2025-07-09@21:36:03 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1405
«Yan Zariya»:
Shugaban kasar Iran ya soki lamirin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA A wata tattaunawa ta hanyar wayar tarho da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron a yammacin jiya Lahadi, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi Allah wadai da dabi’ar nuna fuska biyu daga Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya, yana mai cewa irin...
Kasar Sin ta kawo karshen aikin bayar da agajin gaggawa mafi girma a gundumar Rongjiang da ke lardin Guizhou, a yankin kudu maso yammacin kasar da misalin karfe 10 na safiyar ranar Lahadi, yayin da aka kammala ruwan saman da aka tafka kamar da bakin kwarya kamar yadda mahukuntan yankin suka bayyana. Lardin Guizhou da...
Gwamnatin kasar Iran ta gargadi kasashen yammacin Asiya kan cewa mai yuwa yaki ya sake barkewa tsakaninta da HKI, akwai tababa kan cewa HKI zata kiyaye budewa juna wuta da ta cimma da kasar Iran. Shafin yanar gizo na labarai ArabNews na kasar Saudiya ya nakalto Manjo Janar Abdulrahman Musawi babban hafsan hafsoshin sojojin kasar...
Bayan hare-haren da kungiyoyin yan ta’adda masu iko da kasar Siriya suka kai kan wani Cuci a kasar Siriya jami’an gwamnatin kasar Siriya sun nuna damuwarsu da yiyuwar wadannan kungiyoyi su kawo hare-hare a cikin kasar ta Lebanon musamman a cikin wadan nan kwanaki na makokin Imam Hussain (a). Wani Jami’in gwamnati a kasar ta...
Magoya bayan Kwankwaso, wadanda aka fi sani da Kwankwasiyya, sun yi ikirarin cewa Ganduje ya bai wa mutanen Kano kunya, shi ya sa ya yi murabus. Shugaban jam’iyyar NNPP na Kano, Hashimu Dungurawa, wanda ya yi magana a madadin magoya bayan Kwankwaso, ya bayyana murabus din Ganduje a matsayin kwaso abin kunya ga...
Majiyar ‘yan sahayoniya ta ce, sai zuwa watan Oktoba ne za a iya kawo karshen lalacewar da matatar man fetur din Haifa ta yi sanadiyyar harin makami mai linzami na Iran. Jaridar “Time Of Isra’il” ta bayyana cewa a tsawon yakin kwanaki 12, Iran ta yi wa Isra’ila mummunan harin mai ciwo da sai yanzu...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kisa ta hanyar daukar doka a hannu na kara ta’azzara da saka damuwa a zukatan ‘yan Najeriya. Yayin da wasu ke ganin daukar doka a hannu daidai ne, wasu kuwa na ganin hakan zai cigaba da haifar da rashin doka da oda a kasa. Shin ko me...
Da yake jawabi jim kadan kafin tashinsa a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, Gwamna Yusuf ya bayyana marigayi Dantata a matsayin uba ga mutane da yawa, wanda karamcinsa da sadaukarwarsa ya wuce iyaka. Gwamnan ya jaddada cewa, zuwan tawagar a Madina shaida ce ta matukar mutuntawa da jama’a da gwamnatin jihar...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Al’ummar Iran Masu Juriya Za Su Tsaya Tsayin Daka Waje Kare Hakkinsu
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Al’ummar Iran masu juriya za su tsaya tsayin daka har zuwa digon jini na karshe Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Al’ummar Iran masu juriya za su tsaya tsayin daka har zuwa digon jini na karshe a kan duk wanda ya nemi juya akalarsu....

Shugaban Majalisar Dokokin Jama’ar Kasar Mexico: Tunanin Raya Al’umma Mai Kyakkyawar Makoma Ga Dukkan Bil’adama Da Shugaba Xi Jinping Ya Gabatar Ya Kayatar
Shugaban majalisar dokokin jama’ar kasar Mexico Sergio Carlos Gutiérrez, ya bayyana yayin da wakilin babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG ya zanta da shi a kwanakin baya cewa, tunanin raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama da shugaba Xi Jinping ya gabatar ya burge shi matuka. Ya ce, an gabatar...
Manjo Janar Mousawi ya bayyana cewa: Suna shakka da kokwanto kan gaskiyar tsagaita bude wuta shin za ta dore kuwa tsakaninsu da ‘yan sahayoniyya Babban hafsan hafsoshin sojin kasar Iran ya yi gargadin gazawar yarjejeniyar tsagaita bude wuta, yana mai nuni da rashin kwarin gwiwa kan kudurin makiya na cika alkawuran da suka dauka. A...
Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun sake yi wasu sabbin kutse a yankunan Quneitra na kasar Siriya Rahotonni sun bayyana cewa: Da sanyin safiya ne sojojin mamayar Isra’ila suka kutsa cikin yankunan garin Saida da kuma kauyen Abu Mathra da ke yankin kudancin Quneitra na kasar Siriya. Wannan ya zo daidai da wani sintiri da...
Tashin farashin man fetur a kasuwannin duniya ci-gaban mai hakar rijiya ne ga Nijeriya wadda ke kan gaba wajen fitar da mai ta yadda za ta samu makuddan kudin shiga sai dai gagarumar matsala ce ga ‘yan kasa wadanda za su fuskanci karin mai a cikin gida wanda zai zama silar karin kunci a dalilin...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira ga mazauna wani kauyen dake yankin Nyingchi na jihar Xizang mai cin gashin kai, da su rungumi akidar ‘yan uwantakar kabilarsu, da samar da yanayin gudanar da rayuwa mai kyau. Shugaba Xi ya yi kiran ne cikin wasikar da ya mayar ga mazauna kauyen, wadda a ciki...
Alhazan da suka hada da wakilan hukumar alhazai, jami’an hukumar jin dadin alhazai ta jiha, malamai, da sauran alhazai, sun bayyana jin dadinsu ga gwamnati da hukumar alhazai bisa irin kulawar da suka samu a lokacin aikin hajjin. Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan isowar mahajjatan, babban daraktan hukumar jin dadin...
Sojojin mamayar HKI suna ci gaba da kai hare-hare a yammacin kogin Jordan, inda a safiyar yau lahadi su ka kutsa cikin wani gida a garin Jenin,kamar kuma yadda ‘yan share wuri zauna su ka kutsa gidan wani bafalasdine a kudancin Nablus. Rahotanni da suke fitowa daga Falasdinu suna cewa; an yi taho mu gama...

An Kaddamar Da Aikin Hadin-Gwiwar Kafafen Yada Labaran Sin Da Kasashen Waje Wajen Watsa Labarai Game Da Jihar Xizang Ta Kasar Sin
Jiya Jumma’a 27 ga watan Yuni ne, aka kaddamar da wani aikin hadin-gwiwar kafafen yada labaran kasar Sin da kasashen waje daban-daban, mai taken “Ziyara a jihar Xizang don tunkarar zamanantarwa” dake karkashin jagorancin cibiyar watsa labarai ta harsunan Asiya da Afirka ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, da...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran ba ta san mika wuya ba, kuma tana rubuta tarihin mutunci da jinin shahidanta A jawabin da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi bayan halartar jana’izar shahidan Quds ya jaddada cewa: Iran ba ta san ma’anar mika wuya ba, yana mai fayyace cewa tarihi...

Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Ya Jaddada Cewa: Iran Tana Da Hakkin Tace Sinadarin Uranium A Kasarta
Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada cewa: Iran za ta ci gaba da tace sinadarin Uranium a cikin kasarta Jakada kuma zaunannen wakilin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani ya bayyana cewa: Iran tana jaddada matsayinta na cewa dole ne ta gudanar da ayyukan tace sinadarin Uranium a...
Darakta Janar na hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA ya bayyana cewa: Ba zai iya tabbatar da cewa Iran na kera makamin nukiliya ba! A wata hira da tashar talabijin ta Faransa LCI, Darakta Janar na hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA Rafael Grossi ya bayyana cewa: Ba zai iya tabbatar da cewa...
Wani mummunan hatsari ya afku a Masar inda ‘yan mata 18 suka mutu sakamakon fashewar wata motar dakon mai Wani mummunan hatsarin mota ya afku a kasar Masar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wasu mata 18 da direban bas a kan hanyarsu ta zuwa gonar inabin domin girbin inabin. Hatsarin ya afku ne a...
An yi wa marigayi Alhaji Aminu Ɗantata jana’izar Salatul ‘Ga’ib’ a garin Kano. An yi sallar ne a masallacin Umar bn Khattab da ke kan titin Gyadi-Gyadi. Za a binne Aminu Ɗantata a Madina — Iyalansa Mangu: Gwamnatin Filato ba ta aiko da wakilai don yin ta’aziyya ba — Sarkin Zazzau Sheikh Ibrahim Khalil, Shugaban...
Albarkacin ranar yaki da miyagun kwayoyi ta kasa da kasa, ofishin dakile miyagun kwayoyi na kasar Sin ya gabatar da rahoton halin da kasar take ciki a wannan bangare, inda alkaluma suka nuna cewa, a shekarar 2024, hukumomi masu alaka sun binciki laifuka masu nasaba da miyagun kwayoyi fiye da dubu 37, da cafke masu...
