2025-07-09@20:24:16 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1404
«Yan Zariya»:
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu ya yaba da yadda tattaunawa da Amurka kan shirin Nukliyar kasar yana tafiya kamar yadda ta dace. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya nakalto Aragchi yana fadar haka bayan, bayan ya fito daga taron tattaunawa ta ukku wanda aka gudanar...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiyan ya bayyanawa firai ministocin kasashen Indiya da Pakistan a maganar da yayi da su ta wayar tarho a jiya Asabar, kan cewa mu hada kai gaba daya don yaki da ayyukan ta’addanci a yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Pezeshkiya yana fadawa shuwagabannin kasashen biyu, kan...
Kwanan nan, wakiliyar CMG ta zanta da shugaban kasar Azerbaijan Ilham Aliyev wanda ya kawo ziyarar aiki a kasar Sin. A yayin zantawar, shugaba Aliyev ya waiwayi dadadden tarihin cudanyar kasashen biyu da ma zumuncin da ke tsakaninsu, kuma ya yi imanin da cewa, kasancewar dukkansu kasashe masu tasowa ne, kasashen biyu za su hada...
Alkaluman zuba jari na kasashen waje sun hau kan mizani mai kyau a rubu’i na farko, a kan hakan kuwa, kasar Sin za ta kara bude kofarta domin maraba da jarin waje na duniya. Har ila yau ana sa ran karin kamfanonin waje za su zuba jari da gudanar da kasuwanci a wannan kasa mai...
Kwamishina CP Ibrahim Maikaba ya yaba da ƙoƙarin jami’ansa, yana kuma ƙara jaddada niyyar rundunar na yin aiki tare da al’umma domin samar da tsaro. Ya buƙaci mutane su riƙa bai wa rundunar sahihan bayanai a kan lokaci domin taimaka wa yaƙi da laifuka. Rundunar ta kuma fitar da lambobin da za a iya kira...
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da magance cin zarafin da Amurka ke yi ita kadai, ba wai kawai don kare hakki da moriyarta ba, har ma da kiyaye moriyar kasashen duniya. Ya bayyana hakan ne a jiya Jumma’a yayin ganawarsa da takwaransa na kasar...
Kazalika, ya ce, kasar Sin tana son kara zurfafa hadin gwiwa tare da IMF wato asusun ba da lamuni na duniya, da kuma ba shi goyon baya wajen taka muhimmiyar rawa a kan kiyaye tafiyar da tattalin arziki da hada-hadar kudin duniya cikin kwanciyar hankali. Bugu da kari, Pan ya jaddada bukatar gaggauta...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban rikon kwarya na kasar Siriya Ahmed Al-sharaa ya bayyana cewa gwamnatinsa a shirye take ta samar da hulda da HKI a dai-dai lokacinda ya dace. Jaridar Middle East Eye ta kasar Burtaniya ta nakalto Ahmed Sharaa yana fadar haka a wata wasikar da ya rubutawa shugaba Donal Trump Har’ila yau shugaba Al-sharaa ya fadawa...
Bayan ya sake daga sabowar tutar kasar Siriya a cibiyar MDD da ke birnin NewYork ministan harkokin wajen kasar Siriya Asaad Al-shaibani, ya gabatar da jawabi a gaban kwamitin tsaro na MDD a jiya jumma’a inda ya roki kwamitin ya dagewa kasarsa takunkuman tattalin arziki wadanda aka dorawa gwamnatin da ta shude. Jaridar Middle eart...

Dalilin Da Ya Sa Nijeriya Ke Ci Gaba Da Rike Kambun Kasa Na Mafi Yawan Samar Da Danyen Mai A Afirka — OPEC
A cewar kungiyar ta OPEC, wannan ya ya faru ne duk da raguwar yawan man da Nijeriya ta samar a watan da ya gabata, musamman idan aka kwatanta da ganga miliyan 1.46 a kowace rana a watan Fabrairun da ya gabata. Rahoton ya ci gaba da cewa, duk da raguwar, yawan Man da kasar...
