Leadership News Hausa:
2025-09-18@00:43:32 GMT

Bukatar Kafa Dokar-ta-baci Kan Yaduwar Jabun Magunguna

Published: 7th, March 2025 GMT

Bukatar Kafa Dokar-ta-baci Kan Yaduwar Jabun Magunguna

A kasuwar Ariaria da ke Aba, NAFDAC, sun gano jabun magunguna da kudinsu ya kai na miliyoyin Naira.

Bugu da kari, a kasuwar Idumota da ke a jihar Legas, NAFDAC sun garkame Shanguna sama da 3,000 bayan sun gano Shagunan shake da jabun magunguna.

A kasuwar kan Gadar Onitsha, nan ma Hukumar ta sun kama manyan motoci goma shake da jabun magungana, inda a bayan kamen dilolin magungunan suka yi yunkurin bai wa jami’an na NAFDAC cin hancin Naira miliyan 135.

Har ila yau, a kasurgumar kasuwar Cemetery da ke Aba, nan ma NAFDAC ta kama tare da kwace jabun magunguna da kudinsu ya kai na sama da Naira miliyan biyar.

Bisa batun gaskiya, irin wannan bakar hada-hadar jabun magunguna, ya wuce maganar alkaluma, domin kuwa, abinda yafi dacewa, shi ne, yankewa irin masu wannan bakar harkalar hukuncin ta hanyar rataye su, duba da yaddda suka kara jefa rayuwar marasa lafiya a cikin wata ukuba ta hanyar sayar da jabun magunguna.

Abinda ya kara jefa fargaba a zukakan jama’a ne, shi ne, kan irin hanyoyin da irin wadannan bata garin ke bi wajen sarrafa jabun magungunan, musamman ganin yadda suke da kayan aikin da suke sake sarrafa magungunan da suka riga suka lalace.

Kazalika, a wani gwaji da NAFDAC kan mangunan yara, da wadannan bata garin ke sarrafawa suke kuma sayar da shi, kan farashi mai sauki, NAFDAC bata iya gano wani abu da ba daidai ba.

Wannan rashin iya ganowar na NAFDAC ya nuna yadda sarrafa magungunan na jabu, sun jima suna yin sanadiyar mutuwar yara, ba tare da yin amfani da bakin Bindiga ba.

Wannan matsalar dai, ba wai kawai ta tsaya kan daidaikun ‘yan kasuwa masu sarrafa jabun magungunan bane, domin abu ne, da ya karade daukacin miyagun masana’tun da ke da ke sarrafa jabun, inda suka fakewa a matsayin Shaguna suna cikin Karensu babu babbaka ciki har da sarrafa jabun magunguna na yakar cuta mai karya garkuwar jiki.

A yayin samamane na NAFDAC, sama da haramtattun masana’antu 240 da ake sarrafa jabun magunguna aka bankado a kasuwar Cemetery.

A ra’ayin mu wadannan matakan da aka dauka na kai samame a kasuwannin bai isa ba, duba da cewa, hukuncin shigo da kwayar maganin Tramadol zuwa cikin kasar nan ta haramtacciyar hanya, shi ne, kodai yin shekaru biyar a gidan gyran hali ko kuma biyan tararar Naira 250,000, domin kuwa dole mu mayar da hankali wajen kare kiwon lafiyar yan kasar nan.

Mojisola Adeyeye, Darakta Janar ta kasa ta Hukumar NAFDAC, ta bukaci da a rinka yanke hukuncin kisa ga masu sarrafa jabun magunguna, duba da yadda suke jefa rayuwar alumma a cikin matsala da kuma jefa tsarin kiwon lafiya a cikin barazana.

Yawan samun irin wadannan kasuwannin na sarrafa jabun magungunnan duk da kokarin da NAFDAC ke kan yin a rage sarrafa jabun magungunan akalla zuwa kaso biyar a cikin dari a 2025, hakan na ci gaba da zama wani babban kalubale ga hukumar, musamman duba da yadda ake ci gaba da samun karuwar a kasar.

Wani abin bakin ciki shi ne, yadda halastatun kungiyoyin dilolin sarrafa magunguna kamar irin su, EKUMI Plaza Patent Medicine, suma suka bi sahu wajen shiga kazamar hanyar ta hada-hadar kasuwancin jabun magunguna da suka kai na Naira miliyan 50.

