2025-12-13@11:01:52 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2517
«yan damfara»:
Allah Ya yi wa Farfesa Adamu Baikie, wanda ya kasance Farfesa na farko a fannin Ilimi daga Arewacin Najeriya, rasuwa. Farfesa Adamu Bakie ya rasu yana da shekaru 94 ne a daren Jumma’a a gidansa da ke Zariya, Jihar Kaduna. Babban ɗansa, Manjo Muhammad Adamu (Ritaya), ya tabbatar da rasuwar, inda ya ce za a sanar...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 2.6 domin gudanar da ayyukan Hajjin shekarar 2026. Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Jiha da aka gudanar a gidan gwamnati...
Daga Usman Muhammad Zaria Aikin rigakafin watan Disamba a karamar hukumar Sule-Tankarkar ta jihar Jigawa ya samu gagarumar nasara, yayin da iyaye suka fito kwansu da kwarkwata domin tabbatar da cewa an yi wa ’ya’yansu cikakken rigakafi. Wasu daga cikin iyayen da suka kawo ’ya’yansu domin karbar rigakafin yau da kullum da na shan inna...
Babban mai shigar da kara a kuntun duniya mai hukumta manyan laifuka Karim Khan ya fadi cewa gwamnatin Birtaniya ta yi barazanar yanke tallafin da take bawa kotun da kuma ficewa daga matsayin dake taimakawa wajen samun tallafi, idan kotun ta ci gaba da tafiya da sammacin da ta fitar na kama prime ministan israila...
Fitaccen attajirin nan Alhaji Dahiru Mangal, ya ɗauki nauyin yi wa marasa galihu a Jihar Katsina aikin ido kyauta, inda ɗaruruwan mutane ke samun kulawar likitoci ba tare da biyan ko sisi ba. A yayin da wakilin Aminiya, ya ziyarci Asibitin Ido da ke birnin Katsina, marasa lafiya da dama da suka ci gajiyar aikin...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Hukuncin Kisa Kan Maryam Sanda December 12, 2025 Manyan Labarai Tinubu Ya Yaba Wa Jami’an Tsaro Kan Ceto Dalibai 100 Da Aka Sace A Neja December 12, 2025 Manyan Labarai NLC Ta Shirya Zanga-Zangar Rashin Tsaro A Faɗin Ƙasa Ranar 17 Ga...
Alkalin ya kuma bayyana cewa ba daidai ba ne bangaren zartarwa ya yi rangwame ga hukuncin kisa yayin da har yanzu ana da karar daukaka kara a gaban kotu. Don haka, kotun ta kori daukaka karar Maryam Sanda gaba ɗaya tare da tabbatar da hukuncin kisa da kotunan ƙasa suka yanke mata. ShareTweetSendShare MASU ALAKA...
“Umarna ga jami’an tsaro har yanzu ita ce cewa dole ne a ceto dukkan daliban da sauran ‘yan Nijeriya da aka yi garkuwa da su a fadin kasar nan, a dawo da su gida cikin aminci. Dole ne mu tabbatar da an kirga duk wanda lamarin ya rutsa da shi. “Gwamnatin Tarayya za ta ci...
Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta bayyana cewa za ta gudanar da zanga-zangar ƙasa baki ɗaya a ranar 17 ga Disamba, 2025, domin nuna damuwarta kan taɓarɓarewar tsaro a Nijeriya. Wannan sanarwa ta fito ne daga saƙon da NLC ta aikawa dukkanin majalisun jihohi a ranar 10 ga Disamba, bayan taron NEC da ta gudanar...
Shugaban kasar Iran Masoud Pazeshkian, a ganawarsa da tokwaransa na kasar Turkmenietan Gurbanguly Berdimuhammedow a birnin Ashg’abat ya ce, a halin yanzu, fiye da duk wani lokaci – tana bukatar amintaccen madogara, zaman lafiya da kuma hadin kai. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana yabawa kasar Turkmenistan kan shirinta karban...
A Legas farashin shinkafa ya fadi sosai A kasuwannin Mushin da Daleko, farashin buhun shinkafa kilo 50 da ake sayar da shi a da Naira N75,000 cikin Nuwamba, a yanzu ya dawo Naira 54,000. Jihar Delta A Jihar Delta, musamman a Asaba, farashin kayan abinci ya daidaita a manyan kasuwanni irin su Kasuwar...
Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya zargi ‘yan siyasan Nijeriya da zagon kasa ga ci gaban kasar ta hanyar daukar mukaman gwamnati a matsayin gadon gidansu a maimakon amanar jama’a. Da yake jawabi a ranar Laraba a yayin taro karo na 15 mai taken, “ya Isa haka” da ya gudana a jihar Legas,...
Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar bunkasa ilimin manya ta jihar Jigawa tace za ta kashe naira milyan 400 wajen gudanar da harkokin ta a sabuwar shekara ta 2026. Shugaban hukumar. Dr. Abbas Abubakar Abbas, ya bayyana haka lokacin kare kiyasin kasafin kudin hukumar a gaban kwamatin ilimi matakin farko na majalisar dokokin jihar Jigawa. Dr...
Suleiman-Jibia ya ƙara sanar da cewa, majalisar ta amince da kafa Cibiyoyin Horar da Malamai a Katsina, Daura, da Funtua. “Cibiyoyin za su taimaka wajen haɓaka tsarin koyarwar malaman domin samar da ingantaccen ilimi ga ɗalibai a faɗin jihar,” in ji shi ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai EFCC Ta Kama Tsohon Gwamnan Anambra...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Gwamnatin Nijeriya Ta Himmatu Wajen Inganta Tsarin Karatun Allo December 11, 2025 Manyan Labarai EFCC Ta Kama Tsohon Gwamnan Anambra Chris Ngige A Abuja December 11, 2025 Labarai Sojoji Sun Kashe ’Yan Bindiga 11, Sun Ƙwato Makamai A Sakkwato December 11, 2025
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A kwanakin baya, Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da sabon tsarin jadawalin karatu ga makarantun firamare da sakandare. Sabon tsarin, wanda Ma’aikatar Ilimi ta ƙasa ta tsara, yana da nufin inganta koyarwa da koyo, da rage nauyin lodi ga dalibai, da kuma tabbatar da cewa malamai suna da isasshen...
Daga Usman Muhammad Zaria Ma’aikatar mata da walwalar jama’a ta jihar Jigawa za ta kashe naira milyan dubu 10 da milyan 599 wajen gudanar da manyan ayyuka da harkokin yau da kullum a sabuwar shekara. Kwamishinar ma’aikatar, Hajiya Hadiza Abdulwahab, ta bayyana hakan lokacin kare kiyasin kasafin kudin ma’aikatar a gaban kwamatin harkokin mata na...
Shugaban mabiya Shi’a a Najeriya, Sheikh Ibraheem El-Zakzaky, ya ce zai yi hisabi da tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, a gaban Allah kan abin da ya faru a Zariya a 2015. Rikicin ya fara ne bayan da mambobin IMN sun tare wa tsohon Hafsan Soji, Tukur Buratai, hanya. Najeriya za ta buga wasan sada zumunta...
Daga Aliyu Lawal Karamar Hukumar Agwara da ke Jihar Neja ta ce za ta ci gaba da hada kai da Gwamnatin Tarayya ta Jiha Neja wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’arta, musamman masu rauni. Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Iliyasu Zakari, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya rattaba hannu da kansa,...
Tawagar Super Eagles ta Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da ƙasar Masar kafin fara gasar Kofin Afrika da za a yi a Maroko. Wasan zai gudana ne a ranar 11 ga wata. Disamba, da misalin ƙarfe 7 na dare, a filin wasa na Cairo da ke Masar. EFCC ta tsare Malami kan binciken...
Rundunar ’yan sandan yankin Babban Birnin Tarayya Abuja ta kama wani mutum mai suna Ahmed Abubakar mai shekara 32, bisa zargin ƙoƙarin kai harsasai 1,000 ga ’yan bindiga a Jihar Zamfara. Kwamishinan ’yan sanda na birnin, Miller G. Dantawaye, ne ya bayyana hakan ga ’yan jarida a hedikwatar rundunar a Abuja ranar Laraba. Sakkwatawa na...
Wani dalibin shekarar ƙarshe a Jami’ar Ambrose Alli da ke jihar Edo, ya mutu a wani hatsarin mota bayan shi da wasu dalibai sun yi jerin gwanon motoci domin murnar kammala jarabawar ƙarshe. Aminiya ta samu labari a ranar Talata daga wani mai amfani da Facebook mai suna Inside Edo, cewa hatsarin ya faru ne...
A yau ne dokar hana yara amfani da shafukan sada zumunta ta fara aiki a Ostiraliya. Firaministan ƙasar ya bayyana dokar a matsayin abin alfahari ga Ostiraliya, yana mai cewa za ta shiga tarihi a matsayin muhimmiyar sauyi. Anthony Albanese ya ce ƙasarsa na kan gaba a duniya wajen ɗaukar wannan mataki. Yara ƙasa da...
Kananan yara sama da 93,200 ne ake sa ran yiwa allurar rigakafin cutar shan Inna da ake gudanarwa a Karamar Hukumar Ringim ta Jihar Jigawa. Kazalika, kananan yara sama da 53,800 ne ake sa ran digawa sinadarin vitamin A a yankin. Shugaban hukumar lafiya matakin farko na yankin Aminu Abubakar Kwandiko ya yaba da yadda...