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya gargaɗi sabbin masu yin hidimar ƙasa (NYSC) da aka tura zuwa jihar da su guji shiga ƙungiyoyin sirri, da ayyukan siyasa, da kuma nuna kiyayyar addini a duk tsawon lokacin hidimarsu. A cikin jawabin gwamnan, wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan jihar Abdulkadir Mamman Nasir, ya gabatar a...
Jiragen yakin HKi sun kai hare-hare da safiyar yau Asabar a birnin Gaza da hakan ya yi sanadiyyar samun shahidai da dama. Mutane 4 sun yi shahada a harin na jiragen ‘yan sahayoniyar akan wani gida dake unguwar “al-Sabrah’ a kudancin birnin Gaza. Haka nan kuma jiragen yakin na HKI sun kai wani harin da...
A watan Janairu kawai, marigayi shugaban ‘yan fashin daji, Isuhu Yellow, ya sanya harajin naira miliyan 172.7 a kauyuka 25, ciki har da bukatar amfanin gona. A misali, an kakaba wa kauyen Gijinzama harajin naira miliyan 8.5, Dakolo naira miliyan 5 da buhunan wake 20, da Kibari, Kunchin Kalgo naira miliyan 20, Sungawa naira...

A Karon Farko A Tarihi Adadin Lantarki Da Sin Ke Iya Samarwa Ta Karfin Iska Da Hasken Rana Ya Zarce Wanda Ake Iya Samarwa Ta Amfani Da Dumi
Sashen masana’antun samar da sabbin makamashi na kasar Sin ya samu ci gaba cikin sauri a shekarun baya bayan nan, a gabar da ake ta aiwatar da managartan matakai na bunkasa tattalin arziki ba tare da fitar da iskar Carbon mai dumama yanayi ba. Tun daga shekarar 2013, adadin kayayyakin samar da lantarki daga...
Shugaban Amurka ya bayyana cewa: Fira ministan Isra’ila Netanyahu ba zai ja shi zuwa shiga cikin yaki da Iran ba, kuma a shirye yake ya gana da Jagoran juyin juya halin Musulunci da shugaban kasar Iran Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya jaddada cewa: Ba za a sanya shi shiga yaki da Iran ba saboda...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran a shirye take ta inganta fahimtar juna tsakanin Indiya da Pakistan Ministan harkokin wajen Iran Sayyid Abbas Araqchi ya sanar a yau Juma’a cewa: kasarsa a shirye take ta yi aiki mai kyau a fagen sulhunta tsakanin Indiya da Pakistan don inganta fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu...
Bugu da kari, game da amincewar da gwamnatin shugaba Trump ta yi da aikin hako ma’adinan karkashin teku, Guo Jiakun ya ce ba wata kasa dake da ikon karya dokokin kasa da kasa a wannan fanni, ta yadda za ta iya keta dokokin bincike, da bunkasa ayyukan hako ma’adinan karkashin teku ba bisa ka’ida...
Kungiyar Shugabannin Arewa (NEF) ta zargi Shugaba Bola Tinubu da nadin mukaman gwamnati ba tare da daidaito tsakanin yankunan Nijeriya ba, wanda ta ce yana fifita yankin Kudu maso Yamma a kan sauran yankuna shida na kasar. Mai magana da yawun kungiyar, Farfesa Abubakar Jiddere, a cikin wata sanarwa a yau Juma’a a Abuja, ya...
A cikin sabban hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kai kan kasar Yemen a jiya Alhamis sun kai hare-hare kan larduna guda 4 . Tashar talabijin ta Presstva anan Tehran ta nakalto majiyar labarai daga kasar ta Yemen jiragen yakin Amurka suna kai hare-haren a kan kasar kusan ko wani rana. Amurka dai tace tana...
