Bam ya kashe mutum 4 da jikkata wasu a Borno
Published: 21st, March 2025 GMT
Aƙalla fasinjoji huɗu ne suka mutu yayin da wasu huɗu suka jikkata sakamakon fashewar wani bam a ƙarƙashin wata motar kasuwanci a ƙaramar hukumar Biu ta Jihar Borno.
Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta tabbatar ta afkuwar lamarin.
Gobara ta kashe ɗan shekara 7 a sansanin ’yan gudun hijira ’Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in FRSC a BenuweMajiyoyin leƙen asiri sun shaidawa Zagazola Makama cewa, lamarin ya faru ne a ranar 19 ga Maris, 2025, da misalin ƙarfe 2:30 na rana a lokacin da wata mota ƙirar Golf 3 ta Wakil Fari ta tashi daga garin Kimba zuwa garin Biu.
Bayan sun isa mahaɗar Sabon Garin Kimba, motar ta taka wata nakiya (IED), wanda ya kai ga fashewa da ta kashe fasinjoji mata uku da fasinja namiji guda nan take.
Majiyar na cewar wasu fasinjoji hudu kuma sun sami raunuka daban-dabam kuma nan da nan an kai su babban asibitin Biu don yi musu jinya.
Daga bisani likitoci sun tabbatar da mutuwar wadancan mutane huɗu sannan aka ajiye su a ɗakin ajiyar gawa na asibitin kafin a miƙa su ga ’yan uwansu don yi musu jana’iza.
Bincike na farko ya nuna cewa ’yan ta’addar ISWAP ne suka dasa waɗannan bama-bamai (IEDs) a tunanin sojoji za su taka.
Jami’an soji sun tabbatar da faruwar hakan, tare da duba ƙarin barazanar da ake fuskanta daga wadannan ‘yan ta’addan don tabbatar da tsaro ga masu amfani da hanya.
Hukumomi sun kuma ƙaddamar da gangamin wayar da kan al’umma kan haɗarin bama-bamai da ba su fashe ba, don kaucewa faruwar lamari irin ya hakan.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Mutum 9 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa
Aƙalla mutum tara ne suka rasu, yayin da wani kwale-kwale ɗauke da fasinjoji 17 ya kife a Jihar Jigawa.
Yawancin fasinjojin da hatsarin ya rutsa da su ’yan mata ne.
Kamfanin NNPCL ya sake haka sabbin rijiyoyin man fetur 4 a Kolmani Samar da makamashi mai tsafta na zamani shi ne fatanmu — GuterresLamarin ya faru ne da ranar yammacin Lahadi, 27 ga watan Yuli, 2025, lokacin da kwale-kwalen ya taso daga ƙauyen Digawa a Ƙaramar Hukumar Jahun zuwa ƙauyen Zangon Maje da ke Ƙaramar Hukumar Taura.
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis.
Ofishin NEMA na Kano, ya bayyana cewa kwale-kwalen ya kife ne a tsakiyar kogin.
Wasu mazauna yankin sun ceto mutum takwas da ransu, sai dai an yi rashin sa’a mutum tara sun riga mu gidan gaskiya.
NEMA tare da haɗin gwiwar Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa (JSEMA), Hukumar Kula da Hanyoyin Ruwa ta Ƙasa (NIWA), da jami’an Ƙaramar Hukumar sun wayar da kan al’umma kan muhimmancin bin ƙa’idojin tsaro yayin tafiya a ruwa.
NIWA, ta kuma raba wa mutanen yankin rigunan kariya na ruwa don kare kansu daga irin wannan hatsari.