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bada sanarwan kubutar da yan makaranta 100 daga cikin wadanda ‘yan ta’adda suka sace a wata makaranta a jihar Naija a cikin watan Nuwamban da ya gabatata. Tashar talabijan ta almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto kamfanin dillancin labaran reuters na cewa jami’an tsaron kasar sun sami nasarar kubutar da yan...
Daga Bello Wakili Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya isa Abidjan na kasar Côte d’Ivoire, domin wakiltar Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu a wajen rantsar da Shugaban Alassane Ouattara a wa’adinsa na hudu. Za a rantsar da Shugaban ne a yau Litinin, 8 ga watan Disamban 2025, a Fadar Shugaban Kasa da ke Abidjan, wanda...
Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce Gwamnatin Tarayya ta gaza wajen shawo kan matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara a faɗin kasar nan, lamarin da ya ce yana barazana ga haɗin kan ƙasa da zaman lafiya. Kwankwaso, wanda ya taɓa zama Ministan Tsaro,...
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi wa kasar Najeriya alkawalin taimaka ma ta domin ta fuskanci matsalolin tsaro, musamman ma dai ta’addanci a arewacin kasar. Shugaban kasar Faransan ya ce, takwaransa na Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya bukaci taimako domin fuskantar matsalar tsaro a arewacin kasar. Macron ya rubuta a shafinsa na X cewa;...
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta tabbatar da rasuwar wasu mutum biyar sakamakon haɗura uku da suka auku a jihar. Kakakin hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ya ce hatsrin farko ya faru ne da safiyar ranar Alhamis a unguwar Badawa Layin Day by Day ca Ƙaramar Hukumar Nassarawa. Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a...
Kungiyar ‘yan wasan ” Taekwondo” Iran dake kasa a shekaru 21 sun zama gwarazan duniya da aka yi a birnin Nairobi, bayan da su ka sami zinariya 3 da azurfa 1 sai kuma tagulla biyu. Kamfanin dillancin labarun “Irna” ya nakalto cewa; a jiya Asabar ne aka kawo karshe gasar wasan na ” Taekwondo” wanda...
Hukumar Kula da Rajistar Kamfanoni (CAC) ta ba wa dukkan masu gudanar da harkar kuɗi ta PoS a fadin Najeriya, wa’adin ranar 1 ga Janairu, 2026, su yi cikakken rajista ko ta rufe su. A ranar Asabar, Hukumar ta sanar cewa yawaitar masu PoS marasa rajista a sassan ƙasar nan ya yawaita. Don haka ta jaddada...
Wasu mutane uku sun rasu yayin da suke tsaka da aikin yasar rijiya a garin Badume da ke Ƙaramar Hukumar Bichi a Jihar Kano. A yayin da suke aikin haƙar rijiya, ɗaya daga cikinsu ya shiga domin yasowa biyu kuma na janyo ƙasar da aka haƙo. Ana cikin haka igiyar ta tsinke, inda nan take...
Kotu ta yanke wa wani wanda ya yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyaɗe hukuncin ɗaurin rai-da-rai a Ƙaramar Hukumar Guba ta Jihar Yobe. Babbar Kotun Jihar Yobe da ke zaune a ƙaramar hukumar Gujba ta yanke wa mutumin mai shekaru 31 mai suna Ali Kwano. An gurfanar da shi ne a kan zargin...
Hukumar Tsaro ta DSS ta kama wani likita da ake zargin yana ba da magunguna tare da kula da ’yan bindiga masu garkuwa da mutane da ke wasu sassan jihar Kwara. An kama wanda ake zargin, wanda ba a iya gano sunansa ba a lokacin rahoton, a yankin Jebba bayan rahotannin sirri sun nuna cewa...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baghaei ya yi tir da takunkuman tattalin arzikin da kasar Amurka take ci gaba da dorawa JMI na shekaru masu yawa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bada nakalto Baghaei yana fadar haka a dai dai ranar tunawa da ranar haramcin takunkuman tattalin arziki na bangare...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Masu iya magana kan ce banza ba ta kai zomo kasuwa. In ba haka ba, me ya kai matasan da ake zargi da aikata manyan laifuffuka ofishin ’yan sanda, suka kuma fit oba tare da wani ya harae su ko ya yi mutsu tsawa ba, balle ya saka...
Majalisar Dattawa ta amince da wani sabon ƙudiri da ke neman a gyara dokar yaƙi da ta’addanci, domin a ɗauki garkuwa da mutane a matsayin babban laifi na ta’addanci. Ƙudirin, wanda Sanata Opeyemi Bamidele ya gabatar, ya tanadi hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da laifin satar mutane, ba tare da wata zaɓin tara...
Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatinsa na shirin sayen jirage marasa matuƙa da wasu kayan aiki domin kare yankunan da ke iyakar Kano da Katsina. Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne, ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba. Gobara ta ƙone kasuwar katako a Abuja CBN ya...
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya soke iyakance adadin kuɗin da mutum ko kamfani za su iya ajiyewa a banki sannan ya ƙara yawan kudin da za a iya fitarwa a mako da ₦100,000 zuwa ₦500,000. Wannan na cikin wata sanarwa da Daraktar Sashen Tsarin Kuɗi da Dokoki ta bankin, Dr. Rita Sike, ta sanya wa...
Wata gobara da ta tashi da safiyar Litinin ta kashe magidanci da matarsa da ’ya’yansa uku a unguwar Kofar Sauri da ke cikin garin Katsina. Wadanda gobarar ta rutsa da su sun haɗa da Muhammad Habibu mai shekara 35, matarsa Fatima Muhammad, da ’ya’yansu uku; Khadija, Abubakar, da Aliyu, wadanda dukkansu suka ƙone har lahira....
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya yi watsi da barazanar Shugaban Amurka Donald Trump na cire Pretoria daga taron G20 na shekara mai zuwa, yana mai sake tabbatar da matsayin Afirka ta Kudu na memba da aka kafa wannan dandali na kasa da kasa tare da ita. Trump ya sanar a ranar Laraba da...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismael Baqaei ya bayyana cewa Amurka ce Babbar barazana ga zaman lafiya da tsaro a duniya, saboda ganin abinda take yi a halin yanzu a kasar Venezuela da kuma wasu kasashen Afirka. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalyo kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar yana fadar haka...
’Yan sanda sun gano tare da miƙa wa wata mata zinarenta da kuɗinsu ya kai Naira miliyan 23 da suna ɓace a lokacin wani harin Boko Haram shekara 13 da suka gabata a Jihar Borno. Jami’an tsaro da ke sintiri a kan iyakar Jihar Borno da Nijar ne suka gano kayan zinaren da suka ɓace...
’Yan sanda sun gano tare da miƙa wa wata mata zinarenta da kuɗinwu ta kai Naira miliyan 23 da suna ɓace a lokacin wani harin Boko Haram shekara 12 da suka gabata a Jihar Borno. Jami’an tsaro da ke sintiri a kan iyakar Jihar Borno da Nijar ne suka gano kayan zinaren waɗanda suka haɗa...
Daga Bello Wakili Najeriya ta ƙarfafa ƙoƙarinta na kawar da cutar HIV nan da shekarar 2030, inda Uwargidar Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga ’yan Najeriya, shugabanni da jami’an lafiya su haɗa hannu wajen cimma wannan manufa. Yayin jawabi a bikin ranar Yaki da Cutar AIDS ta Duniya ta 2025 da aka...
Ana ci gaba da ta ƙaddama kan Naira dubu ɗari bakwai da hamsin da Jami’ar Amurka ta Maryam Abacha (MAAUN) da ke Jihar Kano ta wajabta wa ɗalibanta da suka kammala karatu biya a matsayin kuɗin bikin yaye ɗalibai. Jami’ar MAAUN ta sanya wa kowane ɗalibin da ya kammala karatu biyan Naira dubu ɗari bakwai...
Wata fitacciyar sinima a Faransa, Cinematheque Francaise, ta rufe ɗakunan kallonta na tsawon wata guda saboda yaɗuwar kuɗin cizo da aka gano a cikinta Cibiyar wadda ke gabashin birnin Paris ta ce rufe sinimar zai ba ta damar tabbatar da cewa masu kallo sun samu “aminci da kwanciyar hankali” bayan ƙorafe-ƙorafen da aka yi na...
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa ya koma jam’iyyar ADC ne saboda ita kaɗai yake gani za ta iya ceto Najeriya daga matsalolin tsaro da na tattalin arziki da take fama da su. Yayin ƙaddamar da ofishin jam’iyyar a Jihar Taraba ranar Asabar, Atiku duk da a baya ya kasance a jam’iyyar...
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya buƙaci Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya daina siyasantar da harkar tsaro a jihar. Ya ce kamata ya yi gwamnan ya mayar da hankali kan matsalolin da ke damun jihar. Yadda ’yan mata ke kuɗancewa da kasuwancin fara a Kano DSS ta gayyaci Datti Baba-Ahmed...
Iran da wasu kasashen yankin Tekun Fasha sun yi Allah wadai da sabon kutse da farmakin da sojojin Isra’ila suka kai ta kasa da kuma ta sama a birnin Beit Jinn da ke kudancin Siriya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 13, ciki har da yara. A cikin wata sanarwa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen...