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana cewa duk waɗanda ke son barin jam’iyyar PDP su tafi yanzu, domin a bai wa masu kishin jam’iyyar damar sake gina ta. Saraki ya fitar da wannan bayanin ne a martani ga yawan sauye-sauyen jam’iyya da ake yi a PDP, ciki har da ficewar Gwamnan Jihar Delta,...
”Wannan lokaci ne na bakin ciki, kuma a cikin irin wadannan lokutan ne kuka san wadanda ke kulawa da ku da gaske.” Ribadu ya bayyana cewa Gwamnatin Bola Tinubu ta gaji tashin hankali da ke fama da shi a kasar nan, kuma tana aiki tukuru don gyara abubuwan da suka lalace. Ya ce,...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Zazzaɓin cizon sauro, wato maleriya, na cikin cututtuka mafiya shahara da kuma haɗari a Najeriya. Wani rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya nuna cewa Najeriya na da kaso mafi girma na mace-macen da cutar take haifarwa a duniya. Sau da yawa wanda ya kamu da cutar...
Sabbin ‘yan sama-jannatin da aka tura, za su gudanar da gwaje-gwaje da bincike game da yanayin rayuwa a sararin samaniya, da kimiyyar karamar fizgar kasa ko jazibiyya (micro-gravity physics) da sabbin fasahohin sararin samaniya. Kazalika, za su kuma yi tafiye-tafiye mabambanta a sararin samaniya don kakkafa shingayen kariya daga baraguzai da tarkacen sararin samaniya,...
Kafafen watsa labarun HKi sun amabci cewa daya daga cikin sojojinsu ya halaka a Gaza, yayin da wasu 7 su ka jikkata. Kafafen watsa labarun na HKI sun ce, Harin da aka kai wa sojojin ya kunshi harbi daga kwararren maharbi da kuma harba makamin dake fasa motoci masu sulke. An ga jiragen sojan mamaya...
A daidai lokacin da sabani yake yin tsanani a tsakanin India da Pakistan, bayan wani hari da aka kai a Kashmir da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 26, ministan tsaron kasar Pakistan Khajah Asif ya ce; matukar India ta keta hurumin kasarsa, to kuwa za ta fuskanci mayar da martani mai tsanani. Minista Khajah Asif...

Shugaba Xi Ya Jaddada Aniyar Kasarsa Ta Goyon Bayan Kudurorin Kyautata Yanayi Da Ci Gaba Marar Gurbata Muhalli
Ya ce, “Muddin muna da kwarin gwiwa, da karfin goyon bayan juna da hadin kai, za mu kai ga kawar da manufofi masu illa, da wanzar da daidaito da ci gaba a manufofin jagoranci a fannin kare yanayi da samar da ci gaba. ” (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
Ban da haka, yadda gwamnatin Trump ba ta da tabbas a kan manufofinta na haraji yana kuma ba kasashen duniya mamaki. Ba a jima ba da gwamnatin Amurka ta sanar da matakinta na harajin ramuwar gayya a kan kasashen da ke ciniki da ita, sai kuma ga shugaba Trump ya sanar da dage harajin a...

Kasar Iran Ta Bayyana Cewa Kakaba Takunkumi Kan Kasarta Ya Sabawa Hikimar Gudanar Da Zaman Tattaunawa Da Ita
Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ta bayyana cewa; Kakaba takunkumi kan kasarta ya sabawa ikirarin Amurka na yin shawarwari da ita Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan matakin da Amurka ta dauka na kakabawa wasu gungun mutane masu alaka da bangaren makamashi, man fetur da iskar gas da kuma...

Gwamnatin Siriya Tana Daukan Matakan Matsin Lamba Kan Gwagwarmaya Domin Samun Yardan ‘Yan Sahayoniyya
Sabuwar gwamnatin Siriya tana kara matsa lamba kan bangarorin ‘yan gwagwarmaya domin Isra’ila ta janye daga wasu yankunan kasarta Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da tura kayayyakin soji zuwa tsaunukan Dutsen Harmon, yayin da suke hanzarta gina abin da suka kira “Katangar tsaro.” Har ila yau, sun karfafa wuraren tsaro da suka kafa a...