Karafafa yakar wannan lamarin bai wadatar ba, domin kuwa kamata ya yi a yiwa fannin rabar da magunna na kasar nan garanbawul baki daya.

Ci gaba da samun wanzuwar irin wadannan kasuwannin na sayar da jabun magunguna na kara haifar da gibi a bangaren tsarin kiwon lafiyar kasar.

Ya zama wajbi Gwamnatin Tarayya ta sake yin nazari kan bayar da takardun fito na shigo da magunguna cikin kasar, musamman domin a tallafawa halastattun masana’atun cikin gida da ke sarrafa magungunan.

Ya kuma kamata a kara karfafa shirin Inshorar kiwon lafiya na kasa NHIS, wanda hakan zai taimaka a rinka samar da ingantatun magunguna kuma a cikin farashi mai sauki, wanda hakan kuma zai sanya, durkushewar bakar kasuwar ta sayar da jabun magunnan a kasar.

Kazalika, akwai bukatar a rinka ilimantar da alummar gari kan illar irin wadannan jabun magungunan.

Bai kamata bangaren Shari’a ya rinka yin hukunci mai sauki ga masu wannan dabi’ar ba, musamman duba da yadda kawai irin masu wannan dabi’ar da suka shiga hannun hukuma ake cin su tara ‘yar kadan.

Dole kutuna sun tilatsa tsauraran hukunci, ciki har da yanke hukunci zaman gidan Yari da kuma yanke hukuncin haramtawa wadanda aka kama suna sarrafa jabun magunguna kara yin duk wata sana’a da ta shafi sarrafa magunguna.

Yawon da irin wadannna jabun magungunan a cikin alumma, tamkar yankewa iyalai hukuncin kisa ne.

Bugu da kari, ya zama wajbi daukacin ‘yan Nijeriya su tashi tsaye mu yi aiki tukuro domin kawo karshen wannan bakar dabi’ar, mu kuma jajirce har sai mun ga an a sayar da ingantatun magunguna a kasar.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: sarrafa jabun magunguna sarrafa magunguna irin wadannan

এছাড়াও পড়ুন:

Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Aka Yi Wa Sharrin Safarar Ƙwayoyi

Hukumar NDLEA ta bayyana cewa wata ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi ce a filin jirgin sama na Kano ta boye jakunkunan ƙwayoyi a cikin kayan matafiyan.

An kama shugaban ƙungiyar, Ali Abubakar Mohammed (wanda aka fi sani da Bello Karama), tare da wasu abokan aikinsa.

Hukumar ta ce mutanen ukun ba su da laifi kuma an zalunce su ne kawai.

An saki su ne bayan bincike da kuma ƙoƙarin diflomasiyya na tsawon makonni.

Lamarin ya tayar da hankali kan tsaro a filayen jirgin sama a Nijeriya da yadda masu aikata laifuka ke amfani da fasinjoji marasa laifi.

Hukumar ta ce za a ɗauki ƙarin matakai don hana faruwar irin wannan lamari.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yakin Haraji Da Cinikayya Ba Zai Gurgunta Fifikon Da Sin Ke Da Shi A Fannin Raya Masana’antun Sarrafa Hajoji Da Kasar Ta Gina A Tsawon Lokaci Ba
  • Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers
  • Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas
  • Yanzu-yanzu: Shugaba Tinubu Ya Ɗage Dokar Ta-ɓaci A Jihar Ribas
  • Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Aka Yi Wa Sharrin Safarar Ƙwayoyi
  • Tinubu Ya Taya Amusan Da Gumel Murnar Samun Nasarori A Ɓangarori Daban-daban
  • Bayanin Bayan Taron Doha Ya Yi Kira Da A Kafa Runduwar Hadin Gwiwa Ta Kare Kai
  • Kundin Bajinta na Guinness ya taya Hilda Baci murna
  • Tattalin Arzikin Sin Ya Samu Ci Gaba Ba Tare Da Tangarda Ba A Watan Agusta
  • Dole sai mun tantance wa’azi kafin a yi —Gwamnan Neja