Yemen Ta Cilla Makamai Kan Kataparen Jirgin Ruwa Mai Daukar Jiragen Yaki Na Amurka A Tekun Red Sea
Published: 18th, March 2025 GMT
Majiyar gwamnatin kasar Yemen ta basa sanarwan kai hare-hare har sau biyu kan kataparen jirgin ruwa mai daukar jiragen yaki na kasar Amurka dake cikin Tekun Red sea, wato USS Harry Truman. Inda suka cilla makami mai linzami guda da kuma jiragen yake wadanda ake sarrafasu daga nesa kan jirgin.
Har’ila yau sojojin yamen sun ce sun kaiwa wasu sojojin Amurka hare-hare da jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa duk a cikin sa’oi 48 da suka gabata.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin sojojin kasar Yemen Burgediya Yahyah Saree ya na fadar haka a safiyar yau talata, ya kuma kara da cewa sojojin kasar za su ci gaba da maida martani da kuma hana jiragen ruwan kasashen da take gaba da su a tekun maliya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Falasdinawa 13 Ne Suka Yi Shahada Wasu Da Dama Suka Jikkata A Hare-Haren Sojojin Mamayar Isra’ila A Gaza
Falasdinawa 13 ne suka yi shahada da suka hada da yara kanana da mata a hare-haren bama-bamai da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan gidaje da matsugunan Falasdinawa a Gaza
Sojojin mamayar Isra’ila sun ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza da asubahin ranar Talata, inda suka kai hare-hare kan gidajen fararen hula da matsugunan ‘yan gudun hijira. Hare-haren sun yi sanadiyyar shahadan fararen hula 13 da suka hada da yara da mata, yayin da wasu da dama suka jikkata a wasu munanan hare-hare ta sama da aka kai a yankuna daban-daban na zirin.
Asibitin Al-Shifa ya sanar da shahadan Falasdinawa hudu ciki har da wani jariri, sakamakon harin da jiragen yakin sojin mamayar Isra’ila suka kai a wani gida da ke kusa da kasuwar Carrefour a unguwar Tel al-Hawa da ke kudu maso yammacin birnin Gaza. A halin da ake ciki kuma, asibitin Baptist ya sanar da shahadan Falasdinawa biyu tare da jikkata wasu sakamakon harin da aka kai a gidan Khader al-Jamasi da ke kusa da masallacin al-Ibki da ke unguwar al-Tuffah da ke gabashin birnin.
Wata majiyar lafiya a asibitin Al-Awda da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat ta bayyana cewa: Hari ya jikkata wasu fararen hula a lokacin da makarantar Abu Helu al-Sharqiya da ke dauke da ‘yan gudun hijira a sansanin ‘yan gudun hijira na al-Bureij da ke tsakiyar zirin Gaza ta fuskanci hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila ta kai kai tsaye, lamarin da ya haifar da firgici ga iyalan da suka rasa muhallansu.