Har yanzu dai gwamnatin Syriya ba ta komai ba game da barna da hasarar rayuka da makamai da kuma jiragen da ake amfani da su da ta sararin samaniyarta ke haifarwa ba. Shafin Intanet na kafar Enab na kasar Syria ya wallafa wani labari a ranar 15 ga watan Yuni game da shirun da gwamnatin...
Iran ta gudanar da gagarumin jana’izar tare da karramawq ga kwamandojinta da masana kimiyyar nukiliya da wasu ’yan kasar da Isra’ila ta kashe a yankin kwana 12 da aka gwabza a tsakanin ƙasashen. Iran ta shirya gagarumin jana’izar a ƙwaryar birnin Tehran kwana huɗu bayan Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da...
Iran ta gudanar da gagarumin jana’izar tare da karramawq ga kwamandojinta da masana kimiyyar nukiliya da wasu ’yan kasar da Isra’ila ta kashe a yankin kwana 12 da aka gwabza a tsakanin ƙasashen. Iran ta shirya gagarumin jana’izar a ƙwaryar birnin Tehran kwana huɗu bayan Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da...
Taron dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya na lokacin zafi na Davos, wanda aka gudana a tsakanin ranar 24 zuwa ranar 26 ga watan nan da muka ciki, a birnin Tianjin na kasar Sin, ya samu halartar wakilai kimanin 1800 daga kasashe da yankuna sama da 90, adadin da ya kai koli cikin tarihi. Kamar...
Koyon ilimi ta kafar sadarwa ta zamani yana kara bayyana muhimmancin koyarwa musamman, ma ga wadanda suka dade suna koyon.Akwai samfuna dadama wadanda ake amfani dasu wajen koyarwa wadanda ana tsara su ko shiryasu ne domin su kasance daidai,da fahimtar dalibai.Irin yadda ake bi ko amfani da hanyoyi wajen tabbatar da cewar an samu inganta...
An watsa shirin talibijin mai taken “Yawon bude ido a Tuscany” a Florence na Italiya, da babban rukunin gidan radiyo da talibijin kasar Sin CMG da hukumar yawon bude ido ta yankin Tuscany na Italiya suka tsara da kuma gabatar cikin hadin gwiwa. Shugaban CMG Shen Haixiong da babban jami’in hukumar sun shaida bikin gabatarwar,...
Ofishin kula da aikin harba kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya ba da labari cewa, jiya Alhamis da karfe 9 da mintuna 29 na dare agogon Beijing, ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-20, wato Chen Dong da Chen Zhongrui da Wang Jie sun cimma nasarar fitowa daga akwatin gwaji na Wentian, yin tattaki...
Yau Jumma’a da safe, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Senegal Ousmane Sonko da shugaban kasar Ecuador Daniel Noboa a birnin Beijing, fadar milkin kasar Sin. Wadannan shugabannin biyu sun zo kasar Sin ne domin halartar taron dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya na lokacin zafi na Davos. A yayin ganawarsa...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Doctor Zainab Muhammad na daya daga cikin mata a Arewacin Najeriya da ta jajirce tare da kudirin cika burinta na karantar kimiyya duk da kalubalen da wasu matan dake yankin Arewa suke bayyanawa suna fuskanta wurin karantar fannin. Doctor Zainab ba kimiyya kawai ta karanta ba, ta karanci...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ban da haka kuma, wani babban dalilin da ya sa kasar Sin ke kokarin tallafa wa sauran kasashe a fannin aikin likitanci, shi ne akidarta ta “kafa al’ummar duniya mai kyakkyawar makoma ta bai-daya”. A cikin gidan kasar, an yi nasarar kawar da talauci, da kokarin neman wadatar da dukkan al’ummun kasar, lamarin da ya...
An harbe wasu mutum biyu da ake zargin ’yan fashi da makami ne a ranar Talata a yayin wani artabu da jami’an tsaro suka yi a unguwar Makera da ke Kakuri a Jihar Kaduna. Rundunar ta kuma kama wasu mutane biyu da ake zargin tare da ƙwato tarin makamai da kayayyaki masu daraja da aka...
Bello, a wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Muawiyah Yusuf, ya bayyana matukar bacin ransa da alhininsa kan wannan mummunan harin. Sanata Bello wanda kuma tsohon gwamnan jihar Neja ne, ya yi jinjina ga sojojin da suka rasa rayukansu a bakin aiki, inda ya bayyana...
An kama daya daga cikin mutanen da ake zargi da yin garkuwa da mutum uku a ƙauyen Daku da ke Gwagwalada Abuja lokacin da yake tsaka da cin kasuwar shanu ta Izom da ke Guraran jihar Neja. Rahotanni sun ce a ranar tara ga watan Yunin 2025 ce dai aka sace wasu makiyaya su biyu...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Benuwe, sun kama mutum biyar da ake zargi da hannu a kisan wasu matasa biyu ’yan asalin Jihar Kano. Waɗanda aka kashe sun haɗa da Jamilu Ahmad da Barhama Suleiman, kuma an kai musu hari ne cikin daren ranar Litinin a unguwar Agan, kusa da ƙofar shiga Makurdi. Gwamnatin Neja ta...
Rahotanni sun bayyana cewa, wasu ‘yan bindiga dauke da makamai karkashin jagorancin wani fitaccen kasurgumin dan bindiga mai suna Babaro sun kwace iko da jagorancin karamar hukumar Kankara a jihar Katsina. Wani mai sharhi kan harkokin tsaro, Bakatsine ne ya bayyana hakan a wani sharhi da aka wallafa a shafinsa na X, yana mai cewa,...
Majiyoyi sun kuma ce “an kashe adadi mai yawa na ‘yan bindigar”. Shugaban karamar hukumar, Abbas Adamu Kasuwan-Garba, ya ce harin ya kara firgitar da manoman yankin. Ya ce taimakon gaggawa daga barikin soji na Kontagora ya tilastawa ‘yan bindigar tserewa zuwa dazuka. Ya kuma ce ‘yan bindigar sun yi awon gaba...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kula da lafiya na nufin yin abubuwa da ke kare mutum daga kamuwa da cututtuka da kuma tabbatar da cewa jiki na aiki yadda ya kamata. Wannan ya haɗa da cin abinci mai gina jiki, motsa jiki akai-akai, da dai sauran su. Sai dai a wannan zamani...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, sun kashe ’yan fashi biyu, sannan sun kama wasu biyu a unguwar Makera da ke Kakuri. Wannan ya biyo bayan musayar wuta da jami’an tsaro suka da ’yan fashin. Gwamnan Nasarawa ya sanya wa gadar sama sunan Tinubu PDP ta mayar wa da na hannun damar Wike kujerarsa ta sakatarenta...
Yaya girman neman fadadar kungiyar NATO yake? Alkaluma ne za su iya fayyacewa: Abun da aka kashe a duniya kan aikin soji a shekarar 2024 ya kai dala triliyan 2.72, inda kungiyar NATO ta dauki dala triliyan 1.5, wato kaso 55 na jimillar ta duniya. Duk da rashin daidaiton karfin soji tsakanin kasashen duniya, NATO...
Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai wa motar ’yan sanda hari a Zariya, inda suka harbe ɗaya daga cikinsu har lahira, tare da raunata wasu uku. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:30 na daren ranar Talata, a unguwar Dalan Waje da ke kan hanyar Galadimawa, a Ƙaramar Hukumar Zariya da...
Da yake gabatar da kudirin, dan majalisar, Abdullahi ya nuna matukar damuwarsa kan kisan da aka yi wa matafiyan a ranar Juma’a, a lokacin da suka bata kan hanyarsu a yayin da suke tafiya don halartar wani daurin aure a karamar hukumar Mangu. Ya ce, wadanda aka kashen, ba su dauke da wani makami,...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Xi Jinping Zai Halarci Bikin Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Cimma Nasarar Yakin Kin Jinin Harin Sojojin Japan Da Yakin Kin Tafarkin Murdiya
Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya bayyana cewa, shugaban kasar Xi Jinping, zai halarci bikin tunawa da cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin kin jinin harin sojojin Japan, da yakin kin tafarkin murdiya, da safiyar ranar 3 ga watan Satumban bana, tare da gabatar da jawabi. Kazalika a ranar, kasar Sin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A zamanin yau, ba kira da tura saƙo kawai ake yi da wayar hannu ba; baya ga haka, muhimmiyar hanya ce ta samun kuɗi da bunƙasa sana’o’i. Ko kun san dabarun amfani da wayoyinku don samun kuɗaɗen shiga? NAJERIYA A YAU: Matakan daƙile kisan matafiya a hanyoyin Najeriya...
Ya ce: “Duk da cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da haƙƙin ofisoshin jakadanci na ƙasashen waje, ciki har da na Amurka, na fitar da gargaɗin tafiye-tafiye ga ‘yan ƙasar su, yana da muhimmanci a faɗa a fili cewa Abuja tana da tsaro ga ‘yan ƙasa da mazauna da kuma baƙi baki ɗaya.” Ya bayyana...