Shahararren Malamin Addini Islama A Adamawa Sheikh Ibrahim Abubakar Daware Ya Rasu
Published: 8th, February 2025 GMT
Jihar Adamawa ta rasa shahararre kuma babban malamin addinin musilunci, Sheikh Ibrahim Abubakar Daware, ranar Juma’a, bayan fama da rashin lafiya.
Sheikh Daware ya kasance malami mai karamci wanda yake koyar da darussan addini da kuma gudummawa a kasashen musulmi daban-daban da sassan jihohin Nijeriya da dama.
An gudanar da jana’izar malamin kamar yadda addinin musilunci ya tanada a gidansa da ke karamar hukumar Fufore a ranar Asabar.
Sheikh Ibrahim Daware, ya rasu ya na da shekaru 71, ya bar matan aure hudu da ‘ya’ya 43 da jikoki 53.
কীওয়ার্ড: Adamawa Rasuwa Sheikh Ibrahim Abubakar Daware
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Lawal Ya Naɗa Sabon Sarkin Gusau
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da naɗa Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin sabon Sarkin Gusau kuma Sarkin Katsina na Masarautar Gusau.
Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Malam Abubakar Mohammad Nakwada ne ya sanar da hakan, inda ya bayyana cewa an yi naɗin ne bisa ga shawarwarin da masu zaɓen sarakuna na masarautar Gusau suka bayar, tare da bin al’ada da dokokin da suka dace.
A wata sanarwa da mai taimakawa na musamman kan harkokin yaɗa labarai a ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Sulaiman Ahmad Tudu, ya fitar, ya ce sabon Sarkin, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello, shi ne ɗa na farko ga marigayi Sarki, kuma kafin naɗin nasa yana riƙe da mukamin Bunun Gusau.
Alhaji Abdulkadir ya hau karagar mulki a matsayin Sarkin Gusau na 16, bayan rasuwar mahaifinsa, Mai Martaba Dokta Ibrahim Bello, wanda ya rasu a ranar 25 ga Yulin 2025, bayan shafe shekara goma yana mulki.
Yayin da yake taya sabon sarkin murna, Gwamna Lawal ya bukace shi da ya ci gaba da rike kyakkyawar jagoranci da mutumtaka da aka san kakanninsa da shi, musamman kasancewarsa tsatson Malam Sambo Dan Ashafa.
Gwamnan ya kuma bukaci sabon Sarkin da ya kasance jajirtacce wajen kawo haɗin kai, zaman lafiya da cigaba, tare da ƙarfafa hadin kai a ciki da wajen masarautar Gusau.
Daga Aminu Dalhatu