Abin da ya sa na sauya sheƙa daga APC zuwa SDP — El-Rufai
Published: 10th, March 2025 GMT
Tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya tabbatar da sauya sheƙa daga jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar zuwa jam’iyyar SDP.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da ya wallafa ranar Litinin ne a shafukansa na sada zumunta.
’Yan bindiga sun yi garkuwa da matashi a Kano Tsohon Mataimakin Gwamnan Kogi Patrick Adaba ya rasuEl-Rufai ya ce, “yanzu na yanke shawarar komawa jam’iyyar Social Democratic Party, kuma zan kasance a cikin ta wajen tafiyar da al’amurana na siyasa a nan gaba.
Ya ce a matsayinsa na wanda aka kafa jam’iyyar APC da shi, zai ci gaba da tunawa da faɗi tashi da kuma kyakkyawar mu’amalar da ya yi da duk abokan hulɗarsa.
Ya ce ya yi fatan cewa jam’iyyar APC wadda da shi aka kafa ta tun a shekarar 2013 za ta tsaya a kan tubalin da suka assasa ta har zuwa lokacin da zai yi ritaya daga siyasa.
Sai dai ya ce a tsawon shekaru biyu da suka gabata, ya lura cewa akwai halin ko-in-kula gami da sauka daga kan tsari da aƙida a ɓangaren waɗanda ke riƙe da madafan ikon jam’iyyar a yanzu, da ba su da burin magance matsalolin da suka addabi jam’iyyar.
Ya ce a nasa ɓangaren, ya bayyana damuwa a cikin sirri da kuma kwanan a bainar jama’a game da halin da jam’iyyar take ciki, amma ya ga babu mafita face ficewa daga jam’iyyar domin sauya sheƙa zuwa wata da zai ci gaba da gudanar da al’amuran siyasa da zai kawo ci gaba a Jihar Kaduna, Arewa da kuma Nijeriya baki ɗaya.
“A matsayina na ɗan jam’iyya mai kishi, na yi aiki wajen taimaka wa jam’iyyar APC ta samun nasara a zaɓukan 2015, 2019 da 2023.
“Ina ɗaya daga cikin gwamnoni da dama da aka zaɓa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar a 2015 da 2019, waɗanda suka tsaya tsayin daka wajen tabbatar da dimokuradiyya da ka’idojin ciyar da ƙasa gaba.
“Tsawon shekaru takwas da na yi a matsayin Gwamnan Jihar Kaduna, na duƙufa wajen aiwatar da tsare-tsare masu inganci don ciyar da al’umma gaba a fannin ilimi da kiwon lafiya, da faɗaɗa ababen more rayuwa, samar da ayyukan yi da jawo jari.
“Waɗannan bayanan kaɗan ne a cikin manufofin da jam’iyyar APC mai ci ta yi watsi da su a yanzu tare da wulaƙanta mambobinta a shekaru biyu da suka gabata. Na ga abin ba mai karɓuwa ba ne.
“A yau 10 ga Maris, 2025, na miƙa takardar barin jam’iyyar APC a mazaɓata ta Kaduna.
“Sai dai kafin ɗaukar wannan matakin, na kammala tuntuɓar mashawarta, abokan aiki da magoya baya a duk faɗin ƙasar game da hakan.
“A yanzu na yanke shawarar shiga jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), kuma na ɗauke ta a matsayin inuwar gudanar da harkokina na siyasa da sauran ayyuka.
“Saboda haka, zan mayar da hankali wajen yin cuɗanya tare da jawo hankalin sauran ’yan jam’iyyun adawa su shigo cikinmu, mu taru a karkashin tsarin dimokuraɗiyya bai ɗaya domin ƙalubalantar jam’iyyar APC a duk wani zaɓe da zaɓen fidda gwani da za a yi daga yanzu zuwa 2027 da yardar Allah.
“Don haka ina kira ga dukkan magoya bayanmu da sauran waɗanda suka damu da makomar ƙasarmu da su shigo jam’iyyar SDP don ganin Nijeriya ta bunƙasa a matsayin abin alfahari ga ‘yan Afirka da duk wani baƙar fata.”
Ana iya tuna cewa tun a kwanakin baya yayin tattaunawarsa da gidan talabijin na Arise, El-Rufa’i ya bayyana cewa “jam’iyyar APC ta sauka daga kan manufofin da aka assasa ta tun fil-azal.”
Ya yi zargin cewa jam’iyyar ta gaza kiran taron shugabanninta na ƙasa tsawon shekaru, wanda ya ce hakan ya saɓa wa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
A yanzu dai wannan ya kawo ƙarshen raɗe-raɗin da ake yi na inda tsohon gwamnan zai nufa bayan raba gari da jam’iyyar APC.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: jam iyyar APC jam iyyar A jam iyyar a
এছাড়াও পড়ুন:
Arakci: Babu Wani Dalili Na Ci Gaba Da Tattaunawa Tsakanin Iran Da Amurka
Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci wanda ya tattauna ta wayar tarho da jami’ar harkokin waje ta tarayyar turai ya bayyana cewa, ci gaba da tattaunawa a tsakanin Iran da Amurka ba shi da wata ma’ana, kamata ya yi jami’an tarayyar turai din su yi Allawadai da wuce gona da irin HKI akan Iran.
Da safiyar yau Asabar ne dai jami’ar diplomasiyyar ta turai Kaja Kallas ta kira yi minsitan harkokin wajen jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci inda su ka tattauna halin da ake ciki a yammacin Asiya da ya hada da harin da HKI ta kawo wa Iran.
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana harin na HKI da cewa, wuce gona da iri ne da keta hurumin kasar Iran, kuma harin da ta kai wa cibiyoyin Nukiliya ya yi sanadiyyar shahadar mutane da dama da su ka hada da malaman jami’oi , da kuma mata da kananan yara.
Ministan harkokin wajen na Iran ya yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su yi Allawadai da abinda HKI ta yi na take dokokin kasa da kasa.
Haka nan kuma ministan harkokin wajen na Jamhuriyar musulunci ta Iran ya yi ishara da cewa, kudurin da majalisar alkalai ta hukumar makamashin Nukiliyar Iran ta fitar akan Iran wanda kuma kasashe uku na turai tare da Amurka su ka gabatar da shi, shi ne ya bude wa ‘yan Sahayoniya mashigar da su ka yi amfani da ita wajen wuce gona da iri akan Iran.
A nata gefen babbar jami’ar diplomasiyyar tarayyar turai ta bayyana rashin jin dadinta akan abinda yake faruwa a cikin yankin na yammacin Asiya na rikice-rikice, tare da bayyana cewa suna goyon bayan aiki da diplomasiyya domin tabbatar da zaman lafiya.
A wani labarin mai alaka da wannan kasar Oman ta sanar da cewa, ba za a yi taron da aka shirya yi a tsakanin Iran da Amruka ba.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Oman ce ta fitar da sanarwar cewa; Tattaunawar da aka shirya cewa za a yi a tsakanin Amurka da Iran ba za a yi ta ba a gobe Lahadi.
Ministan harkokin wajen na Oman ya kara da cewa; Diplomasiyya ce kadai ya kamata ta zama hanyar cimma zaman lafiya mai dorewa.