Wata Miyar Sai A Makwabta…
Published: 13th, March 2025 GMT
Idan ka dauki bangaren tsofaffi da kananan yara, za ka iya cewa su ne mafi rauni a cikin al’umma. Tsofaffi sun gajiya don haka suna bukatar taimako, yara kanana kuma ba su kawo karfi ba, bisa haka dole suna bukatar madafa. A nan, sai mu ce gwamnatin Sin ta yi tunani mai kyau.
Kundin rahoton ya kuma bayyana cewa, a shekarar 2025 gwamnatin kasar za ta kara zage damtse wajen raya kauyukan dake rabe da birane da gyara gine-ginen da suka tsufa.
Har ila yau, rahoton ayyukan gwamnatin ya bayyana cewa, a bana, gwamnatin kasar ta kudiri aniyar kara yawan kudin tallafin muhimman ayyukan inshorar kiwon lafiya ga mazauna karkara da marasa aikin yi na birane, inda aka kara yawan kudin da yuan 30 ga kowane mutum. Ko tantama babu, tabbas wannan zai kara inganta kiwon lafiyar al’umma musamman marasa karfi.
Bugu da kari, tallafin kiwon lafiyar bai tsaya nan ba, akwai wani kaso na musamman da gwamnatin za ta ware na tallafin kudin kiwon lafiya ga daukacin al’umma a bangaren muhimman bukatunsu inda shi ma aka kara yawansa da yuan 5 ga kowane mahaluki da zai ci gajiya.
Baya ga batun tallafi na zuwa asibiti, gwamnatin ta kuma yi wata farar dabara da za ta kara inganta koshin lafiya ta hanyar sanya gina dandaloli da dakunan wasannin motsa jiki a kusa da gidajen al’umma a cikin kundin rahoton ayyukanta na 2025. Wannan dabara za ta kara inganta kiwon lafiyar al’umma saboda kowa ya san yadda motsa jiki ya zama wajibi ga duk wanda yake son samun koshin lafiya.
Kazalika, da yake zamani na ci gaba da sauyawa ta fuskar komai da komai, gwamnatin kasar Sin ta sha alwashin hanzarta komawa amfani da tsarin biyan kudade na zamani da aka inganta domin kara saukaka hada-hada da harkokin kudade.
Duka wadannan abubuwa an bullo da su ne domin cimma muradun jama’a da kara kula da bukatunsu. A gaskiya ina kwadayin ganin irin wannan tsari a kasashenmu na Afirka, saboda muhimmanta bukatun jama’a alhaki ne da ke rataye a wuyar gwamnati. Ya kamata shugabanninmu su sa himma da kwazo don su raba mu da tunanin “wata miyar sai a makwabta”, a duk lokacin da muka ga yadda ake kula da muradun al’umma a wasu kasashe, musamman kasar Sin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: kiwon lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Za a Yi wa Yara 194,000 Rigakafin Cutar Shan Inna a Karamar Hukumar Birnin Kudu
Karamar hukumar Birnin Kudu dake Jihar Jigawa ta bada tabbacin ci gaba da kulawa da harkokin rigakafi da kiwon lafiya baki daya.
Shugaban karamar hukumar, Builder Muhammad Uba ne ya bada wannan tabbacin lokacin taro da ake gudanarwa a kowace rana kan al’amuran rigakafin cutar Polio da aka gudanar a fadar Hakimin Birnin kudu.
Yace karamar hukumar zata kara da bada fifiko wajen tallafawa harkokin rigakafi domin dakile yaduwar cututtuka a yankin.
A don haka, Builder Muhammad Uba ya bukaci iyaye su kara himma wajen bada hadin kai da goyon baya ga jami’an lafiya a duk lokacin da ake gudanar da rigakafi.
A jawabin da ya gabatar mai kula da al’amuran rigakafi na yankin, Malam Abubakar Alhassan Garki yace ana sa ran yiwa kananan yara 194,000 rigakafin cutar shan inna a karamar hukumar.