Leadership News Hausa:
2025-11-02@19:45:31 GMT

Abubuwan Da Za Su Iya Kawo Cikas Ga Bukukuwan karamar Sallah

Published: 29th, March 2025 GMT

Abubuwan Da Za Su Iya Kawo Cikas Ga Bukukuwan karamar Sallah

Tsadar rayuwa tun daga wancan lokacin ne bayan cire tallafin mai,da kwana daya kawai zuwa biyu sai rayuwar wasu dole ta fara sauyawa,kaya ko kayayyakin da ake saya a farashi na kashi 75 zuwa 100 sai abin ya koma farashin wasu har sai da,ya kai kashi 200 zuwa kashi 300 kai wani abin ma, har ya zarce haka,kuma kamar yadda Hausawa suka ce dole ce kanwar na ki ta sa hakan ta kasance,wannan kuma haka ne.

Dole ce tasa haka saboda har an kai ga ganin abinda ya cirewa Buzu nadi wato wahala ke nan.Kuma dole ne cin kasuwa da makiyi wasu abubuwan abin ba,a  iya cewa komai sai dai ayi gum da Baki kawai.

Matsalar tsaro

Ko shakka babu lamarin tavarvarewar tsaro ba karamin koma baya ya kawo ba na lamarin zamantakewa tsakanin al’umma abu tun daga wannan unguwa zuwa waccan har,ta kai ga daga wannan babban gari ma zuwa wancan har ta kai ga daga wannan Jiha zuwa waccan.Irin halin da al’umma suka tsinci kansu ke nan lamarin da ya kan yi tafiyar Kura yadda take gaba sai ta koma baya. Arewa ta sassa daban- daban tana fama da matsalar data shafi tsaro  tunda kuwa ana yin garkuwa lokaci,anan matafiya wasu Jihohi na sashen Arewa maso yamma kamar Kaduna, Katsina,Zamfara,Sakkwato,da kuma Kebbi,masu ta shi daga Abuja zuwa gida wasu suna kan hanyar tasu ake tsaida su a kwashi mutane kamar Dabbobi ayi cikin daji dasu,kai har ma,ta kai ga mutane ko,a gidajensu suke basu tsira ba ana iya zuwa kowane lokaci ayi awon gaba dasu sai kuma yadda Allah yayi.Yayin  da wasu suna dawowa wasu kuwa sun tafi ke nen sai dai  aji labarin an kashe su,wasu ko ma an kai kudin fansar ba,za’a sake su ba.Irin hakan ce ta sa wasu yanzu basu zuwa gida Sallah saboda tsoron aukuwar irin hakan,maimakon hakan sai su yi hakuri su rungumi kaddara ta yin rayuwa kamar irin cikin halin,da suka samu kansu.

Tafiya zuwa yawon Sallah daga wannan unguwa zuwa waccan ko daga wannan gari zuwa wancan,halin da ake ciki yanzu hakan bata yiyuwa ba domin komai ba sai saboda tsoron irin abinda ka iya faruwa gare su,maganar gaskiya yanzu lamarin tsaro ya sa mutane da yawa sun,shiga cikin halin tsoro saboda komai yana iya faruwa a lokacin da ba ayi tsammanin hakan ba.Ba ance babu tsaron bane gaba daya amma su wadannan masu tayar,da zaune tsaye ko ina suna iya zuwa saboda ai suna da wadanda suke basu halin da ake ciki da su kan samu na su kason idan an yi sa’ar dauka da kuma garkuwa da mutane aka kuma biya kudin fansar.

Al’umma da dama basa garuruwan su na asali

Mutane da dama yanzu wasu ma ba Jihar su ta asali suke ba,wasu suna wata Jiha,kai akwai ‘yan Nijeriyar da har yanzu suna kasashen Nijar ko kuma Kamaru,idan ma sun yi sa’ar suna Jihar tasu ne,to su kan kasance ne a wani sansanin ‘yan gudun hijira ne wato wuraren da aka tsugunnar dasu,sanin kowa ne,babu yadda rayuwa za ta yi daidai ga wasu a,irin wadancan wuraren saboda can ma din da akwai nau’oin matsalolin da suke fuskanta a can.Ana iya tunawa shifa sansanin ‘yan gudun hijira wuri ne da aka ware na musamman wanda ake taimakawa nau’oin mutanen da suka fuskanci matsala babu yadda za su iya yi wajen tafiyar da rayuwarsu.Daga karshe sanin kowa ne duk wanda bai garin shi na asali rayuwa Lami yake yin ta domin a matukar takure yake.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: daga wannan

এছাড়াও পড়ুন:

An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano

Mai shari’a Dahiru ya amince da buƙatar, ya kuma ɗage shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Disamba, 2025, domin ci gaba da sauraron shari’ar.

Ƙuli-ƙuli dai nau’in abin ci ne mai taushi da ake yi da gyaɗa, ana soyawa har sai ya zama ƙura-ƙura ta yadda za a ci cikin nishaɗi.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Makarantar Kogi Poly Ta Bankaɗo Masu Ƙirƙirar Takardun Kammala Karatu na Bogi October 31, 2025 Manyan Labarai Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar October 31, 2025 Manyan Labarai NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa October 31, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza
  • Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin Sudan
  • Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
  •  Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada
  • Sanata Sunday Marshall Katung Ya Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar APC
  • An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano
  • ’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi
  • Kotu ta tsige dan majalisar da ya sauya sheka zuwa APC
  • Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare
  • Ana zargin ɗa da kashe mahaifinsa a Kano saboda hana shi ƙara aure