Miji ya yi wa matarsa saki 3 a ofishin ’yan sanda
Published: 21st, April 2025 GMT
Wani magidanci ya ɗankara wa matarsa saki a ofishin ’yan sanda bayan an kama ta a wani otel.
Wani jami’in tsaro ya bayyana cewa an kama matar ce a yayin wani samame da ’yan sanda suka kai maɓoyar dillalan miyagun ƙwaya da ’yan sara-suka a wasu otel-otel a garin Minna.
Ya bayyana cewa sai bayan da aka kawo matar ofishin ’yan sanda, a yayin bincike suka gano cewa matar aure ce, bayan da suka tuntuɓi ’yan uwan mutanen da aka kama.
Ya ce, “Sakamakon yawaitar yadda matasa suke tayar da zaune tsaye ne mataimakin gwamna Kwamred Yakubu Garba, ya umarci jami’an tsaro su ɗauki mataki a kansu.
Yadda uba da ɗansa da wani ango suka rasu a bakin aiki a Bauchi Fafaroma Frasncis ya rasu yana da shekaru 88“Shi ne muka kai samame, muka kama mutanen da ake zargi, cikinsu har da mata. Abin mamaki sai ga wani mutum ya zo, cewa ɗaya daga cikin matan da muka kama mai ɗakinsa ce, kuma nan take ya yi mata saki uku.
“Ba mu san cewa matar aure ba ce, kuma ba mu da masaniyar abin da ya kai ta wurin, domin ’yan sanda ba su kammala bincike ba lokacin da mutumin ya je ya ba ta takarda a ofishin ’yan sanda.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: ƙwayoyi matar aure
এছাড়াও পড়ুন:
Shekara 10 ina sayar da sassan jikin ɗan Adam — Wanda ake zargi
Wani wanda ake zargi da safarar sassan jikin ɗan Adam ya shaida wa jami’an tsaro cewa ya shafe sama da shekara 10 yana sayar da sassan jikin mutum don samun kuɗi.
Dubun mutumin sun cika ne a ranar Asabar din da ta gabata inda sojoji suka kama shi a yankin Kulanla Odomoola da ke Jihar Ogun.
A furucinsa da ya amsa laifin, wanda ake zargin ya amince da sayar da sassan jikin mutum ga masu buƙata don samun kuɗin shiga.
“Na dogara ne da sayar da sassan jikin mutum tsawon shekaru 10 da suka gabata. Yawancin sassan da nake sayarwa ina tono su ne daga sabbin kaburbura a makabartu, yayin da wasu kuma nake samun su daga gawarwakin da aka watsar a gefen hanyoyi,” in ji shi.
Aminu Bayero ya naɗa Sanusi a matsayin Galadiman Kano Dukan farar hula saboda sanya kayan sojoji laifi ne — Janar Chibuisi NAJERIYA A YAU: “Dalilin da muke sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki”Wanda ake zargin, wanda ya amsa laifinsa ga wani taron jama’a da suka yi yunƙurin kashe shi kafin sojoji su cece shi, ana zargin yana kan hanyarsa ne na kai wani sassan jiki ga wani mai siye lokacin da aka kama shi.
Daga nan aka miƙa wanda ake zargin ga ’yan sanda a yankin Noforija don ƙarin bincike da kuma gurfanar da shi a gaban kotu.
Laftanar Kanar Olabisi Olalekan Ayeni, Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojin Najeriya ta 81, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayan kama wanda ake zargin daga baya an miƙa shi tare da kayayyakin da aka samu a wurinsa, ga ’yan sandan Najeriya don ƙarin bincike da kuma gurfanar da shi a gaban kotu.
“Sojojin sun ceto wanda ake zargin daga wani taron jama’a da suka yi yunƙurin kashe shi,” in ji shi.