Aminiya:
2025-03-20@10:47:28 GMT

’Yan bindiga sun yi garkuwa da matashi a Kano

Published: 10th, March 2025 GMT

’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani matashi mai shekaru 20, Muhammed Bello a ƙauyen Zakirai da ke Ƙaramar Hukumar Gabasawa ta Jihar Kano.

Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne yayin da ’yan bindigar suka kai hari a gidan wani mai suna Alhaji Yusha’u Ma’aruf, wanda yake da wani asibiti mai zaman kansa a ƙauyen na Zakirai.

Mun bai wa Akpabio sa’o’i 48 ya dawo da Sanata Natasha — SERAP Ramadan: Abubuwa goma ga ma’aurata

Kazalika, wani ɗan gidan mai suna Abubakar Yusha’u mai shekaru 23 ya samu rauni yayin da ’yan bindigar suka guntule masa yatsa ɗaya a hannunsa na hagu.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:15 na dare, inda maharan su uku riƙe da bindigogi da adduna suka rufar wa gidan Alhaji Yusha’u.

Kazalika, maharan sun arce da wayoyin hannu da kuɗaɗe da ba a kai ga tantance ko nawa ba ne.

Kakakin rundunar ’yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin da bincike ya soma gudana a kansa.

SP Kiyawa ya ce tuni ’yan sanda suka fara farautar ɓata-garin domin ceto matashin da aka yi garkuwa da shi.

Aminiya ta ruwaito cewa, a bayan nan ne ’yan sanda suka kama wasu mutum huɗu da ake zargin ’yan bindiga ne, sannan ta ƙwace makamai da alburusai da kuɗi kimanin naira 1,028,800 a unguwar Hotoro da ke Jihar Kanon.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Jihar Kano mahara

এছাড়াও পড়ুন:

Gobara ta kashe yara 3, ta jikkata 13 a Yobe

Rahotanni sun nuna cewa gobara ta kashe yara uku tare da jikkata wasu 13 a ƙauyuka tara na Jihar Yobe, tsakanin watan Janairu zuwa Maris ɗin 2025.

Gobarar ta kuma lalata gidaje 86, inda ta bar mutane da dama ba tare da matsuguni ba.

Tinubu ya rantsar da Ibas a matsayin mai kula da Ribas Ba tarbiyya nake koyarwa ba — Sadiq Sani Sadiq

Babban sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Yobe (YOSEMA), Dokta Mohammed Goje, ya bayyana cewa rashin kula da wutar lantarki, amfani da gas, ƙonewar daji, da kuma zubar da shara ba bisa ƙa’ida ba, ke haddasa yawan gobara a jihar.

Ya ce lamarin ya fi shafar yankunan Damaturu, Gulani, da Yusufari, inda mazauna ke kokawa kan asarar da suka yi.

Domin magance matsalar, hukumar YOSEMA ta fara wayar da kan jama’a kan hanyoyin kauce wa gobara.

Haka kuma, sun kafa kwamitoci da za su taimaka wajen kare lafiyar al’umma, musamman a lokacin rani da hunturu.

Dokta Goje ya ce hukumar, tare da haɗin gwiwar Hukumar Kashe Gobara ta jihar, za su ɗauki matakan hana ƙone daji da kuma bin ƙa’idojin zubar da shara domin rage haɗuran gobara.

A gefe guda, Gwamna Mai Mala Buni ya umarci hukumar YOSEMA da ta tantance ɓarnar da gobarar ta yi, domin sanin irin taimakon da waɗanda lamarin ya shafa suke buƙata.

Gwamnan ya tabbatar wa waɗanda abin ya shafa cewa za a tallafa musu.

A halin yanzu, hukumomi na ci gaba da faɗakar da jama’a kan muhimmancin kiyaye dokokin kare gobara domin gujewa aukuwar irin wannan iftila’i a gaba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gobara Ta Babbake Wani Shago A Jihar Kwara
  • Fashewar Tanka: Asibitoci sun cika da mutane a Abuja
  • ’Yan bindiga sun sace shugaban kasuwar kayan miya ta Akinyele a Oyo
  • Gobara ta kashe yara 3, ta jikkata 13 a Yobe
  • ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 7 A Jihar Neja
  • ’Yan Banga Sun Ceto Mutum 3 Daga Hannun ’Yan Bindiga A Taraba
  • An shiga zaman ɗar-ɗar yayin da sojoji suka mamaye Gidan Gwamnatin Ribas
  • Janar Tsiga ya shafe kwanaki 40 a hannun masu garkuwa duk da biyan kuɗin fansa
  • Al’ummar Yemen sun sha alwashin tsayin-daka kan barazanar Trump
  • Madalla da hutu ga ’yan makaranta domin azumi