijeriya Na Ke Yi Wa Biyayya Ba Wani Ko Jam’iyya Ba – El-Rufai
  • Kotu Ta Kori Ƙarar Neman Diyyar N1bn A Kan Buhari Da Emefiele Kan Sauya Fasalin Naira
  • Shekara 10 ina sayar da sassan jikin ɗan Adam — Wanda ake zargi
  • Ma’aikata 240 na karɓar albashi biyu, wasu 217 na amfani da lambar BVN ɗaya a Kano
  • NAJERIYA A YAU: “Dalilin da muke sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki”