HausaTv:
2025-05-01@00:50:54 GMT

Sharhin Bayan Labarai: Kasashen Afirka Sun Kori Sojojin Faransa Daga Kasashensu

Published: 9th, March 2025 GMT

Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da ‘Korar sojoijin Faransa daga kasa ta 7 a yammacin Afirka tare bukatar’ macron ya nemi uzurin kasashen’ wanda ni tahir amin zamn karanta.

///…Madalla, Bayan da kasashen Mali da Burkina faso, da Nigerda Ivory Coast suke kori sojojin Faransa daga kasashensu, a yanzun kuma kasar Senegal ta bada sanarwan korar sojojin kasar Faransa daga kasar.

Tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar Mali da kuma korar sojojin kasashen waje, daga cikin har da sojojin kasar Faransa da kuma na Majalisar dinkin duniya daga kasar, daya bayan daya kasashen yankin yammacin Afirka kuma tsoffin kasashen da Faransa tayiwa mulkin mallaka suka suka fara korar sojojin faransa daga kasashensu.

Bayan Burkiya Faso sai Jumhuriyar Niger, sannan Ivory Coast sannan yau kuma Senegal. Wannan yana daga cikin sauye-sauyen  da suke faruwa a kasashen yammacin Afirka a cikin yan sheakrun da suka gabata, wanda kuma yake nuna yadda kasashen da aka yiwa mulkin mallaka a wannan yankin, suke kin wadanda suka yi masu mulkin mallaka, hatta bayan sun basu abinda suka kira yenci.

A zahiri dukkan wadannan kasashe, babu ko da guda wacce take da wani cikin gaban a zo a gani, ta ko wani bangare, fiye da shekaru 60 da kasar faransa tace ba basu yencin kai, ba abinda take yi sai kwasar dokokiyoyin wadannan kasashe zuwa kasashensu.

Misali shi ne, an ce kasha 20% na ton 88,200 na sinadarim Uranium da ya shiga kasar faransa a cikin shekaru 10 da suka gabata ya fito daga Jumhuriyar Niger ne. A kasar Mali kasar faransa tana fitar da ton ton na gola-golan zuwa kasar faransa, amma ba zaka taba ganin wata ci gaba a kasar ba.

Kamfanin dillancin labaran Pars today ya nakalto daga tashar talabijin ta Euronews yana cewa ofishin jakadancin kasar Faransa na cewa a ranar Lahadi 9 ga watan Maris, sojojin kasar Faransa sun mika sansanonin sojoji guda biyu da ke hannunsa ga sojojin kasar ta Senegal.

Kafin haka dai a ranar 2 ga watan Fabrayrun shekara ta 2025 ne kasashen biyu suka kafa kwamitin hadin guiwa na kula da shirin ficewar sojojin faransa daga kasar.

Sai kuma kasar Ivory Coast inda sojojin Faransa suka mika sansanin sojojin kasar tilo a kasar Ivory coast ga sojojin kasar a ranar 20 ga watan Fabrayru. Ministan harkokin wajen kasar Faransa Sepostine Lakunu da tokwaransa na kasar Ivory Coast

Tane Perohimi Watara ne, suka rattaba hannu kan takardun ficewar sojojin kasar faransa, daga kasar.

Kamfanin dillancin labaran Isna na kasar Iran ya bayyana cewa, sojojin kasar Faransa 400 suke zaune a sansanin sojojin kasar. Sannan kwamandan sojojin Ivory Coast ne ya bada sanarwan kawo karshen zaman sojojin kasar Faransa a kasar a wani biki bamusamman da aka gudanar a babban birnin kasar a ranar 19 ga watan Fabrairun shekara ta 2023.

Labarin ya ce a bikinne aka sauke tutar kasar Faransam sannan aka sane shi sai kuma aka daga tutar Burkina faso a inda aka sauko da na faransa. 

Amma kafin haka sojojin kasar Faransa sun fice daga kasar Mali ne a ranar 20 ga watan Augustan shekara ta 2022m bayan shekaru 9 da shiga kasar da sunan tabbatar da zaman lafiya.

Komandan rundunar sojojin kasar faransa a Mali, ya bada sanarwan aikin rundunarsa wacce ake kira Barkhane a wannan ranar, inda suka ratsa ta Niger suka kuma fice daga yankin kwata-kwata.

A niger dai sojojin Faransa 1500 ne suke zauna a birnin Yemai, kafin su fice a ranar 22 ga watan Decemban shekara ta 2023. Haka ma kasar Chadi sojojin Faransa sun fice daga wani sansaninsu a birnin Njamena ne, a ranar 30 ga watan Jenerun shekara ta 2024.

Ya zuwa yanzu dai sojojin Faransa sun fice daga mafi yawan kasashen da take zama a cikin, sai kasar Njibuti, inda take da sojojin 1,500 da kum Gabon inda take da sojoji 350.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: sojojin kasar faransa sojojin kasar Faransa sojojin Faransa daga sojojin faransa daga Faransa sun Ivory Coast

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu gobe Alhamis

Gwamnatin Nijeriya ta ayyana gobe Alhamis 1 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu ga ma’aikatan ƙasar albarkacin bikin murnar Ranar Ma’aikata ta Duniya.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Ministan Harkokin Cikin Gida na ƙasar, Olubunmi Tunji-Ojo, ya fitar a yammacin wannan Larabar.

AU ta janye takunkumin da ta ƙaƙaba wa Gabon Tsoffin ma’aikatan NECO na neman a biya su bashin haƙƙoƙinsu

Sanarwar ta ambato ministan yana yaba wa ma’aikatan ƙasar kan sadaukarwa da jajircewar da suke yi wajen gudanar da ayyukansu.

Ministan ya kuma yaba musu kan gudunmawar da suke bayarwa wajen ciyar da Nijeriya gaba.

Ana dai gudanar da bikin Ranar Ma’aikata a ranar 1 ga watan Mayun kowace shekara a sassan duniya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu gobe Alhamis
  • Araghchi : Za’ayi Tattaunawar Iran da Amurka ta gaba a Rome bayan taron E3
  • Iran ta sha alwashin ci gaba da aiwatar da manufofinta na raya dangantakarta da Nijar
  • An kashe Falasdinawa kusan 30 a wani sabon kisan kiyashin Isra’ila a Gaza
  • Yadda ’yan Tifa da baƙin direbobi ke haddasa haɗari a Abuja
  • Iran Da Iraki Sun Ce An Kammala Shimfida Layin Dogo Daga Shalamcheh Zuwa Basra
  • Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kutsa Cikin Quneitra Na Kasar Siriya Tare Da Kafa Shingen Bincike
  • Karin Wata Kasa Da Bai San Ta Ba A Doron Duniya
  • Shugaban Kasar Yana Maraba Da Masu Zuba Hannun Jari A Kasarsa Daga Kasashen Waje
  • Sama Da Masu Sayayya Daga Ketare 220,000 Ne Suka Halarci Bikin Baje Kolin Canton Karo Na 137