Za a Dawo da Wurin Sarrafa Iskan Shaka Oxygen nan Badadewa Ba – AKTH
Published: 13th, March 2025 GMT
Hukumar gudanarwar asibitin koyarwa na Aminu Kano ta ce ana kokarin ganin an dawo da ayyukan da masana’antar iskar Oxygen da asibitin ke yi.
A cewar Mataimakin Daraktan sashen (Biomedical/ kuma Shugaban Kwamitin Kula da Oxygen), Engr Ahmed Usman a madadin Hukumar, an sanya hannu kan wata yarjejeniya ta fahimtar juna tsakanin asibitin da Dodams Medical Equipt don kula da aikin na tsawon shekaru 2.
Ya bayyana cewa, a watan Janairun wannan shekara ne aka yi duk wani shiri da kuma biyan kudin jirgi, amma saboda hutun karshen shekara da Kamfanoni suka yi, an samu tsaiko wajen samar da wasu sassa musamman na’urar gudanarda aikin, wanda ya iso a ranar Litinin 10 ga Maris, 2025.
Ya ci gaba da cewa, tuni aka fara yi wa na’urar samar da iskar Oxygen aiki kamar yadda ya faru a jiya, wanda ya rage kawai na’urar kwampreso da kuma Oxygen buster, wadanda ke kan aiki.
A halin da ake ciki, a cikin wannan lokacin jirar Hukumar Kula da Asibitin ta fitar da iskar Oxygen a wani wuri musamman daga Kamfanin Loquat, kamar yadda ake yi a wasu asibitoci.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala
Hukumar Tace Fina-Finai da Dab’i ta Jihar Kano ta haramta shirya duk wata muƙabala tsakanin mawaƙan yabon Annabi (S.A.W), tare da gayyatar mawaƙa Usman Maidubun Isa da Shehi Mai Tajul’izzi su bayyana a gabanta.
Hukumar ta kuma gayyaci mawaƙan ne tare da sauran waɗanda suka jagoranci muƙabalar da fitattun mawaƙan biyu suka yi ranar Litinin, da su bayyana a gabanta cikin sa’o’i 24.
Kukan al’umma kan lalacewar hanyar Dukku DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin TinubuHakan na zuwa ne ƙasa da kwana ɗaya bayan ɓullar wata muhawara da aka yi tsakanin Usman Maidubun Isa da Shehi Mai Tajul’izzi kuma ta karade shafukan sada zumunta, wacce hukumar ta bayyana a matsayin karya dokokin aikinta.
Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha ne ya sanar da hakan ranar Talata, inda ya ce ɗaukar matakin wani yunƙuri ne na tabbatar da zaman lafiya, daidaito da bin doka tsakanin mawaƙan nishaɗi da na addini.
El-Mustapha, a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar, ya kuma ce an haramta duk wata nau’in muƙabala daga mawaƙan addini a jihar ba tare da izinin hukumar ba.
A yayin da yake ƙaddamar da wani kwamitin bincike da shugaban hukumar ya naɗa karkashin Daraktan Ayyuka na Musamman a hukumar, Isah Abdullahi, El-Mustapha ya umarci waɗanda aka gayyatar da su bayyana a gaban kwamitin domin amsa tambayoyi.
Hukumar ta ce shirya irin waɗannan muhawara ba tare da izininta ba ya saɓa doka kuma zai iya jawo hukunci mai tsanani ga wanda suka karya.
Hukumar ta kuma jaddada ƙudirinta na ci gaba da kula da ayyukan mawaƙan da masu nishaɗantarwa a faɗin jihar tare da yin kira ga jama’a da su zauna lafiya sannan su ci gaba da ba ta haɗin kai a ayyukanta.