“Ka koma gefe – ba wai kabar wa abokan hamayyarka takara ba, amma don sabbin jini matasa ‘yan Nijeriya da za su iya ciyar da al’umma gaba da sabbin kuzari da tunani.” in ji shi. Ya kara da cewa, ya kamata shugaban kasa ya yi tunani a kan nagartattun abubuwan da yake son bari...
Babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya ba da umarnin ga rundunar sojin Najeriya da ta fatattaki ‘yan bindigar da ke addabar al’ummar kananan hukumomin Baruten da Kaiama na jihar kwara da Borgu da ke dajin Kainji a jihar Neja cikin wata guda. A jawabin da ya yi wa dakarun rundunar soji...
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ba da umarnin gaggawa da a yi cikakken sauyi ga dabarun tsaron ƙasa, yana mai umartar shugabannin tsaro su ɗauki matakan gaggawa don daƙile ƙaruwar tashin hankali da kashe-kashe jihohin Borno, Filato, Binuwai, da Kwara. Tinubu, wanda ya gana da shugabannin tsaro a Fadar Shugaban Ƙasa, ya ce dole ne...
Sanarwar ta kara da cewa, Shugaban tawagar ‘yan fashin, Baba-Beru ya samu munanan raunuka, wanda daga baya ya rasu a Asibiti. “An garzaya da dukkan wadanda suka samu raunuka zuwa Asibitin kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano, inda Baba-beru ya rasu a lokacin da ake jinyarsa, amma jami’an ‘yansanda an sallame su bayan...
Jami’in ya kara da cewa, kasar Sin ba ta son gwabza yakin kasuwanci da karin harajin kwastam, amma kuma ba za ta rungume hannu ta zuba ido ba idan yakin ya kaure, yana mai nuni da cewa, idan har Amurka ta zabi fafata yakin kasuwanci, Sin za ta sha damarar yakin har sai ta ga...

Gwamna Inuwa Ya Bayar Da Gudunmawar Naira Miliyan 10 Ga Iyalan Wadanda Hatsarin Ista Ya Rutsa Da Su A Gombe
Da yake jawabi a fadar Mai Tangele (Sarkin Billiri), Danladi Sanusi Maiyamba, ya bayyana lamarin da matukar bakin ciki tare da fatan samun makoma mai kyau ga wadanda suka rasu, ya kuma warkar da wadanda suka samu raunuka da gaggawa. Daga nan sai Gwamna Inuwa ya sanar da bayar da gudummawar Naira miliyan 2...
A yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, yake-yaken karin haraji da kasuwanci ba su haifar da komai illa tauye halastattun hakkoki da muradun dukkan kasashe, tare da kawo cikas ga tsarin ciniki tsakanin bangarori daban-daban, da kuma yin tasiri mara kyau ga tsarin tattalin arzikin duniya. Yayin ganawarsa da...
Kungiyar da take wakiltar Iran a wasannin Taekwondo na duniya a kasar Sin, ta sami lambobin yabo 8 a ranar farko da bude gasar ta kasa da kasa. An fara wasannin na Tikondu a garin Tayan dake kasar China wanda shi ne karo na 7 da kuma ‘yan wasa 491 daga duniya suke gasa. Daga...
Ba wannan ne karon farko da ake zargin wasu ‘yan ƙasashen waje da kai hare-hare a Nijeriya ba. A baya an yi zargin cewa ƙungiyoyi kamar Lakurawa da ke kai hare-hare a jihohin Sakkwato da Zamfara, sun samo asali ne daga ƙasashen waje. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
Garuruwan da aka fi tsananta wa harajin sun haɗa da Gijinzama da aka tilasta musu biyan Naira miliyan 8.5, Dakolo da aka karɓi Naira miliyan 5 da buhun wake 20, sai Kibari da Kunchin Kalgo da suka biya Naira miliyan 20, Sungawa da Naira miliyan 15, da kuma Yalwa da aka tilasta su biyan Naira...

