’Yan bindiga sun kashe manoma 14 a Ondo
Published: 11th, March 2025 GMT
’Yan bindiga sun kashe aƙalla manoma 14 yayin wani hari da suka kai yankuna huɗu a Ƙaramar Hukumar Akure ta Arewa da ke Jihar Ondo.
Yankunan da abin ya shafa — Aba Alajido, Aba Sunday, Aba Pastor da Ademekun— galibi mazaunansu ƙananan manoma ne.
Abba zai naɗa sabon Kwamishina a Kano Yadda za a samu rufin asiri da sana’ar ɗinki — MuhammadWata majiyar ’yan sanda, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa maharan ɗauke da bindigogi sun auka yankunan ne da tsakar daren ranar Asabar inda suka soma harbe-harbe kan mai uwa da wabi.
Majiyar ta ce kawo yanzu dai an tsinto gawawwaki mutum 14 yayin da ake ci gaba laluben wasu.
Wani mazaunin ɗaya daga cikin yankunan da abin ya shafa da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce har kawo yanzu wasu daga mutanensu da suka tsere cikin jeji ba su dawo ba.
Ya ce tun a ranar Litinin ta makon jiya aka soma kawo musu hari, sai dai mafi munin ciki shi ne wanda ya auku a ranar Juma’a ba tare da maharan sun fuskanci wata tirjiya ba.
“Tun cikin daren ranar Juma’a suka soma kawo mana kuma duk wanda suka gani sai su buɗe masa wuta.
“Mutanenmu da dama sun gudu neman mafaka a jeji kuma ina tsammanin zuwa yanzu sun kashe mutum fiye da 40 a ƙauyukan yayin da wasu da dama sun jikkata.”
Da take zantawa da Aminiya ta wayar tarho, mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, Funmilayo Odunlami-Omisamya, ta tabbatar da faruwar lamarin.
A cewarta, an soma gudanar da bincike kan lamarin wanda kawo yanzu an tsinto gawawwakin mutum 14 a jeji.
Ta ce an tura tawagar jami’an ’yan sanda da za ta bi sawun ɓata-garin kuma tuni tarzoma ta lafa a yankin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga jihar Ondo
এছাড়াও পড়ুন:
Boko Haram Sun Hallaka ‘Yan Zaman Makoki 7, Sun Jikkata Wasu A Borno
Sanata Ali Ndume, mai wakiltar yankin Borno ta Kudu, ya bayyana cewa hare-haren na ƙara ƙamari a yankin abun takaici ne.
Ya ce ya samu rahoto tsakanin Hawul da Garkida inda aka ce an kashe ’yan sa-kai sama da 10 a ranar Litinin.
A cewarsa, sama da mutane 100 aka kashe cikin wata guda a hare-hare da aka kai Sabon Gari, Izge, Kirawa, Pulka, Damboa, Chibok, Askira Uba da wasu garuruwa da dama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp