Ɓarayin kekunan ɗinki sun shiga hannu a Borno
Published: 28th, March 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta kama wasu matasa uku da ake zargi da satar kekunan ɗinki guda 19 a cibiyar koyon sana’a ta Dala Lawanti da ke Maiduguri.
A cewar ’yan sanda, wani mai gadi a cibiyar, Kaka Modu Mustapha, mai shekaru 34, ya haɗa baki da wasu matasa biyu – Bukar Mustapha mai shekaru 16 da Ibrahim Mohammed mai shekaru 17 – domin aikata satar a ranar 22 ga wata Maris, 2025.
Kakakin rundunar, SP Nahum Kenneth Daso, ya ce jami’an ’yan sanda daga yankin Bulumkutu, sun samu rahoto game da satar, inda suka gudanar da bincike tare da kama waɗanda ake zargin, ciki har da mai gadin cibiyar.
Ya ce an samu nasarar ƙwato kekunan ɗinki guda shida daga cikin 19 da suka sace, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano sauran guda 13.
SP Daso, ya buƙaci al’ummar jiharda su kasance masu kula tare da kai rahoton duk wani abun zargi ga jami’an tsaro domin daƙile aikata laifuka.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Cibiyar Koyon Sana o i
এছাড়াও পড়ুন:
Rundunar Ƴansanda Ta Kama Gaggan Ƴan Fashi 9 A Kano
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27 Da Birnin Tarayya October 13, 2025
Manyan Labarai Ta’addanci: Ana Fuskantar Ƙarancin Man Fetur A Mali Sakamakon Datse Hanyoyin Shiga Bamako October 13, 2025
Manyan Labarai Tinubu Ya Isa Birnin Rome Don Halartar Taron Tsaro Na Aqaba October 12, 2025