Rohoton Kwamitin Kare Hakkin Dan Adam Ya Tabbatar Da Tafka Manyan Laifukan Cin Zarafin Bil-Adama A Siriya
Wani rahoton kare hakkin bil adama ya tabbatar da aikata manyan laifuka a gabar tekun Siriya tare da yin kira da a kare fararen hula Kwamitin da ke bin diddigin kare hakkin bil adama a kasar Siriya karkashin jagorancin dan gwagwarmaya Haitham Al-Manna, ya fitar da wani cikakken rahoton take hakkin dan Adam mai shafuka...
‘Yan majalisar dokokin Aljeriya, sun yi kira da a haramta daidaita alaka da Isra’ila. ‘Yan majalisar dokokin Aljeriya da wakilan jama’a na kasar a zaman majalisar dokokin kasar, sun yi Allah wadai da laifukan da Isra’ila ke aikatawa akan al’ummar Gaza, tare da nuna cikakken goyan bayansu ga falasdinawa. Mahalarta taron sun yi kira ga...
A hukuncin da ta yanke, Mai Shari’ar ta ce, “Shaidun da masu gabatar da kara suka gabatar na da inganci kuma masu gamsarwa ne, don haka kotun ta samu wanda ake tuhuma da laifi kuma ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.” A cewar mai gabatar da kara a karkashin jagorancin Lamido Abba-Sorondinki,...
A yayin ziyarar, mataimakin shugaban kamfanin LEADERSHIP Mike Okpere, ya bayyanawa uwargidan shugaban kasa irin ayyukan agaji da Kamfanin LEADERSHIP ke gudanarwa tare da yin fatan hada hannu da shirin tallafin fata na gari ‘Renewed Hope Initiative (RHI)’ da nufin karfafawa mutane 1,000 da ayyukan yi. A cewar Okpere, shirin zai mayar da hankali...
Iyalan Alhaji Surajo Ilyasu Malumfashi (RADIO NIGERIA KADUNA) dana Alhaji Idris Ahmed Accama na farin cikin sanar da bikin aure na ‘ya’yansu, Muhammad Auwal Idris da Zainab Surajo Malumfashi. Za’a gudanar da bikin auren ranar Asabar, 3 ga Mayu, 2025, a Masallacin Juma’a na Dan Fodio, Dake Anguwan Sunusi, Jihar Kaduna. Za a daura...
Sai dai a hakika, ba dole ne kasar Lesotho, da sauran kasashen Afirka su mika wuya ga kasar Amurka, don ta ci zalinsu yadda ta ga dama ba. Kamar yadda Charles Olunaiju, wani masanin kasar Najeriya, ya rubuta a cikin wata makalarsa da jaridar Vanguard ta wallafa, kasar Amurka ba za ta samu biyan bukata...
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: A shirye suke su cimma yarjejeniya yayin da suke kiyaye muradun kasarsu Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran a shirye take ta cimma matsaya bisa kayyade tsare-tsare tare da kiyaye moriyar kasarta, amma idan ba ta son yin shawarwari da ta daga kan matsayinta, tare da...
A daren yau ne shugaba Bola Tinubu ya dawo Abuja bayan kammala ziyarar aiki ta makonni uku a Turai, inda ya gudanar da muhawara da manyan jami’an ƙasa da ƙasa don inganta dangantakar Najeriya a fannin tsaro da ci gaban tattalin arziki. Jirgin shugaban ya sauka ne a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe...
A yau Litinin shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya fitar da sanarwa ta nuna aljinin rasuwar Papa Roma Farancis,sannan kuma ya mika sakon ta’aziyya ga Mabiya darikar Roman Katolika na duniya. Shugaban kasar ta Iran ya rubuta cewa; Daga cikin matsaya da ta kasance fitacciya wacce Papa Roman ya dauka a lokacin rayuwarsa ita ce...